Sashe 59
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari da Safe Amina bata da niyyar zuwa lesson, ta tashi ta hau aikace-aikacenta, ta shiga kitchen ta É—ora sanwa, ta yi girkin safe ta kammala, ta zo ta shiryawa masu gidan nasu Abincin, sannan ta kaiwa Baba nasa ta dawo, ta fara mopping É—in falo.
Hajiya Zainab ce ta fara fitowa, Amina ta gaisheta ta amsa mata da ƙyar kamar an yi mata dole, sai kuma Fadila ta fito, Alhaji Ahmad ne ƙarshen fitowa, ba tare da Amina ta kalli in da yake ba, ta gaishe shi, yana jinta ya shareta, kamar ba da shi take ba.
"Good morning Daddy" Fadila ta faɗa tana ƙoƙarin haɗa tea.
"Morning sweetheart, how are you"
"Am fine Daddy"
Ya ɗan ƙara kallon Fadila ya ce "Meke damunki ne, you look dull today"
Fadila ta É—an yatsuna fuska ta ce "Nothing much, stress ne na school kawai"
"To Allah ya bada sa'a, yau weekends ki samu ki huta sosai"
"Ok Dad"
Ya mayar da hankalina kan Mummy ya ce "My Z ina Khalil ne?"
Mummy da ta kai loma bakinta, ta ƙarasa taunawa sannan ta ce "ƙyale shi kawai"
'in ƙyaleshi kamar yaya, ban gan shi a wurin cin Abinci ba"
"Ka san halinsa wasu lokutan, maybe bacci yake yi"
"Is ok" Daddy ya faÉ—a yana cigaba da cin Abincinsa. Yana yi yana satar kallon in da Amina ke mopping, tayi kicin kicin da rai, ko kallon in da suke bata yi, aikinta kawai take.
ÆŠan guntun murmushi yayi, ya cigaba da cin Abincinsa.
Bayan sun kammala ci, Mummy ta miƙe tsaye, ta kalli Fadila ta ce "Fadila je ki shirya muje ki rakani gidan Hajiya Turai"
Fadila ta É—an tsuke fuska ta ce "Mummy ki je ki kaÉ—ai, ni bana son fita"
"Aikuwa sai kin je, tashi maza muje"
Fadila tana tura baki, haka ta tashi, ya wuce É—aki, dan ta fara shirin yiwa Mummy rakiya, idan ba haka ba ta san halin Mummy, idan ta dinga mata mita sai taji babu daÉ—i.
Suka wate suka bar Daddy a falo, Amina kuma na zaune na goge TV.
"Ke da waye jiya na gani a tsaye a gidan nan?" Amina ta É—aga kai ta duba falon, amma bata ga kowa ba, dan haka ta san da ita yake, maida kai tayi ta cigaba da aikinta.
"Ko in zo in maimaita miki ne?"
Ta ce "Ba kowa"
"Kina nufin ƙarya nake kenan?"
Ta girgiza kai alamar a'a.
"Ke da waye?"
"Bilal ne, a nan layin yake, bayan ka ajiye ni a hanya, ya É—auko ni"
Alhaji Ahmad ya ce "Ban tambayeki wannan ba, abu ɗaya nake son gaya miki, kar ki sake kawo mini wani gida, kin zo gidan nan ne dan kin yi aiki da karatu, idan saɓanin haka ne a ranki, to zan sanar da Malam Hassan tun wuri ya san matakin da zai ɗauka, karki ƙara kawo mini wani gida kinji na gaya miki, idan kuma aure kike so sai kiyi bayani, amma gidana ba wurin tara maza bane" kamar kibbau haka ta dinga jin maganganun Alhaji Ahmad, ba ƙaramin ƙona mata rai suka yi ba, ba tace masa uffan ba, sai wasu hawayen ɓacin rai da suka cika mata ido, bata son ya ga lagonta, dan haka ta tashi ta kwashe kayan aikin nata, ta bar masa falon.
