← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 84

Sashe 62

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amina ta É—an buÉ—e baki ta ce "Au Wai dagaske Habujar zaki?"

Amina ta ce "Ai ban sani ba, sun ce zasu kira shi a waya ne su sanar masa, ina ga shi yasa ya ce in kai masa shayin, bari in je" Amina ta miƙe ta zura dogon hijjabi, a kan kayan da ke jikinta na bacci.

Hajara tabi bayanta da kallo ta ce "Lallai yarinya, ni zaki rainawa hankali, zan zuba ido dai in ta bibiya"

Amina ta É—au kayan tea É—in, ta tafi falon Daddy, tana fatan Allah yasa idon Hajiya Zainab biyu, kuma ya sanya tana É—akin, yadda tana ajiye masa tea É—in zata dawo ta cigaba da sabgarta, dan bata son wani abu ya sake haÉ—ata da Daddy.

Da sallama ta shiga falon, yana sanye da jallabiyya fara ƙal, hannunsa riƙe da remote. Ya amsa mata ba tare da ya waiwayo ya kalleta ba.
Ta zo gabansa ta ajiye tea É—in a kan center table. Ta juya zata tafi ta tsinkayi muryarsa yana faÉ—in "Sai yanzu kika ga damar zuwa?"
Tsayawa tayi cak tana kallonsa, tayi masa shiru tana kallon gefe guda.

"Zo nan" ya faÉ—a cikin command.

Ta juyo ta dawo ta tsaya a gabansa tana kallon ƙasa.

"Zaki saka kaina yayi ciwo, kin tsaya mini a ka kamar sa'anki"

Ta nemi wuri a ƙasa ta zauna, tana cukuikuye hannunta a hijjabinta, kamar mara gaskiya.

Ya É—an kalleta ya kallia shayin ya ce "HaÉ—a mini tea"

Ba musu ta matsa gaban teburin, ta fara haɗa tea, tana tunanin ina Hajiya Zainab take, a irin wannan lokacin da har Daddy ke samun damar keɓewa da ita? Zancen zucin da take, ya bata damar antaya sugar da yawa a cikin shayin.

Sai da ta gama haÉ—a tea É—in nan, sannan ya kalleta ya ce "Amma bani kika haÉ—awa ba ko?" Yayi Maganar yana tsareta da ido. Ta É—ago da sauri ta kalleshi.

Ya ce "Eh mana, wannan kan ki kika haɗawa, wannan sukarin da kika zuba, idan na sha ai sai in rasa raina, kodayake dama haka kike so ko? Oya  Sake haɗa mini wani ki shanye wannan da kika cika sugan"

A raunane ta ce "Ni na ƙoshi"

"Ai kuwa sai kin sha, haÉ—a mini wani"

Haka ta sake haÉ—a masa wani, ba tare da ta zuba sugar sosai ba, ta ajiye masa.

Ta tsaya jiran ya bata umarnin tafiya.

"Ki É—auki shayin nan ki shanye na ce"

"Wallahi na ƙoshi" tayi maganar kamar za tayi kuka.

"Sai fa kin sha" Amina tayi shiru tana mamakin wannan takura haka.

Ya cigaba da shan shayinsa, kamar ya manta da ita a wurin, can har ta fidda ran zai magana ya ce "Meyasa na bada abu a baki, dan kin raina ni kika dawo mini da shi ko? Kuma kika daina gaisheni, gani ga ki idan muka haɗu, sai kiyi fuska ki ƙi gaisheni, meye dalili?"

Tuni ƙwalla ta taru a idon Amina, ta ce "Bakomai"

"Akwai ko mai, sai kin gayamini dalili, ko mu kwana a nan tare"

ÆŠan waro idanunta tayi, amma ba ta iya cewa komai ba.

"Wallahi idan na rufe ƙofar falon nan da mukulli, sai kin kwana a falon nan, kuma kin San halin Zainab ni ba ƙwatar ki zan yi ba a wurinta"

Cikin marairaicwa Amina ta ce "Dan Allah kayi haƙuri, wallahi ban rainaka ba Daddy"

"To menene idan ba raini ba" ya faɗa yana zuƙar tea hankalinsa kwance.

