← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 84

Sashe 41

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tun da kake a gidan nan ka taɓa ganin an sa kuɗi an sai wanna abar? Saboda kalan yunwa da nemawa kai masifa shine kaje ka saya kana sawa a cikinka, baka san da yadda aka yi ta ba, ke zoki ɗauke wannan a bar kuje ku cinye ta" tayi maganar cikin tsawa tana kallon Amina.

Mamaki ne ya kama Amina, duk a kan awarar ake wannan tashin hankalin, wato idan ma abun mutuwa ne su suci su mutu kar ɗanta ya ci. Khalil yana ji yana gani, Amina ta ɗauke awarar kitchen ta kai awarar ta ce "Aikuwa ba zamu ci ba, shi ɗin ne zai cinye a barsa, wannan matar lamarin nata ya wuce tunani" Khalil yayi fushi ya bar Falon, dan ba ƙaramin daɗi awarar tayi masa ba, dan da gani ta musamman ce Hafsa tayi masa.
Ta ƙofar corridor Amina tabi, taje ta ƙwanƙwasawa Khalil ƙofa. Kamar ya share sai kuma ya buɗe.

Amina ta miƙa masa plate ta ce "Ga awararka nan na kawo maka, Naga kana so" ya ɗan ƙura mata ido sannan ya karɓa ya ce "Na gode sosai".

"Never mind" ta faɗa a taƙaice ta juya ta koma.

Fadila tai ta jujjuya maganganun Yusar a kan Yazeed, ƙarshe kawai tayi tsaki ta bar zancen Yusran a shiririta.
Sai dai ba abinda ya sauya, daga yawan mafarkin Yazeed da take yi.

"Baba ga karin kumallo na kawo maka" Amina tayi maganar hannunta riƙe da wani ɗan madaidaicin faranti, tana kallon Baba.
"Yauwa uwata, Allah ya yi miki Albarka".
"Ameen, amma ya aka yi naga idonka yayi ja?"
"Mura ce ta sakani a gaba, ta saka mini ciwon kai da zazzaɓin dare".
Cikin kulawa Amina ta ce "Baba to ka karya sai in raka ka Asibiti mana".
"A'a uwata, zan warware insha Allah, zan dafa rai ɗore in sha, na kuma karɓo magani a Chemist"
"Baba gara dai muje Asibitin"
"Ki bari idan ban warke ba zuwa gobe in Allah ya kaimu sai inje" ya ƙarasa maganar tari na taso masa"

"Sannu Baba, ka karya sai ka kwanta, hannunka ma ya É—au zafi sosai".

Baba yana tsaka da karyawa, Fadila ta fito tana ta wani hura hanci, ta yiwa Baba alama da yazo.
Baba na shirin tashi, Amina ta ce "Baba zauna, bari ni naje" ta tashi ta nufi in da Fadila take.

Fadila ta kalleta a wulaƙance ta ce "Ba ke nake kira ba, Babanki nake kira".

Amina ta ce "Bashi da lafiya ne shiyasa na zo".

"And so? Baki ji me mace bane babanki nake kira bake ba" ganin kamar suna jayayya ya sanya Baba tasowa, ya ƙarasa in da suke tsaye ya ce "Gani".

Fadila ta kalleshi ta miƙa masa kuɗi ta ce "Gashi nan, kaje ka tari Napep kaje gidan su Yusra zata baka saƙo ka kawo mini"

Amina ta ce "Ni ki kwatanta mini gidan sai inje, Baba bashi da lafiya fa".