Alhaji Ahmad ya shirya ya fita, sai dai ya ci karo da Wayar da ya sayawa Amina a cikin motarsa, ya ɗau wayar ya jujjuyata, ya ɗan yi shiru sannan ya jinjina kai tare da faɗin lallai ma yarinyar nan. Ya ajiye wayar ya cigaba da tuƙinsa.
Hajiya Zainab ce tare da Hajiya Turai a falonta suna hira, yayin da Fadila ke gefe a zaune tana latsa wayarta.
Hajiya Turai ta ce "Wallahi kar ki saurarawa yaron nan, kiyi dagaske ki miƙe a kan abinki, idan ba haka ba wallahi kina kallo za a shanye miki shi, sai yadda aka yi da shi"
Mummy ta ce "Wallahi Turai Khalil ya bani mamaki, ban taɓa zaton yaron nan zai kai kansa wurin maƙasƙanciya kamar mak awara ba, me aka yi a kai mai awara? Banda kalen tsiya da rashin sanin darajar kai, ya janyo mini abin faɗa a cikin ƙawaye"
"Bari Hajiya Zainab, yaran yanzu ka haifesu baka haifi halinsu ba, banda abin Kalil waye yake janyo talaka jikinsa, ai kowa arziƙi yake nemawa kansa, ai baki ga abin haushi ba yadda yarinyar ke washe baki, kamar gonar gyaɗa, Allah ya kashe ya bata"
Mummy ta ce "To wallahi yayi kaÉ—an, muddin bai rabu da yarinyar ba, zaiga abin da zan masa daga shi har ita"
Turai ta ce "Ai zuwa zaki har gida, mu kasawa yarinya warning ita da uwarta"
Fadila dai ba ta tofa ba, dan a ganinta Khalil shi ne ya janyowa kansa, ga Yusra nan, ba abin da Allah ya rageta da shi, amma ya watsar da ita ya ce baya so.
Turai ta kalli Fadila ta ce "Daughter, ke kuma wa zaki kawo mana, ina fatan dai ba wahalalle kema zaki kwaso mana ba"
Fadila ta ɗan kwaɓe fuska da murmushin gefen baki.
Turai ta ce "Ai ba murmushin ba, ni dai É—ana ya gani ya ce yana so, insha Allah da ya dawo zan haÉ—aku, dan har Babanaa ya zan zancen"
Mummy ta ce "Ai na fara mata zancen kwanaki, kin san yaran naki ne, miskilaine kamar ubansu, na fara mata maganar ba ta ce mini komai ba dai tukuna, amma dai na san zasu daidaita"
Fadila ta sake gyara kwanciyarta a kan kujera, dan wannan hirarrakin nasu ya isheta, so take su tafi gida kawai.
Sai da Khalil ya tabattar da Mummy ta fita, sannan ya shiga falon, ya saka Hajara ta kawo masa kayan breakfast ya karya, ya ci ne dan kawai yana jin yunwa, ba dan yana son cin Abincin ba.
Bayan ya gama ya fito daga É—akin, ya haÉ—u da Amina a kan baranda, ya kalleta fuskarsa ba walwala ya ce "Daga yanzu idan kun gama girki a dinga zuba nawa ana kai mini É—akina"
Amina ta ce "To insha Allah"
Fadila har suka taho gida, Mummy tana yi mata bayanin yadda É—an Hajiya Turai yake, ita dai Fadila lissafin, yadda zata yi da Kankiya da kuma batun Yazid ne ya dame ta.
Khalil kuwa gidansu Abdul ya wuce, dan ba shi da aminin da yake gayawa damuwarsa wanda ya wuce Abdul É—in.
Tun a kallon fako, da Abdul É—in ya yiwa Abokin nasa, ya san tabbas akwai damuwa, dan a yadda Khalil ya saba, da yazo yake fara zolayarsa, amma yau yana shigowa, ya wuce kan gadon Abdul ya kwanta, yayi shiru ba tare da ya ce musu komai ba.
