Sashe 78
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fadila na kwance a kan gadonta kamar mai ciwo, tana chatting a Instagram tana taya wata riga, notification na what's app ya shigo wayarta.
Komawa tayi what's app É—in dan duba meke faruwa, saboda taga an yi maganganu da yawa a what's app group É—in su na makaranta.
Da saƙon Captain ta fara cin karo "Yau na haɗu da wani abokina wanda ya san Yazid, ya ce Yazid na Asibiti babu lafiya sosai, ku sa shi a adduoinku Please"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un"
AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA
BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL
AREWABOOKS AYSHERCOOL7724
WATPAD AYSHERCOOL7724
43
Gaba ɗaya suka waiwaya dan ganin waye haka? Gaba ɗaya hankalin Amina ya riga ya gama tashi, Hajara ce a tsaye a wurin makunnin ƙwan, ganin duk suna zuba mata ido kuma sai ta hau kame-kame tana faɗin "Amm.... Ban san.."
Ɗauke kai Daddy yayi daga kallon in da Hajara take, ya mayar kan Amina ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Karki manta anjima zan aiko a kai ki banki, a buɗe miki account"
Noƙe faɗa tayi ta ɗan tura baki ta ce "Ni ba zani ba"
"Me kika ce?"
"Bakomai" ta faÉ—a taka sake tura baki.
Murmushi ya yi ya wuce sashinsa, Amina ta cigaba da mopping É—in ta suka mayar da Hajar daidai da kujerun da suke falon.
Gaba ɗaya Hajara rasa abin yi tayi, a baya tunane tunanenta sun fi karkata ga zargi, amma a yau ta sake tabattar da abin da ke tsakanin Alhaji Ahmad da Amina wata alaƙa ce mai ƙarfi da girman gaske, wadda da alama alaƙar tayi ƙarfi sosai da sosai.
Kamar yadda Daddy ya ce, da kansa yaje makarantar su Amina, bayan an tashi sukaje banki, aka yi mata duk abinda yakamata, ya saka kuÉ—i a ciki naira dubu É—ari biyu.
Mamaki ne ya cika Amina ta ce "Daddy wannan maƙudan kuɗin me zan yi da su, idan Baba ya gane fa?"
Daddy ya ce "Ta yaya Baba zai gane, sai dai idan kece zaki gaya masa, kuma ai ba wasu kuÉ—i ne masu yawa ba, Zakiru zai kai ki ki sayi duk abin da kike so, ban fiye son shiga wurare bane saboda identity É—ina, ba dan ke ba wurare da yawa ba zan iya zuwansu ni kaÉ—ai ba, kuma ni bana son a takura rayuta duk in da zaka sai da masu baka kariya"
"Amma meyasa baka so a ganka? Kar a ganmu tare aje a gayawa Maman su Khalil ko?"
Ya ce "Eh, kin san bana son ɓacin ranta da damuwarta"
"Eh amma ni kana son ganin nawa" tayi maganar da iya gaskiyarta.
"Mhmm, me yasa kike haÉ—a kanki da ita? Ita matata ce ke kuma"
Sai yayi shiru.
A ƙule Amina ta ce "Eh ita matarka ce, ni kuma 'yar aiki ba talaka mara galihu"
"Yauwa Ashe kin sani, amma ni bance miki talaka mara galihu ba" yayi maganar da salon ya sake kunna Amina.
Aikuwa ta kai ƙololuwa dan taji haushi ba kaɗan ba.
"Banda rigima irin taki, ina na taɓa ganin wannan ƙarfin hali in ba a wurinki ba, nace kina son mijinta kince me zaki da tsoho".
Cikin tsiwa ta ce "Allah ya kiyaye in yi kishi da wannan matar, ta kasheni da bala'i wadda ba ta san darajar É—an Adam ba"
"Zaki fara ko? Ban gaya miki bana so ki dinga duk wata magana da zata shafi matata ba".
