← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 84

Sashe 22

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi Captain ma abin na Fadila mamaki yake bashi, ganin yadda duk ta ruÉ—e.

Suna zuwa aka karɓi Yazeed, cikin kulawa aka shiga da shi Emergency room, Nurse ta kawo family file ɗin su Fadila.

Doctor Aliyu ya kalli Fadila ya ce "Fadila wannan kuma a ina kika samo shi?".

"Doctor he is my class mate, ya samu asmatic attack ne, shine nace mu kawo shi nan".

Doctor Aliyu ya gyara zaman glashinsa ya ce "Dama can yana da Asma ne?".

Fadila ta ce "I don't know fa, i have no idea kawai a duba shi ni dai kar ya mutu, amma ga abokansa nan a tambaye su".

Captain ya ce "Ni dai ban sani ba, kin san ba shiga mutane yake ba, balle ayi hira ya faɗi yana da wani ciwo, ko kai Aminu ka taɓa jin ya faɗa?" Ya yi maganar yana kallon wanda suka kawo Yazeed tare.
Aminu ya ce "kai baka sani ba balle ni, ni da banda gaisawa babu abin da yake haÉ—amu".

Doctor Aliyu ya ce "Baku taɓa ganin yana shan wani magani ba?".

Captain ya ce "Doctor, bawan Allah nan fa ba magana yake ba, ba ya kula kowa ba ya son hayaniya, kaga ƙawarsa nan Fadila ita yake kulawa ita kuma ba ta saurararsa, wataƙila da tana saurararsa, da ita ya gaya mata".

Fadila ta haɗe rai ta harari Captain ta ce "Zan maka rashin mutunci ka kuma haɗani da shi, a ina na zama ƙawarsa? Yanzun ma akwai dalilin da ya sa na tsaya a kan a kawo shi Asibiti".

Doctor Aliyu yayi murmushi tare da girgiza kai, kasancewar sa family doctor É—in su, kuma nan Asibitin suke zuwa idan ba su da lafiya ya sanya ya san Fadila da halayenta. Gaba ya yi suka bishi a baya.

Suna shiga Emergency, suka tarar da Yazeed kwance an sa masa Nebulizer, yana mimmiƙe a kan gado. Gaban Fadila ya kuma faɗuwa ganin halin da Yazeed ke ciki, ta tuna yadda ta baɗe shi da ƙura da hayaƙin mota, wataƙila ma hakan ne ya sa ciwon ya tashi.

Doctor Aliyu ya cewa Aminu, ya zo ya taya shi a caje Yazeed, ko akwai magani a jikinsa, dan galibi masu irin wannan matsalar suna yawo da magani a jikinsu.
Suka caje jikin Yazeed, jotter shi ce kawai a jikinsa da biro, sai carbi da Naira hamsin, suka ajiye a drower kusa da shi.
Doctor Aliyu ya ce "Na so inga irin maganin da yake sha, amma bakomai bari mu gani zuwa anjima ko zai farfaÉ—o, na rubuta allurai a yi masa".

Fadila ta ce "Amma Aliyu, kana ganin zai warke gani nake kamar mutuwa zai yi fa" tayi maganar ƙwalla na ciko idanunta.

Aliyu ya ce "Ikon Allah, dama akwai abin da zai raunata miki zuciya haka Madam? Zai warke insha Allah, your besty will recover insha Allah, amma ki dinga kula da shi sosai, kin san ciwon nasu baya son wannan weather, banda yawo ba mask, ko zuwa wurin hayaƙi ko ƙura".
"Dan Allah ka daina haÉ—ani da shi, wai wani besty"
Yayi murmushi ya ce "To na daina"

