Sashe 17
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inno kuwa tsawon kwanakin nan, ba ta iya cin Abinci, duk ta zube saboda kuka, da tashin hankali ko bacci bata iya yi, kullum tana kan sallaya tana riƙe da carbi.
Har malaman makaranta su Amina sai da suka zo, suka yiwa Inno jajen ɓatan Amina.
Kamar ko yaushe, Inno na zaune ta duƙufa tana jan carbi, ta jiyo muryar Saminu yana sallama.
Ta amsa masa tare da bashi damar shigowa, ya shiga ya zauna suka gaisa, sannan ya ce "Baba Hassan ne ya aiko ni wurinki".
Inno ta ce "Ka sanar masa da batun ɓatan Amina ne?".
"Ai Amina ba ɓata tayi ba".
Inno ta kalleshi da mamaki, amma ta sunkuyar da kai ta ce "Na sani, Amina guduwa ta yi saboda wannan auren da za ayi mata, ba yadda ba ta yi dani ba a kan in sa baki, amma nasan ko na yi magana ba su ji ba, ni babbar damuwata babu wanda ya san in da take, ta ɓatawa kanta suna a garin nan" ta ƙarasa Maganar tana share hawaye.
"Maman Amina ki kwantar da hankalinki, Amina na tare da babanta a birni"
Dafe ƙirji Inno ta yi ta ce "Kamar yaya?".
Nan ya kwashe komai ya gaya mata, sannan ya É—ora da cewar "Baba Hassan ya ce, kar ki gayawa kowa, ya ce zai zo da kansa garin nan idan komai ya lafa, wayata ta ci speaker ne jiya, da na kira miki shi a waya".
Inno ta kuma ƙasa da muryarta ta ce "Dan Allah Saminu da gaske ka ke, tana lafiya ƙalau a wurin babanta?".
"Wallahi Babar Amina ba zan miki ƙarya ba, tana wurin Baba Hassan".
"To Alhamdilillah, Allah kai ne abin godiya, Allah na gode maka, Saminu Allah ya yi maka albarka, insha Allah zan shiru da bakina, babu wanda zan faÉ—awa sai ya zo da kansa"
Inno ji tayi tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan tsananin farin ciki.
Kwanakin Amina huÉ—u a gidan, Alhaji Ahmad ya shirya komawa wurin aikinsa, ya tabattar wa da Baba Hassan cewa, Khalil zai shigo gari, idan an koma Makaranta shi zai kai Amina Makaranta.
MEYE HASASHEN KU GAME DA LITTAFIN NAN? INA JIRAN RA'AYOYIN KU.
DAN ALLAH BANA SON THANKS ÆŠIN NAN, KO STICKER.
Domin samun update a kan lokaci Follow my Arewabooks Account
@ Ayshercool7724
My Watpad account@ Ayshercool 7724
Ayshercool
08081012143
GABA DA GABANTA
P8
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Amina ta yi murna sosai a kan batun kai ta makaranta, tsananin ɗoki da shauƙi ya sanya ta manta da duk wani batun rashin mutuncin da Hajiya Zainab da 'yar ta ke musu.
Kafin Alhaji Ahmad ya tafi, Baba ya tambaye shi yana son a bashi dama sati mai zuwa ya je ganin gida. Alhaji Ahmad ya amince masa da ya je.
Bayan an idar da sallar Asubahi, Rabi'u Jarmai ya ritsa kawu Bala yana masifa "Gaskiya Bala na gaji, yau kwanaki goma kenan ba yarinyar nan babu labarinta, dan haka na haƙura, kuje ku kwashe ruɓaɓun kayan da ku kai gidana, sannan ku dawo mini da kuɗaɗe na".
Kawu Bala ya ce "Haba Jarmai, ya zaka yi mana haka? Dan Allah ka yi haƙuri, na gaya maka ana ganin yarinyar nan, za a ɗaura muku aure a kai maka ita gidanka"
Jarmai ya ce "Allah ya sawwaƙe, yarinyar da ta iya guduwa daga gidan iyayenta tsawon kwanakin nan, ai kowa ya san bariki ta tafi, dama can waya sani ko a ɓoye yawon bokon nan abin da take yi kenan, kawai ku biyani kuɗina ko in kai ku wurin 'yan sanda a birni".
"A'a ba za ayi haka ba, insha Allah zamu dawo maka da kuÉ—aÉ—enka, ba zata kaimu ga haka ba"
"Ato a san abin yi tun da wuri, kan ta kacame mana".
Kawu Bala ya tafi gida yana jujjuya lamarin a zuciyarsa, ya san jarmai ba shi da mutunci a kan kuÉ—i ba abin da ba zai iya aikatawa ba.
Kawu Bala na zuwa gida, ya sa aka taso masa Lawan suka keɓe.
"Lawan, Jarmai fa na neman ya tona mana asiri a garin nan, yanzun nan ya tare ni a masallaci ya ce mu dawo masa da kuÉ—insa ko ya kai mu wurin 'yan sandan birni"
"Kai Jarmai ba shi da mutunci Wallahi"
"Ai ba laifin Jarmai ba ne, duk laifin wannan shegiyar yarinyar ce, da ta na nan ai da duk haka ba ta faru ba, Allah wadaran yarinyar nan"
Kawu Lawan ya ce "matsiyaciya ba, na san tana can ta bazama bariki, dan da tana garin nan da tuni an ganota, ko ubanta ya san ta gudu oho"
"To waya san musu"
"Ni anya makuwa ba da haÉ—in bakin Hanne yarinyar nan ta gudu ba?"
"Nima na fara zargin haka, dan ban yadda da matar nan ba, amma yanzu yaya za muyi da Jarmai"
"To yanzu dai ya za ayi a mayarwa da wannan masifaffen kuÉ—insa?"
