← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 84

Sashe 63

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah sarki, lallai wannan makaranta taku ana ji daku, lallai da safe na shigo a bani in gani" Amina tayi murmushin yaƙe, ta cigaba da kunna wayarta, bayan Hajara ta fita Amina ta raka bayanta da harara, cike da jin haushin saka idon da take mata.

Hafsa na cikin bargo ta ƙule, ta saka wayarta a silent, tare da rage mata haske, suna chatting da Khalil, sai su daɗe suna chatting basu san dare ya yi ba, ita kanta tana mamakin kanta yadda ta yi wani irin sabo da Khalil, wanda har ya kai idan Khalil baya son abu, har rawar jiki take ta daina, duk abin da ta san zata yi yayi farin ciki tana masa. Haka shima ɓangaren sa tattalata yake tamkar ɗanyen ƙwai a kan dutse, shima yana kaucewa duk wani abu da zai sanya ta ɓacin rai ko damuwa, yana matuƙar tausayinta, hakan ya sanya yake tattalinta yake gudun abin da zai ɓata mata rai ko tayi fushi.

A Hanyar Yazid ta tahowa makaranta, suka haÉ—u da class Captain É—insu, ya É—auko Yazid a babur É—insa, suna tafe yana bashi labarin faÉ—an da Amra da Fadila suka kusa yi jiya, a kan abin da Amran tayi masa.
Yazid dai bece komai ba, sai ɗan murmushi da yayi, Captain ya cigaba da bashi haƙuri, a kan irin abubuwan da wasu daga cikin 'yan ajin suke masa.
Zuwansu yayi dai-dai da tsayuwar motar Fadila.

"Ahh Yazid ga Bestynka nan ta ƙaraso"

"Wace kuma Besty na?" Yazid yayi maganar cikin ko in kula.

"Fadila mana"

Ta rufe motar ta ɗan tsaya tana jiran ƙarasowarsu.

"Captain" ta faÉ—a tana É—an murmushi.

Captain ya ce "Na'am tsigai, sarkin tsiwa"

"Kaga ka kiyayeni bana so"

Yazid yaƙi ko kallon in da Fadila take.

Ya yin da ita kuma take satar kallonsa, Captain ya ce "Bari in yi gaba ku gama ganawa, dama zan karɓo mana Assignment, sai kun taho" yayi gaba ya bar su a tsaye.

Captain na barin wurin, Yazid shima ya yi tafiyarsa ya barta a wurin, gaba É—aya sai taji babu daÉ—i shareta da ya yi, ko dai Kankiya ya kira shi ya yi masa warning ne a kanta, shi ya sanya ya daina kulata?.
Ɗan taɓe baki tayi, ita ma ta nufi aji tana cigaba da zancen zuci.

Sai yau Azima ta dawo daga hutu, suka rungume juna ita da Amina suna ta murna. "Azima shi ne kika ƙi dawowa sai yau?"

"Ke bari, munje hutu da Mummy ne, sai jiya muka dawo"

Amina ta ce "Masha Allah, ya Mummyn?"

"Mummy na nan lafiya, ya Baba da mutanen gidanku marasa mutunci"

Amina ta ɗan ɓata fuska ta ce "Meye haka?"

"Ba dole in faɗa ba, mutuncin ne da su? Wallahi matar nan ta bani mamaki Amina, a gaskiya kina haƙuri sosai, Allah ya ƙara miki haƙuri"

"To Azima idan ban yi haƙuri ba yaya zan yi? Tun da karatu nake son nayi"

"Ke zan yiwa Mummy magana, wallahi da zaki yadda ki dawo gidanmu, ki daina wannan aikin, Mummy zata dinga biya miki kuÉ—in makaranta, meye dubu sittin Allah na tuba, Mummy zata biya miki"

Waro ido Amina tayi ta ce "Azima dubu sittin kuma? Dubu sittin ne kuÉ—in makarantar?"

