Sashe 81
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zakiru ya kalli Amina ya ce "Amina ko zaki haÉ—ani da wanda zasu tayani kwaso kayan da ke motar"
Amina ta miƙe tana faɗin "Ai ko nima sai in ɗauka"
Ya kalleta ya ce "Ki É—auki me? Zo muje ki gani fa" Amina tabi bayan zakiru zuwa mota.
Ya saka hannu ya buÉ—e mata boot, waro ido tayi ta buÉ—e baki da tayi tozali da abin da ke cikin Boot É—in.
Kayan Abinci ne kamar za a buÉ—e kanti, ta kalli Zakiru ta ce "Zakiru, wannan fa?"
"Aike Amina kin ciri tuta a gidan nan, shekaranjiya ya saka na É—au motar nan muke je da shi muka sayo, jiya da daddare ya ce mini a wannan motar zamu tafi, kar in bari ki san da kayan"
"Na shigesu ni Amina, Zakiru kalli uban kayan fa"
"Ke ki gode Allah, Allah ne ya baki, da waccan matar ta sani ba zata bari a baki ba"
Amina ta ce "Zakiru kaima ka É—iba"
"A'a nima ya sallameni, bari in kira wasu su tayani"
Haka aka dinga kwasar kaya ana shiga da su gidan su Amina, nan da nan sai ga matan su Baffa Lawan da yaransu sun cika gidan suma.
Sai da Zakiru ya tabattar da an gama kwashe kayan an shiga da su, yayi musu sallama ya ajiye musu bandir kuÉ—i ya ce in ji Alhaji Ahmad.
Gaba É—aya Mamaki ya gama kashe Amina, amma ta basar kamar bata wani damu ba.
"Ohh Amina, kalli yadda kika koma, lallai yanzu kin wuce ajin Jarmai, birni ya karɓeki" Cewar Amaryar Kawu Bala.
Suka yi ta yaba Amina, suna son jin ƙwaƙwaf, ance musu gidan da Baba yake aiki a nan Amina ma take yi, amma shi tun da yake bai taɓa zuwa da wanan kayan ba, kuma ba a taɓa kawoshi a irin wannan mota ba sai Amina. Suna ta son su tanbaya suyi tsegumi, amma Amina ta haɗe rai ta haye Gadon Inno tana latsa wayarta, dan ba zata manta wulaƙanci da rashin mutuncin da suka dinga mata ba a baya.
Gaba É—aya Fadila ji daÉ—in reaction É—in da Yazid yayi ba, ji tayi gaba É—aya bata son zaman makarantar, dan haka ta É—auki motarta ta wuce gida.
Zuwa azahar sai ga su Baffa Lawan, an je har Gona an sanar da su, ga Amina can an kawota a wata ƙatuwar mota daga birni.
Basu ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da suka ɓangaren su Amina, suka tarar da uban kayan Abinci fal tsakar gida, cikin ɗaki kuma kayan sawa ne da kayan ciye-ciyen da Daddy ya saiwa Amina.
"Ke ina Aminar take, wanann kayan kuma na menene?" Cewar Baffa lawan yana shafa buhun shinkafa.
Inno ta ce "Bismillah Baffa ku shigo"
"Ba zamu shigo É—in ba, ina Hassan É—in ma tukuna?"
Inno ta fito tare da faÉ—in "Ai ita kaÉ—ai ta dawo ban da shi, shi ya zazzo a 'yan kwanakin nan"
Bala ya ce "Ina Aminar ne?"
"Tana É—aki"
"Eh lallai, rashin tarbiyyar ta ta har ta kai ta kasa fitowa ta gaishe mu?"
Inno ta ce "A'a ba haka bane ba, ke Amina fito mana" banda Inno ta saka baki babu abin da zai sanya Amina ta fito.
Gaba ɗaya suka bi ƙofar ɗakin Inno da kallo, Amina ta yi ƙiba, fatarta ta ƙara haske.
