← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 84

Sashe 14

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saminu ya ce "Subhanallah, babar Amina lafiya kuwa? Aminan ce ta rasu ko kuwa mai ya faru?".

Aikuwa Inno ta sake fashewa da kuka,maƙwabciyar su Inno ce ta iya cewa "Ka san yau za'a ɗaurawa Amina aure, har kafi anje an yi an gama komai yau ɗaurin Aure, an wayi gari an nemeta an rasa".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, an nemeta an rasa kamar yaya? Ba sai wani satin É—aurin Auren ba?".

"A'a an dawo da shi yau, sai wayar gari aka yi babu Amina babu dalilinta a garin nan".

Saminu ya girgiza kai ya ce "Ta ina zan fara gayawa mahaifinta wannan mummunan labarin haka? Kunga illar Auren dole kenan".

"Wallahi Hanne ba ki isa ba, duk in da yarinyar nan ta shiga garin nan kin sani, Wallahi sai kin nemota dan ba zaki mayar da mu ƙananan mutane ba, yau ɗaurin Aurenta ace an nemeta an rasa, duk mun zagaye garin nan kowa yace bai ganta ba" Kawu Bala kenan, har wani irin yawu ne yake tsartuwa daga bakinsa, saboda azabar masifa da jaraba.

Inno kuwa ta sake fashewa da kuka, ita ba batun Auren ne ya dameta ba sanin in da Amina ta tafi ne ga bata da lafiya shi ne babban damuwata.

"Wallahi yau duk in da yarinyar nan take sai an nemota, ko gawarta aka tsinto a gidan Jarmai za a mata sutura, Wallahi Hanne ko ki fito da Amina, ko in je har birni in É—auko miki 'yan doka su kama ki. Kuma bari kiji in gaya miki ko kuna so ko ba kwa so, ko tana nan ko bata nan sai an É—aura mata Aure dan ubanta Hassan".

Saminu ya ce "Haba Baba Bala, a fara mayar da hankali wurin gano in da Amina ta shiga mana, wannan faÉ—an ai duk ba shi ne abun yi ba".

Aikuwa ya dawo da idonsa kan Saminu "Au munafuki Algungumi, ashe kana nan, bana raba É—aya biyu da haÉ—in bakinka yarinyar nan ta gudu, dan na lura da take takenka, ance har tasha take zuwa wurinka".

"Me za ta je tasha ta yi mini, iyakacina da iyalan Malam Hassan saƙo ne su bani in kai masa ko ya bani in kawo musu, kaga tafiyata ba zaka ɓata mini suna ba, Babar Amina Allah ya bayyana ta" dag haka Saminu ya fice, yana jinjina lamarin mugunta na 'yan uwan mahaifin Amina, su b ta ɓatan yarinyar suke ba, ta yadda za a ɗaura kar sunan su ya ɓaci suke yi.

Malam Rabi'u Jarmai ne ya zo har gidansu Amina yana bala'i a kan idan har ba a ga Amina ba, a dawo masa da kuÉ—insa, idan an ganta a san abun yi.

Kawu Bala ya dinga ba shi haƙuri ya ce "Haba Jarmai, ka kwantar da hankalinka za a ganta duk in da ta shiga, idan ma ba a ganta ba, za a ɗaura muku aure a haka, duk in da ta shiga da Aurenka a kanta idan ya so ds ta dawo sai a daƙumota a kaita gidanka".

Jaramai ya ce "Amma ka raina mini hankali, tana nan baku kula ba ta gudu saboda kun mayar da ni mahaukaci, sai a aura mini gaibu, ni ba zan yadda da wannan sagegeduwar ba, na baku daga nan zuwa ranar Lahadi, idan an ganta to idan ba a ganta ba, ku san yadda za kuyi ku sallame ni".

"Ke Fadila, jarida zazzafa" cewar Amra da ta samu Fadila a Cafeteria.

Fadila ta ce "Jaridar me fa?".

