Sashe 27
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yusra gajiya tayi da zaman Jiran Fadila, ta kirata a waya amma taƙi shiga, gashi Khalil ko kallon in da take ya ƙiyi, gasjiya tayi ta tashi ta kalli in da Khalil yake ta ce "Na tafi sai anjima, na kira lambar Fadila ba ta shiga".
"Ok ki gaida gida"
Yusra ta fito gwiwa a saɓule, a harabar gidan ta ci karo da Abdul, a jikin motarsa, yana ƙoƙarin kiran waya.
Murmushi Abdul ya yi ya ce "Wata sabon gani, Yusra dama kina nan?".
"Ina nan Yaya Abdul, ya kake ya gida?".
"Lafiya ƙalau Yusra, yaushe rabon da na ganki, ya school?".
Yusra ta ce "School Alhamdilillah".
Abdul ya ce "Masha Allah, kin zo wurin ƙawar taki ne?"
"Eh, na tarar ma ba ta nan, ta je school wai za suyi lectures yau".
"Allah sarki, to shikenan, ki gaida gida"
"Yauwa gida ya ji, na gode".
Abdul ya kira wayar Khalil, "Gani a cikin gida, naga baka part É—inka"
"Shigo falo, ina cikin gida" Abdul ya É—an yi jimm, ya ce "To bari in shigo".
Ya nufi cikin gidan, yana fargabar karɓar da zai samu a wurin matar gidan.
Da sallama ya shiga falon, ya hangi Khalil a kan dining, yana cin Abinci.
"Ashe kana nan kana kintsa cikinka".
Khalil ya ce "Ai sai da kintsa cikin, ƙaraso mu ci".
"Ni bana jin yunwa, na ji gidan shiru ko ba kowa ne?" Abdul ya yi maganar yana zama a kan É—aya daga cikin kujerun da ke É—akin.
"Eh basa nan, Fadila tana Makaranta, Mummy kuma ba ta nan".
"Allah sarki, na so inga Fadila ko ba zata kulani ba, ai yau na ga ƙawar nan ta ta Yusra, rabona da ita ina ga tun kan mu tafi karatu".
Khalil ya ce "Hmm ka san wani abin takaici kuwa?"
"A'a sai ka faÉ—a"
"Wai wannan yarinyar Yusra ce, suka haÉ—a kai da Fadila wai sona take".
Dariya Abdul ya yi ya ce "Amma ta taimaki ƙaton tuzuru, to kai ya ake ciki? Yarinyar ai ba laifi".
Khalil ya yi tsaki ya ce "Ƙawar ƙanwar tawa, dan rainin hankali ni sa'anta ne?"
Abdul ya ce "Ji wani zancen banza, dan sa'ar ƙanwarka ce shi ne ba zaka aureta ba, ai masoyi abin a kula da shi ne, meye dan ta ce tana sonka?".
"Dalla, bana son raini, kuma ni bana son ramammiyar mace, na fi son in ga mace a cike"
Abdul ya ce "Banda cin fuska dai malam"
"Kaji da shi, ni idan an yi sallar magariba, zamu je ka rakani wani wuri, in nuna maka wani abu"
Khalil ya ce "Me zan gani?"
"Kai dai ka bari, idan muka je ka gani"
"Ni ina Amina 'yar Makaranta ne?".
Wani dogon tsaki Khalil yayi ya ce "Sai ka tashi ka tafi nemanta ai".
"Wai kai kowacce magana akai maka sai ka kushe" banza Khalil ya yiwa Abdul, ya kammala cin abincin sa, ya dawo ya zauna a falo, suka kunna tv suka cigaba da hira da Abdul.
Fadila kuwa keɓe kanta tayi a makaranta, ta sha karatu sosai da sosai, duk wasu abubuwan sun mata tsaurin da ba ta gama gane su ba, tana buƙatar wanda zai ƙara yi mata bayani. Tana kallon yadda aka haɗa group group, Yazeed yana sake yiwa ɗaliban bayanin abin da ba su gane ba, amma taƙi zuwa gani take idan ta je ta faɗo.
