Sashe 38
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amina tabi Fadila da kallo, Yadda ta ƙanƙame mahaifinta cikin kulawa da ƙauna. Ji tayi ina ma zata iya zagin Alhaji Ahmad, Fadila taji abin da ta ji, lokacin da taci mutuncin nata mahaifin, sai dai kash hakan ba tarbiyyar Amina bace, ko da wasan wasa ba zata iya aikata hakan ba, haka ta wuce ta bar musu falon suna cigaba da farincikin dawowarsa.
Hafsa fa ta É—an shiga damuwa, saboda rashin kiran wayarta da Khalil ya daina yi gaba É—aya, gashi kuma ita ba zata iya kiransa a ta ta wayar ba, saboda a ganinta hakan bai dace ba.
Amina ma sun fara jarrabawa a makaranta, ayyuka sun ɗan yi mata sauƙi, kasancewar yanzu Fadila bata zuwa Makaranta, ta rage tashin sassafe.
Tun da Alhaji Ahmad ya dawo basu haÉ—u ba, har ta tafi makaranta bai fito ba, wasu lokutan baya dawowa sai dare sun kwanta.
Duk kashedin da ake mata a kan zuwa wurin Baba tayi zamanta, ba ta ji ba, dan yau ma tana wurinsa suna hira, kasancewar yau Asabar, Baba yana gyara flowers É—in harabar gidan, tana taya shi.
Ƙamshin turaren Alhaji Ahmad ya cika wurin, Baba ne ya miƙe da sauri fuskarsa ɗauke da murmushi, yana yiwa Alhaji Ahmad barka da fitowa.
"Ina wuni" Amina ta faÉ—a kamar an mata dole, dan ta san Baba zai iya yi mata faÉ—a idan bata gaishe shi ba.
Ya waiwaya ya kalli in da Amina take "Lafiya ƙalau, ya school ɗin?".
"Lafiya ƙalau".
"Good" ya mayar da dubansa kan Baba ya ce "Malam Hassan ya aikin? Babu dai wata matsala ko?"
Baba ya ce "Babu matsalar komai ranka ya daÉ—e".
"To Alhamdilillah, Allah ya yi jagora".
Baba ya amsa da "Ameen".
Amina a ranta ta ce "Shi dai gashi nan, shima yana da wannan taƙamar, sai dai baya wulaƙanci kamar yaransa da matarsa' ta ɗan taɓe baki ta cigaba da sabgar gabanta.
Fadila ce zaune a kan gadonta, tana zazzage jakarta ta Makaranta, ita kanta bata san me take nema ba, wata takarda ce mai ƙyalƙyali ta faɗo daga tsakanin litattafanta.
A hankali ta miƙa hannunta ta ɗau takardar ta buɗe, rubutun larabci ne a jiki, an cika paper da rubutun larabci. Ba rubutun kowa bane face na Yazeed, tamkar inji ne ya tsara rubutun ba hannun mutum ba, ta dinga jujjuya takardar amma ba ta fahimci komai ba, sai sunansa da ya rubuta da Larabci da signing, haka nan taji tana son sanin me takardar ta ƙunsa, ƙarshe ma sai ta fara tunanin ya aka yi takardar ta shiga jakarta?.
Bacci take ji sosai, dan haka ta watsa litatafan ƙasa tai kwanciyarta a kan takadar, wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.
"Ukty, yau kin yi kyau fiye da koyaushe, idanunki kamar ƙara musu kyau ake masha Allah" ya faɗa yana murmushi.
Haɗe rai tayi tana kauda fuskarta gefe guda, matsawa yayi jikinta Sosai yana mata magana. Jikinta ne ya hau rawa, taji tamkar ta fashe da kuka, ga wannan baƙon yanayi da yake kaiwa yana komowa a jikinta.
Fuskarta duk hawaye ta kalli Yazeed "Wai ni meyasa nake jin haka idan ka masto kusa dani?".
Ya É—ora kansa a kan kafaÉ—arta ya ce "Me kike ji?"
"Nima ban sani ba" ta faÉ—a muryarta na rawa.