Aminu ya yi musu sallama ya tafi gida, Captain ma yace zai je school ya dawo, suka bar Yazeed da Fadila kawai a Asibitin.
Fadila sai kaiwa take tana komowa a reception ta kasa zama wuri ɗaya, tana yi tana leƙawa ɗakin da Yazeed yake, kasa jurewa ta yi, ta shiga ɗakin da Ya ke kwance. Ta taka a hankali, ta ƙarasa gaban gadon da yake kwance, ta kalli abubuwan da aka ciro a aljihunsa, ta ɗauki jottersa da carbinsa ta saka a jakarta, saboda kar idan ya tashi, zasu tafi a manta da su.
Gani ta yi yana motsawa a hankali, ta ƙura masa idanu, tubarkallah idan ta ce Yazeed yana da muni tayi ƙarya. Gani ta yi yana rirriƙe katifar gadon da yake, yana ɗaga ƙirjinsa sama, sai kuma ya saki katifar, yana miƙe mata hannu, amma idanunsa a rufe.
Ƙara matsawa ta yi jikin gadon, tana masa sannu, sai dai bai san me take yi ba, hasali ma bai san meye yake yi ba.
Sai miƙa hannu yake yana riƙo duk abinda ya ji a kusa da shi, cikin sa'a ya riƙo hannun Fadila, hannunsa kamar ba na namiji ba, saboda taushi, sai ta zama kamar wata sokuwa ta rasa abin yi, a hankali yake murza yatsunta, yana jujjuya kansa, hawaye na zuba a gefen idanunsa, ga wani irin gumi da yake tsatstsafowa a goshinsa.
Fadila zama ta yi tamkar wata gunki, wani irin abu ne ya fara kai kawo a jikinta, tun daga kanta zuwa ƙafafuwanta, wani baƙon yanahu ya ziyarce ta, tsigar jikinta na tashi, wani irin yanayi na ratsata, saboda a rayuwarta idan ba Khalil ko Daddy ba, babu wani namiji da taɓa samun wannan kusancin da shi haka, har hannunta a cikin nasa, sai doctor Aliyu, idan ba ta da lafiya zai mata allura ko sa ruwa, shi ma faɗa suke yi da shi, ta ce "Ba zai taɓa ta ba".

Ƙoƙarin zame hannunta take daga na Yazeed, cikin jin zafin ciwo ya matse mata yatsu da ƙarfi, wanda har sai da ƙasusuwan yatsunta suka yi ƙara.
"Washhh Allah, kai dalla ka sakar mini hannuna sai ka karya ni tukuna?" Ta faɗa a shagwaɓe.
Ƙoƙarin miƙewa zaune Yazeed ya fara yi, ya kai hannu zai cire abin Nebulizer, ta riƙe hannunsa ta ce "Ka bari magani fa aka samaka" ta faɗa raunane.
Bai saurareta ba ya cigaba da ƙoƙarin cirewa, da sauri ta fita ta kirawo doctor Aliyu, har Yazeed ya cire Nebulizer ya kifa ya kusa faɗowa daga kan gadon.
Da hanzari Aliyu, ya gyara masa kwanciyar ya mayar masa da Nebulizer, ya je ya É—auko wata allura ya yiwa Yazeed. A hankali bacci ya kwashe shi.

Aliyu ya ce "Gaskiya ciwon nan nasa ya zama chronic, ki kirawo masa wani daga gidansu mana, a san halin da yake ciki".

"Ni ina na san wani nasa, É—an ajinmu ne fa kawai".

"I see, amma kin damu da shi da yawa".

"Ni ban damu da shi ba, kawai dai na san koma menene ya sameshi nice sila, idan ya mutu zan iya cewa ina da hannu a ciki shiyasa na damu".

"Shikenan, ki zauna tare da shi, duk abin da kika gani ki mini magana".

Fadila ta ce "to"

Ta koma ta samu kujera, ta zauna a kusa da gadon nasa, ta ɗauko wayarta ta hau chatting da Yusra, a nan take bawa Yusra haƙuri, saboda rashin zuwanta gidansu, kuma ta bata labarin abin da ya faru.

Amina na ɗakinta, sun kammala aiki tayi wanka, ta shirya tana ƙara gyara nata ɗakin, Hajara ta yi sallama. Amina ta amsa tare da kallon Hajara.
"Ki je in ji Khalil".
Amina ta ce "Waye kuma Khalil?".
"Wanda zai kai ki makaranta"

Ta buÉ—e baki ta ce "Haba da gaske?".

