Sashe 21
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fitarsa babu daÉ—ewa ya dawo, ya zaune a kan dininga ya zuba Abinci ya fara ci.
Amina sai satar kallonsa take, ko zai yi magana amma bece komai ba. Tana cikin wannan zullumin Fadila ta faɗo falon babu ko sallama, ranta a haɗe da alama ta gaji matuƙa.
Sai dai tana ƙarasa shigowa falon, tayi tozali da Khalil ta saki murmushi.
Ya kalli Fadila shima ya yi mata murmushin ya ce "'yan Jami'a" dire jakarta ta yi ta nufi dining É—in tana cigaba da murmusawa cike da gajiya, ta janyo kujerar kusa da Khalil ta zauna tare da furta "Welcome home dear".
"Ai ke zan yiwa welcome, ya school É—in?".
Ta taɓe baki ta ce "School gamu, muna ta shan wahala".
Ya tsiyayo lemo mai sanyi ya kai bakinta, ta buɗe bakin tana sha tana lumshe ido, Amina zuba musu ido ta yi a ganinta wannan ai fitsara ce, su a ƙauye ai ko kusa da yayyanka namiji baka zama, balle a kai ga bada abu a baki.
Khalil kuwa hirarsu suka cigaba da yi cike da kewar juna. Allah ya rufawa Amina Asiri ganin Khalil ya sanya Fadila ta laifin da Amina tayi mata da safe.
Fadilan ta shiga bawa Khalil labarin abin mamakin da taji game da Yazeed cewa take "Brother bai fa iya turanci ba, ka ji kwaɓar da yake yi idan zai turanci, amma baka ji larabci ba, ni fa har yanzu mamaki nake, anya kuwa shi yake yi?".
"Dama waye ya gaya miki sai ka iya turanci shi ne ka ke da ilimi?".
"Ai ni na gama raina gayen ne gaba ɗaya, kai ka ganshi, kaga dressing ɗin da yake idan zai zo school? Wannan aka bashi taimako karɓa zai yi"
Khalil ya ce "Ke kika ga haka, irin wannan basu da duniya ba balle abin da yake cikinta".
Ta ɗan taɓe baki, tare da janyo plate ɗin gaban Khalil, ta sanya cokali ta fara ci.
Labarin batun Amina tana wurin Baba a birni, za ta yi karatun boko kuwa ya cika gari, wasu suka dinga Allah wadai da tirr da abin da Baban ya aikata shi da Amina a ganinsu wannan tsantsar rashin hankali ne, da rashin sanin ya kamata.
Ko da labari ya iske Jarmai, a ƙulu iya ƙuluwa, yayin da iyalansa suka dinga Allah ya ƙara.
Gidansu Amina ya tafi, zuciyarsa cunkushe da takaici, na yadda ya ga samu sannan ya ga rashi.
Ya sa aka yi masa sallama da Baba Hassan. Babu wani jinkiri kuma Baba Hassan ya fita, ya ƙarasa in da Jarmai ke tsaye tare da yi masa sallama ya miƙa masa hannu su gaisa, Amma Jarmai ya ce "ka ga ni ba wannan ne ya kawo ni wurinka ba, illa in zo in tabattar maka da na samu labarin abin a ya faru, ka haɗa kai da 'yar ka ta gudu, bayan nan an karɓe ni kuɗin Aurena, to tun wuri kaje ka samu 'yan uwanka, ku haɗu ku dawo mini da kuɗina, kafin in ɗauki matakin da ya dace a kan ku".
Baba ya girgiza kai ya ce "To ai kaga ni ba ni na karɓi kuɗin Auren nan ba, bani da masaniya akan komai sai yanzu, dan haka bani zaka tambaya ba".
"Oho dai, ni dai a biyani kuÉ—ina kawai, aikin kawai mutanen banza"
Baba dai bin Rabe kawai ya yi da ido, yana mamakin ƙarfin hali da rashin ta ido irin na Jarmai.
