← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 84

Sashe 19

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rashin sa'a, invigilator ya hango su, aikuwa yana zuwa ya rubuta wa Yazeed -10 marks a paper É—in sa, ba tare da ya hukunta Fadila ba. Babu wanda ya san mai ya faru, sai Fadilan da Yazeed, dan lecturer bai yi magana ba, kawai zuwa ya yi kan Yazeed ya tsaya, yayi masa minusing, yana yi masa minusing É—in kuma, Yazeed yai submitting paper ya tashi ya fita.
Fadila kuwa ko a jikinta, ita dai tun da Allah ya sa ta samu abin da ta rubuta shikenan, Yazeed yayi asarar maki arba'in a test.

Inno kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, ganin Malam Hassan a gida, ta dinga murna, nan ta tashi ta fara ƙoƙarin ɗora girki, ya ce "Ba sai kin dafa komai ba, dafa ruwan zafi ga kayan shayi na taho da shi, 'yar ki kuma ta bada kayan kari a kawo miki".

Inno ta ce "Aikuwa Malam ina ta baza ido in ganku tare, ni nan Saminu ya ce mini tana wurinka, ko dai ƙarya yayi mini?".

"A'a bai miki ƙarya ba, ke dai gama ki zo mu yi Magana".

Bayan Inno ta dafo ruwan zafi, Baba Hassan ya ajiye mata tulin soyayen dankali da miyar ƙwai, Inno ci take tana santi, tana anya na taɓa cin abinci mai daɗin wannan a duniya? Baba Hassan ya yi murmushi, ya ce "bani labari, yaya aka yi da ba na nan game da Amina?".

Nan Inno ta kwashe komai ta gaya masa, har zuwa ɓatan Amina.

Shima nan ya warware mata cewar, Amina wurinsa ta je, kuma ga hukuncin da ya yanke a kanta.

Inno ta ce "Amma malam kaja ganin hakan daidai ne? Yarinyar nan ba ta ɓatawa kanta suna ba kuwa? Kun ɗau bokon nan kun sa a ranku kai da ita kamar ibada".

"Hannatu, boko ba ibada ba ce, amma ba zaki gane rashin boko na cutar mu ba, sai kinji birni kin ga amfanin boko, insha Allah zamu yi alfahari da ilimin da Amina za ta samu".

"To ubangiji Allah ya sa".

"Salamu Alaikum! Salamu Alaikum!" Aka shiga kwaÉ—a sallama. Murayar kawu Lawan ce yake kwaÉ—a sallama shi da Bala.

Baba Hassan ya fita cike da fara'arsa yana musu sannu da zuwa, ya shimfiÉ—a musu tabarma a tsakar gida, suka zazzauna Baba Hassan ya gaida su cikin mutuntawa a matsayin su na yayyensa.

Maimakon su amsa sai kallon Banza da Bala ya yi masa ya ce "Ina fatan labri ya iske ka na abin kunyar da 'yar ka ta yi? Mun zaɓa mata miji za muyi mata aure, amma ta tsallake ta gudu ta shiga yawon duniya".

Baba ya ce "Ashsha, ba yawon duniya ba dai Yaya Bala".

"To yawon me ta tafi? Waye ya san in da take, ta bi ta ɓata mana suna da zuriyar mu a gari".

Baba ya ce "Yaya ba ina goyon bayan abin da Uwata ta aikata bane, amma sanin kan ku ne duk garin nan ba wanda bai san Jarmai ba mutumin kirki ba ne, maiyasa za a bashi Aurenta?"

Lawan ya ce "Idan ba a bashi ba haka za a barta ta cigaba da yawo a gari soƙai-soƙai sa'ar iayyenta ba aure, saboda wata matsiyaciyar bokon banza, to ka sani idan ta dawo daga yawon banzan nata ba dai a gidan nan ba, ta je idan dai bariki ce, na baya ma ba su ci riba ba".

Baba ya ce "Subhanallah, Amina dai ba wani ta tafi ba, tana tare da ni a in da nake aiki a can birni, kuma gidan da nake sun É—auketa aiki, da albashinta zasu dinga biya mata kuÉ—in Makaranta".

Tafa hannu suka shiga yi suna salati.

"Hassan, yanzu abin da ka aikata ka yiwa kan ka adalci kenan? Yanzu wannan zabgegiyar budurwa ka kai birni ta yi boko? A ƙauyen ma ya muka ƙare da ita, har muna faɗa ta faɗa saboda ta yi boko, shi ne ka kaita birni ta yi boko?" Cewar Lawan yana zazzaro idanuwa.

Bala ya ce "Ka kyauta da kuka haɗa kai da 'yar ka kuka ɓata mana suna, mun gama shirin biki da gayawa jama'a ɗaurin Aure, amma ta gudu, ga Jarmai ya ɗaga mana hankali mu biya shi kuɗinsa.
Amma in Allah ya yadda, tun da aniyar alkhairi muka yi niyyar ɗaurawa, amma kasa ƙafa ka rusa kai da ita, ku ka nuna bamu isa ba, insha Allah naku burin ba zai cika ba, in Allah ya yadda sai ta yi cikin shege a birnin nan, sai ta dawo da mummunan abin kunyar da sai ka kasa haɗa ido da mutane, sai bokon nan ta zame muku bala'i da masifa kai da ita!!!"

Dafe ƙirji Baba ya yi ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"

Inno da take É—aki tana jiyo su É—ora hannu ta yi a ka, jin jafa'in da ake janyowa Amina.

