← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 84

Sashe 80

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kalmar usless ɗin nan ba ƙaramin ƙonawa Fadila rai tayi ba, ji tayi kamar ta zagi Kankiya.

Captain ya ce "Sir kayi haƙuri ba shi da lafiya ne, yau ya dawo"

"Shut up! Nace ka sa mini baki ne? Ai ya riga ya san na hana shi zama a ajina, tashi ka bar mini ajina"

Yazid ya ja jikinsa a hankali, ya tashi tsaye, sai da ya tashi Fadila ta lura da Cannula a hannunsa, a hankali yake jan ƙafarsa, tare da dafe gefen cikinsa ya fice daga ajin.
Kankiya yayi tsaki ya ce "Nonsense"
Miƙewa Fadila ma tayi, ta ɗau jakarta ta nufi hanyar fita, tana jin Kankiya na kiranta amma tayi masa banza ta bar ajin da sauri.

Hajiya Zainab ce ta shigo ɗakin Daddy tana masifa "Wai ni ina wannan sakaran direban naka ya tafi? Tun ɗazu nake nemansa, yazo ya karɓo mini saƙo a wurin Hajiya Salma.

Cikin ko in kula Daddy ya ce "Na aike shi ne"

"Zuwa ina? Jiransa nake yi ni akwai in da zani"

"To ke ki ɗauki mota kije ki karɓo da kanki mana, ko ta yi miki aike"

"Haba Baban Khalil, ina gaya maka uzurina kana gaya mini wani abu daban, dan Allah ka kirashi ya zo ya je mini aiken nan"

Alhaji Ahmad ya tashi zaune ya ce "Na aiki Zakiru Shanono, zai kai Amina gidansu"

"I don't get you, and what does that mean? Meyasa zaka aike shi ya kaita ƙauye, a matsayinta na wa?"

"Mahaifinta ya nemi hakan, dan ba zai yiwu ya bar yarinya ita kaÉ—ai ta tafi ba"

Rai a ɓace ya ce "I don't care, me yasa zaka yanke wannan hukuncin ba tare da na sani ba, 'yar aiki tafi aikin gidana muhimmanci kenan? Ubanta ya kaita mana, yanzu waye zai je mini aiken nawa?"

Miƙewa tsaye Daddy yayi ya ce "Zainab, ba Khalil bane da Ahmad kike Magana, duk wanda yake aiki a ƙarƙashina yana da damar ya nemi alfarma a wurina nayi masa" ya fice ya bar mata ɗakin.

AYSHERCOOL
08081012143

GABA DA GABANTA

AISHA ADAM AYSHERCOOL

44

Ganin Alhaji Ahmad ma ya É—au zafi sosai, ya sanyata saurin saukowa daga nata fushin, dan da wuya yayi fushi amma idan yayi fushi wahalar sha'ani ne da shi fiye da tunani.
Dan haka ta ce "Naji shikenan ya wuce, na haƙura da saƙon na san yadda zan yi"
Bedroom ɗinsa ya wuce ya barta, tabi bayansa tana cigaba da lallaɓa shi, amma ya shareta ya ƙi saurarta.

Ba ƙaramin yarfa Kankiya Fadila tayi ba, ganin yadda yake muzurai ake tsoronsa amma Fadila ta yarfa shi a gaban ɗalibai, hakan ba ƙaramin ɓata masa rai yayi ba, kuma hakan ya jefa zargi a zukatan ɗaliban, mai zai sa Fadila ta tsinka malamin haka duk da yadda ake tsoronsa.

"Yazid, Yazid" tsayawa yayi ya waiwaya da jin muryarta a cikin dodon kunnuwansa.

Ta ƙarasa in da yake da sauri, bai ƙosa ba ya jira har ta cin masa.

Cikin damuwa ta ce "Sannu, ya jikin naka? Ashe baka da lafiya?"

"Eh, amma da sauƙi sosai Alhamdilillah"

"Wai meya sameka ne?"

"Rashin lafiya ne" ya bata amsa.

"Wane irin rashin lafiya?" Ta kuma tambayarsa cikin kulawa.

