Sashe 77
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fadila ta zuba wa wayarta ido, tun da garin Allah ya wayez tayi salla tayi wanka a É—akinta ta karya, ta koma kan gadonta ta naÉ—e take chatting tana game, gaba É—aya ba ta jin daÉ—in komai, ta rasa meye yake mata daÉ—i, Khalil baya nan, ta saba ko baya nan sukan yi chatting amma yanzu taga last seen É—insa ya kai 3days,taga alamar kamar ita ma haushinta yake ji.
Ta gaji da latsa wayar, ta É—auko litattafanta ta fara karantawa, ta tsinci kanta da duba ire iren rubutun da Yazid kan yi mata a cikin littafi. Tayi ajiyar zuciya ta cigaba da karatun ta.
Hajara yau naɗewa tayi taƙi yin aikin komai, wai mura ce take nuƙurƙusarta, dan haka ba zata iya aikin komai ba, ta barwa Amina aikin gida gaba ɗaya, sam hakan bai dami Amina ba, yadda zata ga Daddy ta bashi haƙuri ne ya dameta.
Bayan girkin rana da tayi na duka gidan, ta koma ta É—ora faten wake da dankalin turawa saboda Alhaji Ahmad.
Ta tsara masa abinci, sai dai ta shiga zullumin karta kai masa ya yi mata wulaƙanci, tun da fushi yake da ita.
Ta fara zuba na Baba ta kai masa, sanan ta kaiwa Fadila nata ɗakinta, ta tarar da Fadilan na toilet tana alwala, ta kalli yadda ta baza liatattafai a kan gado, kamar wata 'yar Nursery.
Ta kalli wani rubutun larabci, da ke rubuce a wani littafi da yake a buÉ—e.
Amina ta karanta larabcin, kasancewar Amina tana jin larabci kaɗan-kaɗan ya sanya ta fahimci rubutun na soyayya ne, daga ƙarshe ya rubuta sunansa Yazid.
Ɗan shiru Amina tayi tana tunanin a ina ta san wannan sunan na Yazid, jin alamun buɗe ƙofar banɗakin ya sanya Amina saurin ficewa daga ɗakin.
Amina, Tana fitowa taga fitar Alhaji Ahmad, É—an dafe kanta tayi tana tunanin ina za shi haka bai ci Abinci ba, amma jin ana sallar azahar, ya sanya ta ce ko masallaci za shi.
Ta koma É—akinta tayi wanka, tayi sallar azahar ita ma, ta canza kaya ta gyara jikinta.
Cikin sa'a da ta kuma fitowa, taga ya dawo, sai dai fuskar nan tasa babu annuri sam, ya wuce sashinsa.
Da sauri ta koma Kitchen, ta haÉ—o kayan Abinci a tray, har da favorite fruits É—in sa, ta nufi falonsa tana Addu'a.
Sallama ta yi, amma ta ji shiru ba a amsa ba, tayi addu'a ta shiga, tana fatan Allah ya sa yana falon.
Aikuwa ta hangoshi kwance a kan 3seater, idanunsa a rufe. Ta ƙarasa gabansa ta ajiye trayn a ƙasa.
Ta miƙe ta kalli in da yake kwamce ta ce "Daddy" ya buɗe idonsa ya kalleta.
"Ga Abincin rana na kawo maka" ya jinjina mata kai ya mayar da idonsa ya rufe.
Amina ta zauna a kan gwiwowinta a hankali ta fara magana "Daddy ka tashi ka ci Abincin"
Ba tare da ya buÉ—e idonsa ba ya ce "Ki bar shi a wurin zan ci"
A ɗan marairaice ta ce "Dan Allah ka tashi zaune" sake buɗe idomsa yayi, ya tsareta da ido wanda sai da ya sanya ta sunkuyar da kanta ƙasa.
A hankali ya tashi zaune, ya kalli agogon hannunsa, ya fara shirin tashi tsaye, da sauri Amina ta ce "Daddy Abincin fa?"
