← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 84

Sashe 32

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cak Khalil ya tsaya, ya waiwayo, ya kalli mutumin da ke maganar, ya ce 'Malam wani abin ne ya haÉ—ata da wani?".

Mai shayi ya ce "Wallahi wani mutumi ne yake yawan zuwa wurin nan, ya yi mata zagin rashin mutunci a gaban Mutane ya tafi, babu wanda ya san abin da ya haɗata da shi, aikuwa shekaranjiya ta watsa masa mai a ƙafa ya ce zata gani, wataƙila shi ya sa yau bata fito ba"
Cikin hanzari Khalil ya ce ya gode, jikinsa na rawa ya koma mota, gidansu Abdul ya fara zuwa, dan ya fishi sanin kan unguwannin.
Yana tsaye a ƙofar shagon Abdul, ya kira shi a waya, Abdul ya ɗaga tare da "Assalamu alaikum".
"Wa'alaikum salam, kana ina ne? Na zo shago baka nan?".
Abdul ya ce "Wane shagon?"
"Shagonka mana, ina Kano fa, dan Allah kana ina akwai matsala ne".
"Subhanallah, Allah yayi mana maganin matsala, fito titi mu haÉ—u" Khalil ya ajiye wayar, ya ja mota ya koma titi.
A titi ya samu Abdul ya É—auke shi suka tafi.
Abdul ya ce "Wai ina zamu ne? Tukuna ma me ka dawo yi?, kwata kwata yaushe ka tafi da har ka dawo?".
Khalil ya kwashe komai ya gaya masa, Abdul ya jinjina kai ya ce "Ikon Allah, to Allah ya sa lafiya muje mu nemi gidan" Suka ƙarasa makarantar da aka kwatanta musu, da tambaya da ƙyar suka gano gidan, sai dai suna zuwa suka tarar gidan a rufe. Khalil yayi mamakin ganin gidansu Hafsa, ɗan ƙuƙuta kamar ɗakin tattabaru. Hakan yayi daidai da dawowar Malam Sani daga taya Mama neman Hafsa. Ganin yana ƙoƙarin shiga gidan kusa da na su Hafsa, ya sanya Abdul ya ƙarasa, ya yi masa sallama, Malam Sani ya amasa masa, suka gaisa.
Khalil ma ya ƙaraso, suka gaisa da Malam Sani, Abdul ya ce "Dan Allah munga kaine maƙwabcin wannan gidan, munzo wurin su Hafsa ne, kuma basa nan ga layin ba kowa balle mu tambayi wani".
Malam ya ce "Kunga dawowar nan tawa? Daga neman in da yarinyar take nake Hafsa, tun safe 'yan sanda suka tafi da ita, ba wanda ya san ina suka kaita, mahaifiyarta sai bulayi take tana neman ta, duk station É—in da taje sai ace bata nan, shine nima na É—au babur na zaga nima ban dace ba, gashi mu bamu san wani nasu ba, kowani tsayayyen namiji, balle muje tare a cigaba da nemansu, su kaÉ—ai suke zaune a nan"
Khalil ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, me Hafsa ta yi haka har da za a kamata? Yarinyar da babu ruwanta da kowa ya za ai ace tayi laifin da za a kamata?" Nan da nan fuskar Khalil ta sauya, ya harzuƙa matuƙa.
Abdul ya ce "Ka kwantar da hankalinka mana, yanzu ba kumfar baki ce abin yi ba, mota zaka É—auka muje division É—in unguwar nan, muje mu ji me zasu ce"
Da ƙyar Khalil ya kwantar da hankalinsa, Abdul ya karɓi tuƙin, suna tafe Khalil sai zufa yake duk da sanyin AC dake motar, ace an kama Hafsa tun safe, amma babu wanda ya san ina ma aka kai ta.
Kallon tausayawa Abdul yake wa Khalil, dan da alama ya faɗa soyayyar yarinyar nan da yawa, babban abinda yake fargaba shi ne yadda mahaifiyar Khalil zata karɓi batun auren Khalil da Hafsat ba.