Cikin tsawa Fadila ta ce "Nace Babanki na aika bake ba, karki sake saka mini baki a maganata"

"Kiyi haƙuri dan Allah ni ki aike ni, jikinsa da zazzaɓi"

"Baban naki ma ya aka cika idan an aike shi, shi da ya daɗe a birni balle ke bagidajiya 'yar ƙauye kije gidan mutae kiyi musu hauka da jahilicin naki da kika saba ki zubarwa da mutane mutunci"

Baba yayi gyaran murya ya kalli Amina ya ce "Uwata, ai jikina da sauƙi sosai Alhamdilillah, bari inje maza jeki ɗau Abincina ki rufe mini yanzu zan dawo" Baba ya juya ya nufi gate, yana takawa a hankali saboda jikinsa ba daɗi.
Fadila kuma ta koma ciki abunta, Amina kuwa tamkar an dasata, sai ma wasu hawaye masu zafi da suka fara biyo kuncinta.
Tana nan tsaye Alhaji Ahmad ya fito, cikin suffarsa ta kwarjini da kamala, tun da ya fito Amina ta zuba masa idanuwa, har sai da ya tsargu, amma har ya gifta ta ko gaishe shi bata iya yi ba.
Ya wuce ya hau motarsa, wannan karon ba direba da kansa yake tuƙi, Zakiru ya buɗe masa gate ya fice.

"Tabbas kan in bar gidan nan, sai nayi maka abin da har 'yarka ta koma ga Allah ba zata manta ba, sai taji abin da nake ji idan taci zarafin mahaifina".

Ayshercool
08081012143
GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143

*Littafina Aƙidata da kuma Ruɗin ƙuriciya, na kuɗi ne, sauran duk free me*

18-19

Amina ta ja jikinta a hankali, ta koma wurin zaman Baba ta zauna, tana jin yadda sanyi ke ratsata, wani irin tausayin Baba ya mamaye zuciyarta, Allah kaɗai ya san irin ƙalubale da wulaƙancin da ya dinga fuskanta a gidan nan, amma yake dakewa yana shanyewa.
A ƙalla Amina ta shafe awa guda a zaune, amma Baba bai dawo ba, haka ta tashi ta koma cikin gidan, zuciyarta na mata ƙuna game da abin da Fadila ta yi wa Babanta.

Ta tagar corridor Amina ta hango Baba ya nufo hanyar shigowa cikin gidan.
Da sauri ta fito falo, idon Baba duk yayi ja, saboda yadda ya sha ƙura a hanya. Fadila kuwa na zaune sai kaɗa ƙafa take, tana latsa remote hankali kwance.
Baba ya ƙaraso ya ɗan risuna yana miƙa mata ledar hannunsa.
"Wai kai dan Allah duk lokacin da aka aikeka, sai kaje kai zamanka?"

"Yi haƙuri ba haka bane, titunan ne akwai cunkoson ababen hawa, mussaman yau da aka tashi da hazo".

"Ajiye a wurin ka je, Na gode" ya ajiye mata ya miƙe, Amina ta fito ta biyo bayansa, amma Fadila ta kalleta ta ce "Ke zo nan" Amina ta tsaya cak ta waiwayo tana kallon Fadila.

"Akwai undeas ɗina a toilet, ki je ki wanke mini, sannan ki sauke jakunkuna na daga hanger duk ki goge mini su" Wani abu mai ɗaci ya tsirgawa zuciyar Amina, Baba ya kalleta yayi murmushi, yana gyaɗa mata kai cikin bata ƙwarin gwiwa da kwantar mata da hankali.

Amina ta juya ƙafafuwanta suna rawa, ta nufi sashin Fadila.