"Ki bar shi a nan, ranar Alhamis in Allah ya kaimu, ki shirya da wuri, Zakiru zai kai ki ƙauye"
Kan ya tashi tsaye, Amina ta ƙarasa gabansa a kan gwiwowinta ta ce "Dan Allah Daddy, kayi haƙuri, na san ban kyauta ba kana fushi da ni, dan Allah kayi haƙuri"
Kallonta yayi ya ce "Laifin me ki ka yi mini kike bani haƙuri?"
"Daddy na maka laifi mana, baka cancanci in maka magana a yadda nayi maka ba, raina ne ya ɓaci sosai, amma ban kyauta ba, dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba"
Ya É—an girgiza kai ya ce "Hmmm"
"Dan Allah kayi magana, duk na damu da laifin da nayi maka, kayi haƙuri"
"Shikenan ya wuce"
"Ka haƙura?"
"Eh ya wuce"
Ta ɗan marairaice fuska ta ce "kamar ba ka haƙura ba fa"
Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Meyasa kika ce haka?"
"Haryanzu ranka a haÉ—e yake fa"
"To ai bani da lafiya ne, amma nace miki ya wuce ai"
Cikin damuwa ta kalleshi ta ce "Jikin ne haryanzu? Sannu Allah ya baka lafiya"
Ya amsa da Amin.
"To in zuba maka Abincin?" Ya jinjina mata kai. Ta zuba masa Abincin a plate ta saka cokali ta miƙa masa.
Ya karɓa ya kalleta ya ce "Zauna a nan yayi maganar tare da nuna mata kusa da shi a kan kujera.
ÆŠan turus tayi tana ganin rashin dacewar hakan. Amma kasancewar shiri take nema, haka ta tashi ta zauna a kusa da shi.
"Amina?".
"Na'am Daddy"
"Banji daɗin abin da ki ka yi mini ba, kema kina cikin masu mini kallon anfi ƙarfina a gidana ko? Duk abin da nake yi, ina da dalili ina ƙoƙarin baki kariya, bana son ki bar gidan nan karatunki ya samu matsala, amma saboda yadda nake da ke kika kalli tsabar idona ki gaya mini magana haka ko Amin? Da wani ne ya mini abin da kika mini saina hukunta shi, ko da kuwa matar gidan nan ce, amma shikenan. Idan kin dawo daga ƙauye upper week zaku tafi Abuja, before na so inje Abujan nima, in ga competitions ɗin naku, dan sun bani invitation as a special guest, amma I don't think zan samu zuwa"
Hawaye ne ya cika idon Amina ta ce "Dan Allah Daddy kayi haƙuri, gaba ɗaya na san ban kyauta ba, amma ba Baba ba, ko kai na gani wani ya maka haka sai inda ƙarfina ya ƙare, Matarka da 'yarka sun tsani Baba, ban san me yayi musu ba, wallahi ko dukana za suyi ba zan damu ba a kan su ci mutuncin Baba, ina jin zafi a raina, amma dan Allah Daddy kayi haƙuri, ba zan sake ba"
Ya kai lomar abinci bakinsa ya haÉ—iye, sannan ya ce "Ba komai ya wuce"
"To amma naga haryanzu ka haÉ—e rai"
"Abubuwa da yawa suna damuna, ga kuma yanayin jikina dan haka am not in mood, ai nace ya wuce"
Cikin damuwa ta ce "Sannu Allah ya baka lafiya, Daddy kaje Asibiti"
Ya ce "Zaki rakani?"
Ta É—aga masa kai alamar eh.
Ya cigaba da cin abinci, can kuma ya ce "Yauwa, idan zaki tafi ƙauyen me kike ganin za a saya ki kai musu?"
"A'a ba sai an sai musu komai ba" Amina ta faɗa tana ƙoƙarin zuba wa Daddy ruwa.
"Idan zaki tafi ƙauye, me kike ganin ya dace a sai musu?" Ya kuma maimaitawa, hakan ya tabbatar mata he is serious.
