← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 84

Sashe 50

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ok, yayi kyau" ya furta ya raɓa ya bi gefen in da yake jin alamun tana tsaye.

Amina ta ƙarasa ta buɗe ƙofar, ta fita baranda, hasken lantarki ko ina, ta zauna ta bubbuɗe litatafanta, ta fara duddubawa.

Gani tayi an kunna wutar falon, haske ya gauraye falon.
Tashi Amina tayi ta leƙa falon, taga Alhaji Ahmad ne ke ta zagaya falon.

Ji yayi kamar ana kallonsa, dan haka ya waiwayo, sai ya ga Amina a tsaye tana kallonsa.
Amina ta ce "Jikin ne dai?"
Ya jinjina mata kai yana cigaba da zaga falon.
"Wai me ya sameka, naga kana ta zagayawa?" Tayi tambayar kanta tsaye.

"Suga na ne ya hau, da kuma jinina shima ya hau, ƙafafuwana ne suke zafi da cikina" ya samu kansa da bata amsa, ba tare da shi kansa ya san dalili ba.

Cikin tausayawa Amina ta ce "Allah sarki sannu, dama kana da suga amma komai ma kake ci, ba'a tsara maka Abincin da yakamata ka ci? Naga bakomai masu ciwom suke ci ba fa"
Daddy ya cigaba da aikin zagayensa ba tare da ya kuma cewa komai ba.

"Allah ya baka lafiya" ta faÉ—a tare da juyawa ta koma wurin karatunta.

Kusan mintuna talatin ta tashi ta kuma leƙawa, ta ganshi a zaune ya mimmiƙe ƙafafuwansa sai lanƙwasa yatsun ƙafarsa yake yi.

"Sannu Daddy, Allah ya baka lafiya" ya jiyo siriryar muryata a kunnensa.
Murmushi kawai ya yi bai amsa ba.

"Haryanzu ƙafar na maka zafi ne?" Ya jinjina mata kai alamar eh, tare da lumshe idanunsa, da ganin yadda yake gumi zaka san yana jin ciwon sosai.

Komawa tayi, mintuna kaɗan ta dawo ta ce "Daddy zo ga ruwa na zuba maka a bokiti, kazo ka sanya ƙafafuwan ko zasu daina"

"To zan zo" ya bata amsa ba tare da ya buÉ—e idonsa ba.

Ta koma ta cigaba da karatunta, harta fidda ran zai fito, sai gashi ya fito, ta ajiye masa kujerar zama, da bokiti ta zuba ruwa. Ya zauna a kan kujerar, ba tare da ya ce mata komai ba, ya janye jallabiyarsa, ya zura ƙafafuwan a cikin ruwan, a hankali ya lumshe idanunsa jin yadda sanyin ruwa ke ratsa shi, yana samar masa da releif, tun daga ƙafafun nasa zuwa ga ilahirin gangar jikinsa.

Amina ta cigaba da rubuce-rubucenta,  a hankali yake samun releif daga zugin da ƙafarsa ke masa, ya buɗe idanunsa ya na kallon Amina, da take ta aikin karatunta. Shi dai Allahn da yayi shi ba mutum ne mai shiga sabgar mata ba, shi ko wasa da yara bai fiye yi ba, dan magana ma bata dame shi ba, amma har cikin ransa yake jin daɗin yadda take nuna damuwarta da shi.

"Naga kin kasa wannan, kawo mu gani" yayi Maganar yana kallon littafin gabanta
Ba musu ta miƙa masa littafin dake hannuta, tare da biron.

"Me aka yi miki kike kuka É—azu?" Yayi tambayar yana kallon littafai da ke hannunsa.

"Wai ni?" Amina ta tambaye shi.

"A'a" ya bata amsa.

Shiru tayi ba ta bashi amsa ba, ta fara wasa da littafin gabanta.

A hankali yake rubutun cikin nutsuwa, mintuna kaɗan ya miƙa mata littafin.
BuÉ—e baki tayi tana kallonsa, "ya aka yi kayi mini, tun É—azu nake fama na kasa"

Be ce mata komai ba, ya cigaba da kallonta, ita kuma ta cigaba da bin littafin da kallo tana murmushi.

