← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 84

Sashe 16

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Koma meye tsakaninku wani abu ne da ya shafe ku, nan kuma titi ne bai kamata ba abin da kake yi".

Banza yayi masa ya cigaba da surfa rashin mutunci son ransa, amma duk yadda ya so Hafsa ta tanka masa taƙi, ya gama bala'in sa ya hau motarsa ya tafi.

Bayansa ta bi da kallo har ya ɓacewa ganinta, sai da ya bar wurin wasu hawaye masu zafi suka shiga zubowa daga idanunta 'Allah ka nuna mini ƙarshen mutumin nan da ire irensa kan ƙasa ta rufe idona'.

Ganin tana kuka, Mansur mai shayi ya ce "Kiyi haƙuri Hafsat, mutane irin wannan sai haƙuri ba su da mutunci ba su da kirki" Hafsa ba ta ce masa uffan ba ta cigaba da share hawaye, haka ta kammala cinikin nan babu daɗi ta haɗa kayanta ta koma gida.

Tun da Hafsa ta koma gida Mama ta fuskanci akwai damuwa a tattare da Hafsa, duk da Hafsa ba mai yawan magana ba ce, kuma ba Yarinya ce mai fara'a ba, amma shirunta da ƙaruwar haɗe fuskarta ya sanya Mama ta gane hakan.

"Hafsa lafiya kuwa?"

"Lafiya ƙalau" ta amsa a ciki.

"A'a ba lafiya ba, mai yake faruwa ne?"

"Mama bakomai fa".

"To koma meye Allah ya ye miki, Idan ba ki gaya mini damuwarki ba, ban sani ba ko akwai wani wanda ki ke da shi a waje da zaki gaya masa" Hafsa ba ta kuma cewa Mama komai ba, ta cigaba da abinda take yi. Wasu lokutan Mama tana jin haushin miskilancin Hafsa, amma kuma gado ta yi haka mahaifinta ma yake, amma har gara shi a kanta, babban abin da Mama take ji shi ne, ba kowane namiji ne zai iya jure halin Hafsa ba.

Mama ta zuba mata ido, saboda kar Mama ta cigaba da takura mata da tambaya, ya sanya ta dinga ƙaƙalo aiki tana yi, ta kwaso kayan wanki ta wanke a daren, ta tsiri wanke wanken  kayan kitchen gaba ɗaya, ta je ta sayo waken awarar gobe, duk wannan aikace-aikace da take yi, ba ta kula Mama ba, ta zauna zata fara gyaran wake, Mama ta yi gyaran murya ta ce "Ajiye waken nan, ki zo ki zauna ki huta, ba zan sake tambayar ki meke damunki ba, tunda dan gujewa tambayar tawa ya sa ki ke ta wannan aikace aikace". Aikuwa sum sum kamar munafuka Hafsa ta koma ɗaki, ta nemi wuri ta kwanta ba tare da ta ko ci Abincin dare ba, Mama kuma ba ta kulata ba ta ƙyaleta.

Amina ta wayi gari a birni, ta gabatar da sallar Asubahi, ta zauna ta na karanto azkar É—in ta kamar yadda ta saba, tana nan zaune ta ji motsi dan haka ta tashi ta fita, aikuwa taga Hajara ce ke kaiwa tana komowa.

Amina ta gaida Hajara cikin girmamawa, dan dama Hajara ta girmeta, Hajara ta amsa tare da cewa "Har kin tashi?".

"Eh na tashi, nuna mini hanyar fita waje, in je in gaida Baba".

Hajara ta nuna mata, Amina ta fita ta tafi. A ƙofar ɗakin Baba ta tsaya ta ƙwanƙwasa, ya ce "Waye a nan?"

"Baba ni ce"

Baba Hassan ya buɗe ƙofar, ta durƙusa ƙasa ta gaishe shi, ya amsa sannan ya ce "Ya a kai kika fito da duku-duku haka?"

