← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 84

Sashe 29

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amina taje wurin Baba suka sha hira, daga nan ta koma cikin gidan, tana ɗan ƙara dudduba abin da za tayi.
Ta dawo babu daɗewa aka fara bubbuga ƙofar falo. Amina ta je ta buɗe ƙofar falon, wasu mata ta gani su huɗu, sai yara su ku san biyar.
Amina ta ce "Sannunku da zuwa"

Suka amsa mata da yauwa, ta basu wuri suka shiga falo, suka zazzauna.

ÆŠaya daga cikin matan ta ce "Ahmad É—in yana nan ne?" Amina ta É—an yi jimm, tana tunanin wanene Ahmad.

Matar ta ce "Me gidan"
Amina ta ce "Au, ai ba ya gari bai dawo ba, sai da ki kai magana naga kuna kama, 'yan uwansa ne ku?".

Matar ta yi murmushi ta ce "Eh ƙannensa ne da iyayensa".

Amina ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Allah sarki, sannunku da zuwa gashi duk ba sa nan, sannunku" nan da nan Amina ta tafi kitchen, ta dinga jido ruwa da lemuka a fridge, tana kawo musu, ta koma ta haɗo musu fruit a ƙaton faranti, ta zo ta zube musu, cikin hanzari ta koma kitchen, ta ɗora girki, ta sake dawowa falo tana musu sannu da zuwa.

Ɗayar ta kalli Amina ta ce "Amma dai ke baƙuwa ce a gidan nan ko?".

Amina ta ce "Eh baƙuwa ce, aiki nake yi ban cika wata biyu bama".

"Allah sarki yarinyar kirki, Allah ya yi miki Albarka. Mun zo duba wani É—an uwa ne da aka kwantar a Asibiti, muka ce bari dai mu biyo mu duba Ahmadu, tun da shi ya watsar da mu mu bari muzo".

Amina ta ce "Allah sarki, ai kuwa kun kyauta zumunci ai Akwai daÉ—i". Nan da nan kamar sun san juna tun tuni, Suka saba da Amina, abinka da wanda ya ce maka ungo.
Ta shirya musu lafiyayyen girki, yaji uban nama, ta kawo ta ajiye musu, aikuwa suka zage, suka ci Abincin nan, suka yi sallar azahar, Amina ta ware musu A.C ta kunna musu kallo.

Hajara ce tayi sallama, daga kasuwa ta dawo wujiga wujiga. Sai dai tana ganin matan da ke Falon tai turus, ta gaishe su, suka amsa mata, Amina ta tashi ta tayata ɗaukar kayan da tazo da su zuwa kitchen. Suna zuwa kitchen Hajara ta kalli Amina ta ce "Amina, waye ya saki bawa baƙin nan hidima haka, har da girki?"

Amina ta ce "Ban gane ba"

"To ki shirya hukuncinki a wurin matar gidan nan, Allah ya sa ƙarshen zamanki a gidan nan bai zo ba, dan wannan mutanen arziƙin ruwan pure water suke samu idan sun zo, shi yasa suka daina zuwa".

Amina ta ce "Amma Hajara 'yan uwan mai gidan ne fa". Amina ta faÉ—a cikin damuwa.

"Ke ki ka san 'yan uwan mai gidan ne, amma ki shirya karɓar mummunan hukuncin da zaki fuskanta a wurin!!!.

IDAN BA A COMMENT ZAN DAI NA TYPING TABBAS, KO YA KOMA PAID, IN ƁATA LOKACI INA TYPING, KU BINI DA THANKS😏😏😏

GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143

P13

Gaba ɗaya jikin Amina ya yi sanyi, jin abin da Hajara ta gaya mata, mussaman batun korar nan da ta ambata, jiki a sanyaye ta ce "Amma Hajara ai baƙon ka annabinka, ka yi baƙi 'yan uwan mai gida ka wulaƙanta su?".

