Sashe 6
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Na sani Hafsa, ni babban abun da ya dameni, shi ne mu zamana bamu da taro ko sisin da muke juyawa, amma insha Allah komai zai wuce, watarana sai labari, Allah ya kawo dalilin da zai rabaki da wannan siye da siyarwar bakin hanyar, bana so raina ba ya mini daÉ—i".
"Bakomai Mama, Allah ya kawo mana mafita ya baki Lafiya, dangin mahaifina abun da suka yi mana, Allah ya ninka musu" ta ƙarasa Maganar hawaye na zubowa daga idanunta, alamun tana cikin damuwa.
Mama ta girgiza kai ta ce "A'a Hafsa, Allah ya shirye su kawai, ki daina kukan nan" Mama tayi Maganar tana share mata hawaye.
Hafsa ta share hawayenta ta ce "Naji tsayuwar Napep a waje, bari in tafi kar in yamma, me zan taho miki da shi?".
"A'a bana buƙatar komai, Allah ya tsare, ki kula da kan ki, kar ki wasa da mutuncinki".
"To Mama insha Allah" ta kwashi kayan sana'arta, ta fita da su.
**********
Fadila na falo tana kallo, duk tayi kaca_kaca da falon, in da suka ci Abinci ita da Yusra sun bar komai a falon, ga tarkace duk ta tara shirgi, Asabe na ta kaiwa tana komowa tana gyarawa, ita kuwa ta hakimce akan kujera tana ciye-ciye.
Mummy na zaune a gefe, tana danna wayarta, tana chatting da abokan kasuwancinta.
"Hmm, wai kin san me Yaya Khalil yayi mini kuwa Mummy?".
"A'a sai kin faÉ—a".
"Gaba É—aya ya gama yarfani yau É—in nan, mussaman na yiwa Yusra waya akan ya zo gari, ta bar abun da take ta zo gidan nan, amma kin ga da ta gaishe shi da yadda ya amsa?".
Mummy ta ce "Ai ni na rasa gane kan yayan nan naki, sam ba shi da alƙibla, yarinyar tana da kirki da hankali, gata 'yar masu kuɗi, sam banga aibunta ba".
"Kema dai kya faÉ—a Mummy" suna tsaka da hirar sai ga Khalil yayi sallama".
Mummy ta amsa ban da Fadila, da ta kuma haÉ—e rai.
Khalil ya ce "Mummy na dawo É—azu ki bani National id card É—ina, zan cike wasu takaddu, amma ba kya nan".
"Eh naje duba shagona ne na zoo road, sun yi mini waya wai wasu kayan sun ƙare".
Khalil ya sauke idanunsa a kan Fadila ya ce "Yawwa, ke kuma na dawo gareki, daga yau idan yarinyar nan ƙawarki ta kuma zuwa, ki ka sa tana mini shishshigi sai na makeki a gabanta".
Mummy ta ce "wai kai shikenan ba'a masa abun Arziƙi kenan? Meye laifin Yusran nan ne?".
"Ba na son raini, kawai sai in fara Soyayya da ƙawar ƙanwata, dan abun Kunya? Wata bushshiya da ita ba fasali".
"Kai dai ba'a yi maka abun arziƙi, ban da wulaƙanci meye laifin yarinyar nan? dan ma ka samu ance ana sonka da wannan masifar taka da zafin rai".
Khalil ya ce "Dama bance ace ana sona ba, a bar ni in samo Yarinya daidai da ni, wadda ta yi karatu me zurfi mai hankali da tunani".
Mummy ta taɓe baki ta ce "Ka ji da shi dai, a garin zaɓen zaka zaɓo mummuna, ni dai fatana a samo mini 'yar babban gida, kar a kwaso mini 'yar talakawa, wanda ba su san mutunci ba".
Khalil ya ce "Mummy kin ga yadda ginina na Abuja yayi nisa kuwa? Tunanin yarinyar da ta dace da gidan nan nake".