"Ina wuninku"
Kawu Bala ya riƙe baki ya ce "Ba shakka, yanzu dama irin wannan rayuwar Hassan ya zaɓi kiyi, shi ya sanya ya tattaraki ya kai ki birni? Ko in ce kuka haɗa baki kika gudu, yawon ta zubar ai shikenan gaki ga duniyar nan, kin ƙi sunnar ma'aiki kin shiga duniya bin yaran yahudawa"
"Kawu Bala, Tazubar kuma?"
"Eh yawon ta zubar mana, idan ba haka ba wani irin aiki ne kike yi haka da kika samo wannan kayan, tun da uban naki yake aikin a birni ya taɓa zuwa da makamancin haka ne?"
Ran Amina yayi bala'in ɓaci, kawai ta tashi ta bar musu tsakar gidan, dan idan ta cigaba da zama zata iya rama cin zarafin da suke mata.
"Ka gani ko Yaya Bala, wai mu muke mata magana ta tashi ta tafi, idan ba bariki ba mai zai kawo haka?" Ita dai Inno tayi mus shiru, suka gama cin mutuncinsu suka tafi.
Inno ta koma ta samu Amina a ɗaki ta ce "Amina kiyi haƙuri, wallahi tun da kika tafi suke surutai da ƙanann maganganu"
Amina ta ce "Aikuwa sai sai suyi, dan bani da lokacinsu, na gaba ya riga yayi gaba, kuma Inno a É—ibar musu wani daga kayan Abincin nan a basu, aniyarsu ta bisu"
Da yamma Amina ta shirya, ta tafi sada zumunci wurin sauran 'yan uwa, kowa sai son ya ganta yake yi, masu ƙananan maganganu kuma suka cigaba da yi.
Su Bala kuwa da aka ɗebi kayan Abinci aka basu, lumi suka karɓe duk da suna iƙrarin kayan haram ne.
Da daddare Amina da Inno suna tare, Amina tayi musu girkin dare, suna ta hira Inno na bata labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarta, haka ita ma Amina ta dinga bawa Inno labarin birni makaranta da yanayin rayuwar mutanen birni.
"Gaskiya Inno an mana nisa, cigaba yana birni, in Allah ya yarda a dalilin karatun nan nawa sai garin nan ya samu cigaba na gaske"
"To Allah ya sa, amma da fari nima naso kiyi aurenki duk da ba Jarmai na ke so ki aura ba, amma yadda na ganki É—in nan naji daÉ—i sosai, kin san bayan tafiyarki Jarmai mata biyu ya aura ya saka"
Amina ta ce "Allah ya rufa mini asiri, da tuni nima ina ciki"
Wayar Amina ce ta fara vibrating tana kawo haske, ganin sunan Daddy ya sanya ta kalli Inno ta ce "Ina zuwa"
Ta miƙe ta bar ɗakin ta koma wani, ta zauna sannan ta amsa wayar tare da yin sallama.
Sai da yayi ajiyar zuciya sannan ya amsa ya É—ora da cewa "Da ba zaki É—aga bane?"
"Wace ni in ƙi ɗaga wayarka, ina tare da Inno ne ina cin abinci"
"Ok, nayi zaton kin yi bacci ai"
"Ai dare bai yi ba sosai"
Daddy ya gyara kwanciyarsa Sannan ya ɗora da cewar "Ina fatan kin ci kin ƙoshi"
"Na ƙoshi sosai ma, gani ga Inno muka ci fa, nayi kewarta sosai"
Yayi murmushi ya ce "That's good, ni kuma na kasa cin Abincin"
ÆŠan waro idonta tayi ta ce "Me yasa?"
"Ba a bani wanda nake so ba, fruit kawai naci na kwanta"
Cikin damuwa da tausayawa Amina ta ce "Meyasa baka sa an dafa maka wanda kake so ba? Kar ka kwana da yunwa fa"
Ya shafi cikinsa ya ce "Abincin ne bana jin daÉ—insa idan bana ki ba, na san da kina nan zaki dafa mini abin da nake so"
"Kar ka kwana da yunwa kaji Daddy, dan Allah ka ci wani abu"
"To me zanci, kar ki damu zan kwana haka ba wata damuwa"
Noƙe kafaɗa tayi ta ce "Ni ban yarda ba"
Dariya yayi ya ce "Rigima ko?"