Abdul bai kula shi ba, sai da ya kammala abin da yake yi, sannan ya dawo ya zauna a kusa da Khalil, ya kalli Khalil ya ce "Kalil, meke faruwa ne, tashi kayi mini bayani"
Kamar Khalil na jiran ƙiris, ya tashi zaune, yana share gumin da ya tsatsafo masa, ya kalli Abdul ya ce "Abdul, na ga samu, ina shirin ganin rashi"
"Kamar yaya kenan?"
"Abdul, Mummy, Mummy"
Abdul ya sake gyara zamansa ya ce "Me ya faru? Me Mummyn tayi"
Kamar Khalil zai yi kuka ya ce "Bayan wahalar da na sha wurin farautar soyayyar Hafsa, na yi nasara na samu, tana sona mun shaƙu, sai dai ina shirin zuwar wa da Mummy maganar Hafsa, ƙawaywen Mummy sun gano ni a wurin Hafsat, sun sanarwa da Mummy, baka ga cin mutuncin da ta mini ba, yanzu haka ma ta ce lallai in rabu da Hafsa, dan Allah Abdul yanzu ta yaya zan koma in janye maganata da Hafsa, bayan ta gama bank dukkanin yarda, da saka ran samun salama a wurina tayaya Abdul"
Abdul ya jinjina kai ya ce "Akwai damuwa, ka san iyaye gaba suke da dukkanin wani abu na san rai da son zuciyarmu, amma kuma yakamata ita ma Hafsa a duba a yi mata adalci, kaima kana da ƙanwa mace, alhakin Hafsa zai iya kama Fadila da bata ji ba bata gani ba"
"Kai Abdul, ba zan iya haƙura da Hafsa ba, duk da ban san wane irin mataki Mummy zata iya ɗauka a kaina ba, bana jun zan iya rayuwa babu ita!!!
DOMIN SHIGA VIP GROUP, POSTING KULLUM KU TUNTUÆENI TA WANNAN LAMBAR
08081012143
GABA DA GABANTA
BY
AISHA ADAM
(AYSHERCOOL/JAKADIYAR AREWA)
P34
Abdul ya gyara zamansa ya sake fuskantar Khalil ya ce "Ibrahim, kai ka wuce aboki a wurina yanzu, kai É—an uwana ne, ba zan so ka aikata abin da zaka zo kana dana sani ba, kar ka biyewa soyayya ka zo ka rasa yarda da soyayyar mahaifiyarka, Ka bi komai a hankali, har Allah yasa Mummy ta fahimta, shawara ta farko mai zai hana kaje ka samu Daddy, shi ka yi masa bayanin, na san zai fuskance ka kuma zai yiwa Mummyn bayani"
Khalil yayi wani guntun murmushi sannan ya ce "Abdul ya kake abu kamar ba ka san wacece Mummy ba ne? Kai ka san babu yadda za a yi na samu goyon bayan Daddy, muddin Mummy ba ta son abu, ba zata taɓa yarda ba, kuma wallahi ina matuƙar jin tausayin Hafsa, idan na rabu da ita ban san wane hali zata shiga ba, bari ayi sallar magariba, muje tare ka shaida yadda yarinyar nan ta shaƙu da ni, ta yarda dani ta saki jiki zan Aureta, amma Mummy tana barazanar rabani da ita, dan Allah Abdul ko Hafsa na da wani aibu da so ya rufe mini ido ban gani bane?"
Abdul a ransa ya ce 'Talauci, shine aibun da mahaifiyarka bata so' amma a fili ya ce "Ai Hafsa yarinyar kirki ce, ba ta da wani aibu, ba wanda ba zai so haɗa zuriya da ita ba, kuma tana cikin yanayin da take buƙatar taimako, zaman soya awarar nan bai dace da ita ba sam"