← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 84

Sashe 70

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilal bai saurreta ba, ya cigaba da binta, suna tafiya tare, gaba É—aya hankalin Amina baya kan Bilal, sai surutu yake mata, ba tare da tana amsa masa ba.

Sun ƙarasa titi tana jiran mota, ba tsammani sai ga motar Daddy ta zo wucewa, lokacin da ta fito daga gida ko tashi baiyi ba, amma har ya shirya ya fito, sai da ya zo daidai in da suke, sanan ya ɗan ja motar a hankali, yayi musu horn, dan Amina ta san ya ganta, sannan ya ja motar da sauri ya bar wurin.

Sai da cikin Amina yayi ƙara, ba ta san hukuncin da Daddy zai yi mata ba, saboda yayi mata gargadi a kan Bilal.

Sai da Bilal ya tabattar da ta hau mota, ya biya kuÉ—in, sannan ya juya ya koma.

Yau Fadila ita da kanta taje wurin zaman Yazid, sai kallonta yake yana murmushi, ta miƙa masa wata 'yar ƙaramar jaka ta ce "Gashi nan, kayan birthday ne, na kawo maka"

"Ohh ni Yazid, har da ni a cikin kayan, to Allah ya sanya abin da kika bani É—in na iya ci"

"Idan ma baka iya ba saika koya"

Ya ce "To shikenan, zauna muyi wata Magana"

Fadila ta nemi wuri ta zauna, ya ɗan dubeta ya ce "Da kika ƙara shekara a duniya, kuma kika kama hanyar komawa ga ubangijinki, wace Addu'ar ki ka yi?"

Fadila ta ɗan taɓe baki ta ce "Wace Addu'ar kuma?"

"Au ke baki Addu'a ba, sai iyayi"

"Ba wani iyayi, family and friends sun yi wishing É—ina, that's all"

Yazid ya ce "No, yakamata ki roƙi Allah gafara, ki yiwa kanki kyakkyawan fata a cikin abin da ya rage miki a rayuwarki, kiyi Addu'a a kan karatunki, da kuma fatan Allah ya kawo miki abokin rayuwa na gari, wanda yake sonki"

Ta É—an kalleshi ta ce "Waye abokin rayuwar?"

"Miji mana, na gari mai sonki saboda Allah, ko da kuwa Kankiya ne"

HaÉ—e rai ta yi, ta ce "Wai sau nawa zan gaya maka, kar ka sake haÉ—ani da mutumin nan, bana son irin haka na gaya maka"

Yazid ya ce "Ikon Allah, to ke haka ake yi? Ba Addu'a nayi miki ba, ai idan kana neman azaɓin Allah, barwa Allah komak ka ke, baka zaɓe-zaɓe"

"Over my death body in auri wanan mutumin mara tunani"

Da sauri Yazid ya ce "Subhanallah, Ukty malaminki ne fa"

Ai tamkar da kankiyan take magana, ta ce "And so what? Ko na rasa mijin Aure ni ba ajinsa ba ce, yana rayuwa kamar wani bagidaje da bai san meya ke yi ba, a haka zan so shin?"

Jikin Yazid yayi sanyi, Kankiya ma kenan, da ya na ɗaukar wanka, ina ga shi, da kayan sawarsa ma ba su fi a ƙirgasu ba.

Har tayi shiru ta cigaba da mita, "Allah na tuba, ko a ƙafata a ka ɗaura mini shi ba sai na kwance shi na yar ba, kai mini wata Addu'ar banda Wannan, ni waima waye ya ce maka zan yi Aure ne? Da in yi Aure da kar in yi duk normal ne"

Yazid yayi murmushi ya ce "A hakan da kike?"

Ta É—an kalleshi da mamaki ta ce "Kamar yaya a hakan da nake?"

Ɗan taune lips ɗinsa na ƙasa ya yi ya ce "Bar zancen, amma kina buƙatar abokin rayuwa na gari, ai kin kai girman da kin zama mutum 'yar yarinya"

"Haka nace maka?"

