← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 84

Sashe 25

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a fa uwata, yanzu ba Makaranta É—ansa ya kai ki ba? Idan mutum ya miki ba daidai ba, ki bishi da alkhairi albarkacin addu'a da kike musu, sai Allah ya miki abin da ba ki zata ba"

"To Baba zan dinga yi musu insha Allah, bari in je in wanka nayi salla, ka ci Abinci kuwa?"

"Eh naci, Hajara ta kawo mini, maza kije ki yi salla"

Ta amsa da to Baba, ta miƙe ta shiga cikin gidan, cike da fara'a da jin daɗi.

Kallo ɗaya Mummy ta yi mata tare da kwaɓe baki, ganin yadda ta goyo uwar jakar Makaranta tana washe baki.
Amina tayi mata sannu da gida, amma da ƙyar ta iya amsa mata. Hajara ma tsokanar Amina ta dinga yi, tare da tayata murnar samun cigaba da zuwa makaranta.

Fadila ba ta dawo gida daga Asibiti ba, sai bayan biyar na yamma, ta dawo a gajiye matuƙa, kuma rai a ɓace saboda abin da Yazeed ya yi mata, kai tsaye sashenta ta wuce, ba tare da ta nemi ko in da Mummy take ba, dan ba abin da take son yi, banda ta yi wanka tai salla ta ci Abinci.
Duk da ranta a ɓace yake, amma abin da ta tarar a part ɗinta, yayi mata daɗi sosai. Tayi wanka tayi salla, ta fito ta nufi kitchen da kanta, a kitchen ta tarar da Hajar da Amina na ƙoƙarin ɗora girkin dare, sai bawa Hajara labarin makarantarsu Amina take yi.

"Wacece ta gyara mini É—aki a cikin ku yau?".

Amina ta ce "Nice".

"Biyoni" ta yi maganar cikin bada umarni. Bayan Fadila Amina ta bi, tana fargabar kar abin Arziƙi ya zama na tsiya.
Da suka ƙarasa ɗakin Fadila, Fadila ta ƙare wa ɗakin kallo sannan ta ce "Naga aikin da ki ka yiwa ɗakin nan, kin canzan labulaye kin wanke waɗancan, kin ɗaga gado da wardrobe kin gyara kin canza musu fasali, na ji daɗin hakan, keep it up Ina son sauye sauyen Abubuwa lokaci zuwa lokaci".

Amina ta ce "To insha Allah"

Fadila ta ce "ɗan tsaya" ta ƙarasa ta ɗakko wata babbar ledar siyayya ta store, ta sakawa Amina turamen atamfa uku, da dogayen riguna, sai hoda da turare ta ce "Gashi nan kije kya saka" Amina ta karɓa cikin fara'a ta ce "Na gode Ubangiji Allah ya ƙara Arziƙi" ta amsa da Ameen.

Sai da Amina ta fara zuwa ta nunawa Baba kayan, sannan ta je tana nunawa Hajara, sai dai ran Hajara ya sosu, dan tun da take ba'a taɓa bata makancin wannan kyautar ba a gidan.

Amina ta ce "Yaya Hajaru, ki É—au doguwar riga É—aya, zan É—inka atamfa biyu in ajiyewa Inno É—aya".

A fuska Hajara ta ce "An gode madalla" amma a zuciyarta kuwa sam ba ta ji daÉ—in hakan ba.

Tun da Khalil ya baro wurin Hafsa yake tunanin mai ya fito da ita zaman titi da irin wannan sana'ar haka? Gashi ita ba gwanar fara'a ba, balle ya samu ya tambaye ta, to matar da ko fara'a ba ta yiwa kwastomominta, ga taƙamar tsiya ina zata saki jiki har kayi mata wasu tambayoyi?
Duk yadda ya so ya manta da batun Hafsa, ya cigaba da sabgarsa, amma ya kasa, duk in da ya motsa tunaninta kawai yake yi, har haskowa yake irin kyan da zata yi, idan har tayi dariya ko murmushi.