"Bayan fitar ki daga class, Mutumin nan ya ce ayi Attendance, 30mrks duk wanda baya nan babu shi a 30mrks É—in nan, ba kawai sai gayen nan yayi miki ba"

"Wane gayen?".

"Wannan Zaidu yake ko Yazeed, wanda aka ce shi ya ci class work, aikuwa ya gano shi ya ce da ke da shi ba ku da 30mrks É—in nan".

Fadila ta ja tsaki ta ce "To uban waye ya sashi yayi mini? Allah ya ƙara"

"Kai mutuniyar baki da dama, Allah ya ƙara ma zaki ce?".

"Idan ba Allah ya ƙara ba me zance? Ni muje class ɗin ma in ƙare masa ta tas kar ya sake mini shishshigi a lamurana".

Aikuwa Amra ta dinga zigata, suka nufi aji, suka tarar da shi yana wurin zamansa, yana motsa bakinsa a hankali da alama karatu yake yi.

"Kai wurinka na zo" Fadila ta yi maganar tana tsare shi da manyan idanunta.

Ya É—ago kai ya kalleta, ba tare da ya ce komai ba.

"Uban waye ya saka ka yi mini Attendance? Na ce maka ina buƙata ne? Ai ni malamin nan ya gama mini komai da kaima ya soke naka Attendance ɗin, uban shishshigi kawai" lumshe idanunsa yayi a hankali, ba tare da ya ɗago ba, balle ta sa ran zai tanka mata.

"Da kai nake magana fa"

"Wai ni?" Yayi Maganar yana kallonta.

"Au duk maganar da nake, baka ma san da kai nake ba saboda ka raina mini hankali?".

"Yi haƙuri" ya faɗa a taƙaice.

"Aikin banza kawai" É—an murmushin gefen baki yayi, tare da kau da kansa gefe, dan tuni idanun sauran 'yan ajin ya dawo kansu.

Class rep ya ce "Haba babbar yarinya, duk ajin nan babu wanda ya tuna da ke ya yi miki Attendance sai shi, amma sai taimako ya zama faÉ—a?".

"Kaga saurara mini babu ruwanka da ni, ai ba da kai nake ba, na gaya masa ina buƙatar taimakonsa ne? Ya ji da tsummar rayuwarsa kan yayi tunanin shiga rayuwata ya taimaka mini".

"Dalla class rep ka daina shiga sabgar yarinyar nan, gaba É—aya ba ta da kunya Wallahi" cewar wani matashi shima mai ji da kansa, wanda suke kira da Babson.

"Lokacin da aka raba kunyar ni ba a haifeni ba, idan an raba kana nan zaka iya É—ebar mini a taka".

Babson ya ce "Ni kike gayawa haka?".

"Na gaya maka É—in waye kai? Banza useless"

Ganin Babson ya miƙe ya hayayyaƙowa Fadila, kuma bakin Fadila ya ƙi mutuwa, sai cigaba da tunzura Babson take.

Yazeed ya miƙe ya riƙe Babson ya ce "Ɗan uwana dan Allah kayi haƙuri ka ƙyaleta. Fadila ba mutuncinki bane ki dinga rigima da mutane mussaman maza, muryarki al'aura ce, sai ɗagata ki ke yi...

"Dalla yi mini shiru, ji yadda kake ambatar Sunana kamar kai ka raÉ—a mini, idan ba ka kiyayi shiga sabgata ba saina kwarfeka na bi ta kanka a gaban mutane"

Dariya jama'ar wurin suka fara, tana fama da kayan rama, kamar a busheta ta faÉ—i, amma ta kalli zabgegen namiji kamar Yazeed ta ce zata kwarfe shi.

Babson ya ce "Dan Allah ku ƙyaleni in tattaka wuyan yarinyar nan, in kawo ƙarshen fitsararta".

"Sai dai kayi ka kaɗai, ƙazami mai warin hammata kawai" ba dan Yazeed yana riƙe da Babson ba, da ba abin da zai hana ya yiwa Fadila mahangurɓa.