"Wane course zaki karanta, idan kika kammala sakandare?"

"Ni sakandare kawai nake son nayi, Baba bashi da halin da zai biya mini jami'a".

"Wane course zaki karanta a jami'a idan kin kammala sakandare" ya maimaita mata.

"Bani da zaɓi"

"Meyasa?" Ya faɗa a taƙaice.

"To idan na sakawa raina ga abin da nake so, ai babu me biya mini, shiyasa ni bana tunanin wata jami'a".

"Zaki iya medicine?" Yayi Maganar yana kallonta.

Ƙwalalo ido Amina tayi ta ce "Taɓ, korata za a ayi, bani da ƙoƙari"

"Kina wahal dani, bana son doguwar magana, ke in an tambayeki sai kin yi amfani da different formulas kafin ki amsa".

"To yi haƙuri"

Ya sunkuyo da fuskarsa kunnenta, wanda hakan ya haddasa mata faÉ—uwar gaba "Gaya mini, me zaki karanta?".

"Kome Allah ya sa na samu, ina so". Ta amsa tana janye jikinta gefe.

"Idan kin yanke shawara ki gaya mini, zan ga abinda zan iya yi a kai"

"You mean zaka barni in cigaba da karatu a gidan nan, naji ance É—awainiyar jami'a ba kamar na sakandare bane"

"In dai karatun bai fi ƙarfin talaka kamar ni ba, zan yi wani abu a kai Insha Allah, kina da ƙwaƙwalwa bai kamata a barta haka ba ki tsaya iya Sakandire ba"

Daddy ji yake tamkar suka É—ai ne a duniyar, dare ya tsala, ko tunanin wani ya zo wurin baya yi.

Hawaye ne ya wanke fuskar Amina, tana kallon Alhaji Ahmad, amma ta kasa Magana.

"Komai aka yi miki sai kuka?"

"Na gode sosai Daddy, kana da kirki sosai ba kamar.." Sai kuma tayi shiru.

"Ba kamar wa ba? Hmm ko kusa karki bari ta ji kin faÉ—i wani mummunan abu a kanta, kin san abin da zata iya yi miki, let's keep this as our secret, kar ki gayawa kowa sirrinmu ne, ciki har da Baba, idan kuwa kika bari zancen ya fito, to abinda ya biyo baya ba ruwana, dan ba lallai Zainab ta bari"
Amina ta É—an kalleshi, yana da zuciyar taimako, amma yana shakkar matarsa.

"Insha Allah ba zan gayawa kowa ba, na rufe bakina, Allah ya baka abin da kake so duniya da lahira"

"Ameen" ya amsa tare da jingina a kujera.

Bacci ne ya ɗauke shi, ƙafafuwansa na cikin bokitin ruwa, Amina ma bacci ne ya kwasheta, ta kife kanta a gefen kujerar ta hau bacci.

(ALLAH YA SA HAJIYA ZAINAB TA ZO TA KAMA KU🥴)
Ayshercool
08081012143
GABA DA GABANTA

AISHA ADAM AYSHERCOOL

26-27

Tsananin sanyin da yaji yana ratsa shi ne ya sanya ya buɗe idanunsa, gari ya ƙara yin duhu baƙi ƙirin, ba kajin motsin komai sai haushin karnuka a waje, ya kalli in da Amina ta dunƙule a wuri ɗaya, ta jingina da kujerar da yake kai tana bacci, da alama tana jin sanyi sosai, amma bacci ne a kanta.
A hankali ya zare ƙafafuwansa daga cikin bokitin ruwan nan, ya tattara litattafanta da ta baza a wurin, bironta ya ɗauka yana shafa mata a fuska, yamutsa fuska ta yi, ta kai hannu ta kori abin da yake bin fuskar tata, amma ya kuma shafa mata.
"Ki tashi kije ki kwanta"
Amina ji take tamkar a kan katifarta take, dan haka tayi wani irin juyi tana ƙoƙarin faɗawa jikinsa ta cigaba da baccinta.
Cike da rashin sabo, da yi mata kallon 'yar cikinsa, ya sanya hannayensa ya ɗagata ya tsayar da ita a kan ƙafafuwanta, ya ɗan girgizata ya ce "Open your eyes" a hankali take buɗe su tana lumshewa, tamkar zata faɗi. Ya danƙamata litattafanta, ya buɗe musu ƙofar falon, ya kunna fitilar wayarsa, ya rakata har bakin part ɗinsu, sannan ya wuce sashen Hajiya Zainab.
Ya tarar da ita ta rashe, sai baccinta take hankali kwance. Ya lallaɓa ya hau kan gadon, cikin ikon Allah, ya rage jin zafin da tafin ƙafarsa ke yi masa sosai.
Ya janyo bargo, ya rufa musu shi da Mummy, ya kwantar da kansa a wuyanta, yana shaƙar ƙamshin turaren da take fitarwa mai daɗin gaske a hancinsa. Tuna halinta ne ya sanya shi sassauta rungumar da yayi mata, dan yanzu sai ta farka ta hau shi da masifa.