Sai da Hafsa ta yiwa Khalil mita a kan kuɗi da ya bata haka da yawa, ta dinga mita tare da cewa ya zo ya karɓi kuɗinsa, a karo na farko da ya nuna mata ɓacin ransa tun bayan haɗuwarsu, sai kuma taji babu daɗi dan ƙarshe ma kashe wayarsa yayi.
Sai da ya wuni be kirata ba, idan ta kira shi kuma yaƙi ɗagawa, gaba ɗaya ta shiga damuwa.
'Kenan da gaske na fara son Khalil? Idan kuma ya san wacece ni ya ƙi aurena fa ya zan yi?' ta tambayi kanta, take kuma taji kanta yayi mata wani irin dumm babu daɗi, ta shiga taradaddin halin da zata shiga idan Khalil ɗin ya kasa ɗaukar ƙaddarar da ta faɗa mata.
  Kasancewar an tashi da hazo sosai, ya sanya Hafsat take ta kula da Mama, dan kar ta fito tsakar gida ko tace za tayi wani aiki, saboda yanayin jikinta, ba ta da cikakkiyar lafiya, amma hakan bai hana tari ya sarƙe Mama ba, duk wani taimako da Hafsa zata iya bata ta bata, amma abu yaci tura, dan har numfashinta ya fara sama sama.
Cikin hanzari ta tashi ta samo abin hawa, suka tafi Asibiti. Suna zuwa aka basu gado, likitoci suka fara ƙoƙarin suga numfashin Maman ya daidaita.
Hafsa ta ƙurawa Mama ido, an saka mata Nebulizer, ga drip a rataye.
Hafsa ta sa kujera ta zauna, ta cigaba da kallon Mama, ta riƙo hannun Mama tana tuno abubuwan da suka gabata a rayuwarsu, da kuma yadda aka yi Mama ta haɗu da wannan larurorin da suka mamayeta. A hankali wasu irin hawaye suka shiga zubowa daga idanunta, ba dan kuɗin da Khalil da ya bata ba da bata san ya zata yi da ciwon Mama ba.
  Kwanansu biyu a Asibiti, amma Khalil baya ɗaga wayarta, gaba ɗaya ta shiga cikin damuwa, sai da hakan ta faru sannan ta gane a 'yan kwanakin nan ba ƙaramin sabawa tayi da Khalil ba.
Shi kansa Khalil daurewa yake yi, baya jin daɗin rashin wayar da ba ya yi da Hafsa, amma dole ya dinga nuna mata fushinsa idan ba ta kyauta ba, yana matuƙar son ta, kuma yana son ya taimakesu, mussaman duba da yanayin halin da suke ciki, amma taurin kan Hafsa yafi ƙarfinta.
A kwana na uku ne, Hafsa na saka ran a sallami Mama, dan a kwanakin nan kuɗin wurin Khalil da ke hannunta sun ƙare, harta fara shiga na sana'arta, dan kullum cikin kawo kawo ake a Asibitin kamar ba na gwamnati ba.
Ba tsammani taga kiran Khalil, amma ta share, sai da Mama ta kalleta ta ce "Ba kiran wayarki ake ba?"

"Eh wayata ce".

"To ki É—aga mana"

"To zan ɗaga" ta amsawa Mama amma taƙi ɗagawa.

Ganin Mama ta ƙura mata ido ne, ya sanya ta ɗaga wayar, tana tura baki ta amsa masa sallamar da yayi da ƙyar.

"Na je gida ba kowa, kuna ina ne?"

Ta kalli idon Mama sannan ta ce "Muna Asibiti Mama aka kwantar"

"What? Amma baki gaya mini ba, wane Asibitin ne?".

"Ai sallamar mu za ayi yanzu, likitan dare muke jira ya sake dubata mu tafi".

"Ba wannan na tambayeki ba, wane Asibitin ne?" Har ga Allah Hafsa bata son yawan É—awainiyar da Khalil yake yi da su.

"Hafsa magana nake miki fa"

"Mhm nifa nace maka gida zamu taho"

"Wai ya kike mini jayayya ne?" Ya faÉ—a a hasale.

Haka ta haƙura ta gaya masa tana tura baki, dan taji haushin ɗaga mata murya da yayi.

Da hanzari ya shiga falo yana dube-dube.

"Ya aka yi ne?" Mummy ta tambayeshi.

"A nan na bar car keys É—ina?"

"Me zaka yi da makullin mota yanzu da daddare ba ka dawo gida ba kenan?".

"Eh zani wani wuri ne".

"Ina ne wani wuri?" Tayi maganar tana tsare shi da ido.

"Mummy sai kace wani mace, wani wuri zani fa, yanzu zan dawo" yayi Maganar yana É—aukar key É—in da yake kan dining yayi waje.

Fadila ta ce "Wurin wata zashi, ina ga wannan Yarinyar ce, ko ita aka kwantar Asibiti, ko wani nata, kan ki fito ya shigo yana waya".
Chapter 41 · 0% Book details