Baba sai kiran wayar Saminu yake, a kan batun tahowar su tare da Amina, Saminu ya tabattar masa da cewar Amina ta ɓata an nemeta an rasa.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" shi ne abin da Baba Hassan ya dinga maimaitawa, tare da dana sanin rashin zuwansa ƙauye akan lokaci, take ya fara dana sanin zaɓar aikin nan a kan zuwa ƙauye wurin tilon 'yar sa.
Gaba ɗaya Baba ya rasa abin yi, jikinsa banda rawa babu abin da yake, banɗaki ya fara zagawa yayi gudawar fargaba, sannan ya ɗauro alwala ya zo ya tada salla ya kaiwa Allah kukansa, sannan yayi tunanin mafita. Baba Hassan mutum ne mai matuƙar tawakalli, dan haka ba lallai ka karanto damuwar da yake ciki a halin yanzu.

"Baiwar Allah, ke tun safe na ga mota ta sauke ki, amma kin zo nan kin duƙunƙune a nan, lafiya kuwa?".

Amina da ke jin jiki ta kalli mutumin ta ce "Dan Allah a tashar nan kake?"

"Eh a nan nake".

"Dan Allah ka san wani Saminu, É—an garin Shanono, direba ne shima"

Yayi shiru sannan yayi ajiyar zuciya ya ce "Gaskiya ban san shi ba, amma ke ina zaki je?"

"Wurin Babana na zo, kuma Saminun ne kawai ya san in da Baban yake".

"Idan ba zaki damu ba muje in baki masauki mana"

"Nace maka ina buƙatar masauki ne? Ka bari na gode kawai".

Amina na nan zaune ta ji ana cewa wani Sarkin tasha, miƙewa ta yi tabi bayan Sarkin tashar, zuwa wani Office da ya shiga, ba tare da ya san tana bin sa ba.

Yana ƙoƙarin zama ya ga Amina a tsaye a bakin ƙofar ofishin, ta zuba masa ido.

"Lafiya kuwa?".

"Dan Allah yayana tambaya nake"

"To Allah ya sa lafiya, ya sa kuma na sani"

"Dan Allah ka san Saminu direba, yana zuwa daga Shanono?".

"Ahh na san Saminu wani dogo baƙi, yana jan mota KIA?"

"Eh shi, dan Allah idan kana da lambar wayarsa ka kira mini shi"

"Eh ina da ita, amma ta sayarwa ce"

"To nawa ce?" Amina ta faÉ—a da mamaki.

"Eh, amma ba da kuɗi ba, ƙofar ofishin nan kawai zamu rufe, mintuna kaɗan sai in baki wayar ma kyauta".

Amina ta kalleshi tsaf tayi ajiyar zuciya, kawai ta juya ta bar wurin, tana tunanin wannan wane irin abu ne haka? Babu wanda zai iya yi maka alfarma a birni, sai ya nemi mutuncinka?.
"Da in koma gida a mini wannan Auren, gara in cigaba da yawo a nan" ta faÉ—a a fili. Ta koma in da ta bar kayanta ta yi alwala tayi sallar Azahar

Tana nan zaune, sai ga wanda ya fara yi mata magana da farko ya dawo wurinta, ya ce "Ke, na gane Saminun da kike nufi, ke 'yar uwassa ce?".

Amina ta jinjina masa kai, alamar eh.

"Ok bari in kira miki shi a waya" ya kira wayar Saminu ya bawa Amina.

"Saminu gani a tashar Kano, dan Allah ka gaya mini ina zan bi inje wurin Baba?".

"Amina, dama nan kika tafi, kin sa ana ta nemanki a gida?".

"Dan Allah ni dai ka taimaka mini, kuma kar ka gaya musu in da nake dan Allah".

"Shikenan, kwantar da hankalinki, kin ganni a hanya na kusa shigowa 1 21Kano, idan na shigo zan kai ki in da yake".

"Yawwa na gode sosai, Allah ya kawo ka lafiya"
Chapter 14 · 0% Book details