← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 84

Sashe 68

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fadila ce tsaye a gaban mudubi, sanye cikin doguwar rigar abaya, ta É—an gyar fuskarta, ta É—auki turaren wurin Yazid ta shafa, ta É—aura abin hannun, sannan ta É—auki wasu turarukan ta shafa, ta É—auki jakarta ta jefa mukullin motarta a jaka, ta tafi É—akin Mummy.

Bata tarar da ita a falon ba, dan haka ta wuce É—akin Daddy.

A can ta tarar da su a falon Daddy, a tare ta gaishe su suka amsa.

Daddy ya ce "Har kin shirya?"

"Eh Daddy, and karku manta, tonight in Allah ya kaimu, za muyi party"

Daddy ya ce "To Allah ya kaimu"

Ta ce "Amin" ta É—au jakarta ta fito falo, a falo ta haÉ—u da Amina, ta kalli Amina ta ce "Yauwa, idan kin dawo daga school, zan É—an yi mini party na birthday na, dan haka a gyara ko ina, zamu zo ni da Yusra, za ayi decorations a falon nan"

Amina ta ce "To, Allah ya kaimu"

Fadila ta fice, ba tare da ta amsawa Amina ba.

A ƙofar ajinsu taga Yazid, kamar me jiran wani abu.
Tun daga nesa yake mata murmushi, har ta ƙaraso.

Tana ƙarasowa ta tsaya tana kallonsa ta ce "Wa kake jira ne? Naga kana ta fara'a kamar an maka kyautar wani abu"

"Ke kawai nake jira, in ga kwalliyar ranar birthday, kin yi kyau sosai".

Ta ce "Ikon Allah, ba zaka daina sa ido ba ko?"

"Ai ke kaÉ—ai nake sawa ido, bayan ke bana sawa kowa" ba ta kuma cewa komai ba ta shiga aji.

Yazid kuwa murmushi ya yi, ganin abin hannunta da ya bata, da kuma tashin ƙamshin turaren lailatul sahara a jikinta.

Lectures É—aya tayi attending, ta tafi gidansu Yusra, ita Yusra basu da lectures.
Ta tarar Yusra ta gama haÉ—a mata cake É—in ta da duk wani snacks da za tayi amfani da shi, suka rankaya tare zuwa gidansu Fadila.

Kusan wuni suka yi, suna decorating É—in falon, Amina na taimaka musu da wasu abubuwan, yayin da ta zuba ido tana ganin yadda suke gudanar da komai.

Khalil ya kasa jurewa, ya shiga damuwa da tashin hankalin rashin sanin dalilin da ya sanya Hafsa bata É—aukar wayarsa, dan haka da yamma ya shirya ya tafi wurin sana'arta, dan ya san a daidai wannan lokacin ba zai sameta a gida ba, ta fito sayar da awara.
Sai dai tun daga nesa ya ga wurin nata ba kowa. Ya ƙarasa ya yi parking ɗin motar, ya sauko ya nufi wurin, ya shiga wurin mai shayi, suka gaisa da Khalil.
Khalil ya ce "Hafsa ba ta shigo bane?"

"Eh, ba ta zo ba yau, ai wasu mata ne suka zo wurin nan jiya, suka watsar mata da komai na kayan sana'arta, suka yi mata zagin tsamar nama suka tafi"
A firgice Khalil ya ce "Tsaya, ban gane ba me tayi musu?"

"Oho ina na sani, biyu ɗima-ɗima, ɗaya sirirya a wata ƙatuwar mota, haka suka zo suka yi rashin albarka suka tafi, dama da ganinsu kaga 'yan duniya, na rasa a in da Hafsa ke zuwa tana kwaso rigima, rannan sun yi da wannan ɗan iskan, jiya kuma da waɗa nan mata" Khalil dana fahimtar me mai shayi yake faɗa masa yai, ya juya da hanzari a koma wurin da motarsa take, ya shiga ya rufe, ya bar wurin.

