← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 84

Sashe 51

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu ne lokacin da yakamata ka zo aji? Ni in baro gidana tun bakwai takwas tayi mini a nan, amma ka zo yanzu kuma kai tsaye ka ce zaka shigo mini aji?"

"Ayi mini afuwa malam, insha Allah ba zan sake ba"

"Sorry for yourself malam, ɓace mini daga nan"

Yazid ya yunƙura zai kuma magana, amma malamin ya buga masa tsawa ya kore shi.

Duk iya wulaƙanta mutum da Fadila ta ƙware a kai, taji babu daɗi yadda malamin ya kyari Yazid ya koreshi, ga shi 'yan aji gaba ɗaya sun zuba masa ido, duk da Yazid mai sa'a ne a wasu lokutan, kuma mutum mai haƙuri da ladabi, amma wasu lokutan yana yawan shiga komar malamai su wulaƙanta shi. Duk da Yazid ya bar ajin, hakan bai hana malamin cigaba da ƙananan maganganu, a kan Yazid ba.

Bayan fitar malamin daga ajin, Yazid ya shigo ya samu wuri ya zauna, ba tare da ya kalli kowa ko ya kula wani ba.

"Kowa ya tabattar ya mallaki littafin da Sir Bello ya ce a saya, dan da alama wani abun yake shirya mana a kan littafin nan, zai iya kada mutum idan ba shi da shi a jarrabawa, dubu uku ne, ga takadda nan ta na zagawa, duk mai so ya rubuta sunansa, na bada aron kuÉ—ina naje kasuwa na sayo mana, duk mai so sai ya bada kuÉ—insa in bashi" Cewar Captain dake tsaye a gaban ajin, yana bayani daki-daki kamar me koyar da karatu.
Tana hangen Yazid daga in da take zaune, kamar mara lafiya, sai ya kifa kansa a kan benci, sai kuma ya tashi yana É—an lumshe idanunsa yana buÉ—ewa, idanun duk sun yi ja, sai tayi tunanin ko duk dan saboda abin da lecturer yayi masa ne.

Aka miƙawa Yazid takarda, ya rubuta sunansa in zai sai littafi, amma ya girgiza kansa, ya mayar da kansa ya kifa kamar yadda yake da farko.

Da takardar ta zo kan Fadila, sai ta sayi kwafi biyu a take, É—aya nata É—aya na Yazid, amma tana jinjina yadda zata bashi littafin, dan bata son yawan shiga sabgarsa.
Tana nan zaune taga ya tashi ya fita, ita ma ta tashi ta bi bayansa, tana biye da shi, ba tare da ya sani ba, taga ya shiga wani aji da babu kowa, 'yan ajin suna wurin excursion, mutanen da ke ajin 'yan tsirari ne, wasu na cin abinci wasu na abin da ya damesu.
Wuri ya samu can ƙarshen ajin, ya je ya samu wuri ya zauna ya kifa kansa.
Ta tsaya daga bakin ƙofa tana saƙawa da warwarewa, daga bisani ta yanke shawarar shiga.
Har taje inda yake bai ɗago ba, ta saka hannu ta ɗan daddaki ka bencin da yake kai. A hankali ya ɗago ya kalleta, idanunsa sun yi jawur, ta kalli ƙafarsa tayi futu futu, kamar wanda yayi tafiya a sahara.
Sauke mask ɗin fuskarsa yayi, tare da sakar mata murmushin ƙarfin hali "Ya aka yi kika san ina nan?"

Ɗan taɓe baki tayi, ta saka hannu a jakarta, ta ɗauko littafin da ta saya masa da handout ta ajiye masa "Gashi nan, kuma ya rarraba group a aji, ya bada assignment za'a yi presentation next week in Allah ya kaimu, na saka sunanka, sai kaje ka dudduba handout ɗin"
Zuba mata idanunsa yayi gaba É—aya amma ya kasa magana, sai kallonta kawai da yake yi.
"Magana fa nake maka, amma ka zuba mini ido".
A hankali ya ce "Yi haƙuri zan yi magana, numfashina ne yayi mini nauyi"
A É—an tsorace ta kalleshi "Jikin ne?"
Lumshe idanunsa yayi, ina ma yana da damar gayamata abin da yake damunsa, rabonsa da Abinci tun kunun jiya da safe, Ulcer ta riƙe masa ciki da ƙirji har bayansa, haka ya lallaɓa ya taso ya taho Makaranta da wuri, saboda saurin da yake yi, yaji numfashinsa yana isa huhunsa da ƙyar, a wahale ya ƙaraso makarantar.