"Ba kai ne ba" sai kuma tayi shiru, saboda kukan da ya ƙwace mata.

Daddy ya ce "Ikon Allah, to gama kukan sai ki mini bayani, kafin ki gama ma na gama shan shayin nawa"

Aikuwa Amina ta gyara zama, ta dinga kuka, sai da tayi mai isarta ba tare da Daddy ya ce tayi shiru ba, tana yi ta goge hawaye da hijjabinta.

Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Kinga ga tissue nan, ki dinga goge hawayen da majinar da ke ƙoƙarin zubowa, kar ki mini ƙazanta ina cin Abinci" aikuwa sai ta ƙaro sautin kukan nata, jin ya jefeta da kalmar ƙazanta.

Ya ce "Cigaba da É—aga murya, Allah yasa ta jiyo ki, ta zo ta tarar da ke kin saka mijinta a gaba kina kallonsa"
Ba shiri Amina ta fara ƙoƙarin haɗiye kukan nata. Shi kuma ya dinga murmushin gefe ɗaya, yadda ba zata gani ba.

Sai da ta gama kukan, sannan ya ce "Masha Allah, in kin gama ina jinki"

"Ba kaine Kai mini gori ba, shi yasa na dawo maka da wayar ka"

Dariya yayi ya ce "Subhanallah, Ohh ni Ahmad, to mai yasa kika daina gaishe ni"

"Daina amsawa kayi, idan na gaisheka sai ka harareni"

Sosai Alhaji Ahmad yayi dariya da jin abin da Aminar ta faɗa cike da wauta da ƙuruciya.

"Ni Ahmad naga ta kaina, na yi miki gori nace me?"

"Cewa kayi gidanka ba wurin tara maza bane, kuma ni Bakomai tsakanina da shi, ranar da ka ajiyeni a hanya ne, ya kawoni gida sai gaisawa da muke da shi shikenan"

"Saboda na ce Kar ki sake kawo wani gidan nan shine kike jin haushina? Amina na fiki shekaru, hankali da kuma gwagwarmayar rayuwa, muddin kika haɗa karatunki da shirmen samarin zamanin nan, to ba zaki mayar da hankali ba, idan ki ka biyewa samarin zamani da soyayya karatunma sai ya gagareki, soyayya ba abin da ba ta sakawa. kuma ni idan kin gaisheni ba hararki nake ba, bana amsawa ne saboda ki fahimci kin mini laifi, ki bani haƙuri amma ki kayi mirsisi ashe ke nan fushi kike dani ne ko? Wace irin 'ya ce haka mai fushi da babanta har ta daina kula shi, ya bata abu ta mayar masa anya kuwa kina Baban da ni?"
Amina tayi shiru ta sunkuyar da kai.

"Shikenan, ni bari in sauko in baki haƙuri"

Da sauri ta ce "A'a kayi haƙuri dan Allah kar ka bani haƙuri"

"To tunda fushi kike, har da cewa na miki gori gara in bada haƙuri ai"

"Kayi haƙuri dan Allah, bana fushi da kai"

"To sai kuma me nayi miki?"

"Kace mini ƙazama" ta faɗa har cikin ranta.

"Yaushe kuma na ce miki ƙazama?"

"Yanzu" ta faÉ—a tana tura baki.

"Eh ai ƙazamar ce, kalli yadda kika ɓata hijjabinki da hawaye, kuma haka kike mana girki, kina mana ƙazanta, shi yasa Abincin yake daɗi ashe".