Bakinsa yake ƙoƙarin sakawa a nata, amma ta fara ƙoƙarin kauda kanta, sai dai riƙon da yayi mata bana wasa bane. "Yazeed dan Allah" ta faɗa fuskarta duk hawaye, jikinta kuma na cigaba da rawa.
Sai da Yazeed ya yi galaba a kanta, wurin saka bakinsa a nata. Ba zata iya misalta ko rarrabe wane yanayi haka suka wanzu a ciki ba ita da Yazeed.
"Yazeed" ta faɗa da ƙarfin gaske, ta tashi daga baccin a razane, fuskarta duk hawaye, tana haki.
Amina dake durƙushe tana tattare litattafan da Fadila ta zubar a ƙasa ta kwashe ta gyara ɗakin, sai da ta razana, ta saki litattafan. Ita ma ta maimaita "Yazeed kuma"
Fadila sai haki take tana rarraba ido, ta kai hannu fuskarta taji hawaye.
Ta kalli in da Amina ke tsaye tana binta da kallo.
Ji tayi tamkar yawun Yazeed ne a bakinta, saboda bata taɓa zaton mafarki ne ba gaske ba. Da sauri ta duro daga kan gadon, ta tafi banɗaki tana zubar da yawun bakinta.
Amina tabi bayanta da kallo, tana tunanin dama ana mummunan mafarki da rana tsaka haka? Kodayake in mutum baya Addu'a ba abin da ba zai sameshi ba.
Haka Fadila ta dinga zubar miyau, tamkar a gaske mafarkin ya faru, har irin ƙamshin turaren da ke jikinsa, take ji a hancinta. Bata haƙura ba sai da ta sa brush ta wanke bakinta, sannan ta fito daga banɗakin.
La'asar liƙis, Khalil ya shigo garin Kano, salla kawai ya tsaya yayi, kai tsaye gidansu Hafsa ya nufa.
A ƙofar gida ya tsaya yana sallama, Mama ce ta leƙo da kanta, tana ganin Khalil ta fara murmushi, ya duƙa har ƙasa ya gaida ita, ta amsa masa cike da kulawa tana faɗin "Khalil kwana biyu"
"Mama ayyuka ne suka yi mini yawa, kuma da yake ba a nan Kano nake aikin ba, shiyasa".
"Allah sarki to Allah ya dafa, kuma gashi bata nan, tana wurin bikin wata ƙawarta"
Khalil ya ce "Dama Hafsa na ƙawaye?".
Mama ta ce "Kaima ka fuskanci halinta kenan, tana da su irin wanda suka yi Makaranta a baya".
"To Mama ina ne wurin bikin?"
Mama ta gaya masa yayi mata godiya ya tafi.
Ba tsammani taga lambar Khalil yana kiranta, duk da bata yi Saving lambar ba, amma ta haddacce ta tsaf.
Cikin hanzari ta É—aga wayar, sai dai bata iya jin komai saboda hayaniya.
Tashi tayi ta fita harabar wurin bikin, jikin wata mota ta tsaya, ta saka wayar a kunnenta tare da yin sallama.
"Wa'alaikum salam, Baby ya kike?" Taji maganarsa a bayanta. Da sauri ta waiwaya taga Khalil a tsaye a bayanta.
"Ya aka yi ka san ina nan ka zo?" Ta faÉ—a cikin mamaki.
"Miracle" ya faÉ—a yana dariya.
Ƙare mata kallo ya shiga yi, tana sanye da riga da skirt na atamfa, ta kashe ɗauri, hannunta ya sha lalle.
"Ina wuni" ta faɗa a taƙaice.
Maimakon ya amsa mata sai ya shiga É—aukarta hoto a wayarsa. HaÉ—e rai ta yi ta ce "Ka bari bana so".
"Tom na bari, kin yi mamakin ganina ko kya ce na fiye naci, ba laifina bane, laifin zuciyata ne". Hafsa ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta.
"Kin yi shiru, ashe biki kuke babu labari. Nayi mamaki da mama tace mini bikin ƙawarki ne, ashe kina da ƙawaye?".
