Sashe 71
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amina dai cike da tsoro ta ce "Kunga, ku gaya masa mu haÉ—u a gida, amma ni ba zan hau motar 'yan sanda ba, kalli jikinku da kaki, kawai idan na shiga ku wuce dani prison"
Ɗaya ɗan sandan dai mamakin ƙarfin hali, da kuma taurin kan Amina yake, ɗayan kuma sai lallaɓata yake.
"Kinga bari in kira miki shi a waya"
"Aiko shi zaka kira nan wurin ba zan hau mota da 'yan sanda ba" ta faÉ—a tana duba hanyar da zata bi ta gudu.
Wayarsa ya É—an danna, Sannan ya saka a kunnensa.
"Yauwa barka dai yallaɓai, gamu a ƙofar makarantar, mun zo ɗaukanta, amma ta ce ba zata hau mota ɗaya da mu ba, infact ma bata yadda kai ka turo mu ba"
Daddy ya ce "Na san a rina, bata wayar"
Ɗan sandan ya kalleta ya ce "To kinga, ya ce a baki wayar kuyi magana" A ɗan tsorace ta kalleshi ta ce "To idan na karɓa nayi maganar, zaku barni na tafi?"
"Eh, sai abin da ya ce dai"
Kamar wadda ake miƙawa kashi, haka ta karɓi wayar, tana Addu'ar Allah ya sa ba tana Magana wani abin zai sameta ba, ko matsafa ne.
"He..h....hello Daddy"
"Mmwummm" shi ne abin da ya faÉ—a daga cikin wayar.
Kamar mai tsoron magana ta ce "Daddy kana jina?"
"Mmm"
"Daddy dan Allah kayi magana, wasu ne wai zasu tafi da ni in jika"
"Baki iya sallama ba sai Hello?"
Ya faÉ—a yana gyara kwanciyarsa a kan kujerar 3seater.
"Yi haƙuri a tsorace nake ne, 'yan sanda ne fa suka zo zasu tafi da ni"
"Eh laifi kika yi, na turo su su kamo mini ke"
Zaro ido tayi kamar tana gabansa ta ce "Laifi ni É—in, me nayi da zaka haÉ—ani da police?"
"Sai sun kawoki zaki ji laifin da ki kayi, idan kuma kika cigaba da yi musu gardama, za su saka miki handcuff su sako mini ke a motar su kawoki".
"Na shigesu ni Amina, 'yan fashi fa ake sawa wannan sarƙar, dan Allah kayi haƙuri" tayi maganar cikin shagwaɓa tana marairaicewa.
"Oya, ban da gardama ki biyosu ni na turo su"
Jiki a sanyaye ta ce "To" ta miƙawa ɗan sandan waya, ta bisu, suka buɗe mata mota, ta shiga suka ja suka tafi.
Gaba É—aya zatonta gidan da suke zasu tafi, amma taga sun sauya hanya.
"Bayin Allah ya haka?" Ta faÉ—a tana waige waige.
"Meyafaru?" Cewar É—an sandan da ya haÉ—ata da Daddy a waya.
"Naga mun tafi wani wurin daban, ba Tudun yola zamu ba?"
"Ba nan zamu ba, gidan da kuka je tare ya ce a kaiki"
"Na shiga uku ni Amina" ta faɗa a hankali, tare da sallama cewar wani aikin zai kuma sakata yauma, gashi ta gaji matuƙa yau ɗin nan.
Tana ta zancen zuci, har suka isa gidan, parking suka yi a cikin gidan, wurin ajiye motoci, Amina yau har da motocin da bata gani ba wacan karon ta gani yau, har mamakin yadda Daddy yake yi da motoci take.
Suka buÉ—e mata ta fito, ta É—aga kai ta kalli gidan sannan ta ce "To yana ina Daddyn?".
"Ki shiga, yana ciki"
"Ciki ina kenan?"
Ɗan sandan ya fara ƙufula da surutunta da tambayoyi, amma ya daure ya ce "Hanyar da kuka shiga wancan karon, ita zaki bi.
