← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 84

Sashe 67

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wani ɗan ajinmu ne Yazid ya bani, as a birthday gift, but you, you even forget about it, you don't even wish me" tayi maganar cikin shagwaɓa.

"Ohh my dear, ai naga birthday É—in naki sai gobe in Allah ya kaimu zai cika, kuma ni banga kina mana organising komai ba".

Fadila ta ce "Yusra zata yi mini cake, then just chill with you tonight, mu ci Abinci tare snap pictures together that's all, ba zan haÉ—a hayaniya ba"

Ya ce "Hmm, alright Allah ya kaimu"

"Ameen Daddy, amma me zaka bani as my birthday gift?"

Ya ce "Mmmm, what do you want?"

"Kome ka bani yayi"

"To shikenan, Dubai or Umrah"

Fadila ta É—an zaro ido ta ce "Daddy Umrah, ina son komawa Saudiyya"

"Fine, amma ke da Mummyn ki zaku je, idan kun yi hutun makaranta"

"Alhamdilillah, Daddy na gode sosai, Much Love my Hero" tayi maganar tana rungume Daddy tana murmushi.

Amina da ke gefe, ta kwaɓe baki, ganin yadda Fadila ke ta nan nan da babanta, tana zuba taɓara, amma ta iya zagewa ta wulaƙanta wani, ba tare da tunanin yadda take jin son babanta a ranta haka kowama yake ji ba.

"Daddy, ka san Mummy cewa tayi wai turaren nan wari suke yi kar in shafa"

Daddy ya ce "Aikuwa turaruka ne masu kyau"

Fadila ta nuna masa hannunta ta ce"Kalli, har abin hannu ya bani, da turaren nan, Daddy baka ga ƙoƙarinsa ba sai dai Yaizd bai iya turanci ba, kaga yadda yake larabci kamar balarabe"

"Dama ai haka lamarin ilimi yake, kuma turanci yare ne kawai"

Hajara ce ta leƙo falon, ta ga Daddy zaune shi da Fadila suna hira suna kallo, Amina kuma ta kame a ƙasa ita ma kallon take yi.

A ranta zuciyarta ta ce Lallai ma yarinyar nan, ina can ina aiki, kin zo kin zauna a cikin masu gida kina kallo

A fili ta ce "Amina, ko zaki zo ki yanka mini alayahhu muyi mu kammala girkin dare kan Hajiya ta dawo?"

Daddy ya ce "Kallo, take yi, kiyi aikin a hankali ba sai kin yi gaggawa ba, tun da ba yanzu za aci Abincin ba"

Da É—an mamaki Fadila ta ce "But Daddy, she's also a maid, ai ba kallo ta zo yi ba"

"Yes i know, she's facing her SSCE,  yakamata tayi passing, kuma abin da take kalla is educative, bana son yin asarar kuɗin makarantar da nake biya"

Jiki a saɓule, gwiwa a sace Hajara ta koma kitchen, tana masifa tare da mamakin yadda Amina ke abin da taga dama, da wasu abubuwa da ke faruwa, wanda ta kasa gane kan in da suka dosa.

Fadila ta tashi tsaye ta ce "Daddy, zanje in É—an yi karatu, exams is around the corner"

"Ok Best of luck"

"Thank you" ta nufi É—akinta.

Sai da ya tabattar Fadila ta bar falon, sannan ya ce "'yar Daddy" shiru Amina tayi ta cigaba da kallonta.

"Amina am talking to you fa" a hankali ta waiwayo ta kalleshi.

"Ya naga kin haÉ—e rai, any problem?"

"Nothing" ta faɗa a taƙaice.

"Oya kawo mini Apple, da ruwa" ta miƙe ta nufi kitchen, ta tarar Hajara ta cika tayi famm, tana aiki ita kaɗai.

Tana ganin Amina ta ce "Yauwa, ga alayahun nan, kk É—auka ki yanka"

"Wai baki ji me Daddy ya ce ba? Kallo nake yi, kuma wallahi da nice ba zan takuraki sai kin yi aikin nan ba, duk ni zan abina, amma ke ba damar in É—an huta sai ki sa mini ido, ke fa wuni kike a gida ni kuma ga makaranta ina zuwa haba.