Bala'in Jarmai ya sanya su Bala a uku, dan duk in da ya tsuguna zaginsu yake a garin nan, kuma duk inda ya gansu ya dinga yi musu tijara kenan a kan kuÉ—in aurensa.
Haka suka ƙuƙuta, suka mayarwa da dillaliya kayan gadon da suka saiwa Amina, amma tayi musu sayen wulaƙanci, suka tattara dubu talatin da ƙyar suka kai masa, a wulaƙance Jarmai ya karɓa sannan ya kalli Kawu Bala ya ce "Amma dai ka san na baku kuɗi sun kai dubu tamanin ko?"

Bala ya ce "Haka ne"
"To banci nanin ba, nanin ba zata ci ni ba, ba ƙira ba abin da zai ci gawayi, ina ganin mutuncinku ne shi yasa ban kai ku ƙara birni ba, kuma wannan dubu talatin na karɓeta ne dan kar nayi biyu babu, amma daga nan zan fara wucewa wurin mai gari, in fara kai masa ƙarar".

Kawu Lawan ya ce "Haba Jarmai, dan Allah kar mu yi haka da kai mana, insha Allah zamu ciko maka sauran kuɗinka, kayi haƙuri".

Jarmai ya gyara wata daƙalƙalalliyar babbar rigarsa ya ce "Ai haƙuri shi ne kawai in ga uwar kuɗina a hannuna".

Kawu Bala ya ce "Insha Allah, zamu cigaba da lalubawa zamu baka sauran kuɗinka" da ƙyar suka lallaɓa Jarmai, ya haƙura bai kai su ƙara ba.

Washegari da Fadila ta koma Makaranta, Captain ya tambayeta ya mai jiki, ta sanar da shi tun a jiyan aka sallame shi ya tafi gida, 'yan aji suna son suyi tsurku su ji yadda abubuwa suka wakana, amma sanin halin Fadila ya sanya ba wanda ya tanka mata.
Ta dinga zuba ido, ta ga ta ina Yazeed zai shigo aji, amma babu Yazeed babu alamar sa, har aka yi lectures É—in ranar aka gama.
Nan cikin Fadila ya sake ɗurar ruwa, ta san ba zai wuce ace jikin ne ya hana shi zuwa Makaranta ba, nan zuciyarta ta dinga saƙa mata abubuwa daban daban, ciki har da tunanin ko jikin ne ya tayar masa ya mutu? Nan da nan ta yi saurin kawar da wannan tunanin daga ranta.
Da aka tashi daga Makaranta ta samu Captain ta ce "Musa, kun yi waya da gayen nan ne?"

Captain ya ce "Wa kenan?".

"Wanda muka kai Asibiti jiya"

Murmushi ya yi ya ce "Hajiya Fadila ta mu, sunan nasa ne ma ba za a iya faÉ—a ba. Wallahi tun jiya nake kiran wayarsa, amma ba ta shiga, kuma ina kyautata zaton jikin ne ya hana shi zuwa yau" Fadila ta ce "Ok shikenan"

Daga haka ta wuce ta nufi motarta, tana cigaba da tunani.

A kwanakin nan kowa da abin da ya dame shi a jama'ar gidan, Khalil ya kasa sukuni saboda tunanin Hafsat, gashi ya kuma komawa amma bata nan bai sameta ba.
Fadila kuwa gaba ɗaya tunanin halin da Yazeed yake ciki ne ya dame ta, dan a rayuwarta bata taɓa aikata abin da ya dameta ba kamar abin da ta yiwa Yazeed ba, saboda ta tsorata da irin yanayin ciwonsa.  Bata taɓa ganin mutum a mawuyacin yanayi na ciwo kamar Yazeed ba.
Tana zaune a aji, tana ƙoƙarin ɗauko littafi tayi rubutu, ta ga jotter Yazeed, ta ɗauko jotter ta fara bubbuɗewa, rubutunsa a tsare yake kamar musamman yake shirya rubutun, sai dai fahimtar abinda ya rubuta ɗin sai ƙwaro ko kuma shi kansa da ya rubuta abin sa.
Rubutu ne na turanci, jotting ɗin lectures ɗin da ake yi ne, sai yayi sentence ɗaya biyu ya gauraya su da rubutun larabci, ga wasu irin manyan Words na turanci, da bata taɓa jinsu ba.
To ya akai ya iya turanci a rubuce, amma bai iya a baki ba? 'Maybe yana da matsalar public speaking ne' ta bawa kanta amsa.
Bakomai ta iya ganewa a jotting É—in nasa ba, saboda yadda yake rubutun larabci kamar rubutun yarensa na haihuwa.
Ɗan taɓe baki tayi, ta ajiye jotter, tana fatan Allah ya sa dai ba jikinsa ne ya hana shi zuwa Makaranta ba.

