Sashe 24
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, bari in nuna maka litattafaina an cika mini jakata da litatafai, gobe in Allah ya kaimu za a bani Uniform, Baba ya sai mini takalmi da safa"
Ta zuge jakar tana nuna masa, yace "Masha Allah, Allah ya sa a amfana, bari da yamma zanje da kaina in sayo miki takalmin".
Amina ta girgiza kai ta ce "A'a Baba fa zai saya mini, kar ka damu, sai daÉ—i nake ji na koma Makaranta".
Abdul ya ce "Sai kice Alhamdilillah, wai ni kuwa ya aka yi kika iya turanci haka?".
"Malaman mu ne suke koya mini, a makarantar mu ana zuwa da ni debate ko quiz, su suke koya mini, kaga kuma muna da ƙaton Library, amma babu ɗalibai sosai 'yan garinmu ba su damu da karatun ba, akwai litattafai sosai a ciki, kuma ina da dictionary da nake duba Words, mu uku ni da wasu ƙawayena ake mana extra lessons a ƙauyenmu"
Abdul ya jinjina kai ya ce "Lallai ashe gifted ce?"
"A'a ni ba gifted ba ce, dagiya nake yi in gaya maka"
"To ya aka yi ki ke son cigaba da karatu a nan? Ko can babu senior secondary School".
Yamutsa fuska ta yi, ta tura baki sannan ta ce "Ƙannen Baba ne za su yu mini Aure, wai ba sa son ina zuwa boko, ni kuma na gudo wurin Baba"
"Da an yi asarar talent, wannan ƙwaƙwalwar ta ki atleast yakamata ko secondary ki kammala ai"
Amina ta sake ta dinga bawa Abdul labarin yadda tai karatu a ƙauyensu faɗi ba a tambayeka iri iri.
"Ke shut up dalla!" Khalil ya buga mata wata uwar tsawa, da sai da cikinta ya kaÉ—a.
Abdul ya ɓata fuska ya ce "Khalil ya haka?, Ya muna hira da yarinya zaka yi mata tsawa?".
"Duk ta bi ta cikawa mutane kunne, ko haÉ—iyar yawu ba ta yi, i hate nonsense, ta kuma magana Wallahi sai ta sauka".
"Khalil waye ya gaya maka irin wannan yaran ana katse musu hanzari? A irin wannan surutun nasu ba sa na banza, kuma ba a kan karatu take Magana ba?" Khalil yai wa Abdul banza ya cigaba da tuƙi. Tun da Amina ta firgita da tsawar da Khalil ya yi nata kasa magana ta yi, sai jikinta da ke ta tsuma.
A ƙofar gida suka sauketa, ta yiwa Abdul godiya ta shiga gidan. Khalil ya wuce kai Abdul gida, suna tafe suna faɗa. Abdul ya ce "Kana hantarar 'yar mutane ba abin da tayi maka, ƙila ma ita zaka saka a wannan gidan da kake ta ƙerawa"
Khalil ya ce "Kai fa mahaukaci ne wasu lokutan, da Mummy kaÉ—ai ta isheni, kai idan aka ce zan auri wannan yarinyar sai ka yadda?"
"Eh mana ba mace ba ce? Meye aibunta 'yar duma duma black beauty"
"Yawwa an zo wurin, sai kace mini sonta ka ke yi"
Abdul ya ce "Ai ni ka san wadda nake so, kuma alamu sun nuna ba za ka bani ba"
Kalil Yayi guntun tsaki ya ce "Kai ka fiye shirme Wallahi" daga haka ya basar da zancen ya kai Abdul gida ya sauke shi yayi gaba.
Wata hanya ya biyo, domin ya yi yanke, ya samu sauƙin go slow.
A ƙofar wani kanti yayi parking, dan ya sai ruwan roba, na motarsa ya ƙare, ya miƙawa wani yaro kuɗin ya ce ya karɓo masa.