"Baba gaisheka na zo na yi, sannan in ganka"

Yayi murmushi ya ce "To bismillah" suka shiga ɗakin da Baba yake, abin ka da 'ya da uba, an daɗe ba a haɗu ba, suka dinga hira ta bashi labarin abubuwan da suka faru a ƙauye, har ƙazafin cikin da suka yi mata, da sayar da gonarsa da irin kayan da suka saya mata ta gaya masa.

Baba ya yi ajiyar zuciya ya ce "Bakomai, watarana sai labari, ni dai fatana da burina ki mayar da hankali kiyi karatun nan kin ji uwata"

"To Baba zan yi insha Allah"

"Yawwa uwata, Allah yayi miki Albarka".

"Ameen Baba, amm ai zakaje ƙuye su biyaka gonarka ko?"

"A'a Amina, ai gona ta riga ta salwanta, zan dai je garin in musu bayanin kina wurina".

"Baba ba wani mataki da zaka É—auka? Dubu É—ari uku fa suka sayar da gonar".

"Ba komai, Allah ya mayar mini da alkhairi".

"To Wallahi Baba ka yi musu Allah ya isa".

Baba Hassan ya buÉ—e baki ya ce "Uwaki nace, yayyen nawa zan yiwa Allah ya isa?"

Sai Amina ta fara hawaye "Haba Baba, tun da na buÉ—e ido suke cutarka, kai baka cewa komai, su yi ta zaluntar ka dan sun ga babu mai tare maka, Wallahi Allah zai saka maka"

Baba Hassan ya ƙurawa Amina ido, yana jin soyayyar 'yar ta sa a ransa, ita dai a duniya kar a taɓa mata shi, ko a cutar mata da shi.

Ya sa hannu ya share mata hawayen fuskarta ya ce "Tashi maza ki koma ciki, kar su neme ki, zamu cigaba da hirar" da ƙyar Baba ya sa Amina ta tashi ta koma cikin gidan.

A falo ta tarar da Hajara, na ƙoƙarin fara moping, a nan ta tsaya Hajara ta dinga nuna mata yadda ake ayyukan gidan, da wuraren da suke ajiye kayan amfani.

Daga nan suka shiga kitchen, suka fara ƙoƙarin haɗa Abincin karin kumallo. Ƙarfe takwas da rabi suka kammala komai, Hajara ta lura Amina ba ta da ƙyuwa sam, ga kaifin basira.

Sun gama shirya Abincin a kan dining, Hajiya Zainab ta fito daga sashin Fadila, tana gaba Fadila na binta a baya.

Hajara ta risuna kamar baiwa tana gaida Mummy da Fadila, Amina kuwa da murmushi a fuskarta ta gaida su, sai dai yadda suka amsa gaisuwar a wulaƙance ne ya bawa Amina mamaki, dan ita Fadila ma ko amsa gaisuwar ba tayi ba.

Hajiya Zainab ta kalli Amina sannan ta mayar da kallonta ga Hajara ta ce "Ina fatan kin fara nuna mata yadda aikin gidan nan yake?".

"Eh Hajiya na fara nuna mata"

"Yawwa, ki buɗe kunnenki da kyau ki ji abin da zan gaya miki, da dokokina na gidan nan, idan kika karya mini doka korarki zan ki koma in da kika fito. Na farko bana son ƙazanta, bana son munafunci da sa ido, duk abin da zaki ga an yi a gidan ba ruwanki, tun da ba gidanku bane ba. Sannan bana son munafunci da gulma, sannan duk wanda ya saki a gidan nan kome kike dole ki ajiye kiyi abin da aka saki. Ina da yara biyu ɗayan namiji ne baya nan amma yana zuwa hutu gida, ba na son shishshigi a kan abinda ya shafi rayuwata da ta yarana. Abu na ƙarshe idan kin san ki na da wani mugun hali na sata ko makamancin haka ki tabattar kin baro su can a ƙauyenku, dan ba zan ɗauki duk wani rashin daraja da rashin ɗa'a ba" Amina ta ji haushin kalaman da Mummy ta yi amfani da su wurin yi mata bayanin aikin nata, amma ba ta nuna hakan ba sai ma cewa ta yi "Insha Allah zan kiyaye"

Mummy ta ce "Fadila do you have anything to say?"