Cike da fargaba da salati, Amina ta nufi hanyar da suka bi tare suka shiga gidan a wancan karon.
Babu kowa a makeken falon, sai dai ko ina fes da shi. Ko yana ina oho? Ta tambayi kanta da bawa kanta amsa.
Wata siriryar hanya ta bi, zuwa falon da ya saka ta jera Abinci ranar da yayi baƙi.
Ta tura ƙofar ta shiga, ya ɗago idonsa ya kalleta a cikin uniform ɗinta, riga da skirt sun mata kyau sosai, sai uwar jakarta ta goyo. Shi kuma yana sanye da yadi mai taro taro maroon, kansa babu hula, yana shan ruwa a kofi.
Girmansa da kwarjininsa suka cika mata ido, ta ƙarasa cikin falon, ta durƙusa ta ce "Ina wuni?"
"Ban ganshi ba" ya bata amsa.
ÆŠagowa tayi tana mamakin irin amsar da ya bata.
Ya É—an É—age mata gira ya ce "Yes, ban ga yini ba, ko in ce yana gidan biki ko?"
Amina ta sunkuyar da kai, saboda haka kawai take jin ta takura, wannan keɓewar tasu bata dace ba.
"Na saka an kamo mini ke, saboda laifin da kika yi mini".
"Laifi kuma?" Tayi maganar a É—an raunane.
"Eh laifi mana, ai ke ba kya daina laifi, na fuskanci kina da taurin kai"
Amina tayi shiru tare da sunkuyar da kanta ƙasa, dan ita dai bata san laifin da tayi ɗin ba.
"Me nace miki game da tsaya da wani, dan tsabar rashin ji kuma a titi, zaki tafi makaranta"
Sai yanzu ta tuna, da safe ya gansu tare da Bilal, ta É—ago ta ce "Daddy tsaya ka ji nayi maka bayani"
"A zaune nake ai, ba wani bayani da zaki yi mini, ba kya jin Magana ne kawai, kuma zan gayawa Malam Hassan É—in abin da kike"
Ta marairaice ta ce "Ka tsaya ka ji dan Allah, wallahi shi ne ya biyoni wai sai ya rakani, ai kaga ba zan kore shi ba, wulaƙanci babu kyau"
Alhaji Ahmad ya gyara zamansa ya ce "Ni meye ya hana ki nemi in rakaki?"
"Ni a wa? Ni dai dan Allah kayi haƙuri, ka sa a mayar da ni gida"
"Aminatu ba kya ji sam, sai na É—au mataki a kan abin da kika yi"
"Wallahi Daddy ina ji, kayi haƙuri, ni ban san ya zan masa ba, amma zan gaya masa ka ce kar ya sake shiga harkata"
Kan Alhaji Ahmad yayi magana, aka kira shi a waya, ya sa hannu ya É—aga wayar, ya kai kunnensa.
Ba ta jin me ake cewa daga cikin wayar, ta dai ji yana cewa "Jiki Alhamdilillah, ya yi sauƙi jinin ma ya sauka, shi ma sugarn nawa ya sauka sosai"
Amina dai ta sake gyara zamanta, tana É—an satar kallon Alhaji Ahmad.
"Eh, da ina tunanin zan ɗan je wata ƙasar in ɗan huta, amma a yanzu na samu wata Cartoon me Sani nishaɗi"
Dariya yake sosai a wayar, sannan yayi sallama da wanda suke wayar, ya ajiye, ya kalli Amina a ya ce "Oya, a É—an sama mini abin da zan ci, kan ki tafi"
Æata fuska Amina ta yi, ta ce "Dan Allah Daddy..." Sai kuma tayi shiru.
"Ina jinki" ya faÉ—a yana danna wayarsa.
"Kaga Baba bai san ina nan ba, kuma ni Hajara tabi ta saka mini ido, gani take wani abu ne a tsakanina da kai"
"Wani abu kamar me?"