Abdul na parking, Khalil ya buÉ—e motar da sauri, kamar zai faÉ—i ya shiga cikin station É—in.
Abdul ya ƙarasa kashe motar da hanzari, ya fito ya bi bayan Khalil, dan kar yaje yayi kataɓora.
Khalil ya yi sa'a D.P.O yana nan, aka yi musu iso suka shiga cikin ofishin DPO.
Bayan sun gaisa Khalil ya yi masa bayanin meke tafe da su. DPO ya ce "Gaskiya ba station É—in nan aka kawota ba".

Khalil ya ce "Ai a shiyyarka take, dan haka ka bincika mana in da aka kai ta"

Abdul ya ce "Haba Khalil, ka bi a hankali mana, ya kake magana a haka?"

"Bar shi yayi mini rashin kunya, yanzu in sa saka mini shi a cell".

Khalil ya ce "Ni zaka dubi kamata kace a sakani a cell, ai ko kisan kai nayi nafi ƙarfin sarƙa Wallahi"

"Shut up Khalil, meye haka wai?" Cewar Abdul da yake zarewa Khalil ido.
"Malam ka daina zare mini ido, kana ji zai raina mini hankali dan yana kan wannan kujerar" da ƙyar Abdul ya sa Khalil ya yi shiru, ya lallami DPO da ƙyar, sannan ya bincika musu in da aka kai Hafsa.

Tuni su Fadila sun fara jarrabawa, kuma ba ƙaramin ganin amfanin abin da Yazeed yake koya mata tayi ba, a sauƙaƙe take karatunta, kuma take rubuta jarrabawar ta cikin nasara.

A gobe ne zasu rubuta jarrabawar course ɗin da ta tsana, saboda bata ganewa, tana matuƙar buƙatar taimakon Yazeed, amma ba zata iya cewa ya koya mata ba, dan a ganinta idan tayi hakan ta faɗo. A haka ta tunkari ajinsu, ranar ba su da jarrabawa, wasu daga cikin ɗalibai ne suka shigo karatu.
Sassanyan ƙamshin turarenta ne ya shiga hancin Yazeed, wand ya saukar masa da wata irin nutsuwa ta mussaman.
Yana zaune cikin ɗalibai, yana musu tutorial, galibinsu mata ne, duk sun kewaye shi, ciki har da wata yarinya Azima, sai nanuƙar Yazeed take, shi kuma yana takure jikinsa, yana matsawa, kallo ɗaya zaka yi masa ka san a takure yake musu koyarwar nan. A hankali ya ɗaga idanunsa ya sauke su a cikin Fadila, da take tsaye tana kallonsa.

"ماذا حدث ىااختي"
Ya faÉ—a yana kallonta fuskarsa É—auke da murmushi.
A hankali ta janye idanunta, tare da lumshesu, ta nufi wurin da take zama, hakan ya so tafiya da hankalin Yazeed, dan ta ƙasan idonsa ya cigaba da binta da kallo, har taje ta zauna, saboda ba ƙaramin kyau ta yi masa ba, ta ɗanyi kwalliya yau, sai dai abin da bai masa daɗi ba shi ne yadda ta yi parking ɗin gashinta, ta fito da shi.

Captain ne ya kalli Fadila ya ce 'Babbar yarinya, irin wannan wanka haka kamar zaki gasar sarauniyar kyawawan Nigeria?" Harar captain ta yi ta basar, wani irin kishi ne ya kama Yazeed, amma ya danne ya cigaba da ƙoƙarin cigaba da abin da yake.

"Malam Yazeed wai ya ne, sai gaba muke kana dawowa baya?" Azima ta yi maganar tana ƙoƙarin taɓa shi.

Cikin sauri ya janye jikinsa ya cigaba da koya musu, sai dai lokaci lokaci ya kan É—aga kai ya kalli Fadila, da sun haÉ—a ido, sai ta harareshi ba gaira ba dalili.