"Amina rashin kunya zaki mini?".

"Ni ban miki rashin kunya ba, kece ba kya jan girmanki"

Daga haka Amina ta ƙarasa gaban fridge, ta buɗe ta ɗauko Apple, ta ɗora a kan plate da wuƙa ta bar kitchen ɗin, ta bar Hajara da mamakin da tambayoyin da babu mai bata amsarsu.

Ta kawo wa Daddy ta ajiye masa.

"Yanka mini mana 'yar Daddy"

Amina ta zauna ta yanka  masa ta miƙa masa, yasa hannu ya karɓa yana ci.

Can Amina ta ce "Daddy, ya sugan naka ya sauka kuwa?".

"Ban duba ba, naji daÉ—in jikina Yanzu sosai Alhamdilillah"

"To Allah ya raƙa lafiya"

"Ameen 'yar Daddy, anjima ki hau online muyi hira"

Ta É—an kalleshi ta ce "Karatun fa?"

"Wai ke ba kya hutawa karatun nan ne? Ki dinga hutawa ranki"

"Ai ba iya karatun boko nake ba, bana son haddata ta zube dole sai ina tilawa"

Cike da girmamawa ya kalli Amina ya ce "Masha Allah, 'yar Daddy, kina nufin kina haddar Alqura'ani?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Kai, dole in san abin yi, ban goyi bayan haddar nan ta zube ba, kin haddace duka ne?"

"A'a, ban haddace duka ba"

Daddy ya ce "Matso nan kusa da ni muyi magana"

Amina ta matsa kusa da ƙafafuwan Daddy, ya ajiye ɗan ƙaramin plate ɗin da ta zuba masa Apple a kai, a kusa da ita, sannan  ya ce "Na daɗe banga mutum mai ƙwazo kamarki ba, zanga abin da ya dace, yakamata in samo wanda zai cigaba da koya miki a gida ina biyansa"

Amina ta washe baki ta ce "Ai ba sai ka kirawo wani ba, direbanka Zakiru malami ne, ka ce ya dinga koya mini, sai ka dinga biyansa shi"

Daddy yayi murmushi ya ce "To shikenan, zan yi Magana da shi in sha Allah"

"Na gode Daddynmu"

Yayi murmushi ya ce "idan kin yi tilawa, ki dinga yiwa Daddynki Addu'a".

"Me zan roƙa maka?".

"Abubuwa da yawa, amma ba zan gaya miki ba, kan ki yayi ƙarami ba zai ɗauka ba"

Hajara kuwa tana laɓe ta hanyar shigowa falon, tana hango Amina da Alhaji Ahmad, amma ba ta jin me suke cewa, bata iya hango Alhaji Ahmad, amma tana ganin Amina tana murmushi, Amina ta miƙe, ta ɗau ragowar plate ɗin da Alhaji Ahmad ya gama da shi, ta ɗan tsaya a kan Daddy tana sauraren abin da yake faɗa mata.
Idan ba gizo idanun Hajara suke mata ba, kamar shagwaɓa Amina ke yiwa Daddy, shikuma ya kashingiɗa yana kallonta.

"Na shiga uku ni Hajara, me ake aikatawa a gidan nan ne? Ita ma matar gidan uwar gantali, tana can yawo ana munafurtarta, kai amma wannan an yi tsohon banza, wannan 'yar tamilon 'yar zai tsaya tana masa barikanci yana kallo, yo ko ya aka yi ma ta samu wannan damar oho?"

Amina ta nufi hanyar ƙofar kitchen, sai ga Hajiya Zainab ta turo ƙofar falon, sai da Amina ta ɗan razana, ta tsaya ta zubawa Hajiya Zainab ɗin ido.

"Ke uban me kike kallo, sai kace mayya kin tsaya kin zubo mini ido, ko kin aike ni ne?"

Amina ta girgiza kai, ta nufi barin falon.

"Ki kawo mini ruwa, da exotic ƙishirwa ta isheni" tayi maganar tana ƙarasawa in da Daddy yake.