Amina ta ce "Amma ai kai ka fara bani ba, wallahi Daddy seriously yakamata ka kula sosai, Allah ya baka dukiyar da zaka amfanar da al'umma, amma an gindayeta wuri ɗaya daga ita sai iyalanta, duk wanda ya raɓoka zai mora an dinga yi masa gori kenan da kallon banza, wallahi idan baka gina lahirarka ba daga ranar da ka mutu, wanan dukiyar aka raba musu, su sadaka ma Allah ya kai ladan kabarinka sai wanda ya dubi Allah.
Na san naganganuna sun yi tsauri da yawa, amma dan Allah kayi haƙuri Daddy, wallahi gaskiya nake gaya maka. Dan Allah yanzu dan Allah ya baku arziki ya dace aje aci mutuncin 'yar mutane dan Khalil ya ce yana sonta, ba a gabana aka yi ba, amma yadda ya zo yana faɗar zancen naji zafi sosai saboda nima tsatson talaka ce, da na motsa a gidan nan sai kyara da gori, wallahi Daddy kaf mutanen da ke aiki a cikin gidanka suna yi ne dan basu da wata sana'ar da zasu samu su rufawa kansu asiri, ban da haka mai zai sa ka zauna a gabanka ana kiran mahaifinka nusari, soko da sauran miyagun maganganu?" Ta ƙarasa maganar hawaye mai ƙarfi suka ƙwace mata.
Ba ƙaramin tasiri maganganun Amina suka yi a zuciyarsa ba, duk da ba wata babba bace ba, amna wasu lokutan tana da matukar hangen nesa da son faɗar gaskiya. Yana jinta tana kukan Amma bai rarrasheta ba kuma bai ce mata komaia ba, har tayi ta gama tayi shiru.
Wasa² rashin sanin halin da Yazid yake ciki ya addabi Fadila, tun tana dannewa har ta kasa ya kai ga ta kira Yusra a waya. Ta zayyanewa Yusra duk abin da ke faruwa.
Yusra ta ce "To ni yanzu da kika kirani me kike so in yi miki? Da kina da lambarsa ne ma sai a kirashi, ko kuma ki tanbaya a 'yan ajinku ko akwai mai lambarsa"
Cikin damuwa ta ce "An bani lambar na kira baya shiga"
"Wai to meye duk kika bi kika É—aga hankalinki?"
Fadila ta ce "Haba Yusra, kamar ba a gabanki kinga halin da yake shiga idan ba shi da lafiya ba, ko da yake ke lokacin da kika zo ya farfaɗo, ni da muka kaishi Asibiti ban zaci zai rayu ba, yau fa ina miki maganar yafi sati baya zuwa school, aikuwa duk abin da zai san ya yaƙi zuwa makaranta ba ƙaramin abu bane ba"
"Na gane, yanzu dai ki kwantar da hankalinki, ki cigaba da Addu'a Allah ya sa yana lafiya, da an san ko unguwarsu ne ma da anje an tambayi in da gidansu yake"
Fadila ta ce "Ni banji wanda yace ya san unguwarsu ba, shikenan dai sai anjima" ta ajiye wayar tare da dafe goshinta, gaba É—aya tana cikin zullumi.
Khalil dauriya kawai yake yi, ko yaje zuwa wurin aiki sai dai baya iya wani abin kirki, lamarin Hafsa ha tsaya masa a rai nesa ba kusa ba, yana matuƙar sonta da tausayinta, baya son ta faɗa hannun wanda bai san ƙaddara ba, tsananin yardar da tayi da shi ne ya sanya ta gaya masa wani babban sirri na rayuwarta, da baga gayawa kowa ba sai shi, yanzu gashi Mummy ta shiga ta fita, yanzu da wani ta gayawa wannan sirrin ba shi ba, ha zamana kuma bai aureta ba, shikenan haka zai ta kallonta da abin koma yayi ta yaɗawa a gari.
