← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 84

Sashe 34

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin da gaske Yazeed yana shirin tashi ya tafi ba tare da ta kammala ba, ya sanya a hankali fadila ta ce "Ban gama ba fa"
Wani miskilin murmushi ya yi, ba tare da ya bari Fadila ta gani ba, ya É—an tsuke fuska ya kalleta ya ce "Magana kike?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Ban ji me kika ce ba?"
"Ban gama ba?" Ta furta a hankali.
"Kina buƙatar taimakona ne?" Ta jinjina kai alamar eh.
Yazeed ya gyara zamansa ya ce "Me kike buƙata?"
Nan ta gaya masa wanda ba tayi ba a tambayoyin. Ya ajiye mata takardarsa ya ce "Gashi nan kwafi".
"Ka karanto mini, bana iya ganowa sosai".
Murmushi Yazeed ya yi, yana karanta mata a hankali.
Invigilator ne ya fita, hakan ya bawa sauran É—aliban ajin, damar cigaba da taimakawa junansu, tuni Fadila ta manta ta matsa kusa da Yazeed tana wanke takardarsa, jin jikinta ya fara rawa ne ya sanya ta lura tana kusa da shi, dan haka da sauri ta ja da baya, tana sauke numfashi. Kallonta yayi yai murmushi ya ce "Kin gama ne kika matsa?"
"Ban gama ba" ta faÉ—a a raunane.
"To ƙarasa mana, zan tashi in kai fa".
"To ka karanto mini mana"
"Ki kwafa mana ni na gaji" ya faÉ—a yana jin daÉ—in yanayin.
A hankali ta kuma matsawa kaÉ—an ta cigaba da kwafa, amma tuni gumi ya fara yankomata, tana rubutu hannunta na rawa.
"Ki nutsu mana, lokaci ya kusa ƙurewa kuma sai rawar jiki ki ke, kin kasa rubutun" da ƙyar Fadila ta ƙarasa saboda gaba ɗaya bata iya tantance yanayin da take shiga idan tana kusa da shi, idan yana nesa da ita ne take iya tatala masa rashin mutunci son ranta, amma da sun samu kusanci sai ta rasa nutsuwarta, sai da ta gama sannan Yazeed yaje yayi submitting.
Ajiyar zuciya ta dinga saukewa a jere, saboda yadda ta sha da ƙyar, bayan ta fito ta hango Yazeed a wurin motarta yana waya, da 'yar ƙaramar wayarsa, ya jingina da jikin motar dan haka ba halin ta buɗe motar.
Tsayawa tayi ya kammala wayar, tana ta tunani a zuciyarta, godiya zata yi masa ko kawai ta share shi? Ya juya harshe sai zuba larabci yake a waya tamkar bai taɓa jin hausa ba, abin ya ƙara bata mamaki, abubuwa da yawa suna bata Mamaki game da Yazeed.
Ya kammala wayar sannan ya waiwayo ya ce "Am sorry na tsayar da ke".
"Never mind" ta faÉ—a a sanyaye.
"Za muyi karatu ne ko yau ma tafiya za ayi?" Yayi Maganar yana tsareta da idanunsa.
"Ni yunwa nake ji, kuma na gaji sosai".
انت جميل ياحببتي
Ya faÉ—a yana lumshe idanunsa. Kallonsa ta yi dan bata gane me yake nufi ba.
"Yunwa ki ke ji, kuma ke kin gaji, kar ki nuna kin san Yazeed gobe in Allah y kaimu a exam hall".
"Eh ai nima ba daƙiƙiya ba ce, yau ɗin ma dai kawai na kakare ne" tai maganar cikin tsiwa tana masa kallon up and down.
"Ni a ina nace miki daƙiƙiya ukhti? kalen faɗa ne dai kike yi, kuma ba zaki yi dani ba, aje gida a ci Abinci lafiya". Ɗan taɓe baki tayi, ta hau motarta ta kunna ta ja ta bar wurin.