Hajara na ganin Amina ta ce "Mmm su Amina manya, kina sha'aninki" ko kallon Hajara Amina ba ta yi ba, ta cigaba da sabgarta.

Alhaji Ahmad ya É—an É—aga murya ya ce "Sweetheart kin dawo?"

Mummy ta ce "Na dawo, kana gida kenan?"

"Na dawo tun É—azu, ban sameki ba masu aikinki sun ce mini ba kya nan"

"Eh, fita ce ta sameni da gaggawa"

Ya ce "Ok, sannu da zuwa".

"Yauwa, Fadila ta dawo ne?" Ta faÉ—a tana zama a kusa da Daddy.

Daddy ya ce "Ta dawo, yanzu ta gama yi mini mita, wai gobe in Allah ya kaimu birthday É—inta, ban wishing É—inta ba"

Mummy ta ce "Ƙyaleta rigimammiya"

Daddy ya ce "Nan ta nuna mini turare, wai an bata gift, amma ni ban bata komai ba"

Mummy ta ce "Naji ta ce za'a yi mata girki, ayi hotuna tana ta lissafinta dai".

Daddy ya ce "Na yi mata alƙawarin umara, zaku je ke da ita, maybe idan sun yi hutu"

Mummy ta ce "Inyee 'yar gidan Daddy, to Allah ya kaimu, dama nima ina son zuwa, to Allah ya kaimu"

"Wai ni Khalil ya koma ne?" Daddy yayi maganar da É—an damuwa.

A daidai nan Amina ta kawowa Hajiya Zainab ruwa da lemo.

Hajiya Zainab ta ce "Mata da wannan yaron, wani halin rashin mutunci ya É—aukar wa kansa, amma zan yi maganinsa"

Daddy ya ce "No, wani abun yana damunsa ne, idan har yana gidan nan, ba zai ɗauke ƙafa daga shigowa gidan nan ba"

Mummy ta ce "Ka rabu da shi kawai" ta mayar da idonta kan Amina ta ce, "Ki buÉ—e ki zubamini, kin zo kin tsaya a kanmu kina rarraba ido".

Amina ta tsuke fuska, ta fara ƙoƙarin zuba wa Hajiya Zainab ruwa a kofin, ta zuba zata miƙa mata ruwan, Daddy ya kalli Amina ya kashe mata ido ɗaya.
Aikuwa sai hannunta ya kama rawa, har ta zubawa Hajiya Zainab ruwa a jiki.

"Ke mahaukaciya, ba kya gani ne? Ke wace irin dabba ce, kalli yadda kika zuba mini ruwa a jiki, ba kya gani ne?"

Cikin rawar murya Amina ta ce "Kiyi haƙuri, ba da sani na bane"

Dama Hajiya Zainab har yanzu a ƙule take, duk da sunje sun yiwa Hafsa rashin mutunci, amma bata huce ba, dan haka take ƙoƙarin ƙara hucewa a kan Amina, a hasale ta ce "Dalla ɓace ki bar gabana, dabba kawai"

Hawaye ne suka cika idon Amina, amma Daddy ya shiga girgiza mata kai alamar kar tayi kuka.

Duk yadda Mama tayi da Hafsa, a kan ta daure ta ci Abinci, ƙi tayi, tana sallar isha'i, ta kwanta, ta zubawa wayarta ido, tana kallon yadda kiran wayar Khalil da saƙonninsa ke shigowa babu ƙaƙƙautawa, amma bata ɗaga ko guda ba.
Ƙarshe ta saka wayar a flight mode, ta shiga gallery, tana kallon hotunan Khalil da ke wayarta, da Videos ɗin da yake haɗa musu, na hotunansu shi da ita.
Wata irin soyayyarsa ce take sake fizgarta, tana jinta wani iri iya awannin data kwashe daga fitarta zuwa wurin sana'a zuwa yanzu da ba suyi waya ba, ta san yana can cikin damuwar rashin É—aga wayarsa da ba ta yi ba.
Ta ƙanƙame wayar a ƙirjinta, ta toshe bakinta, ta cigaba da kuka, dan tun a yanzu ta fara jin kewarsa, tana matuƙar ƙaunar Khalil har cikin ranta.
Chapter 67 · 0% Book details