Sashe 39
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta kashingiÉ—a da jikin seat, a hankali ta ce "Baka da wani aibu, hasali ma a karamcinka duk da halin ko in kula da nake yi maka, bai hana ka taimake ni ba, Amma meye amfanin fara son ka bayan a gaba na san zan iya samun tangarÉ—a a aikata hakan?"
"Wace irin tangarÉ—a? Ina sonki Hafsa"
ÆŠago kai tayi ta kalli Khalil cikin rauni "Ina ganin hakan a idonka, amma... Sai kuma tayi shiru hawaye na zubowa daga idanunta.
"Akwai ƙaddarar da zata iya zame mana shamaki, bana son in fara sonka, wani abu yazo ya kawo mana tangarɗa, ka san wacece ni ka guje ni".
Khalil ya haɗa hannayensa ya ce "Dan Allah Hafsa, ni ba ruwana da wata ƙaddara in dai bata haramta mana aure ba a shari'a, Ina sonki, amma wace ƙaddara ce haka da kike tunanin zata zame mana shamaki da cikar burinmu, tunda ai kina sona ko?"
MASU BUƘATA DAGA FARKO, AKWAI A AREWABOOKS KO MANHAJAR WATPAD.
AYSHERCOOL
08081012143
https://arewabooks.com/chapter?id=638e2c023cc3212f4202c4d8
GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143
P17
Shiru Hafsa tayi, ba tayi magana ba.
Khalil ya ce "Yau Allah ya haÉ—ani da gamona ni Ibrahim, Baby magana nake Please answer me" yayi Maganar yana kuma marairaicewa.
Kwaɓe fuska tayi kamar za tayi kuka "Ni ka ƙyaleni ko in yi kuka Subhanallah, ba ƙaramin narka zuciyar Khalil Hafsa tayi ba, saboda a rayuwarsa yana son shagwaɓaɓɓiyar mace.
"Kar ki yi kuka Please" yayi Maganar yana kwaiwayonta.
"Ni ba haka nake magana ba"
"To ya kike yi?" Yayi Maganar yana kallon in da take.
"Kaga muyi sauri, kar Mama taga na daÉ—e ta hanani zuwa na gobe in Allah ya kaimu".
"Allah ya sa ta hanaki zuwa" ya faÉ—a yana kunna motar.
"Allah ya sa ta hanani zuwa ko?" Ta maimaita tana leƙa fuskarsa.
"Eh mana, gaba É—aya ma ni kishi ne ya ke damuna, duk an gama ganinki, ga mayafinma ba wani babba ba"
Kallon kanta tayi da mayafin, ta sake jan mayafin tana rufe jikinta.
"Me zaki rufe bayan an gama ganin komai?"
"Me aka gani?".
"Kyakywar surarki mana, shiyasa duk naji haushi ai" haÉ—e rai tayi, tana sake gyara zamanta.
Haka Khalil ya yi ta janta da hira, ga mamakin Khalil ashe Hafsa na magana sosai, duk a hirar tasu ma, idan ba ta ga dama ba, shiru take taƙi tanka masa, amma yau ta ɗan sake da shi.
Har ƙofar gida ya kaita, sannan ya kalleta ya ce "Babyna, yau zan kwana cikin farinciki, duk da ban samu amsar tambayar da nayi miki ba, amma naji daɗin kulani da kika yi, Ina sonki Hafsa" Hafsa ta ɗaga ido ta kalli Khalil, haka nan taji tana tausayinsa, tabbas ya nuna mata so, ko ga wannan sintirin da yake yi a kanta.
"Sai da safe, ka samu kaje gida ka huta, Allah ya kiyaye hanya".
"Ameen my love" ya furta a hankali, ta buÉ—e motar ta fita ta nufi gida, har ta shige gida, yana tsaye yana kallonta, sannan ya ja mota ya bar wurin.
Sai ƙarfe goma Sa'annan Khalil ya isa gida, Mummy ce ta rage ba ta kwanta ba, taji ana knocking ƙofar Falon taje ta buɗe, mamaki ne ya cikata da ta ga Khalil.
"Kai, saukar yaushe?".
"Yanzu Mummy".
"A wannan daren? Baka samu Flight É—in yamma ba ne?".
