Sashe 31
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kamar yaya Allah ya sauke ni lafiya, masu ciki fa ake gayawa haka"
Yazeed ya ce "Subhanallah, ba haka nake nufi ba, ina nufin Allah ya kai ki gida lafiya".
"Inyee me ake tattaunawa ne haka besty da besty, yau munga ƙarshen ƙauna, kowa na ƙoƙarin kare ɗan uwansa a kowacce gaɓa da ɗayan yake fuskantar barzana" Cewar Captain da ya ƙaraso yana dafa Yazeed.
Fadila ta haÉ—e rai ta ce "Nifa bana son sa ido, kar ka kuma ce mini wani bestynsa na gaya maka".
Yazeed ya ce "A'a Nothing like besty in Islam, she's my sister in Islam, ƙanwata ce ta Addinin Musulunci ko Fadila?"
"Kai ka sani" tai maganar tana hararasa.
"Kwa dai ji da shi, muna nan mun kasa mun tsare mun zuba ido, muga yadda ƙarshen wasan zai kaya, kwana biyun nan, kullum sai naga ka lallaɓo jikin motar nan kun keɓe kuna ƙusƙus, idan tai wari zata bazu mu ji ai" daga haka ya juya ya tafi yana murmushi.
"Kaga ustaz ka ke ko Sheikh, ka Matsa zan kunna mota, ni bana son damuwa yanzu ka zo kana suma, ace ni ce".
"Sunan nawa ma baki sani ba, amma kin iya rubutawa a cikin littafi ko? Da kuma test ɗin da kika rubuta mini, ni ina ga zanje in gayawa malamkn nan gaskiya, ni ban yi test ɗinsa ba, ƙanwata ce ta yi mini".
"Sai ka dawo" da haka ta rufe motar, ta kunnata ta ja ta a hankali ta bar wurin.
A hankali Yazeed ya dinga shafa sajensa yana murmushi, shi dai in dai Fadila ta kula shi, yana kasancewa cikin farin ciki mara misaltuwa tsawon wannan wuni.
Khalil ya riƙe wuta, wurin yawan kiran Hafsa a waya, kuma sai ya daidaici tana gida yake kiran, gudun kar Mama ta ɓata rai, sai ta ɗau wayar ta amsa masa ciki ciki. Idan ha ji haka sai ya ce ta bawa Mama ya gaisheta.
Duk wulaƙancin da take masa, baya gajiya da safe da yamma sai ya kirata, bayan saƙonnin Soyayya da yake tura mata, amma ko ɗaya bata kulawa, balle ya sa ran zata amsa saƙonnin nasa. Sai dai kasa jure ganinta yayi, dan haka ya ƙudurce a ransa zai zo ko a ranar ne ya ganta ya juya ya koma, ba tare da yaje gida ba
Tana zaune tana fama da masu sayan awara, ta samu ta sallami da yawa daga cikin masu sayen, katsam ta É—aga kai, taga fitowar wanda ta fi tsana a rayuwarta. Gabanta ya faÉ—i dan ba ta san da wacce ya zo ba, dan a kullum idan zasu haÉ—u ba shi da burin da ya wuce yaci mutuncinta, haka kwanaki ya zo ya sameta har wurin sana'arta a gaban mutane ya ci mutuncinta ba tare da kunya ko shakka ba.
Kallo É—aya ta yi masa ta É—auke kanta, ta cigaba da abin da take yi.
"Au haryanzu kina aikin wahalar nan? Ko da yake ba abin mamaki bane ba, tun da ke da uwarki ba ku gaji arziƙi ba, titi dai a nan zaku ƙare"
Hafsa ta sunkuyar da kanta, tana jin wata irin ƙuna a cikin zuciyarta, wanda suka haddasa mata zubar hawaye.
Mai shayin kusa da Hafsa ne ya taso ya ce "Haba Malam, kai wani irin mutum ne mara tunani, kullum sai ka zo cikin mutane kana cin zarafinta, haba malam kamar ba musulmi ba".
