← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 84

Sashe 72

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryar Daddy ta jiyo yana cewa "Me kike ɓoyewa ne? Ai ni ba ke nake kallo ba, na gaji da jirane na zo na ɗauki fruit ne, ina jin yunwa sosai".

Kunya ce ta sake kama Amina, har ta kasa cigaba da abin da take yi, dan bata taɓa zaton jin hakan daga bakin Daddy ba.

Ai bata gama tunanin ba ta ji shi a tsaye a bayanta, ji tayi tamkar ƙasa ta tsage ga shige dan jinta take a wani yanayi da ta kasa tantance wane irin yanayi ne haka. Gaba ɗaya ƙamshin turarensa ya cika mata hanci, idan tayi ƙwaƙwƙwaran motsi babu abin da zai hana jikinta ya haɗu da nashi.

Miƙa hanunsa yayi, ya ɗauko wuƙa ɗaya a cikin jerin set ɗin wuƙaƙen, dake gefen Amina.

"Calm down, ba taɓa ki zan yi ba, wuƙa zan ɗauka" ya faɗa a kunnenta a hankali.

Ƙiri-ƙiri Amina ta kasa cigaba da aikin, saboda yadda Daddy ya hanata motsi.

Ringing É—in wayarsa ce ta cika kitchen É—in, a tunanin Amina zai matsa ne, amma ga mamakinta sai taga bai matsa ba, ya É—aga wayar ya sanya a kunnensa.

"Hello Madam" ya faÉ—a yana kallon gashin Amina.

"Kayi nisa ne" kasancewar Yana kusa da Amina, tana iya jin abin da ake cewa a wayar, jin muryar Hajiya Zainab a wayar ne ya sanya hantar cikin Amina kaÉ—awa.

Daddy ya ce "Ya aka yi?"

"Eh zan fita ne, idan ka dawo akwai Abinci a dining"

Ya É—an shafi gemunsa ya ce "Ba za'a jira in dawo ba?"

"A'a sauri nake, ban san lokacin da zaka dawo ba"

Atishawa ce ta ƙwacewa Amina, kan Daddy ya katse wayar, tana ƙarewa kuma ta ce "Alhamdilillah" sai kuma ta ɗan zaro ido, tuna waya Alhaji Ahmad ya ke.

"Kai da waye ne naji kamar muryar mace" Daddy ya koma gefen Amina, ya É—an kalli Amina sannan ya ce "Na je wurin Alhaji Sambo ne, ma'aikatansa ne"

Hajiya Zainab ta ce "But it seems that you are so close to the lady that sneeze"

"And who told you she is Lady? Sakatariyarsa ce ta shigo Office É—in"

"Take care" ta faÉ—a cikin isa ta katse wayar.

Ya zubawa Amina ido, ta ɗan ɗago ta kalleshi, ta mayar da kanta ƙasa.

"Kin sani ƙarya, Shi ne kika ƙaƙalo atishawa ki ka yi, dan ta san muna tare ko?"

Amina ta ce "Ni ba ƙaƙalowa nayi ba, zuwa tayi"

"Yanzu idan nace miki ƙazama ki ji haushi, a kan Abinci na kika yi atishawa ko?"

"A'a, ai na kawar da kaina, kuma kai ne ka ke wurin shiyasa ban matsa ba"

"Yarinya idan asirinki ya tonu a wurinta, kina bibiyar mijinta sorrynki Amintako"

Amina ta É—an tura baki ta ce "Ni mai zan yi da mijinta? Kuma ai bani na kawo kaina ba, kai kace a É—auko ni"

"A'a yarinya faÉ—i gaskiya dai, kina bibiyar dattijon mijinta, ba ruwana ni"

"Taɓ, ni mai zan yi da tsoho? Ni yaro zan aura"

"Haba?" Daddy ya faÉ—a yana kai ayaba bakinsa.

Ta jinjina masa Kai.

"Lallai kin samu kanki, da Allah bai sa kin auri Jarmai ba, dole ki faÉ—i haka"

Waro idanunta Amina tayi ta ce "Daddy ina ka san Jarmai?"

"Ina ruwanki matar yara, ƙarasa mini aikina, yunwa nake ji sosai fa" Ya juya ya bar kitchen ɗin.