Ya shiga cikin falon yana faÉ—in, a mota fa na dawo.
"What, mota kuma? Amma baka da hankali, da wani abu ya faru fa, yadda gari babu tsaro?".
"Ai ba abinda ya faru Mummy, baki bacci ba ashe?".
"Eh ban kwanta ba tukuna, bari in taso masu aikin can, su girka maka wani abun ka samu ka ci".
"No bana jin yunwa, a ƙoshe nake, na shigo ne ma kawai dan kusan na dawo, naga motar Daddy a waje yana gari ne?".
"Eh yana nan kusan sati guda kenan yana gari".
"Masha Allah, shikenan sai da safe"
"To Allah ya kaimu lafiya" ya fice daga falon ya nufi sashinsa.
Mama ta lura da yadda Hafsa ke murmushi lokaci lokaci, amma ba taji ta ce mata komai ba.
"Nace Khalil ya biki wurin bikin ne?".
Hafsa taji tambayar a bazata. "Eh yaje mun gaisa"
"Yazo nan nemanki ai, nace masa kina wurin biki" Hafsa tayi shiru tana cigaba da tuna yadda suka kasance yau, haka nan take jin nishaÉ—i itama a ranta, Khalil ya damu da ita sosai.
Bayan ta kwanta, ta shiga cikin abin rufarta, ta ɗau wayarta ta turawa Khalil saƙo kamar haka
  _*Ya kaje gida? Na gode sosai. Hafsat*_
Khalil yana ƙoƙarin saka wayarsa a silent ya kwanta, saƙon Hafsa ya shigo wayarsa, jujjuya saƙonya dinga yi yana murmushi. 'insha Allah sai kin zama tawa Hafsa'.
Ya yi mata reply da
*"Na koma lafiya, amma ai kamata yayi ki kirani kiji, mura fa ta kamani saboda sanyi na daÉ—e a waje"*_
Ta yi masa reply da "Subhanallah, Allah ya baka lafiya, Asuba ta gari".
Kissing ɗin screen ɗin wayar ya yi, ya kwanta, tare da ƙanƙame wayar a ƙirjinsa. Ya ƙudurce a ransa washegari zai jewa Abdul da labari me daɗi a kan Hafsa na daf da fara soyayya da shi.
Fadila har fargabar kwanciya bacci take, saboda babu wani abu da yake zuwa mafarkinta, Kamar yadda Sheikh Yazeed yake zuwa, abun har mamaki yake bata, gashi ta rasa wanda zata gayawa, kawai ta yanke shawarar washegari za taje gidansu Yusra ta bata labari, ko da wata shawara da zata iya bata.
Ba ƙaramin farinciki Alhaji Ahmad ya yi ba, da ganin Khalil, dan a wata shida sau ɗaya suka haɗu, tun bayan fara aikin Khalil, Alhaji Ahmad mutum ne mai son iyalinsa da kyautata musu, duk abin da suke so shi yake musu, baya son duk wani abu da zai taɓa masa su.
Yau gaba É—aya sun haÉ—u a kan dining, suna karyawa, sai hira suke cikin nishaÉ—i da jin daÉ—i, tamkar basu da wata damuwa a rayuwarsu.
Amina ta kallesu sai taji sun burgeta, ita kuwa gidansu duk sun rarrabu, dan nemwa kansu mafita, sun baro Inno ita kaɗai a ƙauye cikin jarabar su Kawu Lawan, nan Baba yana gadi ita kuma tana aikatau, duk dan samun abin da zasu rufawa juna asiri.
"Ya Ubangiji Allah ka wadatamu, ka wadatamu da halal ka nesanta mu da haram, Allah ka sake haÉ—a kanmu a wuri guda cikin farinciki, Allah yasa sanadin karatu nan nawa, ya kawo canji a rayuwarmu" tayi Addu'ar a zuciyarta.
Haka ta jira suka kammala, ta kwashe kayan da suka ci Abincin, ta gyara wurin kamar ba ayi Komai a wurin ba.
Suka kuma komawa falo suka baje, suna ta hira da iyayen nasu. Daga bisani Alhaji Ahmad yayi musu sallama ya koma É—akinsa, dan gabatar da wasu ayyuka.