Ta ce "Lemo da ayaba"
ÆŠagowa yayi ya kalleta ya ce "Dubiya zaki je ko kai ziyara?"
"Ziyara"
"Kuma sai ki kai musu lemo da ayaba?"
Amina ta tura baki ta ce "To ni me zance?"
"Idan ina magana kina cewa ke me zaki ce, zamu ɓata"
"A'a na daina, bana son mu kuma ɓatawa, in muka ɓata ba na jin daɗi"
Murmushi ya yi ya ce "Are You serious?" Ta É—aga masa kai alamar eh.
"To shikenan, ki daina mini abin da zamu yi faÉ—a"
"In Allah ya yarda na daina Daddy, amma zaka zo wurin taron namu na Abujan?"
Daddy ya ce "Babu tabbas"
"Dan Allah Daddy ka zo, ko ba ka haƙura ba haryanzu?"
"Ai nace miki ya wuce"
"To shikenan, na gode sosai, Baba da kansa yayi mini maganar zuwa Abujan, Allah ya biyaka da Aljanna Daddy, in Allah ya yadda ba zan baku kunya ba, zan yi abin da ya dace"
Yayi murmushi ya ce "Allah ya sa, bayan sallar la'asar ki shirya, zaki rakani ganin likita"
Ta miƙe tsaye ta ce "To, amma me zance wa Baba?"
Ya miƙe ƙafafuwansa ya ce "Baba baya nan a lokacin"
"Ina za shi?"
Daddy ya yamutsa fuska ya ce "Tambayoyinki sun yi yawa"
"To yi haƙuri, na tafi".
Ya jinjina mata kai, tare da lumshe idanunsa"
Ta juya da tray É—in Abincin ta fita.
A falo tayi kiciɓus da Hajara, Hajara ta dubeta ta ce "Amina daga ina haka?"
"Kaiwa maigidan nan Abinci"
Hajara ta waro ido waje ta ce "Ikon Allah, da kika kai masa kuma shi ne kika zauna kika jira ya gama kika fito da kwanukan, ni fa na zata ma ba kya nan, tun É—azu nake falon nan ban ga gilmawarki ba"
"Hajara, na kai masa na rana, sai ki kai masa na dare kema" tayi tsaki ta wuce, dan ta fara ƙuluwa da shegen sa idon da Hajara take yi mata.
Amina na tsaye a gaban mudubi, ba wata kwalliya tayi ba, amma tayi kyau sosai, wata doguwar rigar abaya ta saka, wadda Babar Azima ta kuma aiko mata da ita, ta ɗan gyara fuskarta tayi tsaf da ita, ta riƙo wayarta a hannu ta fito falo.
Ko da ta fito ta tarar da Daddy a tsaye yana jiran fitowarta.
Kashe mata ido É—aya yayi ya ce "You look beautiful in this outfit"
Murmushi Amina tayi ta ce "Thank you Daddy"
Hajara da ta daskare a wuri ɗaya, har ƙara leƙa fuskar Daddy take, dan ta sale tabattarwa kanta abin da take gani ba mafarki bane ba, babban abin da yake sake ɗaure mata kai, wanzuwarta a wurin ba ta sanyawa su bar abin da suke yi, bata ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da taga alamar fita zasu yi tare.
Corridor dake cikin sashin Hajiya Zainab Hajara tabi, ta leƙa dan akwai taga da take kallon wurin parking space, aikuwa idanunta suka dake gane mata Alhaji Ahmad ya buɗewa Amina gaban motarsa ta shige, shima ya zagaya ya shiga ya kunna motar.
Fita tayi da sauri ta nufi falo, taji tamkar taje ta kira Fadila ta ce ta zo taga cin amanar da akewa babarta, amma ta tuna Fadila ta tuna halinta na rashin mutunci, dan a 'yan kwanakin nan ta hanata zuwar mata É—aki ma gaba É—aya, Amina ce kawai ke kai mata Abinci idan na zata ci a dining ba, ko kuma gyara mata É—aki.