Sashe 69
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kanta Fadila rashin walwalar Khalil ya fara damunta, kwata kwata ya daina shigowa cikin gidan, ko ba komai ko su haÉ—u suyi faÉ—a yana É—ebe mata kewa.
Ta kalli Mummy da ke zaune tana cin cake, su Hajara kuma na gyara falon,.
"Mummy, wai dan Allah haka za'a zubawa Yaya Khalil ido? Kinga fa ya daina shigowa cikin gidan nan sam, ko ma bashi da lafiya ne?"
Mummy ta ce "Lafiyarsa ƙalau, duk a kan na raba shi da waccan yarinyar ne, yake fushi da wannan iskancin, na ɗau matakin ƙarshe da nake ganin ya dace, in shi ba zai rabu da ita ba, su dolensu su rabu da shi, idan har suna da zuciya"
"Amma Mummy wane matakin kika É—auka"
Mummy ta yi murmushi ta ce "Ke ina ruwanki, ba dai nace miki na É—au mataki ba"
Fadila na shirin yi magana sai ga Khalil ya shigo falon, gaba É—aya ya rame duk yayi wani iri.
Fadila ta ce "Yauwa brother, na je É—akinka babu adadi ina nemanka, yau birthday na duk an yi hotuna babu kai".
Be kula Fadila ba ya ƙarasa in da Mummy ta ke, ya kalleta ya ce "Mummy, ban taɓa zaton zaki mini abin da kika yi ba, dan kawai na ce ina son 'yar talaka ba, yanzu Mummy meye laifin yarinyar da za'a wulaƙanta ta haka? Me tayi ita?"
"Au Yanz zuwa kayi ka titsiyeni ko ka tuhumeni a kan wannan shegiyar yarinyar? To ka kyauta daidia nake da kai, zan ga ni da kai waye ya haifi wani"
Kamar Khalil zai fashe da kuka ya ce "Mummy ba haka bane, Mummy da girmanki da mutuncinki yarinya ce fa ƙarama Hafsa, 'yar cikinki kuma sirikarki"
Miƙewa Mummy ta yi ta ce "Zan tsinke ka da mari, ni zaka zo ka tsayaa kaina kana gaya mini maganar banza, ka kiyayeni Khalil, wallahi ka cigaba da bibiyar yarinyar nan, zan maka abin da tunaninka bai taɓa kawo wa zan maka ba, kuma idan ta cigaba da bibiyarka, wallahi saina ƙasƙanta ta na tozartata fiye da abin da nayi mata yanzu, idan yaso ka nemi wata uwar ka canza ni"
Khalil ya girgiza kai ya ce "A'a Mummy, ke uwata ce, ba yadda za ayi in iya canzaki, ko in fifita wata a kanki, Mummy ina nuna miki illar abin da kika aikata ne, ita ma 'ya ce, uwa ce ta haifeta ya tata uwar zata ji da wannan abin da kika yi mata? Haba Mummy"
"Lallai Khalil, wuyanka ya riƙa ya isa yanka, ka nuna mini ka kawo ƙarfi, gara da na farga na miƙe tsaye, kan kwaso mini wadda zata dinga juyaka, idan kaga na bari kayi aure, to matar da na zaɓa maka ce, tun da naga baka da hankali"
Idonsa fal hawaye ya ce " Shikenan Mummy, kin yi nasara kin rabani da Hafsa, shikenan Mummy"
"Kar ma ta rabu da kai, da ta cigaba da bibiyarka dai, da taga ƙaryar talauci, sakarai kawai"
Ta wuce fuuuuuu ya bar falon.
Khalil ya zauna ya dafe kansa, yana girgiza kan yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa.
Fadila ta zauna a kusa da Khalil ta ce "Brother, wai me Mummyn tayi maka ne?"
Ya ɗago idanuna da suka yi jawurr, jijiyoyin kansa duk suka mimmiƙe suka kumbura, ya kalli Fadila ya ce "Yanzu fisabilillahi Fadila ya dace ace Mummy taje da ƙawayenta, sun ci mutuncin yarinyar mutane a gaban al'umma, suka watsar mata da kaya a cikin ƙasa, ita meye laifinta?"