Mamaki ne ya cika Amina, ya aka yi Daddy ya san Jarmai.

Ta tsaya ta saka rigarta ta uniform, da hijjabinta, ta dinga kai kayan Abinci tana kaiwa gaban Daddy tana ajiyewa.

"Ƙarasa ladanki mana, ki zuba mini"

Amina a É—arare dai ta zuba masa shinkafa kaÉ—an, ta zuba masa ganye cikin plate.

"Wow, kina kula da dattijon nan sosai, God bless you dear"

Ita dai Amina ta takure, tana jiran ya gama, ya bata umarnin tafiya, dan ta gaji da zaman nan.

"Matso muci tare"

Amina ta girgiza masa Kai "Na ƙoshi"

"Aikuwa ba zaki tafi gida ba, muna nan zuwa bayan sallar isha'i"

Amina ta marairaice ta ce "Dan Allah Daddy kayi haƙuri, ban san me zan gaya wa Baba ba".

"To matso mu ci Abinci"

"Wallahi Daddy ban taɓa cin Abinci da wani a kwano ɗaya ba, ba zan iya ba" ta faɗa a rikice.

"Aminatu kenan, wasa nake miki, wannan rikicewar taki ce ke sani dariya. Amaryar Jarmai"

"Dan Allah Daddy a ina ka san Jarmai"

"Ina ruwanki? Juya ki daina kallona kar in ƙware" ta juya masa baya, ta daina kallonsa kamar yadda ya buƙata.

Tana juya baya ya dinga mata dariya ƙasa-ƙasa, gaba ɗaya ya rikita ta lokaci guda.

" 'yar Daddy" ya kirata.

Ta waiwayo ta ce "Na'am"

"Abinci yayi daÉ—i, Daddy ya gode sosai, zo ki ci naki"

"Daddy na ƙoshi, gida nake so na tafi"

"Sai kin ci Abinci zamu tafi, tafiyarku Abuja saura 2weeks, dan haka kan nu tafi zaki je garinku"

"Me zan yi a ƙauyen? Tsoro nake ji kar ina zuwa su Baffa Lawan su riƙeni suce saina Auri Jarmai"

"Idan har ina raye, ba wanda ya isa aura miki wanda ba kya so, zaki je ne dan ki musu sallama, kinga zaki tafiya mai nisa ne, zan saka Zakiru ya kai ki ki musu kwana biyu a dawo mini da ke"

"To kun yi maganar da Baba ne ya yadda da tafiyar?"

"Ba ruwanki da wannan, nace ki bar wannan maganar a hannuna ai"

Amina tayi murmushi ta ce "To Daddy, na gode Allah ya saka maka da alkhairi"

"Ameen Meenalin Daddy, nima na gode sosai kina kula dani da lafiyata, duk da ƙalubalen da kike fuskanta a gidana, ki cigaba da haƙuri watarana sai labari kin ji"

"To Daddy"

"Yau, ci Abinci sai mu tafi gida, zanje in yi sallar la'asar, kwanukan kuma da komai ki bari za a gyara"

Ta jinjina masa kai, shi kuma ya miƙe ya bar ɗakin.

Ta zuba Abinci ta ci, ta kwashe kwanukan ta mayar kitchen, dama tana fashin salla, dan haka ta zauna zaman jiran dawowar Daddy.

Alhaji Ahmad na shigowa, Amina ta tashi tsaye, tana ƙoƙarin ɗaukar jakarta.

Daddy ya kalli fuskarta, ya ce "ya na ganki a tsayem"

"Ba tafiya zamu yi ba?"

"Ban gama abin da nake ba" ya faÉ—a yana kallon agogon hannunsa.

Amina ta kwaɓe fuska ta ce "Haba Daddy, lokaci ya ƙure fa, huɗu fa" kallon yadda take maganar tsakani da Allah yake, wanda gaba ɗaya shagwaɓa take yi.

"Let me see your bag" yayi maganar yana miƙa hannunsa.

Fuskarta babu daɗi, ta miƙa masa jakarta.

Ya karɓi jakar ya nufi wani ɗakin.

Kwaɓe fuska Amina tayi, ta samu wuri ta zauna, gaba ɗaya ranta ya gama ɓaci, so take ta tafi gida duk ta gaji, kawai ta ji wata irin ƙwalla ta taru a idonta.

