← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 84

Sashe 30

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta sallame su sannan suka tashi, Baba ya ja Amina waje, ya kalleta ya ce "Uwata, yanzu har kin manta da nasihar da na miki a kan zamanki a gidan nan? So kike sai kin yi dalilin rasa damarki ko?".

Amina ta ce "A'a Baba, ban san dokar gidan ba ce ba saukar baƙi, amma insha Allah ba zan sake ba".

Baba ya ce "To ki kiyaye, ki daina shiga abin da babu ruwanki, ko kuma aikata abin da ba a saka ki ba, kin ji ko?".

"To Baba insha Allah ba zan sake ba"

"Yauwa uwata, Allah yayi miki Albarka, maza koma ciki abinki" Amina ta juya ta koma, ranar na mata ƙuna, yadda aka ƙasƙanta mahaifinta a gabanta, a kan laifin da ita ta aikata ba shi ba.
Haka ta koma ɗakinta sukuku, ta zauna baƙin ciki ya isheta, ta tuna yadda Baba ya gurfana a gaban matar da ya girmeta nesa ba kusa ba, ba ta kalli furfurar kansa ba, ta dinga zazzaga masifa, da Amina tana da burin idan ta samu ta cigaba da makaranta, amma taga kamar abin ba mai yiwuwa bane, saboda gaba ɗaya zaman gidan ya fara sire mata.

Sai wajen ƙarfe tara na dare, sannan Hafsa ta dawo daga wurin sana'arta, ta tarar Mama ta dafa mata ruwan wanka, ga kuma girkin dare ta yi, ta zauna ta ci Abinci, tayi sallar isha'i sannan ta shiga ta yi wanka da ruwa mai zafi sosai, kasancewar dul zafi duk sanyi Hafsa ba ta wanka da ruwan sanyi, saboda tana jin daɗin zuba ruwan ɗumi ko mai ɗan zafi a jikinta.
Ko da Hafsa ta fito daga wanka, mai ta nema ta shafa, tana yi suna hira da Mama, wayarta ta fara ringing, ta kai hannu ta duba, taga lambar Khalil, wanda sai a yanzu taga missed calls huÉ—u ya yi mata tana wanka, katse kiran ta yi, tare da kashe wayar gaba É—aya.
Mama tana kallonta ba tace mata komai ba, sai da ta bari Hafsa ta gama shirinta tsaf tana ƙoƙarin jan bargo. "Hafsa" Mama ta kira sunanta.
"Na'am Mama".

"Waye ya ke kiranki a waya?".

"Mama ba kowa"

"Ba na miki magana ne dan muyi jayayya ko ki mini musu ba, amsa kawai nake buƙata daga gareki" Mama tayi maganar babu alamar wasa a tare da ita.

Hafsa ta ce "Mama kawai fa..

"Kar ki mini ƙarya Hafsa, namiji ne yake kiranki waye?".

"Mama, ba komai fa tsakanina da shi, kawai zuwa yake ya sai awara a wurina".

"Ina jinki sai kuma aka yi yaya?".

"Cewa ya yi yana sona" Hafsa ta ƙarasa maganar kamar wadda tai saɓo.

"Shi ne kuma ki ke wulaƙanta shi, har ya kira ki katse wayar? Anya Hafsa rayuwa zata cigaba a haka? Bai kamata kowa ya nuna yana sonki ki koreshi ba, ki bashi dama mana, na ɗaga wayar kina banɗaki, ya gaisheni, naji alamun nutsuwa a tare da yaron. Amina ina buƙatar in ga aurenki kan bar duniya, kina gani yau ina da lafiya gobe babu, ina son in ganki a hannu na gari kan in mutu Hafsa".

Cikin matsananciyar damuwa Hafsa ta ce "Mama dan Allah ki daina irin wannan maganar, kin san fa komai Mama, mai zai sa in yi wani ganganci,gara kawai mu cigaba da rayuwarmu ni da ke a haka".

