Sashe 73
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi ya cigaba da yi yana kallonta, sai da yaga idanunta sun ciko da hawaye, sannan ya cire motar daga lock.
Da sauri ta fita daga motar, tana ɗan leƙa wurin zaman Baba, ko zata hango shi a wurin.
Daddy ya rufe motar ya ce "Ki nutsu, Baba baya nan wadda kike tsoron ma haka, ko kin manta muna tare ta mini waya?".
Ajiyar zuciya tayi ta ce "Na manta ne, ina tsoron ta mayar da ni ƙauye in rasa karatuna, dan da na yi laifi sai a fara cewa za'a mayar da ni ƙauye".
"Allah ya sa ta jiki, zaki yi mata bayani dalla-dalla"
"Allah yasa na sauka daga motarka, balle in faɗi wani abu ka saukeni a hanya, da wani abu zan faɗa"
"Aminatu kin raina Daddy fa"
"A'a ban raina Daddy ba, Daddy yana da kirki ne sosai, ba kamar..." Sai kuma tayi shiru.
"Ba kamar wa ba? So kike muyi faÉ—a ko?"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
Hajara ce tayi turus a falo ganin Amina da Alhaji Ahmad tare, da alama tare suka shigo.
"Idan ba kya son muyi faÉ—a, to ki kiyaye abin da zan yi fushi"
"To na daina"
Ya jinjina kai ya ce "Go and have rest, see you later"
Baban abin da ya bawa Hajara mamaki shi ne, yadda ganinta bai sa sun farga sun daina hirar da suke ba, cike da wani yanayi da ta kasa fassarawa.
Daddy ya nufi hanyar sashinsa, Hajara ta risuna tana "Barka da zuwa" ɗaga mata hannu kawai ya yi, fuskarsa a haɗe, kamar ba shi ne ya gama ƙarewa Amina kallo yana murmushi ba.
Waiwayowa tayi ta kalli inda Amina take, Amina ta kalleta sama da ƙasa, ta nufi na su sashin, sai kuma ta tsaya ta kalli Hajara ta ce "Kiji ki ƙi ji, ki gani kuma ƙi gani, idan ki ka matsa kuma hmmm" sai tayi murmushi kawai ta wuce Hajara, ta barta a tsaye sororo tana kallon Amina.
AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA
BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL
AREWABOOKS AYSHERCOOL7724
WATPAD AYSHERCOOL 7724
40
Saroro baki buɗe, Hajara tabi Amina da kallon mamaki, gaba ɗaya gani take kamar ba Aminan da ta sani ba ce, wani ɓoyayyen abu take gani a kan fuskar Amina mai kama da ƙudurin da zata iya jurewa kowace irin barazana. Banda haka, ta yaya zata shigo falon matar gida tare da maigidan cikin wani yanayi da haryanzu ta rasa muhallin da zata saka shi.
Soyayya ce kenan? Ta tambayi kanta.
'a'a ba zai taɓa yiwuwa ba, mutumin da yake aiki a wani gari daban gari mai cike da goggagun mata masu ji da kansu, mai ɗumbin dukiya mai tarin yawa, ta yaya zai ɓige da son 'yar cikinsa, 'yar cikin nasa kuma mai aiki 'yar ƙauye?.
Sukuku haka Hajara ta bi hanyar da Amina tabi, tana tunanin yadda zata samo zaren labarin, ta gane a wani ma'auni zata ajiye alaƙar Amina da Alhaji Ahmad.
Cike da tsananin gulma da take cin Hajara, ta bi Amina É—akinta, ta tarar da Amina ta cire uniform ta É—aura towel zata shiga wanka.
Hajara ta kalli Amina tana ƙaƙalo murmushi ta ce "Wai nikam Amina, ban gane me kike ce mini ɗazu ba, naji kamar wata karin magana ki ka yi"
Amina tayi murmushi ta ce "Idan baki gane ba, ki barshi a haka kawai"
"Ba zaki mini bayani ba kenan, yau naga kin daÉ—e a makarantar"
"Eh, ai kin san muna zama yin lesson, shi ya sanya"
Hajara ta ce "Haka ne, tare kuka dawo da shi Alhajin kenan?"