Amina bata farka ba sai asuba, dan sai da ta kusa makara, sai da ta farka ta ganta a tsakar É—aki a kan litattafanta tana bacci, sannan ta tuno abubuwan da suka faru jiya da daddare, gaba É—aya ta É—auka mafarki take yi, a hankali ta tashi ta shiga toilet, tayi alwala ta dawo tayi sallar auba.
Bayan ta idar, ko karatun Alqur'ani da azkar ba ta samu yi ba, saboda kanta har wani nauyi yake yi mata, ta haye kan katifarta ta hau aikin bacci.
Hajara tamkar ta tashi Amina, ganin har ƙarfe takwas bata fito ba, sai kuma ta fasa, saboda itama ko ƙarfe nawa zata kai ba ta fito ba, Amina ba ta damuwa balle ta taso ta, aikinta kawai take yi, dan haka taga idan ta ce sai Amina ta taso, to tabbas bata kyauta ba.
  Wasa² har goma saura, Amina baccinta take yi, A lokacin Alhaji Ahmad ya fito karyawa, tare da Hajiya Zainab. Ya tarar da Hajara na ta shirya Abinci a dining ɗin, haka nan yaji yana son ganin Amina, dan galibi ita yake gani tana shirya Abinci, amma har Hajiya Zainab ta zuba masa Abinci, yana son ganin ta ina zai ga Amina, kamar ba raba dare suka yi tare ba jiya.
ÆŠanÉ—anon Abincin kawai ya ci, yaji ya banbanta da nata, ya kalli in da Hajara ke mopping ya ce "Ina wannan Yarinyar take?"

Hajara ta kalleshi ta ce. "Wace yarinyar ranka ya daÉ—e?"

" Wadda kuke aiki tare?"

"Bata tashi ba" Hajara ta faÉ—a tana sunkuyar da kai.

"Yau ba taje makaranta ba ne?"

"Ai sun yi hutu" ta bashi amsa, bai ce komai ba ya cigaba da cin Abincin da a bakinsa na Amina yafi daÉ—i.

Hajiya Zainab ta kalleshi ta ce "Kai meye damuwarka da taje Makaranta ko ba taje ba?".

"Saboda kuÉ—ina nake biya, dan haka yakamata in bibiya"

"Shiyasa tun farko ni ban so ka kaita makarantar kuÉ—i ba, sai a kaita ta irinsu, amma ka kaita cikin yaran da ba sa'aninta ba a fannin rayuwa da arziki"
Alhaji Ahmad yayi mata shiru ya cigaba da cin Abincinsa.

Ƙarfe goma saura, gaba ɗaya ɗalibai sun tattara hankalinsu a kan malamin da yake tsaye yana kaiwa yana komowa kamar mazari, a ajin yana gabatar da darasi, sai ga Yazid a wahale, kamar an koro shi, cike da fargaba ya fara yinƙurin shiga ajin.

"Hey stop their, ko É—akin babarka idan zaka shiga sai ka nemi izini, balle aji" cewar malamin da yake yiwa Yazid kallon banza.

"Am sorry sir" ya faÉ—a cikin ladabi.
Gaba É—aya ajin suka yi shiru, suka mayar da hankalinsu kan Yazid.
Chapter 50 · 0% Book details