← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 84

Sashe 40

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ƙofar gidan su Abdul, Khalil yayi parking ɗin motar, kan ya fito sai da ya fara kiran Hafsa a waya, dan yaji ya take, a wannan karon yadda take amsa masa wayar ba ƙaramin daɗi yake masa ba.
"Ina kwana" bayan ta amsa salamarsa ta gaishe shi.

"Yau wace rana an gaishe ni" yayi maganar yana murmushi.

"Mhmm shi ne abin da ta iya cewa kawai".

"Kin tashi lafiya ya mamana?".

"Mama lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya mutan gidan? Ya jikin naka?"

"Kowa lafiya ƙalau, amma meya same ni?".

"Kace mini kana mura mana"

"Lallai kin fara damuwa dani, mura na warware Alhamdilillah, ina fatan kina lafiya ba wata matsala?"

"Ƙalau nake Alhamdilillah".

"To Masha Allah, zan shigo anjima insha Allah, da ƙarfe nawa zan zo?" Khalil yayi Maganar yana shafa sumar kansa.

"Idan an yi sallar isha'i, lokacin ne na dawo gida"

"To shikenan dear, me zan taho miki da shi?".

"Bakomai" ta bashi amsa.

"A'a nifa bana son haka, dan Allah ki gaya mini" yayi Maganar cikin shagwaɓa.

Dariya ya bawa Hafsa, "Wai shagwaɓa kake yi, gaskiya Mama na fama".

Dariyar shima yayi ya ce "Ai kuma kece yanzu zaki dinga faman, duk shagwaɓata ai ban kai ki ba, haka fa kike cewa malam ka rabu dani kar ka sake zuwa in da nake" ya yi yana kwaiwayonta in zata yi masa tsiwa.

Rufe fuska tayi kamar yana gabanta "Am sorry, kayi haƙuri na san na gaggaya maka maganganu marasa daɗi, ba halina bane bana son kowa ya matsi ratuwata ne" ta ƙarasa maganar a sanyaye.

"Na fahimta, kar ki damu sai na zo ki gaishe mini da Mama"

"Zata ji insha Allah" ya katse kiran, sannan ya fito daga motar.

" 'yar yarinya da wa kike wayane haka kike ta wannan fara'a?" Mama tayi maganar bayan ta shigo cikin É—aki, Hafsa na kan katifa tana ta murmushi, shiru tayi tana É—an mazewa ba ta zaci Mama na jiyo ta ba.

"Ya kika yi shiru, ko Khalil ne?" Hafsa ta gyaÉ—a mata kai.
Mama ta zauna a gefen katifar tana faÉ—in "Yauwa ko ke fa? Ki dinga sakar masa fuska, shi har abada wanda yace yana sonka ya gama yi maka komai"
A raunane Hafsa ta kalli Mama ta ce "Amma Mama...

"Shhh na san mai zaki ce Hafsa, ki kwantar da hankalinki, in dai da gaske Khalil yake sonki, na san ba zai gujeki dan ƙaddararki ba, nayi farinciki da shigowar wanda yake saki walwala rayuwarki, duk da halinki na miskilanci da taurin kai".

"Mama taurin kai kuma?".

"Eh taurin kai mana, ke baki san yadda kike da taurin kai ba, ai sai dai Allah ya shirya mink mini ke".

Hafsa kam shiru tayi tana tunani, tabbas ta fara jin Khalil a zuciyarta, dan ma tuntuni basar da shi take, amma Khalil ya haɗu ta kowane ɓangare amma tana tsoron tayi zurfi a sonsa ya san ko ita wacece, ya zo ya rabu da ita, kamar yadda ya faru da ita a baya.

"Girl, kince mini akwai Magana, kuma tun da kika zo kin yi shiru, yakamata muyi magana"
Fadila ta É—an yi shiru tana kallon Yusra, sannan ta ce "Ai ke rainin hankali ne ya miki yawa, ina tsoron in gaya miki ki raina mini hankali"
Dariya Yusra tayi ta ce "Idan ma na raina miki hankali, ai mun saba kema kina mini, ina jinki".

