← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 84

Sashe 48

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau da azahar Fadila ta dawo gida, duk da Sir Kankiya yayi ƙoƙarin ganawa da Fadila a Office ɗinsa, dan har ya tura mata saƙo yana son ganinta a Office ɗin sa, amma ta share tayi tafiyarta, dan zuciyarta raya mata take taje ta tatala masa rashin mutunci, dan ta fara gajiya da takurar  da yake mata.
Haka nan take mamakin meye ya hana Yazid dawowa Makaranta.

Amina tayi farinciki sosai da sakamakon ta na makaranta, ta fara ƙoƙarin cigaba da hora kanta a kan darrussan kimiyya, tun kan a neme su a makaranta, a fara yi musu lesson.
Amina ta rage jin haushin Alhaji Ahmad a kan abin da iyalansa suke mata da kuma shima abin da yayi mata.
Ranar lahadi tun da ta idar da sallar Asubahi bata koma ba, ranar lahadi da su da masu gidan basu fiye tashi da wuri ba, saboda ba wanda yake fita a ranar.
Amina ita kaÉ—ai ce idonta biyu, ta É—ora girki saboda Alhaji Ahmad zai fita.
Kan ƙarfe shida da rabi, Amina ta kammala girkin, har ta tsaftace falo ta kukkuna turaren wuta.
Tana ta sake goge kan dining, sai hamma take, saboda baccin da take ji.

"Sannu da aiki" ta jiyo muryarsa.
da sauri ta waiwaya, ta kalli in da yake tsaye "Ina kwana" ta faÉ—a tana É—an lumshe ido. Maimakon ya amsa sai ya kuma maimaita mata "Sannu da aiki".

Ta fuskanci baya son yayi magana a share, dan haka ta ce "Yauwa na gode, ga breakfast É—in".

Alhaji Ahmad ya ƙarasa ya zauna, ya kalleta ya ce "Afuwan na katse miki bacci" ta ɗan girgiza kai ta ce "Bakomai"
Ya bubbuɗe flask ɗin, yayi mamakin ganin ƙosai da soyayyen dankalin Hausa, da kuma koko.

Kawai sai ta ga murmushi ya mamaye fuskarsa. "Ke kika yi girkin nan?" Haka nan Amina ta tsinci kanta da tura baki, to wa yayi idan ba ita ba, saboda kawai ya raina mata hankali yake tambayarta.

"Hajiya am talking to you"

"Eh nina girka"

Ya jinjina kai, ya zuzzuba ya fara ci, yaji daÉ—in girkin nan sosai, yana son Abincin gargajiya sosai da sosai, amma sam Hajiya Zainab bata so, gashi na wuraren sayarwa baya masa daÉ—i sam ko a Lagos haka nan yake maleji ba daÉ—insa yake ji ba.

Ya tsare Amina ya hanata tafiya, sai da ya gama, ta kwashe komai, sannan ya tashi zai tafi, Amina ta bi bayansa, har ya shiga mota ya hangota, ya tsaya yana jiran ƙarasowarta, ta miƙa masa wata jaka, be tambayi ta meye ba, ya karɓa ya duba, akwai manyan robar ruwa guda biyu a ciki, sai babban kwalin lemo, sai wata jarka guda ɗaya, ya ɗauko jarkar yana dubawa, fura da Nono a ciki.
Ya kalleta ya ce "Ina kika samu fura?"

"Mamana ce ta aiko mini da ita daga garinmu, na baka ne saboda hanya amma idan ba ka sha shikenan bani".

Yayi murmushin gefen baki ya ce "Bayan wauta ashe kina da hankali, ga ruwa ga lemo ga fura duk an bani kar inji yunwa a hanya, Na gode sosai"

"Bakomai Allah ya sanya Alkhairi"

"Ameen ya Allah" ya zura hannu a aljijunsa ya ɗauko kuɗi ya miƙa mata ya ce "Ungo wannan, kya sayi wani abun na gode sosai" ga mamakinsa sai ta girgiza masa kai alamar ba zata karɓa ba.

