← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 84

Sashe 42

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummy ta É—an yi shiru sannan ta ce "Wai ni 'yar waye Yarinyar nan, yakamata in sani tunda wuri".

"Waya san masa, shi zaki tambaya".

Bai fi mintuna Arba'in ba, Khalil ya sake kiran Hafsa, ya ce ta zo ta shiga da shi, amma taƙi fita, ta gaya masa lambar ward ɗin da suke.

Sai da ya daure sannan ya iya shiga ɗakin, marasa lafiya sun kai mutum Ashirin a ciki, sai ƙarni da warin Asibiti da ke surnanowa daga cikin ward ɗin, haka ya daure ya shiga, tun da ya shigo ta hango shi, amma ta basar yaita lalube ya gano su.
  Sai da ya ƙaraso sannan Mama ta gane shi, ya nuna kamar bai ga Hafsa ba, ya durƙusa ya gaida Mama, ta amsa masa cikin kulawa.
Nan ya zauna yana yiwa Mama sannu, Mama ta kalli Hafsa ta ce "Ke baki iya gaisuwa ba?".

Fuskarta ba fara'a ta ce "Ina wuni" ba tare da ta kalli Khalil ba.

"Mama ƙyaleta, bana neman gaisuwata, Fushi nake da ita, Mama kwana uku kina Asibiti amma yarinyar nan ta kasa kirana a waya ta gaya mini, sai ma wani cika da take tana batsewa".

"Da na kiraka kana ɗagawa ne?" tai maganar tana kuma ɓata rai.

Mama sai da ta ƙulu da abin da Hafsa tayi, amma tayi shiru ta rabu da ita, kasancewar likitan da zai sallami Mama bai shigo da wuri ba, ya sanya ya ce Mama ta bari sai da safe.

Ya tashi zai tafi, ya sanya hannu aljihunsa, ya ciro kuɗi ya ajiye a kan side bed, Mama za tayi magana Hafsa ta rigata "A'a ka barsu gaski... Ba ta ƙarasa ba Khalil ya watsa mata wani irin kallo, da ya sanya ta haɗiye maganar da take son ƙarasawa.

Ya kalli Mama ya ce "Mama in dai ni ɗanki ne, bai kamata ki ƙi karɓar abin hannuna ba, Allah ya baki lafiya, gobe Insha Allah in an sallameki, zan zo gida in sake dubaki" yayi sallama da Mama ba tare da ya ko kalli Hafsa ba, yayi gaba abin sa, tabi bayansa da kallo tana jin haushin yadda ya shareta.

Bayan fitar sa sai da Mama ta yiwa Hafsa ta tas, a kan abin da take yiwa Khalil.

  Amina tana ta ƙoƙarin kula da Baba, amma Hajiya Zainab da Fadila suka tsiro da wani wulaƙanci, da sun fuskanci tana son wurin Baba, sai a tsiro da aikin da za'a sakata su hanata zuwa, haka kurum 'yan kwanakin nan suke tsangwamarta, ta rasa me ta tare musu.
  Yau ɗaya daga cikin 'yan ajinsu Amina take sauka Alqur'ani, kuma an gayyaceta, tana son zuwa ko dan ta ƙare sanin kan cikin birnin Kano. Ta nunawa Baba katin gayyatar, ya amince taje, tare da yi mata nasiha sannan ya ce ta tambayi Hajiya Zainab, kar fitar tata ta zamana laifi.
Ba dan Amina ta so ba, ta tambayi Hajiya Zainab, ba ta sa ran ma zata barta ba, amma cikin ikon Allah kawai taji ta amince.
  Amina ta dinga murna, dama sun yi da ƙawarta Azima, zata biya gidansu su tafi tare, dan bata san gidan saukar ba.