A bakin layin su Hafsa ya yi parking, ya sauka ya taka da ƙafafuwansa, zuwa ƙofar gidansu, ya samu wani yaro a ƙofar gidan, ya aika shi ya kira masa ita.

A ƙalla ya shafe mintuna Ashirin a tsaye a ƙofar gidan bata fito ba, ba wai taƙi fitowa bane, dan ta muzguna masa, sai dai tunanin halin da su biyun ka iya shiga, ta daɗe tana kuka, da ƙyar Mama ta rarrasheta ta fito.
Ko da ta fito, bata ƙarasa in da Khalil ya ke ba, a bakin soron gidansu ta tsaya.
Kallo É—aya ya yi mata yaga yadda ta rame, idanunta sun yi jawur alamun tayi kuka har ta gaji.
Da sauri ya nufi bakin soron, ya tsaya cikin damuwa ya kalleta ya ce "Hafsa baki da lafiya ne? Ina ta kiran waya ba kya amsawa, kalli yadda duk kika fita hayyacinki, meke faruwa ne?"
Duk yadda ta so dakewa, sai da hawaye suka zubo mata, ta miƙa masa wata babbar jaka, ta ajiye a gabansa, sannan ta kalleshi ta ce "Khalil, jiya na maka text, ka turo mini kuɗi, ka bani ninkin abin da na nema, na nemi kuɗin nan ne dan mayar da asarar da aka yi mini, na kayan sana'ata, Khalil daga rana mai kamar irin ta yau, ka sa a zuciyarka baka taɓa saɓnin wata mai kama da ni bama, balle tuna mun yi soyayya.
Jiya mahaifiyarka ta zo ita da wasu, sun yi mini kashedin babu ni babu kai.
Tabbas sun yi gaskiya, zaren ba kalar yadin bane, ni da kai bamu dace ba, kyautatawarka a garrni ta ruÉ—eni na fara sonka, ba tare da na kalli banbancin matsayinmu ba.
Ga shi nan duk wani abu daka bani, na tataro na dawo maka da su, zoben nan ne kawai ba zan iya dawo maka da shi ba, saboda kana cikin mutane masu muhimmanci da suka shigo rayuwata, na san ba zan taɓa iya mantawa da kai ba, Na gode Khalil Allah ya haɗa kowa da rabonsa" ta ƙarasa maganar tana zubar da hawaye, ta juya ta shiga cikin soron.
Cikin zafin nama Khalil ya bita, ya riƙota ya juyo da ita tana fuskantar sa.

Kamar zai fashe da kuka ya ce "Haba Hafsa, ina duk alƙawarin da kika yi mini na kasancewa da ni, duk ƙalibalen da ka iya tasowa kuwa, dan Allah karki ce zaki rabu da ni ba, dan Allah kar ki mini haka, in dai Mummy ce zan yi mata bayani, zata fuskance ni kuma, dan Allah Hafsa, muna son junanmu karki yanke wannan hukuncin"

"Bakin Alƙalami ya riga ya bushe Khalil, idan na ce bana sonka nayi maka ƙarya, amma duk wani abu da za ayi iyaye ba sa so ba zai taɓa yin albarka ba, banga alamar Mummy zata fahimceka har ta bari muyi aure ba, dan Allah Khalil kar ka sake shigowa rayuwata, Allah ya haɗa kowa da rabonsa"
Ta zame hannunta daga cikin nasa da ya riƙe, ta shige cikin gidan tana kuka.