"Ko baki faÉ—a ba yanayinki ya nuna Besty, anyway mu bar wannan maganar, Allah ya baki miji nagari, ko da Yazid ne"

Da wani irin sauri ta kalli Yazid, tare da yamutsa fuska kamar wadda ya gayawa saƙon mutuwa ta ce "What? Wane Yazid ɗin?" Tayi maganar babu alamar wasa a tare da ita.

"Kai bari kaji in gaya maka, tun wuri ka mayar da hankalinka, am still the Fadila you know, kawai naga rashin dacewar wulaƙancin da nake maka ne, ya sanya nake kulaka, kan ka yiwa kanka fatan zama mijina, Yakamata ka san waceceni, ba sa'arka ba ce ni, we are just friends, tun da abin da kake tunani kenan, friendship ɗin ma is over now, Fadila ba matar ire-iren mutane kamar baka ce".

Yazid yayi shiru, bai taɓa zaton Fadila zata yi masa haka, ta bishi da wanan kausasan kalaman ba, tun ma bai kai ga furta cewar yana sonta ba, matuƙa kalamanta sun tsaya masa a zuciyarsa.

Ita kuwa tana gama yanka masa wannan maganganun, ta tashi ta bar wurin da yake.

Ya bita da idanuwa, yana jin zafi a ransa.

Ko da yake maganganun Fadila suna bisa turba, ita ba sa'ar aurensa ba ce, matsayinsa da nata ba É—aya bane ba, amma idan aka duba matakan addini, yana da duk wani qualities da za a aureshi domin su.
Shiru yayi yana jin yadda duniyar ta yi masa zafi, yana ji a ransa dama bai yi mata wannan maganar ba, da wataƙila sun cigaba da gaisawa.

Gaba É—aya Ajin ta bari, ta tafi department É—in su Yusra, tana zuwa ta tarar da malami a ajinsu Yusra, dan haka ta jira sai da suka kammala lectures, malamin ya fita, sannan ita kuma ta shiga ajin.

Yusra ta kalli Fadila da ɗan mamaki a fuskarta ta ce "Girl ya dai? Na ganki rai a ɓace".

Fadila ta zauna tana É—an hura hanci.

"Ke wai meye ne?" Yusra ta faÉ—a tana sake tattara hankalinta a kan Fadila.

"Kin san wani abin takaici da raini?"

"A'a sai kin faÉ—a"

"Yazid fa sona yake" ta faÉ—a cike da takaici.

"Au da da nake gaya miki baki yadda ba? Me yayi miki ne?"

"Wai Allah ya bani miji nagari ko shine"

Yusra ta kwashe da dariya ta ce "Gaskiya Fadila baki da wayo, ke ce baki da tunani wasu lokutan, idan ba sonki yake ba mai zai saka yayi ta bibiyarki har ya dinga taimaka miki, yayi ta miki abubuwan da zai burgeki" Fadila ta ɗan yi shiru ta ce "Lalli bani da hankali, kawai na ɗauki alaƙarmu ne a friendship, ni mai yasa mazan nan suka rainani, amma Yazid tsaurin idonsa ya kai in da ya kai, ina shi ina mace kamar ni?"

"Kar ki cika baki malama, tun da ya fara bijirowa a mafarkanki da kika gaya mini, akwai alamar cigaba da tarayyarku ka iya sanyawa ki fara son shi, saboda gayen yana da kirki sosai"

"Ashe kuwa da Mummy ta kwaÉ—ani ta cinye, kin san a tashin hankalin da Yaya Khalil yake dan ya ce yana son mai awara, hmm naga wautar Yaya Khalil"

Yusra ta ce "Ikon Allah, shi kuwa Yaya Khalil meya yi masa zafi?"

