← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 84

Sashe 8

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani haushi ne ya sake kama Amina, ba ta kuma ce masa uffan ba, ta juya ta koma cikin gida tana wani tunani a ranta.

***************
Ku san sati biyu da fara lectures, amma kullum sabbin ɗalibai zuwa suke yi, sai dai haryanzu Fadila ta kasa sakewa da 'yan ajin, sai wasu 'yan mata su biyu, suma dan ta ga irinta ne 'yan ƙarya yaran masu kuɗi, suma ba wani sakewa take da su sosai ba.

Ana tsaka da lectures, sai ga wani matashin saurayi ya shigo, dogo ne sosai wankan tarwaɗa, yana sanye da wani yadi ash, amma yadin nan yayi haske saboda tsufa, amma ya sha guga, kansa ya sanya hula tashi ka fiye naci, sai ɗan ƙaramin asuwakinsa a bayansa, hannunsa ya naɗa shi da wani ɗan ƙaramin carbi.

Sallama ya yi, wanda ya sanya gaba É—aya hankalin 'yan ajin dawowa kansa, saboda yadda yayi Maganar Kamar cikin iyayi.

Aka amsa masa, lecturer ya ce "Kai Ustaz da ga ina?".

"Daga gida Malam" ya faÉ—a cikin girmamawa.

"Gida dama yanzu ne lokacin da yakamata ka zo aji?".

"A'a malam ayi mini afuwa dan Allah, Insha Allah ba zan sake ba"

Lecturer ya bashi iznin ya je ya zauna.

Ƙafarsa Fadila ta kalla, ya sanya takalmi soso irin na maza, takalmin duk ya cinye, ga ƙafarsa tayi futu-futu tamkar an haƙo shi daga rami.

Aikuwa Fadila ta tuntsire da dariya, gaba ɗaya aka juyo ana kallonta, shima waigowa yayi ya kalleta, ya ga ƙafarsa take kallo tana cigaba da dariya, ganin abun da take wa dariya, ya Sanya wasu daga cikin ɗaliban suma yin dariya ƙasa-ƙasa, gaba ɗaya sai wata kunya ta kama shi, sai ya ji babu daɗi sam akan abi nda Fadila ta yi masa.

Lecturer da ya juyo ya ga Fadila ce tayi wannan dariya, bai tsaya jin me take yiwa dariya ba ya ce ta fita ta bar ajin.

Domin gyara sharhi ko shawara
08081012143
Kar a manta ayi following account É—ina na Arewabooks
https://arewabooks.com/u/ayshercool7724

GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

P4
Arewabooks

https://arewabooks.com/u/ayshercool7724

Watpad Ayshercool 7724

Ko a jikinta, Fadila ta É—auki jakarta, ta fice daga ajin.

Shi kam wannan bafulatanin ustazu, ya nemi guri ya zauna, yana ɓoye ƙafarsa, dan ba ƙaramin kunya ce ta kama shi ba, a saboda dizgin da Fadila tayi masa.
  Fadila kuwa gida tayi tafiyarta abin ta, hankali kwance dan tama manta da abin da ta aikata, kuma ba ta damu da korarta da malami ya yi daga aji ba, dan ita gani tayi ma ya taimaketa.

************
A 'yan kwankin nan da dangin mahaifi, suka sako Amina a gaba, duk ta rame ta yi zuru zuru, ga rashin samun damar zana jarrabawa, gashi Kawu Bala ya hanata zuwa ko ina shi da Kawu Lawan idan ba aike ba, ciki har da makarantar allo, kuma dan wani tsabar wulaƙancin, daga can cikin gidan ma, gurin iyalansu, sai a aiko taje a aiketa, ko a sata wani aiki mai wahala, duk dan a cuzguna mata a ɓata mata rai, abin duniya ya haɗu yayi mata yawa, gashi ba ta da waya balle ta kira Baba ta sanar da shi halin da take ciki, gashi su kawu sun matsa a kan lallai ko yana nan ko ba ya nan, sai sun siyar da gonarsa sun mata Aure.
Abin da yake ƙara mata damuwa shi ne, bayan aikin gadin nan, da ɗan gurin da suke zaune a cikin gidan nan, to da Allah suka dogara da Wannan gona kuma guda ɗaya tal, siyar da ita na nufin tozarta Mahaifin Amina ne.