Fadila ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Haka ne, gaskiya Mummy bata kyauta ba, amma kaima Yaya Khalil meye kaika, duk matan duniya ka nacewa wata mai awara, ai koma menene kaine ka janyo mata, tunda Mummy ta nuna bata so ai saika haƙura"
Kalaman Fadila ƙara masa ɓacin rai suke, dan haka ya tashi, ya bar falon zuciyarsa babu daɗi.
Sosai Amina taji tausayin Khalil ya kamata, mussaman ita wadda ake ce anje an ci mutuncin ta a gaban mutane. tana mamakin baƙar zuciya irin ta Hajiya Zainab, babu tausayi ko Allah a ranta, gani take kamar ita ta yiwa kanta arziki ba Allah ne ya bata ba.
Fadila ɗan taɓe baki tayi, ta tashi ta bar falon, duk da Khalil ɗin ya bata tausayi, amma a ganinta matakin da Mummy ta ɗauka yayi daidai, dan Khalil yana da taurin kai wasu lokutan.
Amina wasu lokutan mantawa ma take da wayar da Daddy ya bata, saboda bata son ta É—auke mata hankali da ga kan karatunta sam.
Da Asubar fari Khalil ya shirya kayansa, ya É—auki motarsa ba tare da ya yiwa kowa sallama ba, ya fice daga gidan.
Abdul yana zaune yana azkar, bayan idara da sallar asba, yana jiran gari yayi haske yayi wanka, ya ga wayar Khalil.
Yasa hannu ya É—aga wayar yana faÉ—in "Lafiya kake mini wannan kiran haka da sassafe?"
"Ina ƙofar gidan ku, airport nake son ka kaini, jirgin Bakwai da rabi zanbi in koma Abuja"
Mamakine ya kama Abdul, dan ba suyi wannan zancen da Khalil ba jiya, ya miƙe, ya saka hula ya ɗau wayarsa ya fita, aikuwa yaga motar Khalil.
Ya rufe shagon nasa, sannan ya nufi wurin da motar Khalil É—in take.
Ya buÉ—e motar ya shiga, ya kalli Yadda fuskar Khalil duk ta kumbura, ga idanunsa mu duk sun kumbura sun yi ja, kamar wanda bai yi bacci ba.
"Wai Khalil meke damunka ne? Meyasa zaka koma yau bayan kace mini sai next week zaka koma?"
"Abdul, Hafsa ta rabu dani, ba zata aureni ba" ya faÉ—a tamkar zai fashe da kuka.
Abdul ya ce "Subhanallah, saboda me?"
Cikin damuwa Khalil ya ce "Abdul, could you imagine Mummy da kanta iya da ƙawayenta wai suka je suka yiwa Hafsa warning a kaina, suka watsar da kayan sana'arta a gaban mutane? Abdul waye ni ɗin ne? Me aka yi aka yi ni? Yanzu ya dace abin da Mummy tayi, girmanta ne yin hakan?"
Abdul ya ce "A'a Khalil, yi haƙuri, Mummy uwa ce kar ɓacin rai ya sanya ka faɗi wata maganar a kanta"
"Haba Abdul, ka duba lamarin nan dan Allah, yanzu dama da yaya na samu kan yarinyar nan, maimakon idan ma rabuwar ce, a bari mu rabu ta daɗin rai, in mata bayani mu rabu cikin mutunci, amma anje an ci mutuncinta, meye laifinta? Har Abada ba zata taɓa ganin mutuncin Mummy ba, na rasa dalilin da yasa Mummy ke biyewa wannan ƙawayen nata suna zigata tana abubuwan da basu dace ba, idan nayi yinƙurin gayamata Gaskiya, ta ƙare mini zagi ta nuna mini haryanzu bani da hankali, amma ka duba wannan lamari meye na Hafsa a ciki?"
