Sashe 12
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Allah ya taimaketa ba wanda ya ganta suruf ta shige gida.
Ta tarar Inno bata nan, ta shiga banÉ—aki tayi alwala ta koma É—aki ta tayar da sallar magariba.
Inno ce ta shigo gidan tana 'yan maganganu, tana É—aga labule ta hango Amina na salla, aikuwa ta rafka salati ta ce "Ke daga ina haka? Kika É—aga mini hankali nake ta yawon nemanki?".
Amina ta idar da salla ta yi Adduointa, sannan ta kalli Inno ta ce "Inno tasha naje ko Saminu yana nan, wai ashe bai gayawa Baba saƙon nan ba, yana Ikko ma, aka kira mini shi a waya, shine ya ce mini zai gaya masa".
"Kuma shine sai ki tafi baki gaya mini ba, kin ɗaga mini hankali, nan suka aiko suna neman ki, amma ba kya nan na rasa ƙaryar da zan musu, wato ke dai Amina ba kya gudun magana ko? Ke duk abin da zai sa su zo su ci mana mutunci kin san shi kuma zaki aikata ko?" Shiru Amina ta yi taƙi magana, Inno ta yi ta banbaminta ta gama, Amina ba tace komai ba.
Baba Hassan kuwa kusan suman zaune yayi, bayan Saminu ya kira shi a waya ya wassafa masa irin katoɓarar da 'yan uwansa suke shirin aikatawa, na cefanar da gonarsa da kuma aurar masa da tilon 'yar sa ga mutumin banza da suke shirin yi.
Baba Hassan bai iya cewa Komai ba sai kashe wayar da ya yi, ya san nan duniya ko me zai yi bai isa ya hana wannan auren ba, sayar da gonarsa bai ɓata masa rai ba kamar yadda ake shirin salwantar da rayuwar 'yar sa, dan abin da ya shirya shine, shekara mai zuwa ya biya mata kuɗin jarrabawar, kuma ya dinga tattala 'yan kuɗaɗe saboda harkar makarantar ta, sai dai kash ga abin da 'yan uwansa ke shirin aikatawa.
Amina har zuwa sallar isha'i zazzaɓin jikinta bai sauka ba, ga wani irin koren amai mai ɗaci da take tayi, Inno sai jiƙe-jiƙe take tana ɗura mata, Amina mirsisi ta ƙi sha, saboda wannan jiƙe-jiƙen da take sha su suke ƙara sanyata amai.
Yarone yayi sallama, wai Amina ta je in ji Malam Rabi'u Jarmai.
Inno ta ce "Ka je ka ce masa ba ta da lafiya".
Yaron ya fita ba jimawa, ya dawo ya ce "Wai Kawu Lawan ya ce idan ba ta je ba ya zo sai ya zane ta".
Inno ta kalli Amina ta ce "Amina, lallaɓa kije, bana son fitina da tashin hankali".
Amina ta buɗe baki za tayi Magana, Inno ta girgiza mata kai ta ce "Yi haƙuri, daure kije" haka ta ɗau hijjabinta tana kuka, ga zazzaɓi a jikinta ta fita.
Jarmai na ganinta ya washe baki yana faÉ—in "Amaryata ba faÉ—a mai ya kawo gaba fisabilillahi?".
"Kaga saurara mini, Azzalimi kawai aka sayar maka da gonar Baba ka saya, alhalin ka san kuÉ—in gonarsa ba haka yake ba, to Wallahi ba zan auri Azzalimin mutum irinka ba, ga yaranka marasa tarbiyya da suke mana zarya a gida suna zagina, ba zan iya ba".
"Aikuwa zaki iya, da kin shiga gidana kin sha jar miya zaki watstsake muyi zaman mu".
"Jar miya a Ina? Da jar miyar a gidan naka ka ke kai yaranka bara wasu suna talla? Ina alamar jar miya a jikinka ko jikin 'ya'yanka, saboda tsabar cuta da zalunci ina kai ina ni, da ƙanan shekaru na ka haɗani a wannan gidanka na gayya, to bari kaji in gaya maka, ko da sarƙa a ka ɗaura Aurena da kai sai na warware shi, kuma ba dai in je gidanka ba sai dai a kai maka gawata".