Duk da gidansu Azima bai kai na su Fadila girma da kyau ba, amma suma da gani suna da kuɗi sosai, sai dai halayyar 'yan gidansu Azima ya sha banban da na su Fadila, Maman Azima na ganin Amina, ta karɓeta da fara'a tana faɗin "Yau ga Aminan Azima a gidana, kullum sai an bani labarin Amina H shanono, yau dai gani gata" Amina ta ƙunshe fuska tana murmushi.
Maman Azima ta ce "Tana can tana wanka, ita da idan ta shiga banÉ—aki, tamkar tana É—akinta, bari a kawo miki Abinci".
"A'a Ammi na ƙoshi" ta ɗan tsuke fuska ta ce "Hala ita Aziman bata gaya miki idan an zo gidan nan ba na bada abu aƙi karɓa ba? Dole ki ci Abinci Amina, ga ɗakin Aziman can, ki shiga sai a kai miki Abincin can" Amina ta shiga ɗakin Azima, ɗakin ya haɗu sosai da sosai.
Azima na fitowa daga wanka, taga Amina, ta daka tsalle ta rungume Amina.

"Ke cikani kar ki tsirara malama"

Azima ta ce "Ashe zaki zo É—in 'yar rainin hankali kawai, amma dai ba da wannan shigar zamu je wurin saukar ba?".

Amina ta kalli kanta ta ce "Me shigata tayi?"

"Ke ba zamuje a raina mu ba, kin san halin 'yan ajinmu, bari in shiga shagon Ammi, in É—auko miki sabuwar riga" Amina ta zaro ido tana shirin magana, mai aiki ta shigo É—akin, ta dinga ajiyewa Amina kayan ciye-ciye.

Azima ta fita ta dawo da wata rantsatiyar doguwar riga purple da takalmi da jaka duk kalar rigar.

Azima ta ce "Gashi nan Ammi ta ce a baki ki saka" da yake Ammi na da shagon botiques a cikin gidan.

Jiki a sanyaye Amina ta ce "Azima, kin san ni wacece, dan Allah ki bar kayan nan, in je da na jikina"

"To sai ki je ki gayawa Ammin ai"

Amina fafur taƙi yadda ta saka kaya, sai da Ammi ta zo da kanta, Amina ta ce "Ammi ba ƙin karɓa nayi ba, Baba zai tambayeni ina na samo kayan nan, kuma gidan aikina zasu tambayeni".

"Kar ki damu, direba ne zai kai ku, ya mayar da ke gida, sai a yiwa Baban naki bayani"

Da ƙyar Amina ta yadda, ta cire hijjabin jikinta, da yayi haske saboda ya gaji, tun irin wanda ta zo da su daga ƙauye ne.
Ta canza kaya zuwa doguwar rigar nan, ga uban gashinta da yake natural, ta tattare shi da tsohon ribbon.
Azima ta sakata a gaba, ta saka comb tana taje mata gashin nan, ta shafa mata mai, ta kawo kayan make up, tayi mata simple make up.
Azima ta ce "Ke yarinyar nan Allah yayi miki kyau, amma ko hoda ba kya shafawa haka kike yawonki"

"Ke ni ƙyaleni da wata hoda" yadda Amina tayi kyau, ba zaka ce daga ƙauye take ba, Azima ta buɗe wani irin turare mai ƙamshin gaske, ta shafawa Amina ita ma ta shafa.
Suna fita falo Ammi ta rungume Amina, "Kai Masha Allah da wannan kyakykyawar yarinya, bani wayata in mata hoto"

Amina har mamakin karamcin Maman Azima take yi, ita babu ruwanta kamar ba mai kuÉ—i ba, 'to kenan masu kuÉ—in ba kowane me irin halin su Hajiya Zainab ba?'

Da zasu tafi har harabar gidan Ammi ta rakosu, ta cewa direba "Ga su nan ka kula mini da su, ka kai su wurin walimar saukar, kar a bari magariba tayi, duk in da suka yi awa É—aya da rabi, kai mayar da Amina gida, ga kaya nan na bata, ga wasu a ledar nan, ka yiwa Abbanta bayanin ni na bata, sai ku taho kai da Azima".

Amina tai ta yiwa Ammi godiya, tayi mamakin tsananin karamcinta, sam ba ruwanta da wata É—agawa.