"Ranar fa da ka ce in kai maka shayi na daÉ—e, bina ta dinga yi tana tambayata wai ya aka yi na daÉ—e, da ranar da ka ce ba zan tayata aiki ba, duk ta bi ta saka mini ido, ita ma ka dinga sakata aiki kar ta zata da wani abu a tsakanin mu"
Dariya ta ga yana yi, ya ce "Akwai wani abu a tsakaninmu mana, tsoron me kike ji?"
"Ni meye a tsakaninmu?"
Ya É—an yi murmushi ya ce "Kinga, yanzu dai tashi ki je kitchen, ki sama mini wani abun in ci"
ÆŠan tsuke fuska tayi, tana jin Daddy ya takurata.
Daddy ya ɗan zuba mata ido ya ce "Ko in haƙura?"
"A'a zan yi" ta faÉ—a a sanyaye.
"Yauwa Cartoon É—in Daddy, a taimakawa Daddy"
"Cartoon kuma?" Ta faÉ—a tana É—an tura baki.
"Eh mana, tashi da sauri, dan ki kammala da wuri mu tafi gida"
Amina ta ajiye jakarta, ta nufi kitchen, sai da ta ɗan tsaya tana tunanin mai zata girka, wanda zai iya ci saboda ciwonsa.
Ta cire ƙaramin hijjabinta ta rataye ɓalle rigar saman ta rataye, ya zama daga ita sai rigar uniform ta ciki, da skirt ɗinta, sai kuma hular hijjabin, kana ganin gashinta da ta ɗaure da ribbon.
A nutse ta fara gudanar da aikinta, tamkar tana kitchen É—in gidanta.
Gaba ɗaya Yazid bai fahimci lectures ɗin yau ba, saboda yana cikin damuwa, yayi mamakin abin da Fadila ta gaya masa, bai taɓa tunanin jin wannan maganganun daga bakinta ba.
'banda abinka kai ma Yazid me ya aikeka, ina kai ina ina wannan yarinyar, suturar da take sawa kawai, ta isa ta nuna maka ruwa ba sa'an kwando bane' wata zuciyar ta tunasar da shi.
Haka nan jiki babu ƙwari, ya ja jiki yaje yayi sallar azahar, daga nan ya wuce gida.
Khalil kuwa tun da Allah ya sanya ya sauka a garin Abuja ƙarfe tara na safe, ya wuce gidan da yake zaune a can garin Abujan, ba im da ya kuma fita ya je, sala ce kawai take fito da shi daga gidan, ko Abinci ya kasa yin order ya ci, loka lokaci ya kan buɗe saƙonnin Hafsa da take turo masa a baya, da hotunanta ya zuba musu ido. Maganganunta ha dinga tunawa, da take jadadda masa na ya riƙeta da amana. Har ga Allah ya ci burin auren Hafsa ya zauna da iga saboda Allah, ya sama mata farinciki, amma Mummy ta ɓata komai, babu Wanda za aayi masa abin da Mummy ta yiwa su Hafsa ya iya haƙuri, sai dai idan ba shi da zuciya.
Duk yadda Khalil ya so ya yi tunanin mafita kasawa ya yi, ƙarshe ma kansa ne ya fara ciwo, amma ya kasa yadda zai iya cigaba da rayuwa ba tare da yana cigaba da magana da Hafsa ba, ya ɗauki wayoyinsa duka ya kashe su, ya ajiye.
Amina ta gama girki, sai aikin yanka salak da take yi, tana ta decoration É—insa a tray.
Ji tayi kamar motsi a bayanta, ta juyo gaba É—aya dan ganin meke motsi a bayanta, sai taga Daddy ne ke shigowa.
Tsananin kunya ce ta kama Amina, saboda jikinta babu hijjabi, sai rigarta ta uniform 'yar ciki, kuma rigar ta kama jikinta sosai. Da sauri ta kai hannu tana kare ƙirjinta, ta juya da sauri, sai kuma ta tuna shi kansa skirt ɗin a matse yake, kuma tayi stock in ɗin rigar.
Murmushi Daddy ya yi, ya nufi fridge ɗin kitchen ɗin, still Amina ta kasa sakewa, sai ɓoye ɓoye take.