"Hafsa, duk abin da ya wuce, to ka bar shi a baya kawai, karki waiwaya kan abin da ta wuce idan har ba na Alkhairi bane, ki sa ka magogi ki goge abin da ya shuÉ—e ki fuskanci rayuwarki, zama haka ba zai yiwu ba, ke macece zamanki a bakin hanya kina wannan sana'ar dan babu yadda zan yi ne, zamanki a É—akin ki shi ne rufin asirinmu gaba É—aya".

Hafsa ta kwaɓe fuska za ta yi kuka ta ce "Ni dai dan Mama...
Mama ba ta bari ta ƙarasa ba, ta ɗaga mata hannu ta ce "Ya isa, tun da ke dai ba a baki shawara, ki je kiyi abin da kike ganin daidai da ke ne"

"Mama dan Allah kiyi haƙuri, ba nayi ne dan in ɓata miki rai ba".

"Rabu dani ni" Mama ta faɗa a ƙufule. Haka Hafsa ta kwanta cike da damuwa, ta shiga tuno irin hali da yanayin ƙaddarori, da suka haɗu da su na rayuwa ita da Mama.

Saura kwanaki uku a fara exams, akwai teses ɗin da Yazeed ya yi missing, lokacin da bai zo ba ba shi da lafiya, wasu malaman sun karɓi uzurinsa sun yi masa, wasu kuwa sai wahalar da shi suke yi.
Ɗaya daga cikin malaman da ke wahalar da Yazeed, saboda ya rasa Attendance ɗinsa, kuma ya ce wanda bai yi Attendance ɗinsa na ƙarshe ba, ya sa a ransa ya faɗi jarrabawarsa. Sannan ya fito da wani littafi ya ce lallai kowa sai ya saya, littafin naira dubu biyu ne, kusan sati biyu kenan ana sayar da littafin.
Kwatsam, saura kwanaki uku jarrabawa, É—alibai na ta fama da karatu, ya shigo ajin, ya ce zai yi musu lecturer, kuma da wannan littafin zai yi amfani, duk wanda ba shi da littafin ya tashi ya fita, ko kayi Attendance idan baka da littafin nan, to baka da exams É—in sa, ko da kuwa ka cinye duka. Idan kuwa baka da Attendance, amma ko baka da Attendance, muddin kana da wannan littafin to ka haye exams É—in sa.
Idonta ne ya sauka a kan Yazeed, da ya yi shiru, ko motsawa bai yi ba, balle a sa ran ya fito da nasa littafin, A kunyace tsirarun waÉ—anda ba su da littafin, suke tashi suna fita daga ajin, malamin yana ta musu bala'i cikin tozarci.
Fadila ce ta miƙe tsaye, ta nufi hanyar fita, ta ajiyewa Yazeed littafinta ita kuma ta wuce zata fice.

"Hey Madam zo nan" sautin muryar malamain ta daki dodon kunnuwanta, cak ta tsaya sannan ta waiwayo fuskarta babu alamar wasa, cike da izzarta ta kalli malamin, tana sauraren mai ze ce.
"Ina littafinki?" Ya tambayeta yana tsareta da ido.
"Bani da shi sir, ban samu na saya ba" ta faÉ—a ba tare da wata shakka ko damuwa ba.
"Shi kuma wancan littafin da ki ka ajiye masa fa" ta yi mamakin yadda aka yi ya ga ta ajiyewa Yazeed littafi.
"Ba nawa ba ne, na sa ne ya ara mini".

"Ƙarya ki ke yi, Malam fito nan"
Yazeed ya fito jiki a sanyaye, yana jinjina irin ƙasƙancin da za a masa a gaban mutane. Ga ajin yayi shiru an maida ido kan su.
Lecturer ya kalli Yazeed ya ce "Littafinka ne ko nata?" Yazeed zai yi magana, Fadila ta ce "Sir ba fa ƙarya nake maka ba, littafinsa ne ba nawa ba"
Yazeed baya son ya faÉ—i wani abin da zai janyowa Fadila matsala, ko cin mutunci, hakan ya sanya ya kasa magana.
Lecturer ya karɓi littafin daga hannun Yazeed, sai dai yana buɗewa ya ga sunan Yazeed da Admission number ɗinsa.
Shi kansa Yazeed bai san ya aka yi ta rubuta ba, Ya miƙawa Yazeed littafin sannan ya kalli Fadila ya ce "Kina nufin baki sai littafin ba?"