Ya gyara zamansa, ya kashingiÉ—a da seat É—in motar, ya É—an waige ya hango wata matashiyar budurwa tana juya awara a cikin mai, tana sanye cikin gogaggen hijjabi ash, sai dai fuskar nan tata a É—aure tamau, wani matashi na gefenta a kan babur, da alama tsarata yake yi, amma ko sau É—aya ba ta É—aga kai ba, balle ta kalle shi!.
Follow my Arewabooks Account
Ayshercool7724
Watpad
Ayshercool7724
08081012143
GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Domin samun update a kan lokaci, ko samun book É—in daga farko
Follow me on
Watpad Ayshercool7724
Arewabooks Ayshercool 77724
What's app
08081012143
P11
Zuba mata idanu ya yi, yana kallon yadda take gabatar da sana'ar ta ta cikin nutsuwa, ba hayaniya ko ƙazanta komai nata a nutse, amma mamaki ne ya biyo bayan tunanin da yake yi, me wannan budurwa take haka a titi? Yafi dacewa ace tana gidan Aure, ko kuma tana makaranta, amma kalleta a titi tana suya.
Yaron da ya aika ne ya kawo masa ruwan, ya barwa yaron sauran canjin, ya cigaba da kallon in da Hafsa take, sai dai yadda take gudanar da lamarin nata ne, da gani ka san za ta yi izza, saboda sai shan ƙamshi take, tare da haɗe rai dan kar ma wani ya kawo wargi. A hankali Khalil ya yi you tune, ya koma hannun da Hafsat ke zaune tana gudanar da sana'ar ta. Parking ya yi a gefenta, ya fito daga motar, ya ƙaraso in da take suyar awarar ya kalleta ya ce "Sannu dai" ba tare da ta ɗago ba ta amsa masa ƙasa ƙasa da 'Yawwa".
Ya miƙo mata dubu biyu ya ce "Zuba mini abin nan na 2k" wani irin kallo Hafsa ta yiwa Khalil, irin kallon ka raina mini hankali ma, ba ta ce masa uffan ba, ta cigaba da sallamar yaran da ke gabanta.
Khalil gani ya yi ba ta da niyyar sake ko É—aga kai ta kalleshi, ya kuma matsawa ya ce "Magana fa nake yi, ki sa mini na 2k"
"Ka bari idan ka san sunan abin da nake sayarwa, sai ka dawo in sayar maka" ta bashi amsa.
Khalil ya ce "To, ikon Allah am serious ki karɓa ki bani".
"Malam nace ka bari ka san sunan abin da nake sayarwar sai ka siya".
Yaron da ke tsaye zai sayi awara ya ce wa Khalil, "Sunan abinda take sayarwa Awara".
Khalil ya ce "Ok na gode sosai, ki bani awara ta dubu biyu".
Ba tare da kalleshi ba ta ce "Ni awarata ba ta kai ta dubu biyu ba, ta É—ari biyar kawai za ka iya samu".
"To bani ta ɗari biyar ɗin, sai ki riƙe canjin"
Hafsat ta É—ago idanunta ta harari Khalil ta ce "Malam ba fa bara nake ba, sana'a nake yi".
"Ai nima bance bara kike ba, kyauta ce kawai na baki, ta ɗari biyar ɗin ki rabawa yara sadaka, sai ki riƙe canjin".
Ba ta kuma tankawa Khalil ba, ta cigaba da iza wutarta, ya tsaya ya zuba mata ido, ta gama soya awarar dake cikin mai, ta zuba masa a leda ta miƙa masa .
Khalil ya ce "Ai ba ni zaki bawa ba, sadaka zaki bayar".
Hafsa ta ce "Ai kai ma kana da hannu, zai fi kyau ace kai ka raba musu da kanka" Nan Khalil ya shiga jinjina halin yarinyar, ana mata abin Arziƙi amma ba ta gani, sai jin kai da tsabar taƙama.