"Na gaya miki kefa ki ka san wannan, ita ba ruwanta, kawai ki saurari kwandon bala'in da zata zo ta sauke miki a ka, kiyi fatan ya tsaya a iya tijarar da zata miki"

Jikin Amina yayi sanyi, amma babu yadda zata yi, tun da har ta riga ta musu kyakywar tarba, kuma ita ba taga aibun abin da ta aikata ba. Jiki ba ƙwari ta fito falon, ta tarar sun fara haramar tafiya.
Amina ta ɓoye damuwarta ta ce "Ya naga kun fara shirin tafiya? Ba zaku jira su dawo bane?".

"A'a kar yamma ta yi mana, gara muje mu tari motar garinmu".

"Au dama ba a garin nan ku ke ba?"

Ƙaramar cikinsu ta ce "A'a, mu daga jigawa muka zo" suna tsaka da maganar, Hajiya Zainab ta turo ƙofar falon,  Fadila na bayanta. Tana shigowa ta yi turus ganin mutane a falon, ta bi su ɗaya bayan ɗaya da kallo, ta sauke idanunta a kan farantan da ke falon, alamar an ci an sha, dan har da taunannun ƙasusuwa, da ragowar kabeji a cikin farantan, ta sauke idanunta a kan Amina, da tayi tsuru-tsuru kamar ta yiwa sarki ƙarya.
Cikin takunta na isa da taƙama ta ƙarasa shigowa falon, tana cigaba da yi musu kallon ƙasƙanci.

ÆŠaya daga cikinsu ta ce mata "Sannu da zuwa"
Sai da ta sha ƙamshi sannan ta ce "Yauwa" tayi gaba ta nufi sashinta, Fadila ta bita ba tare da ko gaida su ba.

"Hmm mai hali baya fasa halinsa, ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta, Ahmad dai ɗan uwanmu ne, ko anƙi ba za a taɓa canzawa tuwo suna ba"

Amina ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri".

"Babu komai, ke dai mun gode sosai da karamcin da kika mana, dan rabon da mu zo gidan nan a kalle mu da mutunci har mun manta, mu mun tafi sai an jima". To muje in rakaku. Amina ta bisu Suka fita tare,  na ta sake basu haƙuri, ta rakasu har haraba, sannan ta dawo ta kwashe kwanukan da suka ɓata, ta gyara falon tsaf, ta shirya wa su Hajiya Zainab na su Abincin a kan dining, ta koma kitchen ta yi wanke-wanke, tana ta tsumayin jin kiran Hajiya Zainab amma shiru, ba tace mata komai ba.

La'asar liƙis, Bayan an idar da sallar La'asar, Khalil ya kasa jurewa, ya ɗau wayarsa ya fara lalubar lambar Hafsa.
Hafsa kuwa ta kammala haÉ—a kayanta na fita wurin sana'a, ta tsaya yin sallar la'asar.
Wayarta ce ta fara ringing, har ta katse ba a ɗaga ba, aka sake kiran wayar, Mama ta gaza haƙuri ta ɗaga ta ce "Salla take" ta katse wayar.

Da Hafsat ta idar sa salla, ba ta bi ta kan waye ya kirata ba, ta cigaba da shirin fitarta, tana daf da fita aka kuma kiran wayar a karo na uku. Ba tunanin komai ta É—aga tare da yin sallama "Assalamu alaikum warahmtullah".

Khalil ya yi wata ajiyar zuciya sannan ya amsa ya ce "Babyna ya kike?".

Sarai ta É—au muryarsa, amma ta haÉ—e rai ta ce "Wake magana?".

"Khalil ne".

"Wane Khalil É—in" ta faÉ—a tana yatsuna fuska.

"Khalil coustomern ki, kuma masoyin ki" É—if ta kashe wayar, tare da wani guntun tsaki, ta ja kayanta ta bar gidan.