"Yazid" ta kira sunansa, karo na farko da yaji sunansa a harshen Fadila, wanda kiran sunan nasa ba ƙaramin tasiri yayi a zuciyarsa ba, ya haifar masa da wata nustuwa ta mussaman ba.

"Kaje Asibiti ne?"

"Eh na sha magani" ya bata amsa da ƙyar, dan baya son yin ƙarya ko kaɗan.

Ya jingina da teburin, ya lumshe idanunsa, ita kuma ta tsaya a tsaye, ita bata zauna ba ita bata tafi ba tana kallonsa.

Kamar wadda aka yiwa dole, ita a lallai bata damu da shi ba ta ce "Ko zaka tafi gida ne?"

Ya girgiza mata kai ya ce "Zan ji sauƙi yanzu insha Allah, ganinki ɗin nan ma kawai ya sanya mini nutsuwa da jin na warke" tsuke fuska tayi ta harare shi, tare da ɗan hura hanci.

"Allah ya sawwaƙe, ni na tafi" ta juya ta nufi hanyar ficewa, ta bar masa handout ɗin da littafin ya zubawa bayanta ido, har ta bar ajin.

Ɓangaren Amina kuwa, bayan tayi wanka ta nemi abin da za ta ci taci, bayan ta tabattar da an kaiwa Baba nasa Abincin, ta koma ɗakinta ta ɗora da rubutun Alqur'ani da take yi.
Sai wajen azahar sannan Amina ta fito, ta haɗa wanke wanke tayi, tare da gyara duk in da aka ɓata, duk da Hajara taji haushin yadda yau Amina taƙi kataɓus ta sha baccinta, haka ta jure ta danne fushinta, saboda ita ma Aminan ba ta mata ƙorafi.
  Yau Alhaji Ahmad a gida ya wuni, sai ƙarfe huɗu sannan ya shirya zai fita, yau ba da Zakiru direba zai fita ba, shikaɗai zai fita, ya shiga motar, yana ƙoƙarin kunnawa, ya hango Amina a wurin Baba, riƙe da littafi, tana ta aikin nata na surutu, tana yi tana kallon littafin hannunta, Baba kuma yana ta ɓare gyaɗa yana miƙa mata, tana karɓa tana ci.
Ya ɗan jima a zaune a cikin motar yana kallonsu, gwanin sha'awa, ita 'ya mace duk in da Allah ya baka ita, ya baka Sarauniya ko da kuwa kai ba sarkin bane, Alhaji Ahmad yana son yaga ana tattala mace,baya son ya gansu a wulaƙance, shiyasa yake matuƙar ji da Fadila, shi namji duk in da yake zai iya kula da kansa, amma mace tana buƙatar kafaɗar da zata jingina.
Sai karɓe gyaɗa take daga hannun Baba tana ci, tana nunawa Baba littafinta, duk da Baba mutumin karkara ne, kuma ba wanda yayi ilimin zamani ba, amma wasu lokutan yadda yake gudanar da rayuwarsa a waye, ba girman kai ba hayaniya.
A hankali ya fara jan motar, zuwa wurin gate, daidai in da suke ya tsaya da motar, Baba ya taso da sauri, ya tsaya jikin motar ya risuna yana gaida Alhaji Ahmad, Ya amsawa Baba cikin sakin fuska, Amina ta wani basar, kamar bata san da wanzuwarsa a wurin ba.
"Aminatu ina wuni" Alhaji Ahmad ya faɗa lokacin da ta ɗago suka haɗa ido, tana ƙoƙarin mazewa ta kau da kanta.