"Mhmm ka daina ce mini ƙazama"

"To ki daina goge hawaye da hijjabinki"

Ya É—an tsura mata ido, sannan ya ce "Jeki janyo drower can, wayarki na ciki, ki É—auko ki haÉ—o mini da abin gwajin suga na" tamkar wata kurma haka ta tashi, taje ta É—auko abin da ya sakata, ta dawo ta zauna, ya sauko daga kan kujerar ya zauna a kusa da ita, hakan ya sa ta sake takurewa.
Ya fito da kayan gwajin, ya yi gwajin sugan nasa, ya kalleta ya ce "Kin gani sakamakon daina kula dani, suga na ya hau duk abin da kika ga dama, dafawa kike ki bani, suga na ya hau ya kai sha biyu da É—igo uku"

Ita dai ba tace masa komai ba, sai sunkuyar da kai, kamar mara gaskiya.

A ranta ta ce 'Hakkin azababbiyar matarka ne ai bani ba, abin da aka ce in dafa ai shi zan dafa'

Ya miƙa mata wayar ya ce "gata nan, lokaci lokaci, zan dinga karɓa ina dubawa"

Ta Sanya hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode Allah ya saka da alkhairi, naga takalmi da jaka ma, Baba ya bani Allah ya ƙara buɗi"

"Amin rigimammiya, mutanen nan ma da kika mini Maganana akan su an biya musu kuÉ—in shekara biyu, na bawa Maigidan fili ya gina kamar yadda kika nema"

A gigice Amina ta kalleshi ta rasa me zata ce masa sai ta sake fashe masa da kuka.

"Ke wai komai ma kuka kike masa, tashi ki tafi Allah ya bamu alheri"

"Allah ya biyaka da Aljanna Daddy"

Yayi murmushi ya ce 'Ameen, tare da ke da kika ankarar da ni nayi aikin alkhairi. To Yanzu mu shirya ko?" Yayi Maganar ƙasa-ƙasa.

Ta É—aga masa kai alamar eh.

"Bana son É—aga kai, amsa mini zaki"

"Eh mun shirya" ta faÉ—a cikin jin kunyar abin da tayi.

"To shikenan, tashi muje in rakaki bakin ƙofa" ta miƙe tsaye hannunta riƙe da kwalin wayarta.

"Kun koma makaranta yau ko?"

Tace "Eh Daddy. kayi magana da Baban kuwa a kan tafiyar?"

"Kar ki damu, zamu yi maganar in sha Allah, ke dai ki cigaba da karatu"

"Ina nan ina yi, ka dinga yi mini addu'a"

"Sai kin biya tukuna, kawo abin sadaka, ai miki Adduar" dariya Amina tayi ta ce "Zan kawo, idan kai mini addu'ar na ci"

"To shikenan, kije ki duba wayar, abin da baki gane a ciki ba, sai ki mini magana"

"To Daddy na gode" ta juya ta fice, Daddy ya tsaya yana binta da kallo, harta ɓacewa ganinsa, sannan ya koma ciki, yana shafa gemunsa.

Hajar kuwa tun da Amina ta tafi wurin Daddy take yi tana leƙa falo zuwa kitchen, dan taga dawowar Amina, amma shiru babu Amina babu dalilinta, ji take tamkar ta zama tururuwa ta rarrafa taje ɗakin Alhaji Ahmad, ta gano meke faruwa Amina ta zauna haka? Tun tana zuba ido taga dawowar Amina har ta gaji, ta tafi ɗakinta ta zauna tayi shiru tana tunani, tashi ta kuma yi ta leƙa ɗakin Amina, ta tarar da ita a tsakiyar katfarta tana kunna sabuwar waya.

"Amina ashe kin dawo, naga kin daÉ—e daga kai shayi, ki kayi wannan zaman?"

"Kai Hajara, ban gane me kike nufi ba, da na kai masa shayin fa suna tare da Hajiya, na ajiye musu na tafi baranda na cigaba da karatuna, me zai zaunar da ni kuma?"

Sai kuma cikin borin kunya Hajara ta ce "Au, na zata wani laifin ki kayi ai, duk hankalina ya tashi, wannan sabuwar wayar fa" Amina ji tayi kamar ta zagi Hajara, amma idan ba ta bi Hajara a sannu ba, zata sanya kwaɓarta tayi ruwa, dan haka ta ce "A makaranta ne aka bamu, saboda mu dinga amfani da ita wurin karatu"
Chapter 62 · 0% Book details