"A samo wadda za'a iya kai maka kayan Arziƙi dai shine fatana"
Khalil ya kalli Fadila da ta haÉ—e rai ya ce "Ke yaushe zaku fara lectures ne?".
"Saura sati biyu" ta faÉ—a tana cunkusa baki.
"To ki maida hankali dai, dan Jami'a ba gurin zuwa ayi sakarci bane".
Hararsa ta yi a fakaice, dan ya gama ƙular da ita yau ɗin nan.
"Ki yiwa yaran nan magana su kawo mini Abinci na kan dining, and Abdul ya ce yana gaisheki".
Fadila ta ce "Waye wani Abdul kuma?".
"Ban sani ba" Khalil ya bata amsa.
"Nifa ya dena wani rawar kai a kaina, me zan yi da shi?, yana lecturer mai na sama ya ci balle ya bawa na ƙasa?".
"Fadila me kike cewa?" Khalil yayi Maganar a fusace.
"Ai nima naga cewa kayi ba ka son ƙawata, ita da tafi wani Abdul komai, nima dan me zan so shi, kuma shima ya san ni ba kalarsa ba ce, Nasan albashinsa ko mayukana da turaruka na ba zai siya ba".
Khalil zai yi Magana Mummy ta dakatar da shi ta ce "Kar ka takura ta ƙyaleta, nima ban goyi baya ba".
"Amma Mummy me yasa? Naga Abdul É—in nan abokina ne, tare muka yi School, kun san halayensa gaba É—aya".
"Kai babanka ne ya biya maka kaje karatu, shi kuma gwamnati ce ta bashi tallafi, aikin da yake ma ba babanka ne ya samo masa ba? Idan yana da kunya ai ya san Fadila ba sa'ar sa ba ce".
Shiru Khalil yayi jin Mummy ta goyi bayan Fadila, amma har ga Allah bai ga aibun abokin nasa ba, kuma ya san da Fadila za ta Aure shi, za ta ji daɗi saboda yana da kirki, kuma yana matuƙar sonta, amma ya kasa gaya mata saboda yadda Izzarta take masa kwarjini.
************
Amina ce zaune a É—aki, ta sanya langar koko a gaba, tana ta uban kuka tamkar wadda aka cewa babanta ya mutu.
Inno ce ta É—aga labulen É—akin ta ce "Wai ba zaki daina kukan nan ki tashi ki karya kumallo ba?".
Shiru Amina ta yi, ta cigaba da raira kukan ta".
"Ji min 'yar abar da malam ya hana ni faÉ—a, ba magana nake miki ba, ai ni Kawu Balan ya gama yi mini komai da ya hanaki zuwa bokon nan".
Sake fashewa da kuka Amina ta yi ta ce "Haba Inno, haka zaki ce?".
"Eh haka nace, me ake da wata boko? Ki tashi ki karya ki zo ki É—ebi kayan wankin nan, ki je ki wanko mana su".
Haka Amina ta tashi, ta ɗauki kokon nan ta kafa kai, babu siga sam a cikin sa ga gasarar ta yi tsami sosai, amma haka ta kafa kai tana zuƙarsa kaɗan-kaɗan.
**************
Baba Hassan ya zabga uban tagumi, ya san ko ba'a gaya masa ba, Amina na can a cikin damuwa akan kuÉ—in da ta tambaye shi, amma babu yadda ya iya dan yayi iya yin sa, amma bai samu ba, kuma ya san da gayya Hajiya Zainab ta hana shi kuÉ—in nan, ba wai dan babu kuÉ—in ba.
Yana ganin shige da ficen Khalil a gidan, amma ba zai iya tambayarsa ba, duk da ya san idan ya tambaye shi zai bashi, amma yana jin nauyin yaron sosai.
Gashi ya san idan ya kira mai gidan ya ce ba'a bashi kuɗin ba, nan ma wata matsalar ce, yana gudun haɗa fitina a tsakanin ma'auratan, kuma dama shi kansa mai gidan akwai taƙama, ba ya son takura sam.