"Meyasa ba zaki karɓa ba?"

"Baba zai mini faÉ—a, kuma yana bani kuÉ—i shima"

"Ke kuma sai ki gayawa Baban na baki kuÉ—i?"

Cike da wauta ta ce "Ai ni duk abin da aka yi sai na gaya masa, saboda idan nayi ƙarya yana ganewa"

"Ai yanzu ba zai sani ba, idan ma kika gaya masan, kice ni na baki"

"Ni dai a'a gaskiya, ban taɓa riƙe kuɗi me yawa ba, ba ruwana, kuma dama ai aiki nake kuna biyana meyasa zaka bani kuɗi?"

"Ai nima babanki ne, ki karɓa"

Girgiza kai tayi ta ce "Babansu Fadila ne, ni Baba ne Babana" shi mamaki ma ta bashi, yaran yanzu da son abin duniya, amma ta dage ba zata karɓa ba, baya son cigaba da takura mata, dan haka ya ce "Shikenan, na gayawa Baban idan na baki abu ba kya karɓa" ba ta ce komai ba ta juya sumi-sumi ta koma ciki.

Tana zuwa ɗakinta, ta nemi wuri ta kwanta, dan ta samu ta rintsa, cikin barci, taji hayagagar Hajiya Zainab a ƙofar ɗakinta.

"Uban waye ya ce a girka mini wannan abin a gida, gidan nan yayi miki kalar in da za a sha wannan kayan fitsarin da saka gudawar, taso ki fito ki girka mana wani abin da zamu ci" iya ƙuluwa Amina ta ƙulu ƙarshe, bata ga meye aibun koko da ƙosai ba, kuma banda wulaƙanci ga Hajara nan amma ba za a sata aikin ba sai ita.
A gajiye take matuƙa tana son hutawa, amma an tasheta da tijara, duk aikin da tayi a gidan kan su tashi ba su gani ba, haka ta fito rai a ɓace ta kuma shiga kitchen.

Ranar Litinin lectures da komai ya cigaba da gudana, amma ba Yazid babu dalilinsa. "Bismillah" taji sautin murayarsa ya shiga cikin kunnuwanta, a rikice ta kalleshi, sai ka ce Aljani sam ba ta ga shigowarsa ba sai zamansa a kusa da ita.
ÆŠaga kai ta yi ta kalleshi, tana son yin magana amma ta kasa.
"Ukty, ko nemana ba kya yi, ban dawo school ba babu ko cigiya"

"Ni nake biya maka school fees da zan damu da rashin zuwanka?"

"Kar mu fara haka dake daga dawowata mana, ya kike ya hutun?"

Ɗan kallonsa tayi amma taƙi magana, Sir Kankiya ne ya shigo ajin, hakan ya sa kowa shiga hankalinsa saboda ba shi da wasa sam ga kwarjini da yake da shi.
Yana ganin Yazid a zaune kusa da Fadila, ya haÉ—e rai "Kai malam babu wani wurin zaman ne, sai nan kusa da mace?" Yazid ya kalli ajin kowa in da ya ga dama yake zama, kuma ba wai matsarta yai ba, amma Kankiya na neman ya dizaga shi a cikin mutane.

Fadila ta ce "Tare muke zama da shi"

"Yaushe kika fara ƙarya? Ai ba dake nake ba, next time ka nemi wani wurin daban ka zauna" Yazid ya jinjina kai tare da sunkuyar da kai.

Fadila ba ƙaramin ƙular da ita Kankiya yayi ba, amma ta basar, aka cigaba da lectures. Mistakenly biron Yazid ya faɗi ƙasa, ya durƙusa ya ɗauko amma ya kuma jiyo muryar Kankiya yana faɗin "Kai wane irin mutumin banza ne, kalleka a haka kamar mutumin kirki, zo ka fita ka bar mini aji" Saroro Yazid yayi yana son gane laifin da yayi, gaba ɗaya idon 'yan ajin ya dawo kan Yazid.

