← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 84

Sashe 33

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Su Khalil basu tarar da DPO division É—in ba, sai yaransa, bayan sun gaisa Aminu ya sanar da su cewar sune wanda suka zo wurin Hafsa.
ÆŠansandan ha kallesu ya ce "To mintuna uku kacal zaku yi, dan kotu zamu kaita".
"Wai a kan ta aikata wane laifin?" Khalil ya yi maganar a hargitse.
Abdul yayi saurin dakatar da Khalil ya ce "To Yallaɓai, a bari mu gantan".
Aka fito da Hafsa, idanunta jawur, tana rarraba ido taga Mama, kawai taga Khalil da Abdul, aikuwa tayi sak tana kallonsu, ta ƙaraso gaban teburin ta tsaya tana sunkuyar da kai.
"Hafsat, me kika yi aka kawo ki nan?" Khalil ya yi maganar yana kallonta cikin kulawa.
Fashewa da kuka Hafsat tayi, ta kasa magana.

"Ai na zata faɗa ba, tayi attempting illata mutum, kina mace amma kina abin 'yan daba, ta ƙonawa mutum ƙafa da mai, kuma ta rarumo makami tana nema ta sokawa mutum" cewar wani ɗan sanda mai jajayen idanuwa.

Tsaki Khalil yayi, ya ce "Wanan dalilin ne ya sanya aka kawota nan, wace irin magana ce wannan? Ta yaya zata É—au makami tace zata illata wani, Yarinyar da ko kuzarin kirki ba ta da shi?"

"Kaga shi mugu fa ba a ido ake ganinsa ba, wanda ya kawo ƙararta ya ce bai yadda da sulhu ba, a kai su kotu a bi masa hakkinsa"

Khalil ya ce "Shi dabban ina ne da zai kai mace kotu ya tsaya a kotu ya ce wai ta ɗau makami zata masa illa? Wace doka ce ma ta bada damar a riƙe mutum tsawon wannan lokaci family ɗinsa ma ba su sani ba, a bani belin ta".

DPO ne ya shigo yana zazzare ido "Yaya, Yaya, meke faruwa nake jin hayaniya haka?"

"Welcome sir, wannan ne ya zo zai mana tsageranci, wai sai an bashi belin wannan 'yar dabar".

"Wallahi ka kuma ce mata 'yar daba, saina ɓata maka rai".

"Kai nutsu, nan station ne, kar kai mana fitsara" Cewar DPO yana zarewa Khalil ido.

Abdul ya ce "Dan Allah Khalil abi komai a sannu".

Khalil ya ce "Wallahi ba zan bi a sannu ba, ya za'a kama yarinya ba bisa ƙa'ida ba, kuma aci zarafinta, sun ajiyeta daga ita sai su a wuri ko danginta basu san in da take ba?"

DPO ya ce "Au rashin kunya zaka mini, kai ku mayar da ita ceil, ba za a bada belin nata ba, sai ta É—au nauyin maganin wanda ta illata".

Khalil ya ce "Bari in ɓullo muku in da ya dace" kawai ya fita daga cikin station ɗin, kuka Hafsa ta saka, da taga Khalil ya juya ya fita. Abdul ya bi bayansa da sauri.

Mintuna bakwai, DPO ya fito a gigice yana faɗin "Suna ina? Wannan wane irin ɗan tijara ne, maimakon ya tsaya a sasanta sai ya kunno mini wuta daga saman ƙololuwa? Ku kira mini shi mana".
Khalil ne ya shigo ya ce "To zaku bani ita ko kuwa?".
"Za a baka, ai ban sai kai waye ba, ashe É—an gidan controller Ahmad Dutse ne".

Khalil Ya ce "Wannan matsalarku ce, a bani ita kawai".

DPO ya ce "Ai irin haka bayani ake yi, ba bankaɗo mini wita daga sama ba, wadda zata ƙone 'yar kukeear tawa ba, a fito da ita".
Aka fito da Hafsa, DPO ya ce "Amma zaku dawo gobe in Allah ya kaimu, za'a kashe case ɗin da wanda ya shigar da ƙarar".
Aka bawa Khalil wata takarda ya yi rubuce-rubuce, Sannan aka bawa Hafsa damar bin Khalil.

Suna fitowa harabar wurin Khalil ya ce "Babyna ba suyi miki komai ba dai ko?".
Ta jinjinawa Khalil kai. "Ki gaya mini ko sun miki wani abun?"
Ta kuma girgiza masa kai. "To Allah, maza muje mota, Mama na can gida bata san in da ki ke ba".
Ba musu ta bi Khalil, ya buÉ—e mata bayan motar ta shiga, Khalil ya shiga É—aya gefen ya zauna, Abdul kuma ya ja motar suka tafi.

