← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 84

Sashe 61

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta miƙe da ledar a hannunta ta koma ciki, Hajara na ganin Amina da leda, ta fara washe baki, "Amina sayayya aka yo mana haka?" Ko kallonta Amina ba tayi ba, ta wuce ɗakinta.
Zuwa tayi ta zauna ta bubbuɗe ledar, jaka ce mai tsadar gaske, da takalmi da safa, kai da ganinka san kaya ne masu matuƙar tsada.

Fadila sai dubawa take taga Yazid a ajin, amma babu Yazid babu dalilinsa, har aka yi lectures ta farko aka gama, ba taga Yazid ya zo ba.
Suka yi ta 10_12 ma, still Yazid bai zo ba, gashi tana lectures É—in 2-4 za suyi presentation É—in nan, amma Yazid bai zo ba, gashi presentation É—in nan shi ne zai É—au maki mafi yawa.
Taje ta yo salla ta je Cafeteria ta ci Abinci, ta nufo aji.
  A wuri ɗaya ta hango shi a zaune, ya sunkuyar da kansa, da alama wani abu ne mai muhimmanci ya ɗauke masa hankali, ba ta san ya aka yi murmushi ya suɓuce mata ba, ta nufi in da yake zaune "Kai dama zaka zo school ɗin nan, amma kayi missing ɗin har lectures biyu?"
Tayi maganar ba tare da ta zauna ba, Yazid ya É—ago a hankali ya kalli Fadila, ya mayar da kansa ya cigaba da kallon wayarsa dake hannunsa.

"Am talking to you" tayi maganar tana kallonsa.

Ya ce "Ina jinki ai"

"Kana jina Kai mini banza?" Cigaba da kallon wayarsa ya yi.

Haushi ya kama Fadila, ta sa hannu ta zare wayar daga hannunsa, ko É—aga kai bai ba balle ya kalleta.
Duk da ƙaramar waya ce amma Alqura'ani ne a kai yake karantawa.

Zama tayi a kusa da shi "Wai yau ma azumin maganar ka ke yi?".

KashingiÉ—a yayi da jikin bencin, ya ware mata idanunsa a kanta, still bai ce komai ba.
Da sauri ta janye nata idanun, jin tsigar jikinta na tashi, ga wani gumi da bata san na menene ba yana tsatsafo mata a goshi, ta kasa tashi ta kasa komai, shi kuma ya cigaba da kallonta, kamar ya samu majigi.

Samun kanta tayi da miƙewa tsaye, tana ƙoƙarin barin wurin, amma cikin shammata ya janyo hannunta wanda hakan ya tilasta mata zama jikinsu na daf da haɗewa har tana iya jin saukar numfashinsa a fuskarta, Allah yasa ajin babu mutane, kowa sabgar gabansa yake yi.

Sosai jikinta yake rawa, kamar wadda ake yiwa gangi, ga idanun Yazid da suka dasa mata wani shocking da yake tsirga mata tun daga kanta har yatsun ƙafarta, yawun bakinta har wani bushewa ya yi.

Bakinta ya dinga bi da kallo, ɗan madaidaici a kyakykyawar fuskarta, da ya ƙware a wurin iya tsiwa da masifa.

"Bani wayata" ya furta yana sake ƙoƙarin sanya idonsa a nata, amma ta hana hakan, ta hanyar sunkuyar da kanta.

"Bani mana" ya sake maimaitawa, amma ta kasa motsi, sai jujjuya idanunta da take yi.

Hnnunsa ya sa ya zare wayarsa daga hannunta.

Mafarkan da take da shine suka dinga dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, maganar Yusra ce ta dawo mata 'Wataran sai kin rungumeshi a zahiri'

Firgigit ta dawo hayyacinta, daga duniyar da ta lula, har ta kasa gane mafarkan da ta saba yi ne, ko kuma zahiri ne, dan wani irin yanayi ta shiga wanda da ta kasa fassarawa kanta wane irin yanayi ne haka.

Miƙewa tsaye tayi, ta bar wurin da sauri, tana ta sauke numfashi a jejjere.