Khalil ya yi shiru yana kallon hotunan da ya yiwa Hafsa jiya, duk da bata so ya yi mata hotunan, amma tayi kyau matuƙa, Kamar a saceta a gudu.
Mummy ce ta fizge wayar ta ce "Bani nan in ga abin da kake kallo haka ko ƙwsƙwaran motsi baka yi"
Mummy ta zubawa hoton Hafsa ido, ta kalli Khalil ta ce "Ita kuma wannan fa?"
Khalil ya yi shiru bai ce komai ba.
"Ko ita ce wadda kake so É—in?".
Jin abin da Mummy ta ce, ya sanya Fadila tashi da sauri, ta karɓi wayar.
Ta kalli hoton Hafsa kwaɓe baki ta ce "Taɓ dan Allah kalleta ga kumatunta da ido kamar wata Philippines, ko ɗan murmushi babu a fuskarta gaskiya ka faɗo".
"Bani wayata dan ubanki, ta fi ki kyan gani dai".
"Wallahi na fita kyau, Dan Allah Bro dame wannan tafi Yusrana, amma ka watsa mini ƙasa a ido".
HaÉ—e rai Khalil yayi ya ce "zan tattakaki Wallahi".
Mummy ta ce "Kar kuyi mini faɗa ni, ita wannan ɗin a ina take? Kuma 'yar wanene?". Gaban Khalil ne yayi mummunar faɗuwa, shi kansa sai yanzu ya sake ankarewa akwai damuwa a soyayyar su. Miƙewa yayi ya kalli Mummy ya ce "We will talk later" yana gama maganar ya fice.
Fadila ta ce "Mummy, ke sai ki bari ya auri wannan mummunar?".
"Ke Fadila, kina taya Yusra kishi dai, amma ai ba ta da muni, ba laifi".
"Wallahi Mummy ba ta da wani kyau, kalleta fa wata 'yar lukuta da ita, ko fara'a babu a fuskarta Wallahi Mummy kar ki bari ya kwaso mana 'yar wahala".
"Barni da shi tukuna na ga iya gudun ruwansa".
Fadila ta miƙe ta ce "Mummy, a round 11 zan je wurin Yusra".
"Ok sai kin dawo"
Khalil kuwa bayan ya fita daga falon, É—akinsa ya wuce, ya shirya don zuwa wurin Abdul su tattauna, a kan yadda suka yi da Hafsat a daren jiya.
Yana tafe a mota yana saƙe-saƙen yadda zai ɓullowa lamarin, amma shi babbar damuwarsa a yanzu shi ne ya tabattar da soyayyarsa a wurin Hafsat.
Fadila na gaban mudubi, tana shiri dan zuwa gidansu Yusra, wayarta ta fara ringing, ta janyo wayar da ke kan mudubi, ta É—aga ta sakata a speaker, ta ajiye ta cigaba da abin da take yi.
"Assalamu alaikum warahmtullah" aka yi sallama daga cikin wayar.
"Wa'alaikum salam" ta amsa tare da yin shiru dan jin wanda ya kirata.
"Fadila Dutse ya kike?".
"Wake magana?".
"Ai kya amsa gaisuwar tawa da fari ko"
"Idan baka da abun yi ni ina da shi koma waye".
"Kankiya ne" ita gaba É—aya ta manta da waye ma wani Kankiya, banda yanzu da ya kirata, maganganun Yazeed ne suka dawo mata, da ya gaya cewar sonta kankiya yake yi. Tsuke fuska tayi ta ce "Ina jinka"
"Ya kike ya hutun, hope kina jin daÉ—in hutun?"
"Sir ya aka yi ne, kace jarrabawata akwai matsala zaka kirani, kuma ka kirani kana tambayata wasu abubuwa daban"
"Eh, saboda ba saboda jarrabawa na kiraki a wannan karon ba, saboda inji lafiyarki ne"
"But you have no Business with that"
"Who told you so, nafi kowa buƙatar son sanin lafiyarki".
"Sir sai anjima, am busy now" ta katse kiran ta ajiye tana huci, tare da harar wayar.
Nan da nan ta kammala shirinta, ta É—au mota ta nufi gidan su Yusra.