A ƙofar gida suka tarar da Mama, tana ta kuka, maƙota sun kewayeta suna ta bata haƙuri suna rarrashinta, amma sai gursheƙen kuka take yi.
Da gudu Hafsa ta fito daga motar ta rungume Mama tana kuka, Khalil da Abdul suka ƙaraso, suka gaida Mama sannan Abdul ya ce bari suje suyi sallar magariba, sai su dawo dan an fara kiran salla.
Maƙota suka dinga shiga yiwa Mutane su Mama jaje, wasu dama zuwa ganin ƙwaƙwaf suke yi.
Bayan sun dawo daga salla, suka koma gidan su Hafsa, Mama tayi mus iso zuwa cikin gidan, ta shimfiɗa musu sallaya suka zauna, yayin da ita da Hafsa suke zaune a kan tabarma, Hafsa tana kusa sa Mama kamar za a ƙwace mata ita. Khalil kuwa sai mamakin ƙanƙantar gidansu Hafsa, kai da gani ba sai an gaya maka ba suna fama da rayuwa, wani irin tausayin Hafsan ya ƙara kama shi.

Suka kuma gaisawa, Mama ta ce "Sai dai ban gane ku ba, ko jami'ansa tsaro ne na farin kaya?".
Abdul ya ce "A'a Mama, ni sunana Abdul, wannan kuma Khalil" nan ya kwashe yadda suka gano Hafsa har suka dawo da ita gida.
Mama ta ce "Allah sarki, yau gani ga Khalil muna gaisawa a waya, ubangiji Allah ya saka muku da alkhairi, Allah ya jiƙan magabata, idan suna raye Allah ya ja da ransu, yadda kuka faranta mini ubangiji Allah ya faranta muku"

Abdul ya ce "Ameen Mama, bakomai ai yiwa kai ne"

Mama ta mayar da dubanta ga Hafsa ta ce "Hafsa, meya haÉ—aki faÉ—a da namiji a wurin sana'arki har ki É—au makami?".

"Mama wai kin yadda zan É—au makami in illata wani?" Tayi maganar a raunane.

"To Hafsa meya haÉ—aki faÉ—a da wani, har a kai ki wurin hukuma?".

"Mama ni ban nunawa kowa makami ba, Ƙona shi nayi da mai a ƙafa".
Mama ta buɗe baki ta ce "Hafsa wa kika ƙona da Mai?" Cikin kuka ta ce "Mama Najib ne fa, yana zuwa wurin sana'ata ya ci mini mutunci, na kasa jurewa na ɗau wannan matakin"

"Amma Hafsa kin taɓa gaya mini? Sai ki yanke wannan hukuncin haka?"
Khalil ya ce "Mama ayi haƙuri, kinga kamar haryanzu a tsorace take"

Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, na gode muku sosai Allah ya jiɓanci lamuranku"

Abdul ya ce "Ameen Mama, gobe in Allah ya kaimu zamu zo muje station É—in, a rufe case É—in gaba É—aya".

"To Allah Ubangiji ya kai mu na gode sosai".

Har ƙofar gida Mama ta rako su Abdul, tana ta cigaba da sa musu albarka. Khalil ya buɗe motar ya ɗauko wata ƙatuwar leda ya ce "Ga Abincinta da muka sai mata a hanya ba ta samu taci ba" da haka suka yi sallama su Abdul suka tafi gida.

Suna tafe Khalil na sake jinjina yanayin rayuwa da su Hafsa ke fama da shi.

Hall ɗin exam ya cika ya batse, ɗalibai sun duƙufa suna ta rubuta abin da suka sani. Fadila kuwa abin da ta sani bai kai ya kawo ba, ta ɗaga kai taga yadda Yazeed idaan ya samu dama yake taimakawa na kusa da shi, ga lokaci ya ja, tuni wasu ɗaliban sun fara bayar da tasu jarrabawar suna fita, amma ita tana zaune bata rubuta abin kirki ba, kanta ya ɗau zafi sai gumi take ta goshi.
Cikin sa'a ɗalibai suka ragu daga hall ɗin, invigilator ya mayar da Fadila kusa da Yazeed, hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Fadila ba, tana sa ran Yazeed ya taimaka mata. Sai dai taga Yazeed ya yi mursisi ko kallon in da take yaƙi yi. Wankin hula na neman kai Fadila dare, lokaci na ta tafiya, a kowane lokaci za a iya karɓewa, saboda lokaci ya kusa cika.
Bata ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da taga Yazeed yana tattara takardunsa, zai tashi yayi submitting.

TOFA, ZATA BAR YAZEED YYO SUBMITTING, KO KUMA ZATA SAUKE IZZA TA NEMI TAIMAKO?

Domin gyara, sharhi ko shawara
08081012143

READ THE CHAPTER 15 AT AREWABOOKS
https://arewabooks.com/chapter?id=6386388f094c9b1220e3fdb9.

GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143

P 15
Chapter 33 · 0% Book details