Baba ya ce "Ja'ira ke wace irin Yarinya ce Uwata, baki iya gaisuwa ba?"

"Yi haƙuri, ina wuni?" Ta faɗa a kunyace.

"Ƙyaleta malam Hassan, tun da bata gaisheni ba, ai gara ni in gaisheta, tawa gaisuwar zaki amsa"
Amina tayi shiru cike da kunya, dan ta san bata kyauta ba sam.

"Zo" yayi Maganar yana kallonta.

Ta tashi daga kan bencin, ta matsa jikin motar.

"Meyasa baki je lesson ba yau?"

"A makarantar aka ce mu huta yau" ta bashi amsa tana kallon ƙasa.

"Kina gane karatun dai ko?" Ta É—aga kai alamar eh.

Alhaji Ahmad ya kalli Baba ya ce "BuÉ—e mini gate É—in"
Baba ya amsa da to, ya tafi buÉ—e gate.

Ya sake mayar da dubansa gareta ya ce "Me zaku dafa yau da daddare?"

"Hajiya ta ce, a dafa kuskus da miyar ganye" ta bashi amsa tana kallon ƙasa

Alhaji Ahmad ya ce "Likita ya sanya mini ƙa'idoji, saboda sugar na da ya hau, ki dafa mini faten dankalin turawa, da alayyahu, zan yi dinner da shi, yau zaki karatun dare ne?"

"Eh insha Allah"

"Idan na dawo, zan miki magana ki kawo mini"

Ta jinjina masa kai, shi kuma ya ja motar ya fice.

Har aka yi lectures aka gama, Fadila na ankare da Yazid, a hankali yake komai, bashi da lafiya, faɗa ne ba zai yi ba, gefe guda kuma ta danganta abun da wulaƙanci da malamin ɗazu yayi masa, sai kuma ta tuna Cewar abu ne mawuyaci, kaga wani abu mai kama da fushi a tare da Yazid kome za a yi masa, wannan murmushi dai sai ka ganshi a fuskarsa.

Amina ta koma cikin gidan, tayi sallar la'asar, ta shiga kitchen, dan ta san babu lallai Hajar ta kuma yin wani abun, tunda kusan ita tayi aikin yau.

Tun azahar Fadila ta dawo gida, dan har tayi wanka ta kintsa ta dawo falo ta zauna, suna hira da Mummy.
Da sallama aka buɗe ƙofar falon, daga Mummy har Fadila suka mayar da hankalinsu kan ƙofar, wata farar mata ce ta shigo, ita da wata matashiyar budurwa, suturar da ke jikin matar kawai ya isa ya nuna maka Arziƙi ya zauna.
Suka yi sallama, Hajiya Zainab ta amsa tana bin su da kallon rashin sani.
Suka ƙarasa cikin falon suka zauna, suka gaisa da Hajiya Zainab, ta amsa ba yabo ba fallasa, dan suma taga ba kalar talakawa bane.
Matar ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Na san ba zaki shaida ni ba, wannan 'ya ya ce Azima, suna Makaranta ɗaya da yarinyarki Amina, na shigo nan unguwar wurin wata ƙawata, Azima ta nuna mini gidan, nace bari in tsaya mu gaisa"
Mummy ta haÉ—e rai ta ce " 'yar aiki dai ko?"

Maman Azima ta ce "Eh to hakan, ai É—a na kowa ne, dan in saya ya sanya na ce 'yar ki"

"A 'a ba wata sayawa, meye haɗina da ita da zaki jingina mini ita wai 'ya ta? Aiki kawai take mini" Mamaki ya kama maman Azima, yadda Hajiya Zainab ke zaƙalƙalewa, tamkar wadda aka dangantawa ɗan shege.

"To shikenan na fahimta, 'yar aikin ki, mu gaisa sai in wuce"

A wulaƙance Mummy ta ce "Sai ku jira ta fito, dan dai bani zan tashi in tafi yawon kira muku ita ba, ko kume tashi kibi wannan ƙofar, kitchen na nan, ki kirawota" tayi maganar tana kallon Azima.
Chapter 51 · 0% Book details