"Eh Hajara, tare muka dawo, yaje ya É—auko ni daga makaranta ne, shikenan? Ina son zan shiga wanka"
"To bari in baki wuri, Lallai Amina kin shigo gidan nan da ƙafar dama"
Amina bata kuma saurarrta ba, ta shige banÉ—aki ta bar Hajara.
Hajara ta riƙe haɓa tana sake jinjina kai, ga labari amma babu bakin bayarwa, dan ta san ko giyar karnuka ta sha, ba ta isa ta tunkari Hajiya Zainab da wata magana makamanciyar Wannan ba, dan ta san kome zai faru tare da ita zata kwaɓewa, to ta isa ma tayi wani yinƙuri na furta wani mummunan abu a kan maigida meye hujjarta?'
A fili ta ce "Allah ma ya ƙara, ni tsorona Allah ya sa ba lalubeta yake yi ba, ita matar gida tana can gantali kamar 'yar akuya kullum tana tafe kamar iska"
Æangaren Hafsa kuwa, ta rame tayi duhu, gaba É—aya ta daina walwala, waccan rayuwar tata ta baya ta sake dawo mata sabuwa fil, cike da sabon salo mai É—auke da ciwo irin na soyayya.
Tun daga koke koken nan da tayi, take fama da ciwon kai, tayi ta ƙoƙarin kawar da tunani da damuwa da Khalil, amma abu ya gagara tun tana ɓoyewa kar Mama ta gane, har abu ya zo ya zarce mata da zaɓi mai zafin gaske.
A hakan Mama ta gane, saboda ganin yawan kwanciyar da Hafsa take yi, ga rashin cin Abinci.
Cikin dare Mama ta tashi, domin yin sallar dare, ama ta dinga jin sheshsheƙar kukan Hafsa, ta miƙa hannu zata yaye abin rufar Hafsa, amma taji jikinta zafi rau.
"Hafsa meye haka? Meke damunki ne?"
"Mama bakomai"
"Kamar yaya babu komai, ji yadda jikinki yayi zafi, Hafsa kin ɗora kanki damuwa kina nema ki hallaka kanki, Hafsa ƙaddara ba zata samu bawa yayi tawakkali ba?"
Hafsa ta ja jikinta da ƙyar ta zauna, ta ce "Mama ba laifina bane ba, kawai rashin lafiya nake yi"
"Haba Hafsa, nifa na haifeki ba ke kika haifeni ba, na sani kin shaƙu da Khalil haryanzu kina son sa, amma ki cigaba da Addua, Allah ya kawo miki mafita, bana jin daɗin ganinki a wannan yanayin ko Abincin kirki ba kya ci, kuma ni baki gaya mini baki da lafiya ba" Hafsa dai tayi shiru, ba tace komai ba.
"Tashi ki lallaɓa kiyo alwala, ki zo ko raka'a biyu kiyi, kiyi Addua Allah ya bamu mafita gaba ɗaya, ina da guntuwar gasara sai in dama miki kunu ki sha, sai in baki paracetamol"
Cikin yanayi na jin jiki Hafsa ta ce "A'a Mama, dare yayi sosai, bari in sallar kawai"
"A'a ba komai, bari in dama miki, yunƙura ki tashi"
Hafsa ta yunƙura za ta tashi, ama jiri ya kwasheta ta koma luuuuu zata faɗi.
Duk da Mama bata da cikakkiyar lafiya, haka ta yunƙura ta rungumo Hafsa, suka kusa faɗuwa.
Cike da damuwa Mama ta ce "Hafsa har jikin naki ya kai haka?"
"A'a Mama, jiri ne kawai ya É—an É—ebe ni"
Mama ta kama Hafsa ta zauna, sannan ta ce "Kinga zauna, bari in je in dama miki kunun, in baki maganin, zuwa in Allah ya kaimu sai mu tafi Asibiti".