Khalil musamman sai ya shirya ya tafi unguwar su Abdul, yayi shawagi domin kawai ya ga Hafsat, cikin ikon Allah yau yayi sa'a ya tarar da ita a bakin kaskonta bayan magariba, tana ta harhaÉ—a kayanta ta tashi.
Parking ɗin motarsa ya yi, ya fito da sauri ya ƙarasa in da take. "Sannu dai"
ÆŠagowa tayi ta kalleshi ta ce "Yawwa".

"Ba dai har kin tashi ba?"
"Me kaga ina yi?"
"Oh sorry haka ne, na gani haÉ—a kaya ki ke yi, yanzu ba zan samu ba?".
"Eh ta ƙare".
"Kwana biyu na zo ba na ganinki, meyasa ba kya fitowa?"
Hafsa ta ce "Eh da yake ai ba aikin gwamnati nake ba, kuma ba wani ne ya É—auke ni aiki ba balle a tuhume ni"

Murmushi Khalil ya yi, yana jinjina hali irin na Mai awara, ya É—an sosa kai ya ce "Haka ne, am sorry"
"Yawwa dama ina nemanka" tai maganar tana saka hannu a jakarta.
Khalil ya ce "Kina nemana kuma? Allah ya sa ba laifi na miki ba"
Ɗari biyar ta miƙo masa tana faɗin "Karɓi canjinka da ka tafi ka bar mini ranar"
"Ai ba bashi bane, kyauta na baki".
"Ai bance maka ina buƙata ba, ka karɓi canjinka".

Khalil ya ce "Ai kyauta na baki, kuma ba kyau mayar da kyauta".
"Meye tsakanina da kai, da haka kurum zaka bani kyautar kuÉ—i"
"Alkhairi ne tsakanina da ke. Naga kamar gida zaki tafi, ko zamuje in sauke ki?"
"Malam ka karɓi kuɗinka, zan tafi dare nayi"
"Da ban dawo ba ya zaki?".
Ƙoƙarin saƙala masa kuɗinsa take a hannunsa da harɗe a ƙirjinsa. Ja da baya yayi yana kallonta tare da sakin murmushi ya ce "ke dai kin fiye gaddama, dama zuwa na yi in ganki, kuma na sai awara, tun da ban samu awara ba na samu ganinki, shikenan, ki gaida gida" galala ta tsaya tana kallon Ikon Allah, Khalil kuma yayi gaba abin sa yana jin wani nishaɗi da ya rasa na menene.
Yana tafe a mota yana tuna yadda tai kicin-kincin da rai tana bashi kuɗinsa, sam bai gaji da ganinta ba, amma ya lura ba ta son takura, magana kuma na bata wahala, shiyasa ya tafi ya ƙyaleta.
Shiru yayi yana tunanin menene haka yake ji game da yarinyar nan? Wani irin baƙon al'amari yaji yana ratsa zuciyarsa, duk Hafsa daga gaban kaskon wuta ta tashi, ƙamshin turarenta ya haɗe da ƙaurin mai da na hayaƙi, amma a hancin Khalil ƙamshi ya bashi mai daɗin gaske.

Amina kuwa zuwa makaranta ya kankama, dan ta gane hanya, Baba ne yake bata kuÉ—in mota, ta hau abin hawa ta tafi, idan an tashi ma ta taho gida.
Kullum da kiran sallar farko, Amina idan ta tashi bata komawa, duk wani aiki da zata yi, sai ta tabattar ta yi shi, har karin kumallo sai ta dafa, ta gyara ko ina sannan take shiryawa ta tafi makaranta.
Chapter 25 · 0% Book details