Kawu Bala ya ce "Yanzu dai idan gari ya yi haske, aje gidansa a kwaso kayan nan, a mayarwa da Larai dillaliya, kai kuma ka lalubo abin da za a samu a wurinka".
"Me kuwa za a samu a kuÉ—in, kar ka manta a kuÉ—in aka saiwa Gali babur, ka cika kuÉ—i ka sai babbar gona, ai ni ban wani mori kuÉ—in nan ba".
Kawu Bala ya ce "Haka ne, amma duk da haka dole kayi wani abu, ko 'yar wurinka Abu zamu ba shi a madadin Amina?"
Kawu Lawan ya zaro idanu ya ce "Ni in É—auki 'ya ta in bawa Jarmai, Allah ya kiyaye ya sutura, Wallahi gara ta mutu ba aure, sai ka ce baka san waye Jarmai ba? Ka aura masa Sa'a mana ai ita ma ta isa Aure".
"Kai baka Aura masa Abu ba, sai ni zan aura masa sa'a? Wannan mutumin banzan Allah ya kiyaye, dama dai Aminan ce. Yanzu dai idan gari ya yi haske, za a kwaso kayan a mayarwa dillaliya, mu san yadda za mu yi a haÉ—a masa kuÉ—insa".
"To shikenan, Sai an jima, amma dai Wallahi ka je ka ritsa Hanne, dan wataƙila ta san komai, matar munafuka ce".
Bala ya ce "Bar ni da ita, zata gane kurenta"
Yauma wankan doguwar rigar da ta yi, ba ƙaramin yi mata kyau yayi ba, sai da tun da ta shigo kallo ɗaya yayi mata suka haɗa ido, ya sauke idanunsa cike da fargabar kar ta yi masa wata tijarar a cikin mutane, dan ya fuskanci tamkar wani jin daɗi take yi idan ta ci mutuncin sa.
Kasancewar babu malami a ajin, ya sanya Captain ya ce wa Yazeed, ya fito ya É—an yi musu tutorial, a kan wasu courses É—in.
Yazeed bai musa ba, ya fito ya karɓi abin rubutu, sai da ya fara da addu'a, sannan ya kalli 'yan ajin ya fara yi musu bayani da yadda ya fahimci tambayar da malamin nan yayi a ranar da ya ce suyi amfani da waya, sannan ya shiga gaya musu dabarun da ya bi wurin gane amsar tambayar.
Fadila ji tayi ba zata iya zama jin shirmen da Yazeed yake yi ba, duk ajin a rasa wanda zai yi tutorial sai shi, ita gaba daya ta gama raina shi, ta É—au jakarta tana mita, a fili take cewa "Instead of a nemo malamin da ze mana covering Wannan period É—in, kawai an samu a gaba wani yana shirme, mutumin da ko turanci bai iya ba me zai koyawa wasu?".
"Babbar yarinya wai dan Allah mai yasa ki ke haka ne? Wannan fa ba girmanki ba ne, bawan Allah nan mutum ne, ba zai ji daÉ—i ba abin da ki ke yi masa".
"To kar Allah ya sa ji daÉ—in mana, ya daina shishshigi da son nuna ya fi kowa iyawa"
Babson ya ja wani uban tsaki ya ce "Dalla ku share wannan mahaukaciyar ku cigaba da yi mana abin da yakamata".
"Ba zan kula ka ba, barber ka ke ko me? Talauci ne yake É—awainiya da kai ka ke wannan shirmen" ta yi tsaki ta fice.
Har ta yi ta gama Yazeed bai ko ɗaga kai ya kalleta ba, ya karɓi wayar Captain, ya cigaba da yi musu bayani.
Captain ya ce "Yazeed, dan Allah ka yi haƙuri, na sani abin da yarinyar nan take yi maka babu daɗi, amma dan Allah ka yi haƙuri"
Cikin dakiya da basarwa Yazeed ya ce "Kar ka damu Captain, ni ban damu ba" ya cigaba da abin da yake yi.
"Kina Ina? Munafukar banza fito nan"
Sai da cikin Inno ya kaÉ—a, dan tun da taji muryar su Kawu Lawan, ta san ba alkhairi. Fitowa ta yi daga É—aki tana faÉ—in "Lafiya kuwa?"
"Kya tambayi lafiya mana, munafuka ha'ina, ki zo ki fito mana da in da yarinyar nan Amina ta ke, dan babu yadda za a yi ta gudu ba tare da haÉ—in bakin ki ba".
"Haba Yaya Bala, ni meye nawa a ciki? Ya za ayi in goyi bayan Amina ta bijire muku, ko ta gudu? Nima fa Amina 'ya ce a wurina, ba zan goyi bayan ta aikata abin kunya ba, ni ban san in da take ba".
Bala ya ce "Ai kuwa ƙarya ki ke yi, kuma yadda ki ka haɗa baki da ita kika sa ta gudu, sai ki koma ki haɗo abin da ya samu a mayarwa da Jarmai kayan aurensa, tun da ta gudu".
"Meye haɗina da kayan auren Jarmai? Bayan kuɗinsa da komai ku ya dabƙawa kuma babu abin da kuka bamu a ciki?".
"Rufewa mutane baki, amma dai kin san abin da aka yi kuÉ—in ko? Kayan katako aka sayawa Amina da su"
"Amma yaya Bala, ina a kuÉ—in gonar mahaifinta aka saya mata kayan? Ni dan me za a ce in bada wani kuÉ—i"
"Au tuhumar mu zaki yi, to Wallahi sai kin kawo wani abu, dan sunan mu ba zai ɓaci a banza ba a dalilin ku ba, mutanen banza kawai"
Galala haka Inno ta bi su Lawan da kallon mamaki da kuma ƙarfin hali.