← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 84

Sashe 4

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

********
Abun duniya ya saka Amina a gaba, yau saura kwanaki uku ya rage, a rufe karɓar kuɗin jarrabawar su, gaba ɗaya ta sare, ta san Baba ba shi da kuɗin nan ne, dan da akwai su da tuni ya aiko mata da su.
Gefe guda baba Rabi'u ya uzzurawa rayuwarta da takura, akan Lallai sai ta amince da shi, ta yadda ya aureta.
   Fafur ita kuma ta ce ko maza sun ƙare, ba zata auri tsohon da bai san darajar mace ba, balle 'ya'yan da yake haifa.
Ga matsin lamba na gidansu, daga ɓangaren 'yan uwan mahaifinta, na takura da aike saka ta aiki kamar baiwarsu, ga gore-gore, har da sharrin yawon banza ta ke yi a gantalin makarantar bokon da ke yi.
Hakan ya haifarwa Amina shiga cikin matsananciyar damuwa, da tunani daban-daban a cikin ranta.
  

     Baba Hassan kuwa, ya yanke shawarar kiran maigidan a waya, wato baban Fadila kasancewar ba ya gari, ya roƙi Alfarmar ko a cikin albashinsa ne, a taimaka a bashi rancen kuɗin da zai biyawa 'yarsa kuɗin Makaranta.
Haka kuwa aka yi, ya kira maigidan ya sanar masa da halin da yake ciki, da buƙatar da yake da ita, ba tare da wani ɓata lokaci ba ya ce masa 'Zai kira Hajiya a waya ya sanar mata, ya je ya karɓa kawai a biya mata'.
Baba Hassan ya yi farinciki matuƙa, yayi ta godiya da karamcin Alhaji Ahmad, sai dai yadda zai tunkari Hajiya Zainab da maganar kuɗin kawai yake tunani, saboda rijiya ta sha bada ruwa guga ya hana a gidan nan.
Ƙiri-ƙiri mai gidan zai yi alheri ta hana, ko ya ce ayi taƙi yi, kusan duk me son wani abu agurinsa sai ya biyo ta hannun hajiya Zainab, idan kuwa ka na son abun a gurinta, sai ka ƙasƙantar da kanka tamkar bawa, ta gama wulaƙantaka kafin ka samu.

AMINU KANO, INTERNATIONAL AIRPORT.

Tafiya yake sannu a hankali, yana jan wata 'yar madaidaiciyar Akwati, hannusa É—aya É—auke da wayarsa ya kara ta a kunnensa yana tsumayin a É—aga wayar da yake kira.

A É—an hasale ya fara Magana "Wai dan Allah kana ina ne? Na sauka fa ina sauri inje gida, ni da nasan haka zaka yi mini, da babu abun da zai sa in ce kazo ka É—aukeni" Yana gama maganar, ya sauke wayar zuwa cikin aljihunsa, yana jan guntun tsaki.

Sannu a hankali ya cigaba da tafiya, ba tsammani ya ji an ce "To shugaban masu haƙuri, ina daf da kai fa, amma ka kirani kana ta wannan masifar haka" Ya kalli Matashin da yake maganar ya ce "Dalla ware malam, kana sane ma ka shanyani kenan? Dana sani gida na yi waya azo a ɗaukeni".

Matashin yayi murmushi ya ce "Kai dai can da yawarka, masifaffe kawai, bani in tayaka É—aukar jakar".

Ba tare da ya ce masa komai ba, ya sakar masa akwatin, yayi gaba abunsa.

Suna tafe a mota, ba wanda yake magana a cikinsu, can É—ayan ya kalli abokin tafiyar tasa ya ce "Haba Khalil, ka É—an yi murmushi mana, ko har yanzu fushin ne?"

"Ban sani ba, ni dalla ka ƙara speed ɗin motar nan, mu yi muje gida".