Ƙarfe goma na safe, Su Khalil suka je suka ɗauko su Mama, Khalil sai kallon Hafsa yake yi, amma tun da ta gaishe shi bata sake ce masa uffan ba, sai hira da suke da Mama jefi jefi.
Goma da rabi suna station ɗin da aka karɓo Hafsa, suka isa wurin, DPO sai haba haba yake da su, har da yiwa Hafsa wasa, wai "Hajiya Hafsa babu gaisuwa ne?" Wata uwar harara ta watsa masa ta kauda kanta.
Suna nan zaune sai ga Najeeb ya ƙaraso da shi da wasu matasa guda biyu.
Mama na ganinsa ta haɗe rai, taƙi ko kallon in da yake, ya shigo yana ɗingisa ƙafa. Shima wani banzan kallo ya yiwa su Hafsan sannan ya ƙarasa ciki ya zauna, suka gaisa da DPO ya maida idonsa kan Khalil da Abdul dake wurin, yana mamakin su kuma wannan daga ina?.
DPO ya ce "Yauwa Najeeb, ga wanda suka zo suka yi belin Hafsat a jiya, dama na gayyace ku ne gaba É—aya a zo a zauna a teburin sulhu, tun da dai shi sulhu alkhairi ne".
"Kamar yaya aka bada ita beli, haba DPO haka muka yi da kai? Yarinyar da ta nemi ta halakani".
"Dama kai ne kasa aka kamata? Har kake iƙrarin dan me aka bada belinta?, kai ko kunya baka ji, wannan ce zata halaka ka garjejen ƙato da kai?" Khalil yayi Maganar yana zaro ido.
Najib ya ce "Kai kuma awa? Me ya kawo ka cikin wannan case É—in, abu ne na family issues 'yar uwata ce ina ruwanka?".

"Wallahi ni ba ɗan uwan bane, babu wata alaƙa tsakani da shi, dan Allah Yallaɓai ka mini tsakani da shi kar ya sake zuwa in da nake, ba ruwanshi dani, dan Allah" Hafsa tayi maganar tana kuka.
DPO ya ce "Wai dama ka santa ne?" Ya  tambayi Najib.
"Yallaɓai 'yar uwata ce, wani misunderstanding ne kawai ya gifta ake samun wannan akasin"
Duk da sanyin hali irin na Mama, amma nan da nan fuskarta ta sauya, ta ce "Kar ka ƙara danganta kanka da 'yata, baku da wata alaƙa da mu".
Najib ya ce "Ai dama ba dake na ce ba, bani da wata alaƙa da ke, amma ina da ita da Hafsa".
"Shut up malam" Khalil yayi masa tsawa.
"Wallahi kai mana rashin hankali a nan, sai na saka an samaka sarƙa, mahaukaci kawai".
DPO ya ce "Dan Allah ya isa haka, wannan hayaniyar duk ba mafita bace. Ke Hafsa meye haɗinki da shi, da har kika ƙona shi?".
Hafsa ta share hawaye ta ce "Karo kusan uku kenan, yana zuwa wurin sana'ata yana ci mini mutunci yana zagina a gaban mutane, ni kuma na gaji na rasa yadda zan yi kawai na zuba masa mai a ƙafa, kuma ina da shedu a gaban mutane yake zuwa kaina yana ci mini mutunci".

"Amma me yasa baki yi wannan bayanin jiya ba, da muka tambayeki?".

Khalil ya ce "Amma duk ba kuyi wannan binciken ba, kuke iƙrarin zaku kaisu kotu, anya makuwa ka san aikinka?"

DPO ya ce "Wannan abu dai duk kuskure ne an riga anyi shi, saboda shi abin da ya zo ya gaya mana daban, ita kuma taƙi Magana, amma insha Allah yanzu za a rufe case komai ya wuce".