"Ni kike gayawa wannan miyagun maganganun?" Yayi Maganar yana matsawa kusa da ita, wani azabar warin baki gami da na sigari ya daki hancinta, ga ƙarin rana yana yi, kayan jikinsa ne kawai wankakku, suma sai ƙarnin koren sabulu suke.
Ja da baya ta yi ta ce "Kar ka sake matsowa kusa da ni, na gaya maka ɗin, idan kana da zuciya ka biya ka karɓe kuɗin Aurenka ka fasa Aurena, idan kuwa ba haka ba idan ba a kai maka gawata gidanka ba, sai gidanka ya zama sansanin tashin hankali da bala'i na gaya maka".
"Yaro man kaza, mu zuba mu gani ni da ke shege ka fasa, gidana ne Wallahi sai kin shige shi sai na Aureki".
"Za kuwa mu gani, na bika ta lallalami kaƙi fahimta, zan fahimtar da kai ta hanyar nuna maka ni 'yar zamani ce, tsohon kawai". Saroro ya bi Amina da kallo, bai taɓa zaton za ta iya gasa masa miyagun maganganu haka ba, dan kowa kallon saliha yake mata, ga haƙuri da biyayya, a zatonsa duk irin halin mahaifinta ne da ita zai samu tuɓus, ashe abin ba haka yake ba.
Ita kuwa Amina gida ta shige abinta, Inno na tambayarta yaya aka yi, amma tayi shiru saboda yadda zuciyarta ke tafasa, ko ƙaunar jin sunan Rabi'u Jarmai ba ta yi, balle a kai ga batun Auren su.
Ta haÉ—a kai da gwiwa ta dinga rusa kuka, Inno kam ta gaji da rarrashin Amina dan haka ta zuba ido.
Baba Hassan kuwa bakinsa ɗauke da Addu'a, ya shiga falon gidan da sallama, a zatonsa ya je daidai lokacin da zai samu Alhaji Ahmad, sai dai kash bai fito ba, sai Hajiya Zainab ya tarar a falo, tana ta bawa Hajara umarni cikin tsawa da wulaƙanci.
Kasancewar abu ne na gaggawa, ya yanke shawarar sanar da Hajiya Zainab, Alfarmar da ya zo nema, ya risuna ya gaida ita cikin girmamawa, ta amsa ba yabo ba fallasa.
"Hajiya dan Allah wata alfarma na zo nema a wurinki".
"Haka dai, Alfarma ba yau ba gobe ina jinka".
Ya gyara zamansa ya ce "Wallahi wani al'amari ne ya taso mini a garinmu cikin gaggawa game da iyalina, nake son dan Allah a bani dama, ko kwana biyu in je in yi in dawo".
Ta ɗago ta kalleshi ta yatsina fuska ta ce "Idan zamu fita ko mun dawo, mu zamu dinga kokowa da ƙofa wurin buɗewa da rufewa kenan?".
"A'a hajiya, ga Hadi nan sai ya riƙa mini kan in dawo".
"Ban lamunta ba, aikin Hadi daban a gidan nan, naka daban dan haka ba in da zaka a yanzu, idan kuwa ka tafi, to ka tafi kenan" Baba Hassan yayi shiru ya rasa abin da yake masa daÉ—i, ya tashi gwiwa a sanyaye ya bar falon. Idan ya kuskura ya bar aikin gadin nan, tofa rayuwarsa da ta iyalansa za ta shiga wani hali, dan ba shi da wata sana'a da ya iya.
Amina kuwa tun Asuba take amai, ciwo ya ƙi sauƙi kullum sai gaba yake yi, ƙarfe shida da rabi sai ga Kawu Bala da Lawan tare da matansu, da wasu daga cikin yaransu kamar wanda za su je ritsa kwarto, sun shigo suna zazzaga bala'i tun daga hanyar shigowa.