Duk shirin da Amina take yi na zuwa ƙauye, da hidmar da take tayi da kuɗi babu wanda ya tambaye ta ina ta samu kuɗi, hatta wayar hannunta da aka wayi gari aka ganta da ita, Hajiya Zainab bata tuhumeta a ina ta samo ba, sai tsananin saka idanu da take fuskanta daga wurin Hajara.
Ita kuwa Fadila abin da ya dameta daban dan baka ba ta Amina take yi ba, dan idan ta ga dama sai ta wuni a É—aki bata fito ba balle su haÉ—u.
Musamman da aka tashi daga makaranta, Amina ta tafi gidansu Azima, mamansu ta sa aka kaita wurin masu gyaran kai, aka wanke kan aka yi mata kitso ƙanana masu kyau, aka yi mata lalle ja da baƙi, sai bayan la'asar ta dawo daga gidansu Azima.
'yan kwanakin nan Daddy ya auri zaman falo, saboda kawai ha dinga ganin Amina, yana zaune shi da Hajiya Zainab Amina ta shigo gaba É—aya ya mayar da hankalinsa kan Aminar, ba tare da Hajiya Zainab ta lura ba.
Amina na zuwa É—akinta ta ajiye jakar makaranta, ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kyan da kitson kanta yayi.
Wayarta dake kan mudubi ce tayi vibrating. Ta janyo wayar ta duba, sai taga saƙon Daddy ne "Lalle yayi kyau sosai, ki shirya mana dinner a dining yau, ina son zan sake gani"
Murmushi Amina tayi tana sake kallon lallen, tare da mamakin ya aka yi harya ga lallen nan.
Emojin murmushi ta tura masa tare da saƙo kamar haka "Ya aka yi har kaga lallen nan?"
"I watch everything about you, dan haka ba abin mamaki bane, zan jira a dining ki kawo Abincin dare in kuma gani"
Tana daga tsaye sai murmushi take tana bashi amsa, ta tura masa "A gajiye nake, Hajara ce zata shirya dining"
"Kin mai da ni kamar wani kakanki ko? Idan baki zo ba ba ke ba zuwa ƙauye, and i mean it"
Ɗan kwaɓe fuska tayi ta masa reply da "Tuba nake ranka ya daɗe, ba zan iya ɗaukar wannan hukuncin ba, zan zo in sha Allah"
Murmushi ne ya suɓuce masa da ganin abin da Amina ta rubuta masa.
"Ba zan haƙura ba, a haɗa mini fruit salad"
Tayi masa reply da "An gama as you wish"
"Wai dariyar me kake tayi ne kai kaÉ—ai, ka tattara hankalinka a kan waya gaba É—aya?"
Daddy ya É—ago ido ya kalli Hajiya Zainab ya ce "Ke ma ba taki wayar ce a hannunki ba, hira nake da mutane na"
Ta haÉ—e rai ta ce "Mutanenka suwa kenan?"
"Nika ɗai nake rayuwa a duniyar ne, babu abokai da 'yan uwa da zan hira da su in murmushi?" Yayi maganar ransa a haɗe, tuna tana lallaɓa shi dan ta karɓi kuɗi a hannunsa ne ya sanya ta bar zancen ta sauya akalar zancen zuwa wani.
"Baban Fadila anya Khalil yana da hankali kuwa?"
Cikin rashin fahimta Daddy ya ce "Kamar yaya kenan?"
Ta ɗanyi ƙwafa sannan ta ce "Ko kiran wayata fa ba yayi, fushi yake da ni kenan?"
"I don't know, bana ce ba, ya kan gaisheni ni dai ta chat"
"Lallai Khalil, aikuwa zan nuna masa nice uwarsa, a kan yarinyar talakawa zai É—au fushi da ni?"
Daddy ya ce "Idan yana sonta ki ƙyaleshi mana, Khalil fa ba yaro bane ya mallaki hankalinsa, he knows what is right for him, ki ƙyale yara su zaɓi abin da ya dace da rayuwarsu"