A fusace mutumin ya ce "Ba ruwanka da ni malam, ka fita harkata a wannan sabgar, waye ya sa da kai, wannan Yarinyar har wadda za a tausayawa ce, uwatta ta goya mata baya tan zama a kan titi tana tallan kanta, ta ɓige da suyar awara tana karuwanci, ko da yake ai barewa bata gudu ɗanta yai rarrafe, abin da taga uwarta na yi ne" Yadda miyagun matashin suka daki zuciyarta, ba tare da ta shirya ba, ko wani tunanin ba, ta daki kaskon man da ke kan wuta, ya ƙonawa mutumin ƙafa.
Wani irin uban ihu ya saki, nan da nan ƙafa ta yi ja, ya yin da babu alamar nadama a tare da Hafsa.
Salati da salallami mutane suka fara yi da ganin abinda ya faru. Har Hafsa ta yi wannan aika aika ta gama, kuka take yi, mutane suka dinga bashi rashin gaskiya.
"Ba dai ni ki ka yiwa haka ba, to Wallahi zaki gani, zaki ga abin da zan miki, sai kin gwammace kiÉ—a da karatu da ni ki ke zancen".
Mai shayi ya ce "Ai ni kin mini daidai Hafsa, ɗan iskan banza kawai, bari in aika yaro ya sayo miki man ki, ki ƙarasa ki tashi.
Amina ta girgiza kai ta ce "A'a, gida zan tafi" ta yi maganar tana share hawaye.
Mai shayi ya sai mata mai, ya bata, da ƙyar ta karɓa, ta tattara kayanta ta tafi gida, dan ba zata iya cigaba da zama ba. Da ta je gida ma ba ta bari Mama ta gane ba halin da take ciki ba, Maman ma ba ta bi ta kanta ba, dan ta fuskanci Hafsa yau tambotsan nata take ji.
Washegari da sassafe, Hafsa na shirin zuwa ta kai markaɗen wake, aka ƙwanƙwasa ƙofar gida. Hafsa na shirin zuwa ta buɗe, Mama ta ce "Ƙarasa bari in leƙa in ga waye"
Mama ta sanya mayafi, ta ƙarasa ƙofar gidan, tana buɗewa sai ga 'yan sanda biyu a tsaye da motarsu a farkon layi.
Gabanta ne ya faɗi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Yallaɓai lafiya kuwa?".
"'yar ki muka zo nema"
"Me 'ya ta tayi muku?"
"Yanzu ba lokacin yaÉ—a rahotanni bane, idan muka je can kya ji abin da tayi".
Jin Mama shiru ne ya sanya Hafsa ta tashi ta bi bayanta, sai dai tana zuwa soro ta yi turus, ganin 'yan Sanda.
"Mama lafiya kuwa?".
"Kece Hafsa?"
"Eh nice"
"An bamu iznin mu kama ki, dan haka ki zo mu wuce station".
Ayshercool
08081012143
GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143
Page14
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" shi ne abin da Mama take ta maimaitawa, ya yin da Hafsa tayi tsumu tsumu tana tunanin wani lafin ta yi, da har 'yan sanda za su zo gida kamata?.
Mama ta kalleta cikin tashin hankali da firgici da yaya mamaye fuskarta ta ce "Hafsa me kika aikata haka, da za a zo har gida ana ƙoƙarin kamaki?".
Hafsa ga girgiza kai ta ce "Ni Mama ban yi komai ba, ban taɓa kayan kowa ba ba abin da ya haɗani da wani".
"Ke malama, ba lokacin tattauna wannan maganar ba ne, wuce mu tafi" Suka ingiza ƙeyar Hafsa, tana kuka tana kiran Mama, a gaban maƙota, wani maƙocinsu Hafsa ya yi ƙoƙarin dakatar da su, ya ji ba'asi amma suka ƙi saurarsa, Mama ta ce su bari ta ɗauko mayafi su tafi tare, nan ma suka ƙi suka ce ta biyo su a baya.