Haka Baba Hassan ya din ga tunani, amma ya kasa gano mafita gaba É—aya.
**************
"Mummy wai Ina Fadila ne? Tun da na shigo ban ganta ba".
Mummy ta ce "zai wuce ace tana bacci ne?".
"Bacci a yanzu Mummy? Ƙarfe sha biyu da rabi fa"
"To ta fito ta yi breakfast, ta koma É—aki ta kuma kwanciya".
"Amma Mummy kika ƙyaleta, da haka za'a Jami'ar?"
"To yanzu dai tun da ba Jami'ar ta shiga ba, ai ka bar ta ta huta ko? Gwanin na iya, sarkin hantara da zare idanu".
Girgiza kai ya yi ya ce "Idan ta shiga makaranta, wani sakarcin idan ance tayi ba za tayi ba".
"Ai ni shiyasa na so babanku ya kaita ƙasar waje, kamar yadda ake kai kowacce 'yar gata, amma ya ƙi wai rawar kanta ta yi yawa, da shikenan ba ruwanta da tashin hankalin Jami'oin Nigeria"
"Aikuwa tun da haka ba ta samu ba, dole ta koyo sabawa da tashin hankalin Jami'oin Nigeria, kuma ko ina aka kaita ba'a samun ilimi ta sauƙi".
Mummy da ta gaji da tsarin Khalil ta ce "Jeka na ji Babana".
Be kuma cewa Uffan ba ya fice.
Daga gida kuwa kai tsaye gidansu Abdul ya wuce, wanda É—akinsa ya ke jikin gidansu da banÉ—akinsa da komai, dan haka Khalil ba sai ya shiga cikin gidansu Abdul ba.
Abdul yana zaune yana marking tes É—in É—alibai, Khalil ya yi sallama.
Abdul ya amsa masa tare da cewa "Daga ina haka?".
Khalil ya zauna ya ce "Wallahi da ga gida, ni duk garin ma ji nake ya isheni".
"To sai ka tattara ka koma in da ka fito, dama ni mamaki ma na ke, kawai ka baro aikin ka ka dawo gida ka zauna".
Khalil yayi murmushi ya ce "Har wani aiki ake? Ni Wallahi ginina ne ya dameni, ka san wannan Plan É—in da muka fitar shi nake yi fa".
Abdul ya ce "Kai, amma fa zai ci kuÉ—i da yawa".
"Aikuwa yana ci sosai, amma ka san kuÉ—i ba matsala ta bane".
"Na sani, kana ta gini ba matar Aure, kuma maimakon kayi ginin a nan, amma ka tafi Abuja"
"To ba'a can nake aiki ba, Kano ina da gida, Yaushe za'a ƙarasa naka ginin ne malam Abdul?"
Abdul ya yi murmushi ya ce "Abubuwa ne sai a hankali, ka san siblings ɗina, ni ke hidimar karatunsu, rayuwar sai Alhamdilillah, ga yaran Yaya Hameed da ya rasu ya bari, nine kamar babansu Yanzu, ni ke kula da su, ka ga ba zan bari su wulaƙanta ba dan ba ransa".
Khalil ya yi murmushi ya ce "Allah sarki, duk faɗan da muke yi da kunna ni da ka ke wasu lokutan, Halayenka abun koyi ne Abdul, Allah ya ƙara maka Arziƙi, Insha Allah da an samu wani space ɗin aiki zamu haɗe a Abuja".
Abdul ya ce "Kai Khalil, wannan aikin ma da na samu ta silarka na ke yi na ji daÉ—i, bani da bakin godiya, amma ka bar ni kawai, na nemi kasuwanci in haÉ—a".
"Wallahi ba ka isa ba, dole mu tafi tare, kuma filin jikin in da nake gini a Abuja, ka kawo half É—in kuÉ—in, in cika maka kawai ya zama naka".