← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 84

Sashe 74

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fadila ta ɗanyi shiru sannan ta ce "Mummy, bana tunanin sace Yaya Khalil aka yi, wataƙila ya tafi wani wurin ne dan huce haushin abinda kika yi wa yarinyar da yake so"

Cikin mamaki Hajiya Zainab ta ce "Kuma haka ne ko? Yanzu sai Khalil ya bar gidan nan ya tafi wani wurin ba tare da na sani ba saboda haka? Aikuwa idan haka ne da ya ci ubansa, sai na nuna masa nice uwarsa kuma dole ya bini"

"Mummy kibi a hankali, kar garin neman gira a rasa ido"

"Rabu dani da wata ido da gira, zan cigaba da bincikawa muddin na tabbatar haka ne idan bai yi wasa ba saina ci mutuncinsa".

"Amma me Daddy ya ce?"

"Rabu dani da Daddyn nan na ku, nayi masa Magana amma bai mayar da abin serious ba, wai Khalil ba yaro ne ƙarami ba, duk in da yaje zai dawo kar in damu kaina"

"Mummy, gaskiya Daddy ya faÉ—a, ki kwantar da hankalinki zuwa Allah ya kaimu da safe mu ga yadda hali zai yi"

Jinjina kai Mummy ta yi ta bar É—akin Fadila, gaba É—aya ta rasa nutsuwarta saboda rashin sanin halin da Khalil yake ciki, da kuma a ina yake, ta É—ora alhakin duk wannan abun a kan Hafsa, wadda take can tana fama da kanta.

Da safe wajen ƙarfe tara na safe, Mama ta shirya ta dafawa Hafsa ruwan wanka, da ƙyar Hafsa ta rarrafa tayi wanka, kasa cin Abincin ma ta yi, Mama ta taimaka mata, ta shirya suka tafi Asibiti.
Tashin farko teses kawai sun yi na dubu biyu aka rubutawa Hafsa, aka yi mata likita ya tabbatar da jininta ya hau, ga malaria mai zafi da ulcer.
Mama ba tayi mamaki ba jin Hafsa tana da hawan jini, likitan ya ɗan nazarci fuskar Hafsa sannan ya ce "Ƙanwata meke damunki a 'yan shekarunki kika kamu da hawan jini, jininki ya hau fiye da yadda za a iya cewa ko zafin zazzaɓin ne ya sanya jinin ya hau"
Hafsa ta sunkuyar da kanta, tana muza yatsunta na hannu.

"Magana fa nake" ya sake maganar yana É—an dukan teburin gabansa.

Hawaye ne ya taru a idon Hafsa, Mama ta ce "Likita rabu da ita kawai, duk saboda ta rabu da wani saurayinta, shi ne ta saka kanta a uku, nayi nasihar nayi rarrashin amma ta saka abin a ranta"

Likitan ya ce "Mahaifiyarta ce ke ko yayarta?"

Mama ta ce " 'ya ta ce"

Likitan ya ce "Ba abune mai sauƙi ba Hajiya, musamman ga mu mutanen wannan zamani, muna bawa soyayya muhimmanci sosai da sosai, dole zata shiga damuwa, saboda abun ba sauƙi amma kiyi haƙuri ki cigaba da Addu'a ko kina son Mama ta rasaki at your young age, ko ki kamu da ciwon zuciya?" Hafsa ta ce "A'a"

"Tukuna ma, gaya mini sunansa, sannan maiyasa ya yaudareki?"

"Ba yaudarata yayi ba"

"Ok na gane, kin san kowane bawa, akwai rubutacciyar ƙaddararsa, kiyi haƙuri, ga magunguna nan da ruwa, zan riƙe ki a Asibitin nan tsawon kwanaki biyu, sai naga jikinki yayi kyau, jininki kuma ya sauka"

Mama ta yiwa likitan godiya, da jin daɗin yadda ya nuna damuwarsa ga Hafsa, ta riƙe Hafsa suka fita ma'aikatan jinya suka basu gado, Mama taje ta biya kuɗin, da kuma sayo magunguna.