Bai wani jima ba ya fito hannunsa ɗauke da jakar, ya nufo im in da take a zaune ta takure tana zumɓura baki.

" 'yar Daddy, kin gaji ko?"

Ta É—aga masa kai.

"To tashi mu tafi, am sorry" ya faÉ—a cikin sigar rarrashi.

Ta tashi tsaye, ta ce "To Bani jakar"

"A'a bari in riƙe miki muje"

Amina ta É—an kalleshi ta ce "A'a Daddy ai bai kamata ba"

Daddy ya yi gaba yana faÉ—in "To me is normal"

Amina ba ta da zaɓi sai na bin bayan Daddy.

Bayan fitowarsu ma'aikatan gidan suka nufo su suna masa barka da fitowa.
Gaba É—aya sai ya sauya ya koma Alhaji Ahmad É—insa, kamar ba shi ne wanda ya gama zolayarta a ciki ba da suna su biyu.

Ya kalli wani daga cikin ma'aikatan ya ce "A shiga a gyara kitchen da sauran abin da aka yi amfani da shi"

"Ok sir"

Alhaji Ahmad ya buÉ—e motar, ya saka jakar Amina a ciki, Sannan ya kalleta ya ce "Bismillah"

Amina ta shiga ya rufe ƙofar, sannan ya zaga ya shiga motar shima.

Amina ta jingina da jikin kujera ta ce "Washhh Allah"

"Sorry kin gaji ko?"

Jinjina masa kai kawai tayi, tana sake lumshe ido.

"Daddy" ta kira sunansa.

"Meenalin Daddy" ya amsa yana tuƙinsa cikin nutsuwa.

"Meyasa ka bawa Baba kuɗi ya dinga bani, yana zargin ni na roƙeka fa"

"Ai na gaya masa baki roƙeni ba, ni nayi niyya kawai na bayar nace ya dinga ƙara miki in zaki makaranta, bana son na baki ni da ke, na san ba zaki karɓa ba, kuma bana son wani zargi ya shiga, shi ya sanya na bashi, kuma ai ba kuɗi me mai yawa ba"

"Amma meyasa ba ka bawa Hajara sai ni?" Tayi masa tambayar a bazata.

Kallon Amina ya yi ya kawar da kai bai yi magana ba.

"Daddy ka amsa mana"

"Bana son yawan tambaya fa, matsayin Amina daban a wurina, ita ma matsayinta daban"

Amina ta ce "To meye banbancin matsayin namu ne? Naga duk masu aiki ne a gidanka"

"Ki ƙyaleni" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba.

"Dan Allah Daddy"

"Kin raina ni ko? Ni kike titsiyewa hakam"

Da sauri ta ce "A'a"

"Baki san da wa kike tare ba ko? To idan nace bana son abu, bana so"

"To Allah ya baka haƙuri Daddy, ba zan sake ba in sha Allah"

"Good girl"

Ga mamakin Amina, Yau Daddy bai ajiye ta a ƙofa ba, sai da yaje bakin gate ya fara horn.

"Daddy bari in sauka mana" ta faɗa tana ɗaukar jakarta da taji ta ƙara nauyi"

"A'a sai mun shiga nayi parking" yayi maganar yana horn.

A É—an rikice ta ce "Daddy kar Baba ya ganni, ko Hajiya fa".

"Ki tanadi abin gaya musu" maganar ta sa tayi daidai da buÉ—e gate da Zakiru yayi maimakon Baba ya buÉ—e.

Gaba É—aya Amina ta rikice, sai dai ba taga Baba a harabar gidan ba, Alla Alla take yayi parking, ta fito kan wani a gidan ya ganta.

Bayan Daddy yayi parking, cikin hanzari Amina ta fara ƙoƙarin buɗe motar, amma taji a rufe.

Tana waiwayowa ta kalli Daddy, taga ya kashe motar yana dariya.

"Daddy dan Allah ka buÉ—e, kar Hajiya ta ganmu"

"Kamar kin san idan ta ganki  kece a ciki, ni ba ruwana"

"To ka buÉ—e mini dan Allah"

"To ka buÉ—e mini dan Allah" ya kwaikwayi muryarta da tuni ta samu rauni, kamar tayi kuka.
Chapter 72 · 0% Book details