"Amina, wai ke sai kin É—orawa kan ki wata rashin lafiyar saboda wannan tunanin da kike, sannan hankalinki zai kwanta?"

Cikin damuwa Amina ta ce "Ba haka bane Inno? Tunanin ne yake zuwa ko ban shirya ba".

"Yo dama wani tunani ne zai tsaya jiran sai kin shirya? Na san ba zai wuce tunanin boko ba".

Amina ta girgiza kai ta ce "Inno ni na haƙura da karatun boko ma, ni yanzu auren nan nake tunani bana son Auren nan sam, sai kuma gonar Baba da zasu sayar, dan Allah Inno ki saka baki, su ƙyale mana gonarmu"

BuÉ—e baki Inno ta yi ta ce "Ni kaza! Rufamini asiri, kin san ko mahaifinki ba ya jayayya da maganar kawu Bala, balle ni 'yar karo da aka auro".

"To ko ni inje in same shi, in masa maganar?, bamu fa da Komai sai gonar nan, kuma ni wallahi ba zan yadda ayi mini wannan auren ba".

"Ke ki rufawa kanki asiri, kin ga Amina kiyi haƙuri ki runugumi Auren nan, tun kafin su yi miki wani sharrin, kin san kawu Bala da kaidi kamar mace"

"Aikuwa a aurawa wata ba dai ni ba, dan Wallahi da raina da lafiyata ba zan auri Wannan mutumin ba, mara imani wanda bai san darajar Aure ba, mata nawa ya mayar zaurawa, ya auri mace ya saketa ita da 'ya'yanta banda 'ya'yan da ke gidansa, duk kaka sai ya saki mata ya auri wasu haka kurum a kashe mini rayuwa".

"Rigimar ki tayi yawa Amina, ke ba a gaya miki gaskiya ki bi, amma ki rubutawa babanki wasiƙa a kai tasha, gara ya zo garin nan a san abun yi, ya san halin da ake ciki".

Amina ta yi murmushi ta ce "Ashe dai bokona na da muhimmanci Inno, amma ai baba bai iya karatu ba, wa zai karanta masa, ni nafi son muyi magana da shi a waya"

"To a ina zaki samo tarhon?"

Amina ta É—an yi jimm sannan ta ce "Ashirun gidan Jimmale kamar yana da waya".

"A'a ni kin san bana san alaƙa da wannan matar, yanzu sai kiji ƙananun maganganu".

Amina ta ce "to idan na tuna wata mafitar na gaya miki".

Inno ta ce "To shikenan".

************
Sai haki take ta rasa wace kwanciyar za ta yi, domin ta ji daÉ—i, komai ba ya mata daÉ—i, Hafsa na zaune a gefenta, tana ta jera mata sannu, tana yi mata fifita.

Cikin Muryar marasa lafiya Mama ta ce "Hafsa, ki tashi ki dafa ƙullin awarar can, kar yayi tsami".

Cikin damuwa Hafsa ta ce "Mama ba zan iya zuwa gurin suyar awarar nan ba, alhalin kina cikin yanayi na ciwo, ni yanzu hankalina ya koma kan yadda zan samo kuÉ—i mu tafi Asibiti".

"Haba Hafsa, jikina fa da sauƙi kece kike sanyawa kan ki damuwa, amma da sauƙi Alhamdilillah".

Cikin halayarta ta miskilanci Hafsa ta ce "Wannan nishin ma da kike duk cikin sauƙin ne? Kin ji yadda ki ke numfarfashi kuwa? Na san fa kina jin jiki sosai, ni dama ciwon ya dawo kaina in ga kina walwalar ki da lafiyarki".