"Baban Fadila nifa ban gane manufarka ba, yaya zan gaya maka ban san in da yaro yake ba, amma ko a jikinka"

"To yaya zan miki ni? Khalil dai ba yaro bane ba ƙarami, da hankalinsa kuma ke da bakinki kika gaya mini abin da kika yi masa, dan haka yayi wani wurin ne, dan yaje ya ji da tension ɗin da kika saka masa"

Cikin ɓacin rai ta ce "Kana nufin saboda na rabashi da 'yar matsiyata shi ya sanya zai bar gida ban san in da ya tafi ba? To wallahi ko zai mutu ba zai kawo mini jinin tsiya a matsayin sirika ba, zai ga yadda zan yi da shi, bai isa ba wallahi"

Daddy ya ce "Dan haka sai ki daina tayar mini da hankali a kansa, matsla ce da kika kunnota ke zaki maganinta"

"Au haka ma zaka ce?"

"To me zance ni?"

"Zaka ga me zaka cex" ta bar falon Daddy Fuuu ranta a ɓace.

Amina har ta tafi makaranta Baba bai dawo ba, bata san ya aka yi ya tafi ƙauye ba sanarwa ba, bai gaya mata zai tafi ba suka haɗu da Safe tayi masa sallama zata makaranta, amma bai gaya mata cewar za shi ƙauye ba, sai da ta dawo daga makaranta.
Tayi ta ƙoƙarin kiran wayarsa, amma wayar bata shiga, sai ta shiga damuwa tana fatan Allah ya sanya komai lafiya.

Haka ta dawo daga makaranta tana sa ran ganin Baba, amma ta dawo ta tarar bai dawo ba.

Sai wajen la'asar sannan Baba ya dawo, Amina ma bata san ya dawo ba, kawai ta fito da niyyar ta duba ko ya dawo ta tarar da shi yana salla.
Murna ta dinga yi tana godewa Allah, da ya sanaya yana lafiya.

Ta jira ya idar da sallar, yayi Adduoinsa sannan ya kalleta ya ce "Uwata ya makaranta?"

"Lafiya lau Baba, amma baka gaya mini zaka tafi ƙauye ba, sai da na dawo nake ji jiya"

Baba ya ce "Eh, tafiyar ce ba ta shiri ba, nayi ta ƙoƙarin ma in kira wayarki in haɗaki da babarki, amma wayar taƙi shigowa"

Amina ta ɗan ɓata fuska ta ce "Kash, nima nayi ta ƙoƙarin kiranka amma ba ta shiga, Baba dan Allah ka saiwa Inno waya, in dinga jin muryarta"

Baba yayi murmushi ya ce "ai na bayar a saya mata, har layi na bawa Saminu nace ya sai mata mai É—an kyau wadda zata iya gane kanta"

Amina tayi murmushi ta ce "Yauwa Baba, yaya ka baro su, ya kowa da kowa"

Baba ya ce "Duk suna lafiya suna gaisheki, Sa'a an saka bikinta. Mun yi magana da Alhaji Ahmad, yayi mini maganar zuwanki birnin tarayya a kan harkar karatunki, da fari dai na ɗan yi jayayya amma daga baya ya mini bayani na amince, ina fatan zaki kula da kanki Amina, ki riƙe mutuncinki, ki tuna ke ba 'yar kowa bace, ki kula da tarbiyyar da muka baki"

Washe baki Amina ta yi ta ce "Baba, ka amince inje É—in?"

"Eh uwata, na amince ina miki fatan alkhairi, sannan ya ce mini zaki gida kiga gida kuma kiyi musu sallama, saboda doguwar tafiya zaki yi"

Hawayen farinciki suka cika idanun Amina, ta kalli Baba ta ce "In Allah ya yarda ba zan baka kunya ba Baba, zan kula da kaina, ka mini Addu'ar samun nasara"

"Addu'a ai kullum cikinta nake, Allah ya yi miki albarka, ga kayayyaki can babarki ta haÉ—o wai in kawo miki"

Cikin murna Amina ta nufi wurin kayan da Baba ya nuna mata, ta É—au ledar Vivan, tana jin yadda take jin kewar Inno a ranta.