Haka kuwa aka yi, suka fara zuwa wurin sauka, aka yi walimar sauka a cikin ƙawayensu, Amina taji daɗin wannan fitar sosai da sosai.

Kamar  yadda Ammi tayi umarni, har gida aka mayar da Amina, direba ya yiwa Baba bayani kamar yadda Ammi ta umarce shi.
Bayan tafiyar su Azima, sai da Baba yaita yiwa Amina nasiha tare da gargaÉ—inta a kan ta iya talaucinta.

Khalil da ke zaune a mota yana shirin fita, ya zubawa Amina ido, bai taɓa ganinta ba hijjabi ba sai yau, rigar kamar da jikinta aka auna aka yi ta, saboda yadda ta zauna cif a jikinta, yana cikin motar ta zo ta wuce cikin gidan, hannunta riƙe da wata babbar leda.
Ajiyar zuciya ya yi, ya kunna motar ya bar gidan.

Amina a falo ta zauna, ta buɗe robar gugguru ta fara ci, ƙamshin turaren Alhaji Ahmad ne ya fara cika wurin kan ya bayyana, ya turo ƙofar falon da sallama, Amina ta amsa  ƙasa ƙasa.
Duba falon yake yana son gane daga ina yake jin tashin ƙamshin wani turare na musamman. Har ya zo zai gifta kunnuwansa suka jiyo masa muryarta "Daddy sannu da zuwa" kallon in da Amina take yayi, sai dai ba shi tabbacin ko Aminan ce, saboda yadda ta ke haɗe cikin riga mai kyau, kuma shi da hasali ma yarinyar sai ta ga dama take gaishe shi, dan haka kawai ya wuce bai amsa ba.
  Amina ta gama ciye-ciyenta, sannan ta tashi da nufin ta je wurin Hajiya Zainab, ko da aikin da zata yi mata, saboda tana son ta shiga ɗakinta tayi rubutunta na Alqur'ani, wanda idan tana yi, bata buƙatar takura.
Kanta a ƙasa tana sauri, suka yi karo da Alhaji Ahmad dake ƙoƙarin fitowa daga sashin Mummy. Amina ta firgita sosai ɗan ƙaramin mayafin kanta ya sauka, tarin gshinta ya bayyana.
Ganin ya zuba mata ido ya sanya ita ma ta ɗan tsare shi da nata idanuwan, tana ƙoƙarin gyara mayafinta.
"Ba kya gani ne?" Ya furta yana kuma tsareta da ido.

"Yi haƙuri ban san ka taho bane" guntun tsaki ya ja, ya raɓa gefenta ya wuce. Amina ta taɓe baki ta ƙarasa ciki.

Bayan sallar isha'i, Khalil ya koma gidan su Hafsa, 'yan kwanakin nan ya sarƙi zuwa gidan, Jikin Mama yayi sauƙi sosai, Khalil ya ji daɗin yadda ya ganta, suka taɓa hira tare da sake yi mata sannu.
Yau ma bai kula Hafsa ba bata kula shi ba, sai da zai tafi Mama ta ce Hafsa ta raka shi.
Ba ta son yiwa Mama gardama, ta rako shi har gaban mota, ba tare da ta ce masa uffan ba, suna zuwa bakin motarsa ta juya zata koma gida abinta, cikin zafin nama Khalil ya riƙo hannunta, ya buɗe motar sa ya sakata a ciki, ya rufe ƙofar, ya zaga ɗaya site ɗin ya shiga.

"Meye haka? Dan Allah ka buÉ—e mini in fita, sai kasa mutanen unguwa sun mini wani sharrin?"

"Idan sun miki sai me? Ke da mijinki ne ai ko? Hafsa meyasa kike mini haka ne, kin fi son in ta wahala ko baki damu da ni ba?".

Ta tura baki ta ce "Eh ai nima baka damu da ni ba, da na dinga kiranka ka ƙi ɗauka"
Chapter 42 · 0% Book details