"An mini aikin appendix ne, sai kuma asma da ta dameni shikenan amma da sauƙi sosai"

"To yanzu ina zaka daga nan?"

"Gida zan tafi"

"Ok, to muje in sauke ka"

Da sauri ya girgiza mata kai ya ce "A'a ki bari na gode zan tafi"

"Ba ka ganin a yadda kake tafiya, kazo muje in sauke ka"

"Na gode, amma ba zan hau motarki ba, ban kai in hau mota irin wannan ba, ba ta dace da hawan talaka kamata ba" daga haka ya juya yana tafiya a hankali.

Tsayawa tayi tana cigaba da kallon yadda yake tafiya a hankali, har ya ɓacewa ganinta.

Tafe suke suna hira jefi jefi ita da Zakiru, yana bata labarin yanayin zamantakewar gidan kafin zuwanta.

"Ai nake gaya miki, ko 'yan uwan maigidan nan duk zumuncinsu sun haƙura sun daina zuwa, sun zuba masa ido, shi kansa sai lokaci lokaci yake zuwa, dama bata yadda yaranta suje ba, kuma fa 'yan gari ɗaya ne, saboda azabar baƙin halinta, duk son sa da yayi taimako sai dai yayi bata sani ba. Ai matar nan bana zaton tana son taga Annabi"

Amina ta ce "A'a karka ce haka, amma ina mamakin ita ko nata 'yan uwan basa zuwa sai ƙawaye"

"To ina taga wasu 'yan uwa ma, sukan zo wasu lokutan suna ba wani kallon arziki take musu ba, amma a hakan tana jidar kaya ta bani in kaiwa wasu daga 'yan uwanta, ai ita idan kika ga tana rawar kai tana nan nan da kai, to mai kuɗi ne kai, duk ta kanainaye maigidan baya jin maganar kowa sai tata, ai har gara yanzu a kan da, sanyinsa yayi yawa, sai ya fito cikin mutane ya fito yana taƙama baki Ga yadda ake girmama shi a waje ba, amma a gidansa ba shi da kataɓus ga shegen son 'ya'ya kamar masifa, waccan tsigalaliyar 'yar ta sa idan ta zauna tana taɓara abin takaici, gata halinta ɗaya da uwarta na rashin mutunci, ba kunya idan nayi kuskure take ƙare mini zagi, ai Alhaji Ahmad yayi ta kowane fanni amma a gidansa dai damisar kwali ne"

"Zakiru ya isheka haka, wasa yayi wasa banda tsikarin uwar miji da taɓarya" tayi maganar ranta a haɗe.

Zakiru ya ce "Kamar yaya kenan?"

"Ina ruwanka da abin da ke faruwa a gidansa kake ce masa damisar kwali, kai waya san yadda taka matar ke juyaka, ya isheka bana son wannan hirar"

Zakiru ya yi murmushi ya ce "Allah ya baki haƙuri, tuba nake"

Amina ta basar da shi ta haÉ—e rai.

Message É—in Daddy ne ya shigo wayarta.
"Yaya hanya, kun isa kuwa?"

Tayi masa reply "A'a muna hanya"

"Ina fatan ba kya jin yunwa, idan kina jin yunwa ya tsaya ki ci Abinci"

"Ka manta na karya kafin mu tafi, mun shiga Shanono, mun kusa gida in sha Allah"

"Ok, to Alhamdilillah, ki gaishe su"

"Thank you, za su ji" ta É—an yi murmushi ta ajiye wayar.

Hajiya Zainab ce zaune a ɗakinta tana waya da Hajiya Salma "Dan Allah Salma ki ƙara haƙuri, kwanan nan duk na kasa gane kan babansu Khalil, ya ce zai bani kuɗin amma sai wasa yake mini da hankali, da abu ya ɗan haɗamu sai ya hau fushi, a yadda yake ɗin nan idan na matsa, zai iya hana kuɗin nan, kuma ni kinga na tattare kuɗin hannuna na yi order kaya, kuma ba zai yiwu in kwashe sauran kuɗin hannuna in baki ba, saboda suma juyasu nake".