Har zata fita daga É—akin Baba ya ce "Yauwa na haÉ—u da wannan malamin naku na makarantar boko, na manta sunansa, ya cc in gaisheki"

"Laa Malam Sunusi?"

"Eh shi"

"Allah sarki, ina amsawa, yauwa Baba a kawo Abinci ne, ko in dafa maka wani abun?"

"A'a ba sai an kawo ba, nan da kika ganni a ƙoshe nake"

Amina tayi murmushi ta juya ta bar É—akin Baba.

A falon gidan ta tarar da Hajiya Zainab tana kaiwa tana komowa a falon, da waya a hannuta kamar ka taɓata ta fashe sai cika take tana batsewa.
Tana ganin Amina da leda ta ce "Ke!" Amina ta tsaya tare da kallon in da Hajiya Zainab take.

Cikin kaushin murya ta ce "Daga ina kike?"

"Naje wurin Baba ne ya dawo" Amina ta bata amsa.

"Maza kije ki kira mini shi, dama shi nake jira" tayi maganar tana hura hanci.
Sai da Amina ta É—an tsaya tana kallon Hajiya Zainab, tana son gano dalilin da ya sanya take son ta kira mata Baba.

"Ba zaki je bane kika tsaya kina kallona haka?"

Amina ta ajiye ledar hannunta, ta juya ta fita, tun daga nesa Baba ya hangota ta nufo shi, fuskarta a haɗe, tsayaqa6 yayi yana jiran ƙarasowarta.

"Uwata lafiya naga kin dawo?"

"Matar gidan ce ta ce na kiraka"

Baba ya ce "To, Allah ya sa ba wani laifin ki ka yi ba, ko ni nayi ba"

"Nima ban san meye ya sa take nemanka ba"

"To muje, koma meye sai na ji"

Suka rankaya suka nufi falon.

Suka shiga Baba yayi sallama, amma Hajiya Zainab tayi biris tana ta wani kumbura wuya kamar kasa. Ta ƙarewa Baba kallo a wulaƙance, irin kallon yake ƙonawa Amina rai.

"Jiya da yaushe ka bar bakin gate É—in nan?" Ta jefowa Baba tambayar.

Cikin girmamawa ya ce "Sai goma na safe ranki ya daÉ—e?"

"Kenan kana nan Khalil ya fita?"

"Eh, nina buɗe masa ƙofa, bayan sallar Asuba ya ɗau mota, na buɗe masa ƙofa ya fita".

"Wane irin mutum ne kai da zaka buɗe masa ƙofa ya fita bayan sallar Asuba, ina ya ce maka zai tafi?"

"A'a Hajiya, bai gaya mini ba, ko gaisawa ba muyi ba ya fita"

Wani uban tsaki ta ja, sannan ta ce "Kai dai banga amfaninka a zaman gadin nan ba, tayaya yaro zai fita bayan sallar Asuba, amma ka kasa tambayar ina zai tafi"
Ikon Allah Amina ta tsaya tana kallo, aikin Baba buÉ—ewa da rufewa to meye huruminsa na sanin in da wani zai je a gidan?

"Yaya dai meke faruwa ne?" Suka jiyo muryar Alhaji Ahmad, da ya fito yana ta zuba ƙamshi cikin wani vowel baƙi.

Ya kalli Baba Hassan da ke tsaye fuskarsa cikin damuwa, ya risunar da kai kamar mai neman gafara.

"Malam Hassan, ka dawo ashe?"

Baba ya ce "Eh na dawo ranka ya daÉ—e"

Baba ya Kalli Mummy ya ce "Meke faruwa ne?"

"Ka jiye mini wannan rainin hankalin mana, wai Khalil ya fita daga gidan bayan sallar Asuba amma ya kasa tambayarsa ina za shi ko ya sanar mana, ni na gaji da sokoncin wannan mutumin"

"Sokonci kuma?" Amina ta tambaya rai a ɓace.
Chapter 74 · 0% Book details