Gaba ɗaya suka kasa gane kan Yazeed, hankalinsa yana kan Fadila. Haka ya ƙarasa musu ya tashi.
Azima ta ce "Aikin banza, wannan gayen ba shi da zuciya, da yaga yarinyar nan yayi ta rawar kai, tana wulaƙanta shi".
Amra da a baya ƙawar Fadila ce, amma yanzu ƙawancen na su ba sosai ba ta ce "Ke ina ruwanki to, tunda bake yake shigewa ba".

Fadila ta bar ajin, amma motarta na wurin da ta saba ajiyeta, haka Yazeed yai ta dubawa, har ya gano ta, tana zaune a wani wuri ita kaÉ—ai, tana waya.
Ba tsammani taga Yazeed ya zauna kusa da ita, wani irin shocking ta ji a jikinta, gaba ɗaya ta nemi nutsuwarta ta rasa. Bakinta ne ya hau rawa ta kasa cigaba da wayar da take yi, ta waiwayo ta kalli Yazeed, taga ita yake kallo gaba ɗaya jikinta ya ƙara yin sanyi, haka kurum ta ji wasu hawaye da bata san na menene ba suka taru a idonta, ga wani irin mugun kwarjini da yayi mata, wanda da bata taɓa sanin yana da shi, musamman kasancewar kusan kullum da facemask a fuskarsa, yau kuma ya cire, ga sajensa ya ƙara yawa, gashi ya ɗan tsare ta ido.
Yazeed ya yi murmushi ya ce "Gani naga kamar kina son ganina".

Kallonsa tayi ta sake haÉ—e rai. Kamar ba za tai magana ba ta ce "Ka matsa daga kusa da ni".

"Zan matsa, amma meyasa hannunki yake rawa, ko baki da lafiya ne?"

Ɓoye hannun tayi tana jin yadda jikinta ke cigaba da rawa, ba tare da tasan dalilin hakan ba.

"Fadila" ya kira sunanta.

"Kallonsa ta kuma yi, amma ta ji idanunsa sun yiwa nata nauyi a nata idon"

"Naga kina nema ne ne, shiyasa na biyoki nan".

"Ni ba nemanka nake ba" ta faÉ—a tana kauda kanta gefe daga kallonsa.

Yazeed ya ce "Ba nemana ki ke ba, amma kika tsaya kina kallona? Shikenan na ji, É—auko littafin in koya miki, kina son in koya miki abu, amma kin kasa gaya mini, ba ke kika ce in koya miki ba, ni nace zan koya miki, É—auko mu yi" Kallonsa tayi da mamaki, tana tunanin yadda akai ya san abin da ke ranta.

"Ba mamaki zaki tsaya yi ba, É—auko muyi abin da yakamata".

"Malam ka Matsa daga kusa da ni" ta faÉ—a tana haÉ—e rai.

Yazeed yayi murmushin sa mai ƙayatarwa ya ce "Ko na matsa ba zaki daina jin abinda kike ji ba, kuma hannunki ba zai daina rawa ba, amma gashi na matsa, kawo littafin in ga me kika karanta a kan course ɗin".

Miƙewa tsaye tayi ta ce "Dan Allah malam ni ka ƙyaleni, sai kace dole, ka fita daga harkata kar ka sake zuwa in da nake, bana buƙatar taimakon naka, ni ai bance maka ina son ka koya mini abu ba".

Shima ya miƙe tsaye ya ce "Am sorry, Allah ya baki haƙuri, na yi miki shishshigi, ba zan sake ba insha Allah"

Jakarta ta É—auka tai gaba, tana cigaba da yadda jikinta ke tsuma kamar wadda tai artabu da aljan.

Cikin ikon Allah su Khalil suka gano in da aka kai Hafsa, tun safen nan ba ta ci komai ba, sai kuka da take yi, kuma taƙi magana, fuskarta duk tayi jawur saboda kuka, an rufeta a ceil.
Chapter 32 · 0% Book details