Hajiya Salma ta ce "Ni yanzu ya zan yi? Turai ta bani aron million biyu, dama na wajenki nake jira da million bakwai coustom suka ce zan bayar a sakar mini kayana, da ƙyar suka bari a 5million, kuma kinga Alhaji  kwanan nan ya ƙara mini jari ya ce ba zan samu ba"

"Kiyi haƙuri, zan cigaba da lallaɓa shi saina karɓa zan baki in Allah ya yarda, kuma ina ga zan je Abuja a satin nan in Allah ya yarda"

"Too, Zainab me zaki yi a Abuja kuma?"

Hajiya Zainab ta ce "Wurin yaron nan Khalil mana, gaba ɗaya ya ɗauki gaba da ni, ubansa kawai yake tuntuɓa, ba ruwansa dani"

"Kaii yaran zamanin nan, anya ba asiri suka yi masa ba, duk yadda Khalil yake miki biyayya, amma yanzu a kan wannan yarinyar ya daina shiga harkarki"

"Bari kawai Hajiya Salma, bana son babansa ya gano actual abin da nayi masa, kin san halinsa a kan 'ya'yansa, gaba É—aya ina cikin damuwa dole in je Abuja"

"Ke Zainab, ai ba a yiwa yaran zamanin nan haka, ba ke yakamata kije ba, ki kai yarinyar wurin malamai, idan ma wani abun suka masa a karya shi, sannan ki nemo masa wata matar, akwai 'yar ƙanwata  Hajiya Badi'a ai kin santa Kursum ki haɗa shi da ita kawai"

"Kin kawo shawara haka za ayi, zai ga tsiya"

"Ai kawai ba sai kinje ba, sai bayan an kai kuÉ—i da komai, ki ce masa ya zo ga mata shine zaki hukunta shi ki nuna masa ke uwace"

Hajiya Zainab ta ce "Hakan ma yayi, na gode sosai Salma, zan zo gidanma da kaina mu ƙarasa tattaunawa"

"To shikenan, sai Allah ya kawoki" suka yi Sallama Hajiya Zainab na jin ta gamsu da shawarar da Hajiya Salma ta bata.

Amina tayi ta kwatantawa Zakiru hanya har ƙofar gidansu, suna parking ta buɗe motar ta tafi da gudu cikin gida, wasu daga yaran su Kawu Bala suna ƙofar gida suka bi motar da aka kawo Amina da kallo, dan ɗaya ce daga irin jibga jibgan motocin da Alhaji Ahmad yake hawa ne aka kawota.
"Inno! Inno!" Amina ta dinga ƙwalawa Innon kira.

Inno ta saki ƙwaryar hannunta, ta buɗe hannayenta Amina ta zo ta rungumeta, Inno ta ƙanƙame Amina kamar zata mayar da ita ciki, Amina kuwa kuka ta fara yi tana jin tsananin kewar Inno.

"Amina, Amina na rasa mema zance"

"Inno, yaushe rabon da in ganki?"

Inno ta ce "Yau ai gashi kin ganni"

Tuni wasu daga cikin yara har da 'yan matasa na maƙotansu, suka cika tsakar gidan suna kallon Amina.

Suka shiga ɗakin Inno, Amina sai sake ƙanƙame Inno take yi.

"Amina ya gida ya karatun bokon?"

"Karatu lafiya lau Inno"

Inno ta riƙe haɓa ta ce "Ohh, Amina buri ya cika ana can ana boko"

"Inno kenan, ai zaki ga ribar boko in Allah ya yarda, bari in yiwa Zakiru magana ya shigo ku gaisa"

Inno ta ce "Waye shi kuma?"

"Direban gidan da nake aiki ne"

"Au ai na zata siriki ne"

Dariya Amina tayi ta ce "Ba wani siriki"

Amina taje ta kira Zakiru, ya shigo gidansu Amina, suka gaisa da Inno, daga nan suka ɓige da hira kasancewar Inno ta san garinsu Zakiru yayarta tana aure a can.

Mutane sai shigowa suke suna sun zo yiwa Amina sannu da zuwa, nan kuwa gulma suke zuwa yi, suna ta maganganun Amina ta zama ƙatuwa, gashi ta yi fresh ta zama 'yar gayu, ga uwar waya a hannunta.
Chapter 80 · 0% Book details