Hajara ta ce "Zan miki ƙarya ne?"

Kan Hajara ta gama rufe baki, Amina ta yi waje, ta nufi falo. Ta tarar da Khalil ya kammala breakfast, Hajiya Zainab na zaune a kusa da shi tana masa hira.

Amina ta ƙarasa ta durƙusa a gabansa ta ce "Gani".

Bai kalleta ba ya ce "In the next 30minutes, ki shirya zamu je a kai ki makaranta"
Washe haƙora Amina ta yi cikin murna ta ce "Tom, Na gode Allah ya saka da alkhairi, ai ni na shirya ma, bari in je in jiraka".
Hajiya Zainab ta kalli Khalil ta ce "Ban gane ba, kai ne zaka kaita makaranta?, ka bari babanta ya dawo ya kai ta mana".
Khalil ya ce "No, kin san bakomai zai iya yi mata ba, Daddy ne ya bada umarnin hakan".
Tsaki ta yi ta ce "Ni bana son irin haka, a É—orawa mutum wahalar da ba ta sa ba, ba damar ka janyo mutum É—aya, sun dinga É—ora maka É—awainiya da wahalarsu kenan".
Amina da ba ta kai ga barin falon ba, tana jin hajiya Zainab, amma tayi shiru ta wuce É—akinta, ba tare da ta yi magana ba.

Tana zuwa ɗaki, ta canza hijjabi, ta ɗauko littafi ɗaya a litattafanta da ta taho da su daga ƙauye, da bironta ta samo leda ta zuba su a ciki, ta ɗaure murmushin kan fuskarta ya kasa gushewa.

Hajara sai kallon Amina ta ke "Amina sai kace wadda aka yiwa bushara da zuwa makka, wannan fara'a haka".

Murmushi Amina ta yi ta ce "ni dai na tafi, sai na dawo" tayi waje a guje cike da farinciki. Wuri ta samu a nan harabar gidan ta zauna, tana jiran Khalil, ba ta wani daɗe ba saiga shi ya fito da waya a kunnensa yana waya, bai kula Amina ba ya nufi hanyar gate zai fita, ba ta da zaɓi illa ta tashi ta bi bayansa.

Abdul ne zaune a cikin motarsa, ya ƙurawa gate ɗin ido. Khalil ya ƙarasa ya buɗe gaban motar, ya shiga.
Amina kuwa tsaye ta yi, tana zazzare ido, Abdul ya miƙa hannu, ya buɗe mata motar, ta shiga ta zauna sannan ta risunar da kanta ta ce wa Abdul "Ina kwana?".
"Lafiya ƙalau, ya kike ya gida?".
"Ina lafiya ƙalau Alhamdilillah".
"To Masha Allah, sannunki" ya mayar da dubansa kan Khalil da ke danna wayarsa ya ce "Malam ba gaisuwa ne?"
Hararsa Khalil ya yi ya ce "Dan Allah ja mu tafi, anƙi a gaishe kan".

Abdul ya ce "Haka ka iya, sarkin faɗa" A hankali Abdul ya ja motar suka fara tafiya, cikin motar ga sanyin AC, ga ƙamshin turaren jikinsu, ga ƙamshin droomer, duk ya cika motar, yanayin ya yiwa Amina daɗi sosai, sai kallon gari take ta jikin baƙin glass ɗin motar.

Gaba ɗaya tsarin zubin ginin makarantar ya sha banban da irin zubin makarantunsu na ƙauye, ginin kawai ba ƙarmin burge Amina ya yi ba.
A wurin parking Abdul ya tsayar da motar, Amina na ƙoƙarin buɗe motar, Abdul ya ce "Ki zauna muje mu fito tukuna, ni ya sunanki ne ma?".

"Amina Hassan"

Ya ce "Masha Allah, nice name, ki zauna muje mu dawo".

Amina ta amsa da to. Abdul da Khalil, suka nufi dogon ginin da ke cikin harabar makarantar.
Chapter 22 · 0% Book details