"Zo ka bar mini aji nace" Yazid ya miƙe ya bar ajin, ba tare da yayi ƙoƙarin kare kansa ba.
Fadila taji haushin abin da Kankiya yayi, ya kammala lectures É—insa ya fice, ta É—auki biron Yazid da littafinsa, ta nufi ofishin Sir Kankiya.

"Me Yazid yayi maka kake ta ƙoƙarin tozarta shi?" Tayi maganar cikin ɓacin rai.

"Yana bibiyar abin da nake so, idan yana son zaman lafiya ya kammala karatunsa hankali kwance a makarantar nan, to ya nesanta kansa da ke".

"Wai kai wane irin mutum ne? Ni nace maka ina sonka ne? Nayi maka kala da ajinka, nayi maka kalar auren mutum kamar kai? Babu wata alaƙa a tsakanina da Yazid, abokin karatuna ne kawai, dan haka kar ka ɓata masa career"

"Wannan ke ta shafa, da ke da shi, muddin ya cigaba da shiga sabgarki, zan iya kawo ƙarshen karatunsa a makarantar nan, idan kuma kin musa mu zuba mu gani, ba zan cutar da ke a harkar karatunki ba, Saboda ina sonki, amma gwargwadon wulaƙancin da kike mini, gwargwadon yadda zan cigaba da taka Yazid a cikin Jami'ar nan!!!

Ayshercool
08081012143
GABA DA GABANTA

AISHA ADAM AYSHERCOOL

P 24_25

Iya wuya Fadila ta zo, saboda tsabar takaici da ɓacin rai, ta kalli Sir Kankiya ta ce "To mu zuba ni da kai, idan baka ɓata Career Yazid ba, ni zan ɓata taka rayuwar, na ga alamar baka san wacece ni ba, ba zan saka a hukunta min kai haka ba, kaci bulus, saina fara nuna maka ka ba kowa bane ba, face me sanye da rigar tsiya da zai ƙare a cikinta".

"Fadila ni kike gayawa haka dan ina son ki?"

"Na gaya maka ɗin, da na gaya maka ne? Me Yazid yayi maka? Koma menene tsakanina da kai ne, meye nasa, Wallahi ko na rasa mijin Aure ba zan auri mutum irinka ba" tayi maganar cikin huci, ta ja jakarta ta fice fuuuu kamar iska, ta bar office ɗin, cike da ɓacin rai.
  A haraba ajinsu ta hango shi, yana tsaye shi da wasu 'yan ajinsu, fuskarsa babu wata damuwa, kamar abin da ya faru bai ɓata masa rai ba.
Ganinta a tsaye tana kallonsa ne, ya sanya shi takowa zuwa in da take tsaye "Ukty daga ina?"
So take tayi masa magana amma ta kasa, ta miƙo masa littafinsa da bironsa.
Yayi murmushi ya karɓa ya ce "Na gode, ni nama manta da na ajiye su, da sa anzo wata lectures ɗin in tuna" Kallonsa take tare da tunanin wai shi a rayuwarsa baya fushi ne, babu wani abu da yake ɓata masa rai, taje ta gama baloƙoƙo a kansa, amma shi abin da ya farun ko a jikinsa.

Juyawa tayi ta nufi department É—in su Yusra, dan tattaunawa a kan wannan matsalar.
Ta kira Yusra a waya, Yusra ta gaya mata a in da zasu haɗu. Tun da Yusra ta hango Fadila, da yadda ta ɗaure fuska ta san akwai damuwa, Fadila ta ƙarasa ta zauna tana huci.

"Baby me, waye ya taɓa mini ke ya sanya ki fushi haka?"

"Yusra zuciyata na raya mini wani abu, amma ina gudun aikatawa daga baya ace nayi laifi, shiyasa na zo wurinki".

"Subhanallaahi, me zaki aikata?"

"Wani lecture É—inmu zan saka a kama mini"
Yusra ta zaro ido ta ce "Kina da hankali kuwa?"
Chapter 48 · 0% Book details