Sai bayan la'asar Sannan ta bari school ta tafi gida, a Falo ta tarar da Khalil da Abdul suna kallon ball suna hira.
Tana ganin Abdul ta wani haÉ—e rai, Abdul kuwa faÉ—aÉ—a murmushinsa ya yi ya ce "Sannu da Zuwa".
Cikin ko in kula ta amsa, dan ya fidda ran zata amsa ma.
Khalil bai kulata ba ta wuce É—akinta, sai da ta bar falon sannan ya ce "Dan Allah Abdul ka daina shiga sabgar yarinyar nan tana yarfaka".
"Kawai dai kace in haƙura ba zaka bani ita ba?".
"A'a ni bance ba, amma yarfin da take maka yayi yawa"
"Ba komai a hankali zamu daidaita".
"Ai sai kai tayi"
Sai da aka yi sallar magariba sannan suka bar falon, suka tafi masallaci domin yin salla.
Bayan sun fito daga sallar ne Khalil ya cewa Abdul "Muje ka rakani in nuna maka abin da nake gaya maka, amma mu fara biyawa in gaida Mama"
Abdul ya ce "To muje, Allah ya sa abin kirki zaka nuna mini, ba shiririta ba".
"Ni ne ma nake maka shirirtar?"
"To ai kai É—in ne wasu lokutan sai a hankali, muje dai in gani"
Haka suka tafi, suna tafe suna faɗa suka isa unguwar su Abdul, suka shiga Khalil ya gaisar da Maman Abdul, kamar yadda yake ɗabi'arta ta karɓi Khalil hannu bibbiyu, tana ta kwarara musu Addu'a da sa musu albarka, saɓanin mahaifiyar Khalil idan ta ga Abdul, ta dinga masa kallon banza kenan tana hura hanci.
Bayan fitowarsu daga gidan su Abdul, Khalil ya ja mota zuwa unguwar su Hafsa, wanda take a gaban ta su Abdul, bai yi parking a ko ina ba sai a wurin suyar awarar Hafsat.
"Wai mai za muyi a nan ne?" Abdul ya tambayi Kahlil yana kallonsa.
"Zo muje zaka gani"
Suka fito daga motar suka tunkari wurin mai awara.
Abdul ya kasa haƙuri ya sake cewa "Wai wurin wa zaka ne?".
Khalil bai bashi amsa ba, sai janyo hannunsa da yayi suka ƙarasa. Hafsa na ganin Khalil ta tsuke fuska, tana ɗauke kai.
Sallama Khalil ya yi, Hafsa ta amsa tamkar an mata dole, suka zauna a bencin da ke wurin, Abdul kuwa sai bin Khalil yake da kallo ransa cike da tambayoyi.
"Barka da warhaka 'yan mata" Khalil ya faÉ—a yana murmushi.
Wani irin kallo Hafsa ta yi masa, wanda bai gane ko na meye ba, sai dai kawai yaji tsigar jikinsa ta tashi da kallon da tayi masa.
"Ke baki gaishe ni ba, kuma na gaishe ki kin ƙi amsawa".
Hafsa ta ce "Ni gaskiya malam takura mini kake yi, wai me kake nema a wurina ne?".
Khalil ya ce 'Ban taɓa ganin wanda ba ya maraba da coustomer ba sai ke Hafsa" ɗagowa tayi da sauri ba tare da ta yi niyyar magana ba ta ce "Waye ya gaya maka sunana?"
"Ban sani ba" ya bata amsa.
ÆŠan É—age kafaÉ—a tayi ta cigaba da fifitar wutarta, Abdul dai sai bin su yake da kallo.
"Zuba mana ta dubu É—aya" yayi Maganar yana kallon zobunan hannunta.
"Ba zan sayar ba, sai dai in baka ta iya canjinka É—ari biyar da ka bar mini"
Khalil ya ce "Ƙadiran ala man yasha'u, wai ke wace irin Yarinya ce haka, Wallahi ba zan karɓi ɗari biyar ɗin nan ba, ki zuba mana ta yadda na ce mu tafi".
