← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 84

Sashe 55

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalil miƙewa ya yi, ya bar Falon saboda an fara kiran sallar magariba, yaje masallaci ya dawo, ya shirya cikin wasu haɗaɗɗun ƙananan kaya, ya feshe jikinsa da turare, ya ɗauki kayan siyayyar da ya yiwa Hafsa, ya ɗau motarsa ya fice.
Ta wurin da take zaman suya ya fara bi, yaje ya tarar da ita tana ta fama da hayaƙi, ga masu siya sun zagayeta.

"Ke ungo nan bani ta naira ɗari ki riƙe canjin" yayi magana yana bata dubu ɗaya, sam bata san Khalil ya zo wurin ba sai muryarsa da ta ji.

Murmushi tayi tana kallonsa sanann ta ce "Gaskiya ni wannan zuwan be mini ba, kai kayi kwalliya ni kalleni cikin hayaƙi, kuma baka gaya mini zaka zo ba ba zan kula ka ba gaskiya"

Dariya yayi ya tsuguna a kusa da ita "Ni ko a yaya na ganki ƙara kyau kike yi, kawo abun fifitar in fifita miki, sallami waɗan nan"

"A'a ka bari kawai, kar kayi ƙaurin hayaƙi"

Karɓe abun fifitar yayi, yana ffifita mata wuta, ita kuma tana sallamar masu saya. Suna yi suna hira cike da nishaɗi da jin daɗi. Khalil ya saka ta raba sauran sadaka, ya ce ya saya, ba dan ta so ba Khalil ya tayata suka kwashe kayan, ya rufe motarsa suka hau ɗan sahu tare suka tafi gidansu Hafsa, tare da ledar da yayi mata.

Ya zauna a ƙofar gida, ya jirata ta shiga gida tayi kwalliya sama-sama ta fito. Sosai suke hira da Khalil, yana bata labarin wurin aiki.

Can ya nisa ya ce "Babyna yaushe zan turo su Daddy ne? Na gaji da zaman Abuja ba mata"

"To ni me zance?"

"Ban gane me zaki ce ba? Zan sanarwa da Daddy insha Allah zuwa next months zan turo, ginina saura kaÉ—an, shiyasa zan bari sai na kammala sai in turo" É—an shiru tayi, sannan tayi ajiyar zuciya.

"Ya kika yi shiru, ko ba kya sona?".

Murmushi tayi ta ce "Ina sonka Sosai, in ba kai ba sai maliya" tayi maganar cikin dariya.

"Wayyo daÉ—i, dagaske Hafsa?"

"Da gaske nake mana"

"Kar ki saka in tattaro mutane a É—aura mana aure yanzu"

Hafsa ta ce "Sai kace auren sadaka"

"Ai sai yafi albaraka, yakamata mu fara shirin biki ma"

"Ka san wani abu, yanzu kaje gida ka huta, kaga yau ka dawo"

"A taƙaice dai korata kike yi?"

"Ya za ayi in koreka, ni kaina ban gaji da ganinka ba, kaga motarka tana can, ga sanyi ko so kake kayi mura? Kaje gida ka huta kaji nawan"

"Yau ɗin nan jina nake wani na musamman, tattali da kulawa ta zahiri daga abar ƙaunata"

"Ni kaina mamakin kaina nake yi, ka kawo sauyi da farinciki a rayuwata, na gode Allah da ya sa baka yi zuciya ka rabu dani ba"

"Baby Hafsat, duk wanda yaji halin da kika shiga, dole zai tausaya miki, Hafsa ina sonki, zan ɓoye sirrinki zan miki adalci in sha Allah in kula da ke, dan Allah ki aureni kar ki canza ra'ayinki a kaina"

"Zuciyata na gazgata duk kan kalaman da kayi mini, kuma ina sa ran ba zaka bani kunya ba, ina sonka Mu'azzam"

"Kar ki sa in suma dan daÉ—i mana" tashi tsaye tayi tana dariya, "muje in raka ka titi"

"A'a gari da sanyi, koma gida ki huta, idan naje gida zamu yi waya"

"Allah ya kai mini kai gida lafiya"

"Naga idan ban yi da gaske ba, yau a a soron Mama zan kwana" ya bata ledar siyayarta ya tafi.