"Auzubillah, haba Hafsa, sai kace wata mara imani, ni aka ce miki zan iya jurara ganinki cikin ciwo ne? Ki mini Addu'a kawai, Allah ya bani lafiya, kije gurin sana'arki, ko ba yawa ki samo wani abun, mu sai sabulun wanki". Da ƙyar Mama ta takura Hafsa, ta tashi ta fara kiciniyar haɗa kayan sana'ar, ba dan ranta yana so ba.

*****
Duk yadda ya so zuwa Makaranta da wuri, Allah bai yi ba, dan be samu ba sai da ya makara, yana zuwa tuni hall ya cika an fara gabatar da darasi.
Baya son zama a can baya, saboda baya ƙaunar zafi ko kaɗan. Wani space ya hango, dan haka cikin hanzari ya nufi gurin yana ƙoƙarin ɗosanawa ya zauna, tare da ciro wata 'yar jotter da ga aljihunsa.

"Kai meye haka a kusa dani zaka zauna dan ba ka da hankali?".

Cikin magiya ya ce "Dan Allah kiyi haƙuri, ba kusa da ke zam zauna ba, gani na yi da sauran guri, dan Allah ki bari in zauna".

"Wallahi ba ka isa ba, kut haka kurum Wallahi ba za a kashe ni da warin hammata ba, ka nemi wani wurin". Ganin ta fara ɗaga murya har an fara kallonsu, ya sanya shi cire takalminsa a ƙasa ya zauna a kai.

"Kai ba gurin zama ne ka zauna a ƙasa?"Cewar malamin da ke darasi a lokacin.
"Malam bana son zaman baya ne, kuma na makara"

"Ba ka gudun ka ɓata kayan ka?".

"Ba komai, na karkaÉ—e".

Malamin yayi murmushi ya ce "kun ga irin wannan ustazan, da basu ɗau duniya da zafi ba, su ne ƙwarin aji they make it in life".

Fadila ta kalli uwar hular kan gayen nan, tashi ka fiye naci ce a kansa, saboda tsabar tsufa har zaren hular ya fara tashi, babu datti a jikinta, sai azabar tsufa, ya takure ƙafafunsa da suka yi busu-busu da ƙura, ya zauna akan takalmansa. Kamar kullum wata dariya Fadila ta kuma yi, tana cigaba da ƙare masa kallo ta ce "wai su ƙwarin aji manya" yana jinta, sai dai ko ɗagowa bai yi ba ya kalleta ba, ya cigaba da 'yan rubuce rubucen sa, duk da ba ya jin daɗin abin da yarinyar take masa.

Malamin ya cigaba da gudanar da darasinsa, sai da ya kusa kammalawa sannan ya bada damar tambaya, aikuwa ɗan ustazun nan ya ɗaga hannu, malamin ya bashi dama ya miƙe, ya fara tambayarsa sai dai da harshen turanci yake yi, kuma da alama turancin bai zauna a bakinsa ba, dan sai fama yake ya tattara yayi bayani yadda malamin zai fahimta.

Fadila ta ce "Wai turanci ya ga ta kansa, kai kuwa kayi da hausa mana tunda turancin baka iya ba" iya na kusa da su wanda suka ji mai ta ce, suka kwashe da dariya, wanda hakan ya sanya jikinsa yayi sanyi.
Malamin ya ce ya cigaba da tambayar, dan tambaya ce mai matuƙar mahimmanci, wadda za'a ƙaru da ita sosai, ya girgiza kai ya ce wa malamin ya gama tambayar.
  Aikuwa malamin ya dinga fashin baƙin tambayar nan, dan iliminne mai zaman kansa a cikin tambayar.

A ka kammala lectures, kowa ya fita sabgar gabansa, masu neman Abinci su siya da sauransu.
Fadila na tsaye a jikin motar ta ustaz ya zo wucewa, tana ganinsa ta tuna yadda ya dinga kokawa da turanci ɗazu a aji, aikuwa ta sake bushewa da dariya, yana jinta amma ya sake sunkuyar da kansa ƙasa ya wuce ba tare da ya ko ɗaga kai ya kalli in da take ba.
Chapter 8 · 0% Book details