Contact me for the VIP group
AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA

BY

AISHA ADAM AYSHERCOOL

PAGE 38

Wani abu me mai nauyi ya tokarewa Khalil ƙirji, bai taɓa tunanin Mummy zata aikata abin da ta aikata ba, na zuwa ta ci mutuncin Hafsa a gaban mutane.
Tamkar wanda aka zare wa lakar jiki, haka ya ja jikinsa ya buɗe motar, ya shiga ya zauna, ya kifa kansa a kan sitiyarin motar, ya rasa abin da yake masa daɗi, ya rasa ta ina zai ɓullowa wannan lamarin, gab ɗaya komai ya cakuɗe masa, ya shafe a ƙalla mintuna Ashirin a cikin motar ya kasa ko da kunna motar, balle ya ja. Ganin bashi da wata mafita a cikin wannan tsayuwar da yake yi, ya sanya ya kunna motar, ya fara tuƙi, sai dai jin jikinsa yake tamkar an zare masa dukkan wata laka dake jikinsa, da wani dishi dishi yake gani, da ƙyar yake iya jan motar, ya nufi gidansu Abdul.
Shagon Abdul a rufe yake, alama Abdul É—in baya nan, Khalil ba shi da kuzarin da zai kira Abdul, dan haka ya cigaba da zama a cikin motar ta sa yana kuma tuno maganganun da Hafsa tayi masa.
Bai san iya adadin lokacin da ya kwashe a zaune a cikin motar nan ba, knocking É—in glass É—in motar da aka yi ne ya sanya shi dawowa play, har ya sauke glashin motar, Abdul ne a tsaye yana kallon Khalil "Ya aka yi baka kirani a waya ba, ka zauna a mota kana bacci?"
Khalil baice komai ba, ya buɗe motar ya fito, Abdul ya wuce ya buɗe ƙofar shagon, Khalil ya shiga ya nemi wuri ya kwanta, ba tare da ya ce wa Abdul komai ba.

Abdul ma bai takura shi sai yaji meke damunsa ba, ya ƙyaleshi.

Fadila kuwa sai yamma suka gama shirin komai, suka zauna yin kwalliya, har su Hajiya Turai sun zo, Daddy maa da wuri ya dawo gida, sai dai Fadila ba taji daÉ—in rashin Khalil a wurin ba, ta yank Cake suka yi hotuna, zuwa magariba kowa ya watse.

Hafsa kuwa bayan shigarta gida wani sabon kukan ta zauna tana cigaba da yi, Sai da Mama ta ga kukan ya yi yawa sannan ta sameta a ɗaki ta ce "Hafsa, wannan kukan da kike fa babu in da zai kai ki, kiyi haƙuri, kiyi Addu'a Allah ya zaɓa miki mafi alkhairi, ko kin auri Khalil tunda mahaifiyarsa ba ta ƙaunarki, ba zakiji daɗin zama da shi ba, kiyi haƙuri Allah ya musanya miki da mafi alkhairi"

Hafsa ba ta cewa Mama komai ba, dan ita kaɗai ta san me take ji a ranta, a kan rabuwarta da Khalil, ta sani rabuwarsu ba yana nufin rayuwarta ta zo ƙarshe bane, amma samun wanda zai maye mata gurbin Khalil abunne mai wahala, ita ta riga ta gama yadda ba ta da sa'a a rayuwata, duk wani abin alkhairi da zai tunkarota, sai ya lalace.

Can Mama ta nisa ta ce "Yanzu wace sana'ar kike ganin zamu koma yi? Bana son ki cigaba da fitar nan tunda na fauskanci babu alkhairi a hakan, kowa ya tashi sai ya sameki a can ya yi miki wulaƙanci a cikin mutane, yanzu dai bari zuwa jibi in Allah ya kaimu idan kin yi tunanin wani abun da zamu yi sai ki mini magana,tun da muna da Abinci.
Jinjina kai kawai Hafsa tayi, ba tare da ta iya cewa komai ba.

Har Khalil ya gama zamansa a É—akin Abdul, bai cewa Abdul É—in komai ba, sai bayan sallar magariba, sannan ya yi wa Abdul Sallama ya tafi gida.

Ko da ya fito zai tafi gida, zuciyarsa ji yake kamar ya sake komawa gidansu Hafsaz ko zata sakko ta saurareshi, amma yadda yaga hawayen nan a idonta cikin damuwa ya ƙara tabattar masa da gaske take, ta bar shi.
Haka ya shiga motarsa ya tafi gida.
Chapter 68 · 0% Book details