"Au ke da baki sani ba? Dubu sittin ne fa kawai duk term, sai sauran abin da ba a rasa ba, Mummy tana da kuÉ—i sosai, ga shi Daddynmu ya mutu ya bar mana kuÉ—i, ni da Yaya Sagir da nake gaya miki, wallahi da zaki yadda Mummy cewa tayi zata É—auke ki ki dawo gidanmu, ita tana sonki"

Shiru Amina tayi tana tunani, Yanzu duk term naira dubu sittin Alhaji Ahmad yake biya mata na makaranta, kuma gashi ance na shekara ya biya mata, ga kuÉ—in litattafai da sauransu.

"Ya naji kin yi shiru? Zaki yadda ki dawo gidanmu?"

Firgigit Amina ta dawo daga tunanin da ta tafi, ta ce "Azima Baba ba zai yarda in nisa da shi ba, nima ba zan so hakan ba, amma naji daɗi da ƙauna da karamcin da Mummy take nuna mini, shi wannan aikin da nake na lokaci ne, watarana sai labari. Kuma in Allah ya kaimu next year fa zamu gama, da an gama wannan competition ɗin fa za'a fara yi mana lesson ɗin Jamb da na Waec da Neco, Kinga lokaci kaɗan ya rage mana".

"Haka ne Amina, Allah yasa mu gama lafiya"

"Ameen" Amina ta amsa.

Har aka tashi Yazid bai yi gigin zuwa in da Fadila take ba, gaba É—aya sai taji babu daÉ—i, dan a 'yan kwanakin ta saba da shi da nacinsa, ba tare da ta shirya hakan ba.

Hajiya Zainab ta sha mamakin yadda Khalil ya iya daina shigowa cikin gidan, ko gaisheta yayi balle ya ci Abinci, duk dan saboda ta raba shi da wata 'yar matsiyata.
Dan haka a fusace yau ta tafi ɗakin nasa, ta tarar yana zaune  yana dannan system, walpaper system ɗn, hoton hannunsa da na Hafsa ne sanye da zobunan da ya saya musu.

"Sannu mara mutunci salamamme"

A razane ya É—ago ya kalli Mummy.

"Yanzu Khalil wuyanka har ya yi kaurin da dan nayi maka faÉ—a na hanaka kula wata matsiyaciyar yarinya zaka daina shiga harkata, ka daina shigowa cin abinci?".

"Mummy ba haka bane kaw ....

"Yi mini shiru, gaba kake da ni ko Khalil, ka kyauta ka cigaba kar ka fasa, wannan yarinyar ce dai ko, to na rabaka da ita har Abada. Idan kuma ka ƙi ji, ba zaka ƙi gania ba. Ta juya ta fice tana huci, ba ta jin zata iya yiwa Khalil sassauci a kan al'amarin nan sam.
Khalil ya dafe kansa da yayi masa wani irin nauyi, da har yake barazanar yi masa ciwo, ya rasa Wannan wace irin ƙiyayya ce haka Mummy take yiwa talaka, meye aibun Hafsa banda talauci, kuma ai komai na Allah ne.

Washegari ma a school, Yazid ya ƙi kula Fadil, ya cigaba da sabgoginsa, sun yi lectures na farko, sun samu break, Fadila ta kasa jurewa, ta tsinci kanta da tafiya wurin da yake a zaune, a can ƙarshen ajin.
"Ustaz wurinka na zo"
Ya É—ago ya kalleta "Waye kuma Ustaz?"

"Kai mana"

"Baki san suna na bane?"

"Eh sunan naka ne bana riƙewa" Yazid ya gane ba zata iya kiranshi da sunansa bane a gabansa, amma dan rainin hankali ba zata faɗa ba.

"Magana fa nake maka"

"Ba fa kurma ne ni ba, ina jinki"

"To ba zaka amsa ba"

"Ki faÉ—i sunana mana idan so kike in kulaki" yayi maganar ba tare da ya kalli in da take ba.

Share maganar tayi ta ce "Abu nake son ka koya mini dan Allah"

"Ba zan koya ba" ya bata amsa direct.