Da Hajiya Zainab ta dawo, kusan raba dare suka yi da 'ya'yanta a falo suna hira, kowa yana kawo hirar abin da ya dame shi, suka ci Abincin dare tare, suka yi ta hira sai bayan sha biyun dare, sannan suka watse.
Har washegari shiru, Amina ba ta ji Khalil ya yi Magana ba, hakan ya sa ta fara sarewa, wata zuciyar ta ce 'kije ki masa magana' wata kuma ta ce "Ki ƙara ba shi lokaci, kar ki yi garaje' gaba ɗaya ta bi ta ƙosa, gashi idan suka haɗu ko gaishe shi ta yi, sai dai ya kalleta ya ɗauke kansa, amma ba zai amsa ba. Ko aiki ne sai dai ya kira Hajara ya sata, amma ba zai kula Amina ba. Amina ba ta da zaɓin da ya wuce ta cigaba da Addu'a, dan haka ta duƙufa da sallar dare tana fatan Allah kar ya kawo abin da zai mata katanga da samun ilimin ta.
Idan taga Fadila ta shirya zuwa Makaranta, abin ba ƙaramin burge Amina yake ba, tana da burin zuwa Jami'a amma ba ta da tabbacin Baba zai iya ɗaukar nauyinta zuwa Jami'a, shiyasa take taƙaita burinta a iya Sakandire kawai.
Yadin jikinsa kawai ta hango ta san shi ne, saboda zuwa yanzu zata iya ƙirga adadin kayan da yake sawa idan zai zo, dama takalmansa guda biyu ne kacal yake zuwa da su. Sai da taje daidai in da yake, sannan ta tada wata irin ƙura, ta bule shi da ƙura ta yi gaba abinta. Duk wanda suka ga abin da ya faru ba su ji daɗi ba, su kai ta bashi haƙuri, ya nuna musu bakomai ya cigaba da tafiya zuwa ajinsu.
Yau a bencin bayan Fadila ya zauna, yayin da ita kuma take jikin window.
  A nata gudanar da lectures kamar kullum. Tari ne ya sarƙe Yazeed, ya saka hankici ya toshe bakinsa, ya kifa kansa yana ta fama, yana tarin ƙasa ƙasa, ya ɗago idanunsa sun yi jawur. A lokacin lecturer ya fita amsa waya, dan haka Yazeed ya fara kira sunan Fadila a hankali, ta waiwayo tana yamutsa fuska ta ce "Meye?".
"Dan Allah ki taimaka mini, jikin window nake so ki bani, ki dawo wurina dan Allah ba dan ni ba, bana son zafi, bana iya numfashi sosai".
Wata uwar harara ta yi masa ta ce "Au Allah, Sannu ajebo ai ni banga alamar hakan a tare da kai ba, ai da sai ka dinga dakon A.C ko fanka daga gida kana dasawa a wurin zamanka, ba in da zan tashi in je" ta juya ta cigaba da rubuce rubucen ta, shi kuma lecturer ya É—ora da bayani.
"Dan Allah Fadila" ya faÉ—a yana jan numfashi.
"Excuse me sir, kaga Wannan mutumin ya takura mini, sai kiran sunana yake ya hanani jin abin da ake yi".
Lecturer ya ce "Malam meye haka? Kalleka da gemu a haka kamar na Allah, tashi daga wurin nan ka koma baya, seat ɗin ƙarshe na last row" Jimm Yazeed ya yi, sannan ya tashi tsaye a hankali ya nufi in da malamin ya yi masa umarni.
Babson da ke kusa da Captain ya ce 'Shima gayen nan kamar wani maye, duk in da yarinyar nan take yana nan, tai ta sawa ana dizga shi, ni gani nake kamar sonta yake yi".
Captain ya ce "Wallahi ƙila ƙarya take masa, ka san yarinyar 'yar wulaƙanci ce, ta gama raina shi, ni dama ƙanwata yake so, matar da ta auri wannan ta huta, mutum sai haƙuri kamar me".