Abinda ba ta taɓa yi masa ba tayi, murmushi wanda sai da dimples ɗinta da bai taɓa sanin tana da su ba suka lotsa.
A hankali ya furta masha Allah beautiful.
"Ina da ƙawaye mana, kana mini kallon bani da kirkin da zan yi ƙawaye ko? Babbar ƙawata ce tun muna yara muka tashi tare shiyasa na zo bikinta".
"Ashe ma bikin namu ne, duk da ba a gayyaceni ba muje, a bani wurin zama da Abinci daga Abuja nake ko gida banje ba Wallahi" É—an zaro ido tayi dama ga idanun nata tubarkallah.
"Me yasa baka je ka huta ba?".
"Ganinki nake son yi" ta jinjina kai, ta shiga gaba ya bita a baya, wurin taron yayi kyau da tsari, ta sama masa wurin zama, tasa aka kawo masa Abinci da abubuwan sha.
"Shikenan ko kana buƙatar wani abun?".
"Eh ke nake buƙata a kusa da ni, ki zauna idan kika tafi ban san kowa ba, kar ace na zo gayyar soɗi. Ta ɗan murmusa kaɗan ta samu wuri ta zauna.
Ba kunya Khalil ya fara cin Abincin nan, duk da hakan ba É—abi'arsa bace, cin kowane irin Abinci, kuma a gaban mutane, amma so yake Hafsa ta sake da shi, dan haka ya zage yana ziri.
"Allah ya nuna mana ranar bikinmu, muna kan high table kamar wannan couples É—in, wane irin kaya zamu saka?"
Shiru tayi masa tare da ɗan taɓe baki.
"Hafsa meyasa ba kaya sona ne?" Yayi Maganar da dukkan nutsuwarsa.
Ta É—auke kai tamkar ba ta ji abin da yace ba.
Ya kalli agogon hannunsa ya ce "Tashi muje in mayar da ke gida, tara saura yanzu".
"Dama jira nake ka gama, yanzu zan tafi nima".
"Na gama muje" ba tare da ko sallama ta tsaya ta yiwa Amaryar ba suka fito ita da Khalil.
Suna zuwa inda motarsa take ta ce "To ka gaida gida".
"Me kike nufi?"
"Zan hau Napep in tafi gida"
Khalil ya ce "Ke kin isa ma? Dan Allah kar muyi haka da ke" da ƙyar Khalil ya lallaɓata, ta amince ta shiga motarsa.
Suna cikin tafiya ta ce "Ina Yaya Abdul?"
"Yana nan, ko wurinsa ban je ba, sai Allah ya kaimu gobe, ya batun case É—in nan kuwa, ina fatan dai bai kuma dawowa ba?"
"Eh bai sake ba"
"Ai ba dan Mama ba, da sai na sa an rufe mini shi Wallahi, in ga ƙaryar iskanci, amma naji ya ce "Shi ɗan uwanki ne ko?"
Shiru tayi ba tayi magana ba, Khalil ya kalleta ya ce "Ya naji kin yi shiru?".
Kawai sai ta fashe da kuka, irin kukan nan me taɓa zuciya da bayyanar da tsantsar damuwa da ma'abocin yinsa ke ciki.
Da sauri ya yi parking ɗin motar, ya ce "Dan Allah kiyi haƙuri, ban san maganata zata ɓata miki rai ba, kiyi mini afuwa"
Sake rushewa tayi da kuka, tamkar zata shiɗe, wanda hakan ya sake ɗaga wa Khalil hankali, bai san lokacin da ya kai hannu ya ɗago fuskarta cikin damuwa ba "Dan Allah kiyi haƙuri" yayi Maganar a hankali yana share mata hawayen dake ta zubowa ba ƙaƙƙautawa daga cikin idonta.
Duk rarrashin da ya yi mata, bata yi shiru ba, sai da tayi mai isarta, sannan ta kalli Khalil ta ce "Mu tafi dare yana yi".
"Ai ba zan iya tuƙin ba, kin sani a zullumi, ina son sanin dalilin wannan kukan naki, da kuma dalilin da yasa ba kya sona, Hafsat ban miki bane ko ina da wani aibu".