Suna zuwa suka tarar da Amina a zaune dirshen tana amai.
Ladiyo Uwar gidan Kawu Bala ta ce "Wallahi malam zancen ya tabbata, abin da ake ta gudu, wannan aman ai irin na masu ciki ne".
Inno ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wane irin masu ciki kuma bata da lafiya ne fa".
"Ƙarya kike munafuka, dama ance mini an ganta a tasha wai taje wurin Saminu, dama zuwan da Saminun yake gidan nan kenan, Kuna lalacewa, kafira mai siffar munafukai, har an samu wanda zai rufa miki asiri ya Aureki, amma zaki tozarta mu, ashe dagaske ne kullum sai kin je tasha kin bada jikinki a baki kuɗi, wannan cikin ba zaki haife shi a gidan nan, jibi in Allah ya kaimu idan an sakko daga sallar juma'a za'a ɗaura aurenki da Rabi'u, kuma ba wata bidi'a da za a yi, ɗaurin Aure kawai za ai a kai ki dama da ke da bazawara ba maraba, kin gama tsufa a titi da rabawa maza jikinki".
Wani malolon baƙin ciki ya tokarewa Amina ƙirji, ba ta san lokacin da zafin maganganun wan mahaifin nata suka sanyata jan tsaki a fili ba. Ai kuwa hakan ya tunzura shi, ya nufi dangar kara, ya ciro kara suka rufar mata da duka.
Inno ta dinga kururuwa tana faɗin "Kuyi haƙuri, ba ta da lafiya".
Ladiyo ta ce "Wallahi ku casa ta, ko Allah ya sa cikin jikinta ya zube".
Tun Amina na iya motsi tana kuka, har ta sare sai wata irin ajiyar zuciya take, jikinta duk ya farfashe saboda duka.
Bayan tafiyarsu Inno ta É—umama ruwa, ta gargasawa Amina jikinta tana faÉ—in "Kin ga Abin da nake gaya miki ko, shiyasa na gaya miki taurin kai ba shi da rana Amina"
Kwanaki biyun nan, jikin Amina ya ƙara zafi, wai sunan amarya ba kitso ba ƙunshi tana kwace ba lafiya, iyalan su Kawu Bala suka kwashi raftar kayan da suka yiwa Amina aka kai mata gidan Malam Rabi'u.
Ranar Juma'a kiran Sallar farko, Amina ta É—ebi kuÉ—i, daga kuÉ—in da ake bawa Inno gudunmuwar Aurenta, dama tun dare ta haÉ—a kayanta Inno na bacci, kiran sallar farko, ta kwashi kayanta ta fice daga gidan.
Tana tafe a hanya tana kuka ta ce "Babana maganin kukana, na san wataƙila har yanzu saƙona bai riske ka ba, shi yasa baka kawo mini ɗauki ba, duk da ban san wurin da zan sameka a birni ba, amma gara in tafi da tambaya har Allah ya sanya in dace in gano in da kake, dan da in auren nan gara in mutu a hanya".
Arewabooks
https://arewabooks.com/u/ayshercool7724
GYARA SHARHI KO SHAWARA
08081012143
GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
P6
Follow my Arewabooks account
Ayshercool7724
https://arewabooks.com/u/ayshercool7724
Tafiya take tana ratsa tsakanin gonaki, ga duhu ga babu haske, amma hakan bai dameta ba, babban burinta shine ta ga ta baro cikin ƙauyen nan cikin salama, ba tare da wani ya ganta ba.
Baba Hassan kuwa bacci ma ɓarawo ne ya ɗauke shi, tunanin mafita kawai yake yi, zuciyarsa ta dinga raya masa kawai ya haƙura ya tafi ƙauye, komai zai faru ya faru, idan ya so ya haƙura da aikin, amma gefe guda yana tunanin idan ya bar aikin gadin me zai yi? Wace sana'a zai yi? Wata shawara yake ta jujjuyawa a ransa wadda ba shi da tabaccin zata karɓu.