Yazid kuwa binta yayi da kallo, yana kallon yadda ta birkice a lokaci É—aya, duk taurin kan Fadila, ba wuya ya sa ta shiga taitayinta.

Fadila ta cigaba da rarraba idanu, tana jin yadda halin da ta shiga ya kasa barinta haryanzu.

A hankali ɗalibai suka cigaba da dawowa ajin, saboda shiga lectures ɗin su ta ƙarshe, wadda daga ita kowa zai tafi gida, kuma wadda a ita ne, zasu gabatar da presentation ɗinsu.

Lokaci na cika malamin ya shigo ajin, kasancewar mutum nai kiyaye lokaci, kowa ya nutsu ya shiga taitayinsa, kasancewar malamin ba shi da wasa Sam.

Kowane 'yan group sun nutsu, sun haÉ—u wuri guda, suna tattauna yadda za su gudanar da presentation É—in su, banda 'yan group É—in su Fadila, ita tana nata wuri, Yazida ma haka, sauran 'yan group É—in ma haka.

Aka dinga kiran groups É—aya bayan É—aya, suna gabatar da presentation É—insu, duk karsashin group idan lecturer da 'yan bani na iyan aji suka fara suburbuÉ—o tambaya, duk karsashin 'yan group É—in, sai sun karaya.

Da haka aka zo kan group É—in su Fadila, aka kira su, suka fito É—aya bayan É—aya, suka jeru a gaban aji, sai dai Yazid bai fito ba, sai da suka gama fita gaba É—aya sannan Yazid ya fito, yana zuwa ya tsaya a kusa da Fadila, suna fuskantar 'yan aji.
Ji tayi tana neman diriricewa, a hankali ya furta mata "Ki nutsu mana, you are facing the class"

Suka fara gabatar da presentation, aka zo kan Wanda Fadila za tayi, gaba É—aya ba ta da confidence, saboda a halin da Yazid ya sakata, sai dai yadda take zuba turancin ne zaka san ya zauna sosai a bakinta.
Suka gama gudanar da presentation, aka zo fannin amsa tambayoyi, lecturer ya fara yi musu tambaya, Yazid ke da karsashin amsa tambayoyin, tun da shi ya yi Assignment É—in, sai dai ba ya iya public speaking da harshen turancin yadda yakamata, a rubuce ne dai ba laifi, amma banda a baki.
Yana ƙoƙarin bada amsar, sai larabci ya suɓuce masa, ya dinga haɗawa da hausa yana bayani.

"Kai Malam, bafa ajin larabci bane, ba nahawu muke yi ba, da turanci zaka mana bayani" cewar wani É—alibi.

Yazid ƙoƙari yake ya kuma gudanar da bayanin, amma turancin yaƙi fita yadda yakamata.

Ana haka, Amra ta kuma yankowa Yazid wata tambayar.

Ƙoƙarin amsawa yake, gashi ya san amsar, amma bisa kuskure sai ya dinga haɗawa da larabci, babban abin da ya ƙonawa Fadila rai, bai wuce yadda wasu daga 'yan ajin ke masa dariya ba, ba ita ake yiwa dariyar ba amma abin ya ƙular da ita sosai.

Shi dariyar da suke masa, bata dameshi ba, ganin turancin ya ƙi yiwuwa kawai ya juya harshe zuwa larabci, ya dinga zuba bayani, wanda ya tilastawa 'yan ajin yin shiru suna kallonsa, ba zaka taɓa cewa ya jii hausa ba.

Fadila ce ta fara yi masa tafi, 'yan group ɗin ma suka ɗau tafi, lecturer kam zuba musu ido yayi yana kallon ikon Allah, ya miƙe tsaye ya ce "Kai Sheikh haka za muyi da kai, wa zai fassara mana me kace mu da bama jin larabci?"

Yazid ya ce "Sir, ban iya turanci ba, kuma na ji sun ce ba sa so da Hausa".

Lecturer ya dafa kafaɗar Yazid ya ce "Ka burgeni sosai, Allah ya ƙara hazaƙa, ina ɗan jin larabci kaɗan, na kuma fahimta, and you zaki zo mini da abin da kika fahimta a bayanin da yayi a next lectures" lecturer yayi maganar yana kallon Amra.