"Eh na saya, amma nayi karatu na manta shi a aji, na dawo ban ganshi ba".

Malamin ya ce "Ok, ku koma ku zauna, amma ki sake sayan wani".
Yatsina baki ta yi, suka koma wurin zamansu.

Har malamin ya yi ya kammala karatun, Yazeed yana kallon Fadila lokaci lokaci, yana jinjina abin da ta yi masa, ba dan tayi hakan ba da ya fuskanci tozarci da ƙasƙanci a gaban 'yan aji.

Bayan fitar malamin, Yazeed yana son yiwa Fadila magana, amma 'yan aji sun saka ido, suna son ganin Action É—in da su Fadila za suyi, amma Fadila ta haÉ—e fuska tamau, wani na kawo raini zata balbale shi da masifa da tsiwa.
Yazeed ma basarwa yayi, amma ƙasan zuciyarsa so yake ya yi mata magana.
Class rep ne ya shigo da takaddu a hannunsa, na wata test da suka yi.
Ya fara rarrabawa kowa test ɗin, sai dai abin da ya ƙara bawa Yazeed mamaki, bai wuce yadda aka miƙo masa takadda ba, ya karɓa yana dubawa, wannan dai ba rubutunsa ba ne, dan lokacin da aka yi test ɗin ma ba ya nan, gashi nan ya ci 7/10.
Shiru yayi yana sake nazartar rubutun, tabbas na Fadila ne, dan bai manta wanda ta rubuta masa a littafin sa ba.

Yana waigowa ya hangeta ta tashi zata bar ajin, cikin sauri ya tashi ya bi ta ƙofar baya, ya bi bayan Fadila, tana ta sauri ta nufi in da motar ta ke ajiye.

Sauri yake sosai, yana kiran sunanta, tazararsa da ita ba yawa sosai, tana jinsa ta share shi, ta cigaba da sauri.
Sai da taje in da motar take sannan ya cinmata.
Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Ina ta magana kin mini shiru".

"Malam lafiya ta yi maganar kamar bata taɓa ganinsa ba"

"Dama...
"Kaga sauri nake tafiya zan yi"
"Ga littafinki" ya yi maganar yana miƙa mata littafin.
Sai a lokacin ta waiwayo ta kalleshi da fararen idanunta da ke matuƙar narka zuciyar Yazeed.
"Ka riƙe kawai" ta faɗa tana ƙoƙarin ɗauke kanta daga fuskar Yazeed.
"A'a ba za ayi haka ba, Halaccin da ki ka yi mini yanzu ma, Na gode sosai ubangiji Allah ya saka da alkhairi, kuma ga test ma kin yi mini, duk da hatsarin da ke cikin hakan, Na gode sosai ƙanwata".
Ɗagowa tai ta kalli Yazeed "Wacece ƙanwar taka?".
"Fadila mana" ya bata amsa, ta yamutsa fuska ta ce "Ka kiyayeni, ni na maka kama da ƙanwarka, ƙila ma na girmeka tsaurin ido kawai, na ce ka bar littafin, ka bani hanya zan kunna mota in tafi".
Wani irin murmushi Yazeed yake, wanda sai da haƙoransa suka bayyana, wanda ya ƙara masa kyau, daga murmushi ya fara dariya, har da rufa baki, dan ba ƙaramin dariya Fadila ta bashi ba.

"Saboda kina ganin tsayin mu É—aya, shi ne ki ke cewa kin girmeni, ai ko da ki ke doguwa tubarkallah na fiki tsayi, balle ki kalli wannan tsofaffin idanuwan nawa, ki ce mini wai kin girme ni"

"To sannu tsoho" ta faÉ—a tana kallonsa.

"Yau ba zaki tsaya karatun ba?".

"Eh"

"To shikenan, Allah ya sauke ki lafiya?"
Chapter 30 · 0% Book details