Jinsa yake kamar wani sabon ango, cike da nishaÉ—i da jin daÉ—i ya nufi gida.

Kai tsaye cikin gida ya nufa, domin ya ci Abincin dare.

Sai dai yana shiga falon ya tarar da Mummy a tsaye tana huci, tamkar wuta.

"Mummy lafiya kuwa?" Ya faÉ—a yana binta da kallo.

"Ban sani ba, daga gidan uban wa kake?"

Khalil ya ce "Mummy ban gane....

"Nace daga gidan uban wa kake?"

"Wurin Abdul"

"Sai naci........... Kai da Abdul É—in, ni zaka tozarta Khalil? Saboda tsiya da abin kunya? Uban me kake a gaban kaskon mai awara?"

Ƙuuuuuuu cikinsa ya bada wani irin sauti gumi ya shiga tsatstsafowa daga goshinsa.

Cikin dakiya ya ce "Mai awara kuma?"

A hasale ta ce "A'a Ubanka"

Ayshercool
08081012143.
GABA DA GABANTA

            BY

AISHA ADAM (AYSHERCOOL/JAKADIYAR AREWA)

Page 30-31

*Zuwa ga masau sanya mini litattafaina a shafukansu ba da izini na ba, na barku da Allah, Allah ya saka mini, ina wahala kuna ci da gumina*

*Albishirinku masoya, littafin Dare da duhu, da ya samu kyakkyawan rubutu daga gamayyar marubuta uku, AYSHERCOOL, ZEE KUMURYA DA KUMA NIMCYLUV Ya kammala a document, ga mai buƙata ya tuntuɓi wannan lambar dan mallakar naku a kan kuɗi ₦500 kacal*

Cike da matsanancin tashin hankali, Khalil ya ce "Dan Allah Mumy waye ya gaya miki?"

"Au tuhumata ma kake yi? To ubanka ne ya gaya mini"

"Mummy walla..

"Zan taka ka ka mini rantsuwa, mutumin banza da na wofi sakarai, dama ina ankare da take taken ka, na zuba maka idanu in ga in da ka saka gaba, Hajiya Salma da Turai sun je duba shago, suka ganoka a gaban kaskon awara, suna kallonka kuka hau napep, saboda kalen tsiya kuka tafi, har wurin suka je suka tambayar mini, aka ce kana zuwa wurinta wai sonta kake, wallahi Khalil ka bani kunya, kamar bani na haifeka, ko ka manta matsayin ubanka a ƙasar nan? Babu 'yar wanda zaka kalla a manyan attajiran ƙasar nan a hanaka, amma saboda lalacewa da rashin sanin darajar kai, saboda tsiya, bama 'yar masu abinci a restaurant ba, mai soya awara a titi, ashe ita ce gayyara tsiyar da kazo da ita nan kana ci ran nan ko, an maka barbaɗe a ciki ka ci, idan takensu sammako ni a tafe na kwana, ni Zainab ban durƙusa na haifi ɗan da zai kawo mini jinin matsiyat ba, daga kai har ita zan yi maganinku, zan tsananta bincike a kan yarinyar".

Kamar Khalil zai É—ora hannu a ka cikin mariraicewa ya ce "Mummy, dan girman Allah kar ki yiwa Hafsa komai, ba ta da laifi ni na kai kana nace ina so"

"Zaka rufen baki ko saina falla maka mari, sakarai sususu, dalla ɓace daga gabana ka bar mini falo, zan ga uban da ya tsaya mata har ta liƙe maka"

"Dan Allah Mummy ni ki hukunta ni, marainiya ce fa"

"Khalil ni nake faɗa kana faɗa? Zan kwarara maka ashar fita ka bar mini falo" ta ƙarasa maganar a fusace tana nuna masa hanyar fita. A sanyaye Khalil ya fice, yana jin yadda wani abu ya tokare masa ƙirji saboda tsananin damuwa da ɓacin rai.