Ji tayi kamar ba taji daidai ba, dan haka ta ce "Me kace?"

Ya waiwayo ya kalleta ya tsuke fuska ya ce "Ba zan koya ba nace, idan kin koyi faɗan sunana sai in koya miki" Nan da nan ya ga ɓacin rai ya bayyana a fuskarta, kawai ta juya ta bar wurin, ranat yana mata suya, 'laifina ne da nuna na damu da kai, shi yasa har ka yi mini wulaƙanci' ta faɗa a zuciyarta.

Tana bada baya Yazid ya fara dariya ya furta "Yarinya ba wayo" yana ankare da ita har suka kammala lectures na biyu, sai cika take tana batsewa, taji zafin abin da ya yi mata sosai.

Sai da ya daidaici lokacin da yafi sakata a kwana, ya hautsina mata lissafi, ya dawo daga salla, lokacin da É—alibai suka ragu daga ajin, wasu suka tafi salla wasu cin abinci, ya lura ko sallar babu alamar ta je, ta Kwantar da kanta a kan benci.

"Bestyna, what are you thinking about? Tashi muyi karatun É—auko littafin muyi karatun"
Sarai ta gane muryarsa, amma tayi masa banza, taƙi ɗagowa.

"Common, É—ago mana" yayi maganar yana zama a kusa da ita. Da sauri ta tashi zaune, ta kuma matsawa ciki, tana haÉ—e rai.

"ÆŠauko littafin muyi karatun"

"Kaga malam ka ƙyaleni bana so" ta faɗa tana jin kamar a lokacin ya ce ba zai koya mata ba.

"Haba Ukty, kefa kika fara wasan nan, kika ce idan ina da zuciya kar in sake kula ki, kuma ina da zuciya a ƙirjina, tana aiki kuma, kawo hannunki ki taɓa kiji" yayi maganar kamar zai riƙo hannunta.

"Wai meye haka ne, kar ka sake ka taɓa ni"

"Ashe kina tsoro, kawo muyi lesson É—in kin ji Bestyna"

"Bana so, na gaya maka ka ƙyaleni zan maka rashin mutunci wallahi"

"To ni rashin mutunci wanne ne baki yi mini ba, duk haddace in kin mini ba haushi nake ji ba, ni ɗanawa nayi yau, amma ki yi haƙuri muyi da wasa nake miki"
ÆŠauke kanta tayi, tana kallon gefe guda, irin yayi idan ya gaji ya tashi.

"Baƙin gashi, fararen idanuwa, dogon hanci, bakin tsiwa, matsakaicin tsayi, fa tubarakallahu ahsanul khaliƙin, You Are beautiful" murguɗa baki tayi tana kuma ɗauke kai.

"Shikenan, idan kin sakko kya kulani, ni na tafi gida, saurayinki ne zai shigo lectures yanzu, gara in fita in tafi, tun kan ya shigo ya dizgani a gaban mutane saboda ke".

"Kar ka sake cewa saurayina, na gaya maka"

"Saurayinki ne mana, idan ba saboda ke ba me nayi masa ya tsaneni, bai san ba wata alaƙace ta kirki tsakanina da ke ba, ki mini tsiwa lokacin da kike so, ki lallaɓani idan kina buƙatar wani abu a wurina, ko ba haka ba ne?"

"Kai ka sani"

"Dama ni na sani mana, ki kalli idona ki maimaita abin da kika faÉ—a in ba tsoro ba"
Sake kifa kanta tayi, tai masa shiru, tana jinsa ya ɗau biro, yana mata rubutu a jikin hannunta, taƙi ko motsi, sai da taji alamar ya tashi ya tafi, sannan ta ɗaga hannun ta duba, da larabci ya yi mata rubutu, sai dai ba ta gane meya rubuta ɗin ba.
Ɗaga kai tayi taga har ya kai ƙofa, a ranta ta ce 'A haka kamar baya magana, amma ya iya wulaƙancj kala-kala'.
Chapter 63 · 0% Book details