"Oho masa, duk yadda suke da Mummy,tayi masa fata fata, ko cikin gida ba ya iya shigowa, ba kiga ko jiya bai shigo wurin birthday na ba. Ina gama alhakinki ne"

"A'a kar ki ce haka Fadila, Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi"

"Amin dai, da nazo na gaya miki maganar nan har naji sanyi, ni wallahi tausayi yake bani ma, Kankiya ya sako shi a gaba da yawa a kaina, ni kuma bana son a lalata masa karatunsa saboda ni, amma shi ma Kankiya tara sh nake, idan ya kaini bango sai ya rasa aikinsa wallahi"

"A'a Fadila ki bi a hankali dai"

"Ai a hankalin nake bi, ke kin san da ba a hankalin nake bi ba, Kankiyan shi da koyarwa a jami'ar nan har Abada, banda ke babu wanda ya san abin da ke tsakanina da shi, sai Yazid, shi kuma wannan ko ban gaya masa abu ba, ganowa yake kamar aljani"

Yusra ta ce "Do you know one Funny thing? Kin iya faÉ—ar sunansa wallahi, har wata madda kike Yaziiiid"

Tsaki Fadila tayi ta ce "Ke bana son wulaƙanci, bana son duk wani abu zai sake haɗani da shi, kowa yayi rayuwarsa kawai".

Yusra ta ce "Shikenan, tunda kin huce yanzu a kan yadda kika zo mini"

"Bari kawai ya ƙular da ni ne, da wani shegen takalminsa irin na danƙon nan, sai uban saka jallabiya kamar limamin harami"

Yusra ta kwashe da dariya ta ce A'a kar ki zafafa dai"

Fadila ta kai kusan twenty minutes tare da Yusra, sannan ta koma department É—in su.

Da idanun Yazid ta fara cin karo, kallo É—aya zaka yi masa, ka gane jikinsa yayu sanyi, guntun tsaki tayi ta wuce wurin zamanta.

Ƙarfe biyu daidai, aka tashi daga makaranta, Amina tayi sallama da 'yan ajinsu, ta fito gate.
Wata uwar mota ta gani a bakin gate É—in makarantar ta su a tsaye, da wasu 'yan sanda biyu a jikin motar.
Bata kawo tunanin komai a ranta ba, ta cigaba da tafiya. Ji tayi kamar ana binta a baya, ta waiwaya taga 'yan Sandan sun biyota.
Gabanta ne ya faÉ—i , tana sake dubwa taga wa suke bi.

ÆŠaya É—an sandan ya ce "Amina ko?"

Idanuwa waje Amina take binsu da kallo, tana tunanin meye haÉ—inta da 'yan sanda suka biyota makaranta.

"You Are under Arrest!!!"

AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA
            BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL

PAGE 39

Ƙara waro manyan idanuwanta ta yi ta ce "Arrest for what ni Amina?" Tayi maganar bakinta na rawa.

"Arrest by Alhaji Ahmad Dutse order" É—aya É—an sandan ya faÉ—a yana murmushi.

Sai kuma tayi saroro tana binsu da kallo, dan ta kasa fahimtar kan lamarin gaba É—aya.

"Kinga Kwantar da hankalinki, baki gane ni ba ne?" Yayi maganar yana nuna kansa

"Ni ban taɓa ganinka ba balle in gane ka" ta faɗa hawaye na taruwa a idonta.

"Ranar da kuka zo gidan Alhaji Ahmad ke da shi, muna aiki a gate É—in gidan, ai ni na ganeki shi ne ya ce mu zo mu É—aukoki, ya aikemu ne ya ce mu biyo mu É—auke ki"

"Taɓ aikuwa ba zan biku ba, ku 'yan sanda abin yarda ne? Haka kawai ku sani a motar 'yan sanda kamar wata ɓarauniya, naga ai da kansa yake zuwa ya ɗaukeni wataran"

Ɗan sandan ya kalli motar da suka zo da ita, helux ce me baƙin glass, ya sake dubanta ya ce "Lambar motar ta aiki ce, ba tamu ce ta 'yan sanda ba, ta Alhaji Ahmad ce, kuma ba sace ki za muyi ba"
Chapter 70 · 0% Book details