Amina ta sha jinin jikinta, ta tsorata da irin ƙyamar da take yiwa talaka, ta rasa me talaka yayi mata tayi masa wannan tsanar haka, ɗanta na cikinta ta saka a gaba, ta ƙare masa cin mutunci saboda ya nuna yana son 'yar talaka, ƙiyyyar ta wuce misali.
Fadila kuwa tana tare da Mummy aka kirata a waya aka sanar mata da anga Khalil, tare da mai awara, dan haka bata ji tausayin abin da Mummy ta yiwa Khalil ba musamman idan ta tuna yadda ya watsa mata ƙasa a ido, a kan soyayyar da Yusra take nuna masa.

Khalil kuwa wani irin gumi ne ya dinga tsatsatfo masa, saboda azanar tashin hankali, dama ya san a rina, amma yaso ace shi da kansa ya lallaɓata ya sanar da ita, amma wannan algunguman matan suka ɓata masa komai. A gaskiya yana son Hafsa, sai dai ya san babu yadda za ayi ya samu goyon bayan Daddy, muddin ba Mummy ce ta amince ba.
Ya tashi zaune yayi shiru, yana cigaba da tunani, wannan shi ake kira da ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa, ya gama gwagwarmayar samo soyayyar Hafsa da ƙyar, a lokacin da ya ke ƙoƙarin ya miƙa hannu ya kamota kuma, Mummy na ƙoƙarin shiga tsakani.

Hafsa kuwa cike da murna ta dinga bubbuÉ—a kayan da Khalil ya saya mata, turaruka da kayan kwalliya, sai kuma kwalin sabuwar waya mai tsadar gaske.
Ta dinga murna tana jujjuya wayar nan, tana yiwa Allah godiya ashe ita ma zata yi ta'amalli da kayan zamanin nan.

Vibrating ɗin wayarsa ce ya dawo shi daga tunanin da yake yi, ya kai idanunsa kan screen ɗin wayar yaga beauty. Ji yayi kamar kar ya ɗaga, amma ya miƙa hannu ya ɗauka cikin dakiya ya ce "Baby"

"Sweetheart, na gode sosai da sosai, Allah ya saka maka da alkhairi, waya na gani sabuwa dal har da layuka guda biyu, Allah ya ƙara maka lafiyar neman halal, Allah yaja kwanan mahaifanka, ya biya musu buƙatunsu na alkhairi ya kare su a duka in da suke, yadda kake faranta mini, Allah yasa ka shiga aljanna kafaɗa da kafaɗa da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam kamar yadda ya alƙwaratawa masu kula da maraya"
Gaba ɗaya jikin Khalil yayi sanyi, idan Allah ya karɓi Addu'ar Hafsa, yasan ya gama dacewa a duniya da lahira, macen da tun kan ya aureta komai ƙanƙantar kyauta ta dinga kwarara masa addu'a kenan, ina ga idan ya aureta, Hafsa bata taɓa roƙarsa komai ba, kai hasali ma ita kanta tana ƙoƙarin ganin ta bashi kyautuka, duk da arzikin da yake da shi, lokaci lokaci, sai ta saka masa katin ɗari biyar wai ga rabonsa nan, yau tayi ciniki sosai.
Wani irin ƙaunarta ya ƙara dabaibaye zuciyarsa, a hankali ya ce "Tare da ke Babyna"

"Ya naji muryarka kamar baka walwala, lafiya kuwa?"

"Lafiya ƙalau, bacci kawai nake ji"

"Ok, to bari in barka sai da safe, ka kwanta"

Yayi saurin cewa'No, ki yi mini hira mana, raina ne babu daÉ—i"

Cikin damuwa ta ce "Subhanallah, ko na ɓata maka rai ne kan ka tafi?"

"Haba, ni da kika faranta mini mana, ba abin da kika yi mini"

"To Alhamdilillah, Allah ya yaye maka damuwarka, ka san shi ɗan Adam dama ba a ƙyaleshi haka, sai dai ka kasance mai yawan godiya ga Allah, da kuma ambatonsa a halin daɗi ko akasin haka"
Chapter 55 · 0% Book details