Murguɗa baki tayi ta ƙi magana, ta cigaba da sallamar mutane.
"Sauri fa muke, ki sallame mu mu tafi" ya faÉ—a yana nazartar ta.
"Amma kamar ba ɗaure muku ƙafafuwa na yi ba ko?"
Khalil ya kwantar da murya ya ce "Zuciyata ki ka ɗaure, ba ƙafafuwana ba"
Abdul yayi gyaran murya ya ce "A taimaka a sallame mu ƙanwata, ya damu yana son cin awarar ne, shiyasa na rako shi".
Hafsa ta ce "Ba fa ci yake ba, yana zuwa wurin nan ne kawai dan takurawa rayuwata, bana son yi masa wulƙanci, amma gaskiya yana takura mini, sana'a nake bana son yadda maza suke taruwa a wurin nan, ba yadda zan yi ne, shi kuma sai ya zo ya sani a gaba da surutai".
Abdul ya ce "Kina da gaskiya, amma kiyi haƙuri dan Allah, Yanzu zuba mana sai mu tafi".
Hafsa ta ce "Ba zata kai ta yadda ya ce ba".
"To zuba mana wadda ta samu, sai mu tashi"
Hafsa ta zuba ta É—ari shida, ta kalli Abdul ta ce "Ta É—ari shida ce, akwai É—ari biyar É—in sa a wurina, É—arin kuma na bar maka"
Abdul ya ce "A'a ba za ayi haka ba, ai mun cinye ribar, bari dai in biya"
Hafsa ta ce "A'a ka bar shi Wallahi, ka bashi ta ɗari biyar ɗin sa, wadda na baka kuma, ka ci ko ka bayar, ka yiwa mamana Addu'a Allah ya bata lafiya".
Abdul cikin tausayawa ya ce "Allah sarki, ubangiji Allah ya bawa Mama lafiya, ya sa kaffara ne"
"Ameen na gode" Sai Khalil ya zama hoto, yana mamakin yadda Hafsa, ta É—an saki jiki ta yiwa Abdul magana, amma shi take nuna yana takura mata.
Suka miƙe zasu tafi, Khalil ya sa hannu a aljijunsa, ya ciro dubu uku, ya ajiye wa Hafsa.
Miƙewa tayi da sauri ta ce "Malam karɓi kuɗinka, ya zan yi da su?"
Khalil ya ce "Yi makama shi da su"
Yayi gaba abinsa, ta kalli Abdul ta ce masa "Dan Allah ungo ka bashi kuÉ—insa, ni bana son irin wannan abun, meye haÉ—ina da shi zai dinga yi mini haka?".
Abdul ya ce "Nima fa yanzu kika mini kyauta na karɓa, dan haka ba a mayar da kyauta, ki saiwa Mama lemo da shi ba yawa, sai mun sake dawowa" yayi gaba ya barta baki a sake da kuɗi a hannu.
Har suka fara tafiya, Khalil bai ce komai ba, can Abdul ya numfasa ya ce "Khalil, me kake nufi ne?
Khalil ya yi ajiyar zuciya ya ce "Shi ne abin da haryanzu ban tabattar ba, a kallon Farko da na yi mata, na shiga wata duniya da na kasa tantance, tausayi ne ko menene"
"Khalil soyayya kenan fa"
"Ba zan musa maka ba Abdallah, abin da nake ji game da ita, yayi yawa ina jin zan iya komai dan in dinga ganinta a kusa da ni, haka kurum nake jin kishin sana'ar nan ta ta, tana zaune kiwa na kallonta".
Abdul ya ce "Tirƙashi, kai Izza ita miskilanci da rashin son raini".
"Ai Abdul baka ga komai ba, yarinyar nan tana da jin kanta, ga ta da ba kowa ba, sai jan aji, kamar zata wahalar da ni, amma na yi mamakin yadda tai maka Magana, ni sai dai ta harareni ta gaya mini baƙar magana"