Lecturer yayi nasiha sosai, da nuna musu kuskuren abin da suka yi, na son ƙure Yazid dan bai iya turanci ba.

Fitar lecturer babu daÉ—ewa, class rep ya fita gaban allo, ya dinga faÉ—a a kan abin da Amra da wasu 'yan ajin suka yiwa Yazid, duk da irin taimakon da yake musu, a kan koya musu wasu abubuwan da ya shige musu duhu.

Amrah ta ce "Nifa bana son raini, ai naga Fadila ce ta fara yi masa dariya a ajin nan a kan bai iya turanci ba, amma ba wanda ya ce mata komai dan ana tsoron ta sai ni"

"Kar ki ƙara saka sunana a shirmenki, ni ba sa'ar yinki bace wallahi" Fadila ta faɗa daga wurin da take tsaye, tana ƙoƙarin haɗa jakarta ta fice.

Hayaniya ce ta nemi ɓallewa a ajin, Yazid kuwa tuni ya sulale yayi tafiyarsa.

Saura ƙiris Fadila ta tsinke Amra da mari, da ƙyar aka lallaɓata aka sallameta ta tafi, dan Fadila ba ta fiye shiga harkar mutane ba, amma idan ama taɓata ta ƙware a masifa, bata ragawa kowa.

Kusan ƙarefe goma saura na dare, Mummy ta shiga in da su Amina suke, ta ƙwanƙwasawa Hajara ƙofa, Hajara ta buɗe ta fito tana mutstsuka ido, alamun ta fara bacci.
Hajiya Zainab ta kalli Hajara a yatsune ta ce "Ki dafawa baban su Fadila tea, ki ajiye masa a dining, zai fito ya sha" Hajara ta risuna ta amsa da to.

Haka ta shiga kitchen, kamar tayi kuka, dan taji daÉ—in baccin da ta fara yi.

Ta kammala dafa shayin, ta fita falo, ta tarar da Alhaji Ahmad a zaune a falon.

Ta risuna ta ajiye masa shayin, ya miƙe tsaye, ba tare da ya kalli Hajara ba ya ce "Ajiye a nan, ki turo Amina ta kai mini falona" daga haka ya wuce ya barta saroro tana binsa da kallo.

Hurry up and subsribe the VIP GROUP
at affordable price.
08081012143
07063065680
GABA DA GABANTA

BY
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

35

"Too wai meke faruwa a gidan nan ne?" Hajara ta faÉ—a a fili, sai da ta gama surutanta da mamaki, sannan ta tashi ta tafi kiran Amina"

Amina na zaune a tsakiyar katifarta, ta baje litattafanta, tana ta aikin nata na karatu.

Hajara ta É—aga labulen É—akin Amina, ta kalleta, ita lamarin Amina ya fara bata tsoro, kullum tana nace da littafi kamar masifa, har aiki idan tana yi, tana kallon littafi, saboda tsananin saka boko a ranta.

Amina da bata son Hajara ta shigo É—akin ba sai yanzu da ta É—ago kai, ta ganta a tsaye tana kallonta.

"Lafiya kuwa?"

Hajara ta ɗan geɓare baki ta ce "Maigidan nan ya ce ki kai masa shayi falonsa, yana son ganinki"

"Ni kuma? Ba ke na jiyo Hajiya tana cewa ki dafa masa shayin ki kai masa ba?"

"Na dafa masa, amma ya ce ki kai masa" Hajara ta faÉ—a a hasale.

HaÉ—e rai Amina tayi tana É—an tura baki, ganin Hajara ta zuba mata ido, tana nazartar action É—inta ya sanya Amina ta ce "Ina shayin ya ke?"

"Mhmm yana falo"

"To zan kai masa, ina ga zai mini maganar tafiyar mu Abuja ne, wurin competition, ina ga makarantarmu sun masa magana" tayi maganar cike da son kawar da mugun tunani da mummunan zargi a zuciyar Hajara.
Chapter 61 · 0% Book details