"Nothing much, you have said it all. Kawai ni dai a bi abinda nake so a gidan nan a zauna lafiya, idan kuma akasin haka ya faru, za a ga abin da zai biyo baya"

Mummy ta ce "To, kar ki sa ran zuwan ki gidan nan, kamar buƙata ta biya ne, zan jarrabaki na 'yan kwanaki in ga kamun ludayin aikin naki, idan yayi mini shi kenan, idan bai mini ba kuma ki koma in da ki ka fito, idan yayi mini ɗin, sai in ga sashin da zaki din ga kula da shi a gidan nan".

Amina dai ta yi shiru tana wasa da yatsun hannunta. Hajara ta ce "Amina ta so muje mu cigaba da aikin"
Amina ta tashi ta bi Hajara, tana mamakin yadda Hajiya Zainab da 'yar ta ke gatsa magana ba girmama É—an Adam sam.

Hajara ta ce "Amina sai fa kin yi haƙuri, idan har kina son zamanki a gidan nan dole ki ji ki ƙi ji, dan ba ki ga komai ba in dai wannan matar ce"
Amina tayi ajiyar zuciya tare da jinjinawa Hajara kai.

ÆŠakin Fadila suka nufa, Suna shiga É—akin Amina ta yi turus, É—akin kaca kaca, har da kwanukan Abinci a É—akin. Ga takardu da litattafai ko ina, har da kofi a kan gado, ta cire kaya duk ta watsar a É—akin, banda takaddun biscuit da na chocolate duk a É—akin a watse.
Ga É—aki har É—aki mai kyau, amma kamar makwancin mahaukaciya.

Amina ta ce "Wannan É—akin waye?"

"Ɗakin 'yar masu gidan ce, kin ganshi nan dai kamar ɗakin jaka, gashi ba ta son ƙazanta, amma fa Komai sai dai a yi mata. Idan ta tashi daga kan gado, cire bedsheet ake a bayar a wanke, ana wanke mata banɗaki sau uku a rana. Haka ma gyaran ɗaki, kuma idan zaki gyara mata ɗaki sau goma idan ta shigo komai a in da ta ga dama zata watsar da shi. Idan ta dawo daga unguwa ko Makaranta, tun daga falo take fara zubar da kayanta, sai dai ki bi Falon ki kwaso mata kayan, tana da kyauta ba kamar uwatta ba, amma duk alkhairinki a gareta, rana ɗaya idan ki ka yi mata abin da bata so, sai ta ƙare miki cin mutuncin da sai kin rasa ina zaki saka kanki, idan ba ki sa'a ba kuwa har uwatta zasu haɗu su ci miki mutunci, dan haka sai ki shirya! Sai kin mayar da kan ki baiwa a wurinsu zaku zauna lafiya".

Nan take jikin Amina yayi sanyi, tana iya jure komai aiki wahala da makamantansu amma ba ta son wulaƙanci, ta fara wasi wasin anya zata iya kuwa? Zata iya jure a ci mata mutunci a kan abinda bai kai ya kawo ba?. Haka suka gyarawa Fadila ɗakinta, suka koma sashin Hajiya Zainab suka gyara ko ina, amma babban abin da ke sake bawa Amina mamaki bai wuce yadda Hajiya Zainab ke ta faman yi musu tsawa ba, ko Magana za a yi musu, sai cikin tsawa da harara.

Kwanaki biyu kenan ɓatan Amina ya karaɗe ƙauyen nan gaba ɗaya, ga Jarmai ya ɗagawa su Baffa Bala hankali, dan ya riga ya gama saka rai da samun Amina.
Chapter 16 · 0% Book details