"Zan gaya miki damuwata, idan kika gayan ba daÉ—i zan zage ki ne tsaf in tashi in tafi gida".

"Nima ina da bakin ramawa ai".

Fadila ta labartawa Yusra abin da ake ciki, game da mafarkin da take yawan yi a game da Yazeed, da kuma abin da Yazeed ya gaya mata a game da Kankiya.
Yusra ta ce "To sai me dan kina yawan mafarkinsa, kin sa shi a ranki ne, kuma kuna yawan haÉ—uwa a school shikenan".

Fadila ta É—anyi tsaki ta ce "Ke ba kya gane abubuwa, ba fa Normal mafarki nake kawai in ganshi ba" Kan Fadila ta gama maganar, Yusra ta tuntsire da dariya.

"Ke nifa bana son iskanci, gayen nan ya taimakeni lokacin exams, duk da yadda na raina masa hankali, Wallahi idan ya zo kusa dani bana iya cewa komai, sai dai jikina yayita rawa, jikina yayi wani iri, inji kamar zan yi kuka, wasu hawaye su cika mini ido".
Me Yusra za tayi banda dariya, harda hawaye, dan sai da Fadila ta fara ƙuluwa, can Yusra ta ce "Ba faɗa da malam ba daren, yarinya ƙila zuwa yayi yai tsayuwar dare a kanki, saboda iskancin da kike masa, sai ki shiga hankalinki ai"

"Ban gane me kike nufi ba ai"

"Wataƙila Addu'a yayi miki yarinya, waye ya gaya miki ana ja da malamai?".

"Ke ni ki bani shawara kawai"

"To ni wace shawara zan baki? Tun da dai bani nake haÉ—aku a mafarkin ba, you need each other maybe shima yana mafarkin da ke, kin sashi a ranki ne kawai".

"Wai ya za ayi in sa shi a raina, a kan me zan a shi a raina? Ni shishsigin da yake mini ma haushi yake bani, dan dai kawai yana taimaka mini sosai ne".

Yusra ta ce "To ni yanzu me zance miki, idan ba damuwa ki kayi da shi ba, yawan mafarkinsa da kike alamane da yake nuna ruhinku na tare da juna, kuma jikinki na gaya miki yana buƙatar Aure, kuma ɗan ustazu yake so" tayi maganar tana dariya.
HaÉ—e rai Fadila tayi ta ce "Laifina ne da na zo wurinki"

"To idan ba haka ba, duk mazan duniya da wanda kike gani yau da kullum ba wanda kike gani sai shi, na fassara miki abin da kike buƙata kina jin haushi na. Meke saka miki rawar jiki dan kuna tare? Idan baki wasa ba, wataran sai dai kiga kin rungumeshi. Zahiri ki zata mafarki ne, shi zuciyarki da gangar jikinki ke buƙata"
Tsaki Fadila tayi, ta tashi ta É—au jakarta ta ce "Sai kiyi da wata dan ubanki".

"Ubana ya gode matar Ustaz".

"Allah ya isa shegiya, kije dan kanki, Allah ya tsareni haÉ—a jiki da wannan yarom".

"Zaki ga yaro, Amma dai kin san ba ƙazami bane"
Banza Fadila tayi mata ta nufi hanyar fita.
Yusra ta ce "Amaryar Ustaz ko Kankiya, ranar Saturday ki aiko a karɓar miki chocolate cake zan yi" Ko waiwayowa Fadila ba tayi ba, ta yiwa maman su Yusra sallama ta fice.

Khalil ma cike da farinciki ya je wurin Abdul, sun sha hira sosai, yayin da Abdul ya ƙara bashi shawarwari tare da bashi ƙarfin gwiwa a kan yadda zai cigaba da neman Soyayar Hafsat.

Bayan sallar isha'i, Khalil ya sha kwalliya cikin cofee É—in yadi mai laushi, ya sanya hula tare da feshe jikinsa da turare. Ya É—au hanya ya nufi gidansu Hafsa.