"Eh, a rufe case amma ba komai zai wuce ba, idan aka rufe wannan case ɗin ni kuma zan shigar da ƙararsa a kan cin mutuncin da yayi mata, kuma Wallahi CID zan kai shi, ba dai abun wa ka sani wa ya sanka bane? Zan masa abinda ya yi".
Abokan Najib da suka rako shi wanda ba suyi magana ba tunda suka zo, ɗaya daga cikin su ya ce "Dan Allah dai kayi haƙuri komai ya wuce, kuskure ne an yi, ayi haƙuri".

"Dalla rufe mini baki, waye ya sa da kaiz' ba dai kuna ƙaryar rashin mutunci ba, kawai ya sa aka kama yarinya aka rufe, bayan laifinsa ne, ba zaku bar nan wurin ba zan waya azo a tafi da shi, koma a haɗa da ku duka" yayi Maganar yana zaro wayarsa daga aljihu, aka dinga bawa Khalil haƙuri,ƙarshe sai da Mama ta saka baki ta ce "Bakomai Khalil, wannan taimakon da ka yi mana ma mun gode, bana son wani abu ya sake shiga tsakaninsa da 'ya ta, kawai ka sa a musu iyaka, kar ya kuma zuwa wurin da take".
Da ƙyar Khalil ya haƙura aka rufe case ɗin nan, dan sai da Abdallah shima ya saka baki, sannan aka rufe case ɗin, suka ɗau su Hafsa a mota suka tafi mayar da su gida.

Najib kuwa mamaki ya dinga yi, waye Khalil a ina su Hafsa suka samo wanda ya tsaya musu haka? A iya saninsa basu da kowa basu da Komai, amma ya akai Khalil ya shigo rayuwarsu, ya so ya kuma amfani da damrsa ya wulaƙanta Hafsa son ransa, daga ita har Mama, amma ya lura wannan Khalil ɗin yafi shi zafin kai da masu gidan rana, idan ya matsa shi ne zai kwana a ciki.

Khalil ya so yaji alaƙar dake tsakanin su Mama da Najib, amma ganin kamar basa son zancen ya sanya shi yin shiru.
Yau ma har gida suka kai su Hafsa, Mama nata musu godiya da sa albarka, Mama ta nufi gida, Hafsa ma ta biyo ta. Mama ta kalli Hafsa ta ce "Ke wace irin Yarinya ce mara lissafi? Har a miki wannan abin Arziƙi amma ba zaki tsaya ki sake masa godiya ba? Maza koma kije ki kuma yi masa godiya".
Cikin sanyin jiki ta koma inda su Khalil ke ƙoƙarin tafiya, taje ta tsaya ba tare da ta ce uffan ba. Khalil ya sauke glashin motar, ya kalleta ya ce "In zo ne?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
Ya buÉ—e motar ya fito, ya tsaya a gabanta ya ce "Gani ranki ya daÉ—e".

Ta É—an yi turus, Sannan ta ce "Dama, ce maka za yi Na gode sosai da taimakon da kayi mini, Allah ya saka da alkhairi".

Khalil ya yi murmushi ya ce "Meye abin godiya, dan mutum ya yiwa matarsa abin daya dace?" Da sauri ta É—ago ta waro masa manyan idanunta.
"Kin san wani abu Hafsat?" Ta girgiza kai.
"Ina kishinki da yawa, bana son zaman da kike a titin nan, dan Allah ni dai ki daina".

"Idan ban zauna a titi na yi sana'a ba, da me zamu rayu?".

"Ba zai gagara ba Hafsa, ni dai dan Allah ki daina, kuma very soon nake son ayi zancen aurenmu".

"Na gode sosai da taimakon da ka mini, amma ni ba zan aureka ba, ka ƙyaleni a yadda ka ganni kawai"

"Amma Hafsa saboda me?"

Ƙwalla ta taru a idanunta ta ce "Dan Allah kar kayi amfani da damar ka taimakeni ka turasasa mini yin abin da bani da ra'ayi a kansa, dan Allah ka ƙyaleni".
Chapter 34 · 0% Book details