Ya sa hannu ya karɓi ledar awarar, ya miƙa mata dubu biyun, ta kalli hannunsa da yake riƙe da dubu biyun, ta ɗauke kanta ta cigaba da sabgar gabanta.
"Ikon Allah, yau Allah ya haɗani da gamona, to ga dubu ɗaya tun da ba zaki karɓi dubu biyu ba".
Nan ma ɗauke kai ta yi, ta ƙi kallon in da Khalil ya ke.
"Idan ba zaki karɓa ba zan tafi da awarar ba tare da na biya ba".
"Ka daÉ—e baka tafi ba" ta furta a hankali.
Khalil ya durƙusa ya sa mata dubu ɗayan, a gefenta sannan ya juya ya fara tafiya.
Ko É—ago kanta ba tayi ba, balle ta dubeshi, fifita wutar ta kawai take yi.
Yayi gaba ya bawa wasu almajirai awarar, ya kuma waiwayawa yana kallon Hafsa, cike da mamakin wannan tsatstsauran ra'ayi nata.
Amina kuwa tana shiga gida, ta tarar da Baba ya dawo daga ƙauye, wurinsa ta nufa cikin fara'a, shima ya tareta da murmushi yana faɗin "Alhamdilillah".
"Baba an kai ni Makaranta, na zama 'yar Makaranta".
"Alhamdilillah, Allah yayi miki Albarka ya cika miki burinki 'ya ta".
Amina ta ce "Ameen, ka san wani abu Baba?".
"A'a sai kin faÉ—a uwata".
"Baba sufa wannan makarantar a aji biyar ake gamawa, babu aji shida, zuwa baÉ—i ta gaba insha Allah zan gama sakandare".
Baba ya ce "To Alhamdilillah, Allah ya baki miji na gari a birni kiyi Aure, wanda zai kula da cigaban karatunki" Jikin Amina yayi sanyi ta É—an yi shiru tana nazari.
Baba ya ce "Ya kika yi shiru, ko kin fi son ki koma ƙauye ki auri Jarmai?" Da sauri ta ɗago ta kalli Baba ta ce "A'a Baba, nifa ko sunan Mutumin nan bana ƙaunar ji, ni ban tambayeka ya hanya bama, ya ka baro Inno?".
"Duk suna lafiya sunce a gaishe ki, Jarmai kuma ya sa su Yaya Bala a gaba a kan lallai su biya shi kayan Auren da ya kai, yazo ya sameni wai nima saina biya shi, ni kuwa nace masa sisinsa ban gani ba balle in ci, dan haka yaje can wurinsu ya karɓa, amma da ina da kuɗi da na rage masa wani abun".
Amina ta kalli Baba ta ce "Ka jika Baba, Mutanen da ba tare da kai suka ci kuÉ—in ba, akan ne za ka biya abinda ba kai ka ci ba, banda asarar da suka yi maka ma. Baba kalli litattafaina fa, wai duk wannan litattfan nawa ne" tayi maganar tana nuna masa cikin jakarta.
Baba ya buɗe baki, text books kawai sun kai goma sha shida, banda na rubutu, ga math set, da calculator komai akwai, shi kansa Baba ya san wannan kayan sun fi ƙarfin kuɗin aikin da Amina take yi musu.
Baba ya ce "Uwata mutanen nan sun mana karamci, duk na san kina da ƙwazo, amma ki ƙara sannan ki ƙara yi musu godiya, idan mai gidan ya dawo, ki kuma yi masa godiya".
"Insha Allahu Baba zan masa, idan na yi salla fa har Addu'a nake masa, Allah ya ƙara masa Arziƙi da lafiya, ba zan manta alkhairinsa ba"
"Yauwa uwata, har 'ya'yansa ma da matarsa da ahalinsa duk ki dinga saka su a Addu'a".
Amina ta É—an tura baki ta ce "wannan 'ya'yan nasa da basu da kirki".