A kan dandamalin ƙofar gidansu tayi musu shimfiɗa, ta kalleshi tana murmushi ta ce "Kayi kyau sosai"

"Ko baki faÉ—a ba ai ni mai kyau ne"

"To ai sai ka bari a faÉ—a, na ma janye ba kai kyau ba" Khalil yayi dariya ya ce "Daga baya kenan, ina Mama"

"Mama na ciki tana gaisheka" Hafsa ta kawo masa ruwa a Jug, suna hira yana sha, rabon da Khalil ya sha ruwan borehole har ya manta, sai dai ya sha na roba, amma ya sai gashi zaune yana É—aÉ—É—akar ruwan borehole.
  Sosai ya dinga jan Hafsa da hira, yau kam ta biye masa sosai, ita kanta ta san ta samu farincikin da ta daɗe ba tayi ba.
"Hafsa kina sona?" Ya jefo mata tambayar. Gaba daya annurin fuskarta ya É—auke, tayi shiru ba ta ce komai ba.
"Hafsa meyasa kike gudun amsa mini tambayar nan ne?".
"Saboda ƙaddarata"
"Mecece ƙaddarar taki gaya mini, zan fahimceki".
Ta share hawayen da suka fara zubo mata ta ce "Zan gaya maka idan ka sake dawowa, amsarka bayan jin mecece ƙaddarata ita zata amsa maka tambayar da kake mini na idan ina sonka"
"Ki gaya mini yanzu ko zan samu nutsuwa mana".
"A'a dare ya fara yi kuma ga sanyi, zan gaya maka insha Allah"
"Shikenan, jeki ki gayawa Mama zan shigo in gaisheta" Hafsa ta tashi ta tafi, shi kuna ya buɗe jug ɗin ruwan, ya zubar da sauran, ya ƙulle kuɗi a leda ya saka mata, dan ya san idan ya ce zai bata ba zata karɓa ba.

Ya shiga suka gaisa da Mama, Bayan ya fito Hafsa ta biyo shi da wata leda babba, ta bashi. Ya sa hannu ya karɓa ya ce "Ni kome kika bani karɓa zan yi, ni ba irinki bane"
"To ni É—in ya nake?"
"Kin fini sani ai, ranar ai a kan 500 kika kusa yi mini tijara"
Murmushi Hafsa tayi ta ce "Baka da mantuwa ko?"
"Ina zan manta, sai da safe" yayi mata sallama sannan ya tafi gida, aikuwa a hanya Hafsa ta dinga kiransa a waya, ya san a kan kuɗin nan ne, dan haka yaƙi ɗagawa. Gaba ɗaya zuciyarsa ta tafi a kan son sanin ƙaddarar da ke cikin rayuwar Hafsa.

Da yaje gida a falo ya shigo da ledar, jin ledar da zafi tun lokacin da Hafsa ta bashi, ya san cewa abin ci ne a ciki.
Ya sa Amina ta kawo masa plate da cokali, Mummy sai binsa take da kallo, tana tambayarsa daga ina yake.
"Wurin Abdul" ya bata amsa.
Ya zazzage ledar, Awara ce fal, da miyar jajjage ga kabeji da cucumber fal a gefe. Murmushi yayi ya juye a kan plate É—in, ya sa cokali ya fara ci"

"Me kake ci haka ne?" Mummy tayi maganar tana leƙa plate ɗin.

"Mummy awara ce fa" ya faÉ—a yana cigaba da ci.

Yamutsa fuska ta yi ta ce "Awara Khalil? Kaima ka fara irin wannan cimar yunwar? Meye haÉ—inka da wata awara?"

Khalil ya ce "Mummy amma naga Abinci ce itama, ta burgeni ne shi ne na saya".

"Duk Abincin da yake gidan nan ka rasa me zai burgeka sai awara? Me akayi a ka wata awara, wannan ƙazantar da ake sayarwa a bakin hanya, wato shi dai Abdul ɗin nan dole sai ya maida kai irinsa, shike koya maka duk wani halin ƙauyanci da shirme, yanzu idan cikin ka yayi ciwo fa?"

"Mummy ba Abdul ne ya sani saya ba, ni na saya da kuÉ—ina fa".
Chapter 40 · 0% Book details