"Haka ne Khalil, bai kamata Mummy ta aikata hakan ba, amma hakan ba shi yake nufin ka faɗi abin da kake so a kanta ba, kayi haƙuri ka cigaba da yi mata addu'ar Allah ya ganar ita. Ita kuma Hafsa idan rabonka ce, Allah ya daidaita lamarin, ya tabbatar muku da alkhairi, idan kuma ba alkhairi bace, Allah ya haɗa kowa da rabonsa.
Khalil ya sauke wata ajiyar zuciya ya ce "Baka san wani abu ba, cewa fa tayi wai bani ba zaɓar macen da nake so na aura, ita zata zaɓa mini, kuma wallahi na san duk wannan matan ne suka kitsa mata ta hau ta zauna, Mummy tana valueing maganar ƙawayenta fiye da kima"
Abdul ya ce "Kayi haƙuri abokina, ka cigaba da yi mata Addu'a"
Khalil ya ce "Shikenan, muje airport, kai sai ka dawo da motar, idan ka samu lokaci ka mayar musu da motar can gida"
"To shikenan, Allah ya tsare" Khalil ya ja motar suka tafi.
Kamar kullum, yau ma Amina ta kammala shirinta na makaranta, cikin gogaggun uniform ɗinta, ta saɓa jakarta a bayanta, ta fita wurin Baba, ta tsaya suka gaisa da Baba, Baba ya ce "Uwata, kuɗin makarantar da nake baki ba sa isarki ne?"
Cikin rashin fahimta Amina ta ce "A'a Baba me ka gani?"
"Alhaji Ahmad ne ya bani kuÉ—i, kusan dubu goma, wai idan zaki tafi makaranta, in dinga baki isasshen kuÉ—i, saboda ba kya tafiya da Abinci, yunwa na damunki a makaranta"
Amina ta mariraice Fuska ta ce "Wallahi Baba ban ce masa wani abu aba, ranar da na wuni a makaranta ne a wurin lesson, yazo ya É—aukeni na ce ba zan sake zuwa lesson ba, mun wuni a makaranta ina jin yunwa, amma wallahi Baba ni bance masa komai ba"
Baba yayi ajiyar zuciya ya ce "To Uwata, ba zan fasa yi miki nasiha ba, ki iya kankina duk in da kika tsinci rayuwa, kar ki sakankance da mutumin nan ki jamana wata matsala a gidan nan"
Amina ta ce "To Baba in sha Allah"
"To ni yanzu wannan kuɗin zan baki dubu uku, idan sun ƙare sai ki kuma yi mini magana in baki wasu, amma bance kiyi ta kashe-kashen banza ba"
"A'a Baba, dubu biyu ta isheni duka watan nan, ka sayawa Inno kayan shayi a aika mata, ita ma ta dinga cin mai daÉ—i kamar yadda muke ci a nan"
Baba yayi murmushi ya ce "Uwata kenan, ke dai ki karɓa, ni na san abin da zan yi"
Amina ta miƙe daga tsugunon da tayi, ta ce "Baba, bari in tafi, bani yadda ka saba bani, idan na dawo sai muyi maganar kar na makara"
Baba ya saka hannu a aljihunsa, ya cirowa Amina naira ɗari uku ya bata, ta saka hannu biyu ta karɓa, tayi masa sallama ta fita.
Tana ta sauri ta ƙarasa titi, ana ta wucewa da yaran masu kuɗi a cikin motoci zuwa makaranta, ba tsammani taji an kira sunanta.
Ɗan tsawa tayi ta waiwaya, Bilal ta gani cikin suit baƙaƙe.
Ya ƙaraso in da take yana faɗin "Amina, makaranta zaki tafi ne?"
Amina ta ce "Eh, ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ɗan jirani in shiga gida in ɗauko mota, in kai ki mana"
Amina ta ce "A'a sauri nake, ka bari na gode"
"Haba Amina, dan Allah ki tsaya in kai ki"
"A'a ka bari wallahi na gode"
Bilal ya ce "Gaskiya ban ji daÉ—i ba, to muje in rakaki titi"
"A'a karka damu dan Allah, zan ƙarasa"