A kiÉ—ime Mama ta shiga gida, ta yafo mayafi, ta rufe gidan hankali tashe ta nufi titi. Tuni Maman ta fara jin haki, saitin zuciyarta ya mata nauyi, alamun hawan jininta zai tashi, kai tsaye station É—in unguwarsu ta nufa, amma da taje aka ce mata ai ba wannan police station É—in aka kai Hafsa ba.
Rushewa Mama tayi da kuka, tana tunanin ina aka kai Hafsa, 'ya mace a hannun 'yan sanda, ta kuma bazama ta tari wani abin hawan ta tafi wani division É—in.
Khalil ji yake tamkar ana hura masa wuta a ƙirjinsa, babban burinsa kawai shi ne ya ganshi a garin Kano, a gaban kaskon wutar suyar awarar Hafsa, ya yi tozali da fuskarta da take sa shi nishaɗi da nustuwa.
Da fari ya jira ya yi booking É—in jirgi, ya taho bayan kwana biyu, amma ya ji ya kasa jurewa, kawai ya É—auki motarsa da yake amfani da ita a nan Abuja, ya nufo gida, yana tafe yana murmushi, zuciyarsa cike da muradin tozali da fuskar Hafsat.
 Kusan wuni Mama ta yi tana bulayi, amma ta rasa station ɗin da aka kai Hafsa. Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, kuka kam babu irin wanda ba tayi ba, 'ya mace a hannun 'yan sanda abin da tayar da hankali sosai.
Tana komawa gida maƙota suka fara tambayarta yaya ina Hafsan, cikin kuka ta ce ta rasa station ɗin da aka kai Hafsa, yanzu ma kuma bazama za tayi neman in da aka kaita.
Maƙocinsu mai suna Malam Sani ya ce "A'a Maman Hafsa ba za ai hak ba, bari in ɗauki babur ɗina in je in zazzaga nima, amma ki nemi wuri ki zauna ki huta, tunda dama ba cikakkiyar lafiya ce da ke ba".
Da ƙyar suka rarrashi Mama, ta haƙura ta zauna, Malam Sani shima ya tafi zagawa stations ɗin da suke nan shiyarsu.
Ko mintuna Arba'in ba ayi ba, Mama ta kasa jurewa, ta sake É—aukar mayafi, ta cigaba da yawon neman Hafsa.
 Khalil kuwa, a Hotel ya sauka, yayi wanka ya ci Abinci, dan kwana ɗaya zai yi ya koma, baya son Mummy ta tuhume shi dalilin dawowarsa a yanzu, bayan bai daɗe da tafiya ba.
Wajen ƙarfe biyar na yamma, yayi kwalliya ya ɗau motarsa zuwa wurin sana'ar Hafsa, amma ya tarar bata nan.
Ya É—akko wayarsa ya kirata, wayar ta shiga amma ba a É—auka ba.
Fitowa yayi daga motar, ya ƙarasa wurin mai shayin dake kusa da wurin da Hafsa ke sana'a, suka gaisa sannan Khalil ya ce "Dan Allah Hafsa fa?".
Mai shayi ya ce "Gaskiya yau ba ta fito ba, kuma ban jin zata zo, da zata zo da tuni ta almajiri ya fara kawo mata kaya".
"Dan Allah ina ne gidansu?"
"Taɓ, yo wannan ina zata saki jiki da wani har a san gidansu, ni dai na so naji ance gidansu a nan wajen makarantar brilliant yake, daga nan sai ka tambaya".
Khalil ya ce "Masha Allah, na gode sosai, Allah ya sa dai tana lafiya".
Har Khalil ya juya zai tafi, wani a cikin rumfar mai shayin ya ce "Ai nifa ina ga rashin fitowar tata yana da nasaba da abin da ta yiwa mutumin shekaranjiya, dama ya ce zata gani, maybe ko tsoro ta ji kar ya mata wani abu".