"Allah da ina gida da komai dare saina dafa maka Abinci, me zai sa a bar mai nemowa ya kwana da yunwa, rashin kyautawar yayi yawa"
Har cikin ransa yaji daÉ—in abin da ta faÉ—a, na nuna damuwa da shi sosai.
"Ai nace karki damu, na ƙoshi na sha fruit sosai da cock"
"Cock kuma?" Ta faɗa da ɗan ƙarfi.
"Eh Cock" ya bata amsa.
"Daddy ba a hanaka sha ba?"
"To ya zan yi idan ban sha ba?"
"Daddy baka kiyaye lafiyarka sai wani abu ya sameka, daga tafiyata ka cigaba da ciye-ciye ko"
Sosai ta bashi dariya ya ce "Da wasa nake yi, ban sha ba"
"Har naji daÉ—i na zata ka sha"
"Mhmm ban sha ba Meenali"
Amina ta É—an numfasa ta ce "Daddy"
"Mmm"
Ta É—an tura baki ta ce "Ka amsa mana"
"Na amsa ai" yayi maganar yana murmushi.
Ta ce "Kace Na'am Meenali"
Dariya yayi ya ce "Kina son sunan kenan?"
"Eh mana, idan ka faɗa sai in jini kamar wata irin babbar 'yar gayun nan, nan kuwa 'yar ƙauye ce"
Ba ƙaramin dariya ta bawa Daddyn ba, "Allah ya shirya mini ke"
Ta sake nutsuwa ta ce "Daddy, kayan daka saya muka taho da....."
"Shhhhhh" ya katseta.
"Daddy ka tsaya ka ji me zance"
"Keep quiet" yayi maganar cikin bada umarni.
"Daddy dan Allah ka bari nayi magana"
"I say keep quiet"
Ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah Daddy"
"Amina i said you should keep quiet, tun da ba kya ji saida safe"
Da sauri ta ce "Yi haƙuri dan Allah nayi shiru"
"Idan nace bana son abu just leave it immediately"
"To in sha Allah"
"Yauwa ko ke fa, i hope dai baki fita ko ina ba?"
Amina ta É—an sosa kai ta ce "In gaya maka gaskiya?".
"Kin fita kenan?"
"A'a ai ban yi nisa ba, gidan 'yan uwanmu naje, kaga ba zan daÉ—e ba zan dawo"
"Meyasa baki gayamini ba"
"To kayi haƙuri"
Cikin kwaikwayonta ya ce "To kayi haƙuri, mara ji kawai, kije ki kwanta sai Allah ya kaimu da safe kuma"
"To Daddy, ko in hau Online"
"A'a hutawa zaki yi, kun sha tafiya, ki gaida Mutanen gidan"
Amina ji tayi bata son ta katse wayar, amma ta maze ta ce "To, Allah ya tashemu lafiya, don't forget to recite Suratul mulk before you sleep, zan kawo maka Abinci a mafarki" tayi maganar tana dariya.
"Meenalin Daddy, my joy giver zan karanta in sha Allah bye bye" ya kashe wayar, dan shima idan ya biye mata ba zai katse kiran ba.
Ya lumshe idanunsa tare da ɗora wayar a kan ƙirjinsa yana murmushi.
ÆŠaki Amina ta koma, ta tarar Inno na shirin kwanciya.
"Inno har kin gama cin abincin?"
Inno ta ce "To yaya zan yi idan ban ci na tashi ba, kin je kin shantake kin shanyani, wai ma da wa kike wayar ne?"
Amina ta É—an sosa kai ta ce "'yan ajinmu ne fa"
Inno ta gyaÉ—a kai ta ce lallai kam.
Fadila na zaune a babban falo, tana shan tea tana kallon wani Indiyan series, Mummy ta fito falon ita ma.
"Au baki bacci ba dama?"
Fadila ta ce "Eh Mummy, na kasa baccin ne"