Lawan ya É—ora da cewa "Ai yadda ya ja mana abin kunya a garin nan, sai 'yar ta sa ta janyo masa abin faÉ—a da nunawa, ka É—au balagaggiyar yarinya ka kaita cikin wani ahalin da ba muharammanta ba, wai dan ta yi boko, muna nan za aje a dawo da abin nunawa, zaku gani daga kai har ita, hakkinmu ba zai bar ku ba da kai da ita, muna nan mun zuba ido, zaka gani. Yaya Bala tashi mu tafi".

Gaba ɗaya jikin Baba yayi sanyi ƙalau da mugun bakin da yayyaensa suka yiwa Aminan, anya ba za a haƙura da bokon nan ba Amina ta dawo ayi Auren nan ba?!

Domin samun update a kan lokaci, Follow me at Arewabooks
Ayshercool7724
Watpad Ayshercool7724

Ayshercool
08081012143
GABA DA GABANTA

   P9

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Haka su kawu Bala suka ƙaraci faɗansu, kamar zasu tashi sama, suka kaɗe rigunansu suka fice.
Baba ya yi shiru ya rasa abin da yake masa daÉ—i. Inno ce ta fito jiki a sanyaye tana kallon Baba.
"Malam, an ya ba za'a haƙura da wannan karatun ba, ka dawo da Amina gida ba, irin wannan mugun alkaba'i da suke janyowa yarinyar nan, nifa gaba ɗaya jikina ya yi sanyi Wallahi".

Baba ya É—an yi jimm sannan ya ce "Insha Allah, babu abin da zai faru sai alkhairi, ina sa ran a sanadiyyar Amina mutanen garin nan su ga amfanin ilimi mussaman ga 'ya mace".

"Amma Malam, ni fa na karaya wallahi".

"Ki kwantar da hankalinki, babu abin da zai samu Amina sai alkhairi Insha Allah".

Hajara na dininga tana kwashe kwanukan da aka karya a kai, Amina kuwa duk ta sauke kayan kallon falon, tana musu duster saboda ƙurar da suka yi.
Hajiya Zainab ta fito daga sashenta, tana ƙarewa falon kallo, dan ta samu wani laifi da zata sauke musu masifa amma ba ta samu ba, zuwa yanzu ta fara jin daɗin aikin Amina, dan sam bata da ƙyuya, kafin ace ta yi ma tayi, kuma ba ta son ƙazanta sam.

Hajiya Zainab ta ce "Yawwa Hajara, in an jima Khalil zai dawo, ki ɗauki mukullin sashinsa a shiga a gyara masa, sannan ku sanarwa da Isyaku ya wanke masa motarsa, dan na san da ya dawo zai buƙaci ya fita da ita, sai kuma a yi girkin rana da shi, ni zan fita wataƙila har ya dawo ban dawo ba".

Hajara ta risuna cikin ladabi ta ce "To Hajiya, insha Allah za ayi yadda ki ka ce, sai kin dawo".

Har Hajiya Zainab ta kai bakin ƙofar falon, ta waigo ta kalli Amina da take ta aikinta ko kulasu ba ta yi ba ta ce "Ke, wato kin fi ƙarfin ki gaishe ni ko?"

Amina ta É—ago ta kalli Hajiya Zainab ta ce "Hajiya na gaishe ki É—azu da ki ka fito karyawa".

"To kin fi ƙarfin ki sake gaishe ni ko kice mini sai na dawo ne?"

Amina ta ce "A'a ki yi haƙuri, A dawo lafiya Allah ya tsare".

Ba ta amsa ba ta ce "Ki shiga É—akina ki tattara kayana suna nan ki ninke ki shirya mini su, amma sai kin musu kabbasa tukuna".

"To zan yi insha Allah" Hajiya Zainab ta juya ta fice.

Amina a ranta ta ce "Dan jaraba, dole sai an ƙaƙalo abin da za a ƙasƙantar da kai'

Ta É—ago ta ce "Yaya Hajaru, wanda zai dawo É—in nan, shi ne wanda zai kai ni makarantar?".

Hajara ta ce "Eh shi ne".

"Allahu Akbar, to shi ya yake? Yana da kirki ko shima dai duk haka suke?".

Hajara ta ce "Eh to, ba na ce ba, shi dai gashi nan miskili ne dai sosai, kuma bai fiye shiga abin da ba ruwansa ba, kuma ba ya wani shiga sabgar 'yan aiki, shi yasa idan nace miki ba shi da kirki na yi ƙarya, dan bai taɓa yi mini ba"

Amina ta washe baki ta ce "Allah ya sa dai kar yayi mini nima, koma ba shi da kirkin lallaɓa shi zan yi, in bishi a sannu in ta masa biyayya dan ya kai ni Makaranta, ni ɗauko mukullin sashin nasa, muje a gyara".

Hajara ta riƙe haɓa ta ce "Ohh ni Hajara, yadda ki ke ƙaunar karatu Amina, Allah ya cika miki burinki ya sa al'umma su amfana"

"Ameen Yayata".

Ko da su Amina suka shiga sashin Khalil, mamaki Amina ta dinga yi, É—akinsa har ya fi na Fadila tsaruwa, komai akwai sashinsa har da kitchen da kwanukansa da komai, hatta fridge da cooking gas duk akwai.

Amina ta zage suka ƙara tsaftace ko ina, sannan suka baro sashin. Amina na ta fatan Allah ya sa yana dawowa babu ɓata lokaci ya kai ta Makaranta.
Chapter 19 · 0% Book details