Hafsa ba ta ce komai ba, sai lumshe idanunta da ta yi, tana sake jin jikinta babu daÉ—i.
Bayan sallar isha'i Amina tana ƙoƙarin buɗe jakarta ta ciro litattafanta, ta ci karo da tarin kayan ciye-ciye na biscuit da chocolate, da wani turare da kwalinsa kawai abin kallo ne, jan kwali ne kwalbar turaren ma ja ce, mai matuƙar ɗaukar hankali.
Ta fesa turaren a hannunta ta sansana, wani irin sassanyan ƙamshi ne da turaren mai kwantar da hankali. Ko ba a gaya mata ba ta san turare ne mai tsada sosai.
Murmushi Amina ta yi, tana sake jujjuya turaren da kallon tarkacen kayan ciye-ciyen.
Wani murmushi Amina tayi, wanda ita kaÉ—ai ta barwa kanta sanin ma'anar murmushin.
Fadila kuwa a ɗakinta ta ci Abinci ita kaɗai, tayi wanka tana saka kayan bacci tana shafa mai, ta kalli turarukan wurin Yazid, ta zuba musu ido tana kallonsu tamkar Yazid ɗin take gani a wurin, tunani ta shiga yi a kan barkwancinsa, da yadda yake ta nuna mata kulawa daga fara shirin su zuwa yanzu, mutum ne mai haƙurin gaske da kawaici, ta tuno yanayin da ya shiga a lokacin da ta gaya masa tafi ƙarfin sa, har aka tashi jikinsa babu wani kuzari. Guntun tsaki tayi a fili tana tunanin sai me dan tayi masa warning a kan ya fita daga harkarta, ai ya san ruwa ba sa'an kwando bane, kuma kamar yadda Yusra ta gaya mata, sanyin halin Yazid da kyautatawarsa zata iya sawa ta fara son shi ba tare da shirya hakan ba, gara ma tun wuri ta raba gari da shi.
Wayarta ce ta kawo haske, ta kalli in da wayar take taga message ne ya shigo, ta ɗaga wayar ta duba sai taga missed calls biyar, duk na Kankiya saboda wayar na silent bata san ya kira ba. Ta duba saƙon ta ga roƙonta yake wai yana son ta bashi dama ya zo gidansu.
Dire wayar tai tana harar wayar tamkar ita ta turo mata saƙon, "Zan ɗau mataki a kanka, idan ya so ka yiwa Yazid ɗin abin da ka ga dama ku ta shafa" tayi maganar tana ƙoƙarin kauda wani abu mai kama da tausayi a ranta game da Yazid.
Mummy ce ta faÉ—o É—akin Fadila babu ko sallama fuskarta cike da damuwa.
Fadila ta kalleta ta ce "Mummy ya dai?"
"Kin yi waya da Khalil ne?"
"Mummy wane Khalil kuma, wayar me zan yi da shi bayan yana gidan nan"
Mummy ta ce "Khalil baya gidan nan, sai yanzu na farga, tun safe banga gilmawarasa ba, na duba babu motarsa, naje in tambayi wancan shashashan tsohon when last Khalil ya fita, amma na tarar baya nan, sai direban babanku ne ke buɗe gate ɗina, wai ya nemi iznin babnku ya tafi ƙauye, shi kuma bai san lokacin da Khalil ɗin ya bar gidan nan ba"
Fadila cikin mamaki ta ce "Ikon Allah, to Mummy ki kira wayarsa mana"
"Na kira taƙi shiga sam, gaba ɗaya hankalina ya ɗaga"
"Ko ya koma wurin aiki ne?" Fadila ta sake tambaya.
"To wa ya sani ne? Kuma sai ya koma wurin aiki bai mini sallama ba, yaya hakan zai yiwu, kar inje a sace mini ɗa a banza, sai sa na gaya wa babanku, ya samar muku da security, yawonmu haka a gari is not safe, duba sa matsayin da ya riƙe a ƙasar nan, amma ya ce mini no need, ai ga irnta nan"