"Aikuwa in dai wannan shegiyar ce ba zata taɓa son sa ba, idan ta auri irinsa cutarsa zata yi, wai ita 'yar mai kuɗi wata banza da ita".
Captain ya yi dariya Ya ce "Kai dai kawai ba kwa shiri ne".
Tun yana iya ƙunshe tarin da yake, har ya kasa ya miƙe da sauri, saboda ya ɗau excuse ya hanzarta barin ajin, amma kan ya kai ga haka, ya silale ya faɗi a wurin.
Nan 'yan ajin suka waiwaya dan ganin meke faruwa, sai dai Yazeed ko motsi ba ya yi, lecturer ya sa a É—auke shi a fita da shi, ya samu wadattaciyar iska, dan da alama He is asmatic.
Ita kuwa Fadila ko waiwayawa ba ta yi ba, balle ta san waye ya faÉ—in.
Mintuna sha biyar, malamin ya ƙarƙare lectures ɗinsa, Fadila ta zari jakarta ta yi waje, dan gidansu Yusra zata je, saboda yau Yusra ba zata shiga school ba.
Har ta gota in da ta ga 'yan ajinsu suka yi cincirindo, kawai sai ta ji tana son sanin waye ya samu asmatic attack É—in.
Ta koma da baya ta leƙa Yazeed ta gani a kwance, babu alamar yana numfashi, idanunsa a rufe!
AYI TA HAƘURI DA NI RASHIN POSTING A KAN LOKACI, KU SANYA NI A ADDUOINKU, ALLAH YA BANI INGANTACCIYAR LAFIYA.
TO GET THE LATEST UPDATE OF THE BOOK, FOLLOW ME ON WATPAD
AYSHERCOOL7724
AREWABOOKS
AYSHERCOOL7724
08081012143
GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
P10
Zaro idanu Fadila ta yi, ganin Yazeed tamkar ya mutu, a mimmiƙe a wurin, jikinta ne ya yi wani irin sanyi, ta tuna yadda ta ji muryarsa yana roƙonta, ta bashi wurin zamanta saboda ba ya son zafi.
Cikin rawar baki Fadila ta ce "Class rep ba za a kai shi Clinic a duba shi ba?".
"Eh, A motar Hamisu muke so a kai shi, kuma motar tayi faci, sun je a gyara a zo tafi da shi".
Cikin rawar murya ta ce "Kaga ku ɗauko shi da sauri, muje a kai shi a tawa motar". Babu wanda ya taɓa zaton Fadila zata iya abin Arziƙi haka, ganin yadda ta uzzurawa Rayuwar Yazeed.
Cikin hanzari ta yi gaba, ta je ta buɗe motar, aka ɗauko Yazeed aka sa shi a motar Fadila, amma ta haɗe rai ta ce Mutum biyu ne kawai za su shiga, dan ba zata kwashi ƙartin banza a motar ta ba su hautsina mata ciki da warin hammata ba. Aikuwa Fadila ta sha zagi a wurin samarin ajin nan, ba ta bi ta kan su ba, ta take motar da ƙarfi ta bula musu ƙura, ta bar harabar wurin da gudun tsiya.
Suna tafe lokaci lokaci, numfashin Yazeed yana dawowa, sai dai baya wuce ƙirjinsa, ga wani irin sound da fitar numfasin nasa ke fitarwa kamar numfashin zai rabu da gangar jikinsa.
Gaba É—aya hankalin Fadila a tashe yake, tana ji a ranta idan Yazeed ya rasa ransa, to tana da kamasho a cikin faruwar hakan.
"Fadila ya naga kin fita daga cikin School, ba Clinic É—in School za a kai shi ba?" Cewar Captain da ke rungume da kan Yazeed.
"Gara a kai shi wani Asibitin, i don't want too much wahala, akwai asibitin da muke da retainership file, a nan muke ganin likita, bari muje can kawai".