Hajiya Zainab ce ta fito cikin taƙama, fuskarta babu annuri ta kalli Hajara, da ke ta kiwa tana komowa a falon ta ce "Ke kina gidan nan ki ka bari aka saukar mini wannan mutanen a gida? Uban waye ya bada izinin aikata hakan"

Jiki na rawa Hajara ta ce "Wallahi Hajiya bani bace ba, ba laifi na bane, ni bama na gida na je kasuwa sayayya, Amina ce"

Hajiya Zainab ta wani hura hanci, tana huci ta ce "Tana ina?"

"Tana wurin Babanta"

"Wuce ki kira mini ita, daga ita har shi É—in"

Hajara ta ce "To" ta bar falon jiki na rawa ta nufi harabar gidan.

Amina na zaune tana karatu, suna hira da Baba jefi jefi.

Hajara ta ƙaraso ta ce "Wai kuje in ji matar gidan" cikin Amina ne yayi wata tsuwwa, saboda tashin hankali.

Baba ya kalli Amina ya ce "Uwata, lafiya kuwa? Ina fatan ba wani laifin kika aikata ba?"

Amina ta girgiza kai ta ce "Ban yi laifin komai ba Baba"

Baba ya ce "To Allah ya sa, tashi muje muji".

Amina ta tashi suka bi bayan Hajara, ko da suka shiga falon, kallo É—aya Amina ta yiwa Hajiya Zainab, ta san babu mutunci, babu afuwa a tare da fuskarta.

Baba ne ya gurfana a gaban Hajiya Zainab, hakan ya sa Amina ma ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta gurfana ɗin.

"Waye ya baki iznin ki É—au Abincina ki girka ki bawa wannan wahalallun mutanen?" Tai maganar cikin isa tana tsare Amina da idanu.

Amina ta ce "Ba kowa".

"Abincin naki ne, ko kuma da izinin wa ki ka yi hakan?"

Amina ta ce "Wallahi ni ban san ba a bawa baƙo Abinci a gidan nan ba, naga idan wasu suka zo ana basu, kuma ce mini suka yi daga nesa suke, 'yan uwan maigidan ne, shi yasa na basu Abinci".

"Kin taɓa ganin ire-iren wannan mutanen a gidan nan da zaki basu abinci na?, har ki kwashe mini kaya a fridge ki ba su? Talakan ubanki ne ya saya ya ajiye, da zaki ɗebar mini kaya kiyi gwaninta da su?" Damm! Ƙirjin Amina ya buga da ƙarfi, talakan ubanki ta maimaita abin a zuciyarta.

Baba ya ce "Dan Allah, dan Annabi kiyi haƙuri, laifina ne da ban gaya mata dokar ki ba, amma dan Allah kiyi haƙuri ba zata sake ba".

"In yi haƙuri ko kar in yi bai shafeni ba, zaka biya kuɗin abin da ta salwantar a albashinka, kuma wannan shi ne na farko kuma na ƙarshe, idan ta sake makamancin laifin nan, sai ta bar mini gida, ta koma ƙauyen da fito, ta je can ta cigaba da hauka da jahilicin da ta zo da su"
Wata irin ƙunar rai ce ta kama Amina, jikinta har rawa yake saboda baƙi ciki, da ɓacin rai, da gari banza ne wani ya hɗata da Baba ya ci mutuncin ta, da sai in da ƙarfinta ya ƙare, amma yanzu babu damar magana.

Baba ya ce "Ba damuwa Hajiya, insha Allah ba zata sake ba" ya kalli Amina ya ce "Uwata ki bata haƙuri"
Amina kamar zata fashe, haka ta risuna ta ce "Allah ya baki haƙuri, ba Baba ne ya sai Abinci ba, insha Allah ba zan sake aikata haka ba".

Hajiya Zainab ta ce "Kima sake, kiga ƙarshen rashin mutunci" Baba dai ya kwantar da kai, ya cigab da bawa Hajiya Zainab haƙuri.
Chapter 29 · 0% Book details