"Ba zan ƙara ba, in ban sauke ka a titi ka hau Napep ba ba sunana Abdul ba"

Khalil ya ce "Saboda na hau motarka ka ke mini rashin mutunci?".

"Eh, uban waye ya sa ka kirani? na zo na taimaka maka amma kana mini wulaƙanci".

Jinjina kai Khalil Yayi ya ce "Good".

A bakin gate É—in gidansu Khalil Abdul yayi parking, ya kalli Khalil Ya ce

"Mun zo sai ka sauka".

"Wai a nan zaka ajiyeni?".

Abdul Ya ce "Au ban maka ba? Wai kai mai yasa ba a iya maka ne? Ware Malam"

"Wallahi zaka gane ba ka da wayo, zan zo har gida in maka rashin mutunci"

Abdul ya ce "Rashin mutunci yau ka fara yi mini? dalla fita".

Ƙwafa kawai Khalil yayi, ya fice da ga motar.

Asabe ce ta shiga ɗakin Fadila, za ta gyara mata, tana gyaran tana mita ƙasa-ƙasa saboda yadda Fadila ta ke watsar da komai a ɗakin yadda ta ga dama. Hatta kwano sai ta ci Abinci ba zata ɗauke ba sai an ɗauke mata. "Dan Allah kalli ɗakin nan kamar sheƙar mahaukaciya, yarinya ta na mace amma ba ta san gyara ba, saboda tsabar sangarta da iskanci, ɗan kanfai ma, sai da ta saka ta tara sai mun wanke mata, Aikin banza kawai" haka Asabe ta cigaba da tattare shirgin da Fadila ta tara a ɗakin na ta, ta gyara ta wanke mata banɗaki, tare da wanke mata ƙananan kayanta da ta tara a cikin bokiti a banɗaki".

Asabe na kammalawa ta fito falo, ta tarar da Fadila ta na kallo, a wulaƙance Fadila ta kalli Asabe ta ce "ki cewa wannan wadda ku ke aikin tare, meye sunanta Hajara kowa? Za ta bar uwarta da yunwa ne, kamar yadda ta yi mini? Ta bar ni ina jiran ta kawo mini Abinci amma shiru".

Asabe ta risuna ta ce "zan gayamata insha Allah".

"Kar ki kuskura ki sake zuwa gabana da wannan ƙazamin hijjabin, ba kya jin yadda yake wari ne?"

Wani irin haushi ya kama Asabe, amma haka ta dake ta ce "To insha Allah"

Asabe na zuwa ɗakin girki, ta tarar da Hajara na ta ƙoƙarin haɗowa Fadila Abinci, ta kalli Hajara ta ce "Ance idan uwarki ce za ki bar ta da yunwa?"

Hajara ta kalli Asabe ta ce "Kamar yaya?"

"Kamar yadda aka ce in gaya miki"

Jiki a sanyaye Hajara ta ce "Allah ya bamu abun yi mu bar aiki a ƙarƙashin mutane marasa mutunci irin wannan, tun da na shigo gurin nan fa aikin Abincin nake"

"Hmm, ke dai bari, ni kaina na gaji, da ina da wata hanyar samun kuÉ—in, da tuni na bar gidan nan".

Haka suka cigaba da tattauna matsalolin gidan aikin nasu.

Bayan saukarsa daga motar Abdul, gate ɗin gidan ya nufa, ya na zuwa ya tura ƙofar gate ɗin ya ga ta buɗe.

Baba Hassan ya taso yana faÉ—in "Waye a nan?"

"Baba ni ne" Khalil ya furta a hankali.

Murmushin fuskar Baba Hassan ya faÉ—aÉ—a da yaga Khalil ya ce "Kai ne da zuwa haka ba sanarwa? Maimakon ka kira a zo a É—auke ka".

"Bakomai Baba, Abdul ne ya ɗakko ni na same ku ƙalau?".

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya aikin?"

"Aiki Alhamdilillah".

Baba Hassan ya ce "bari in kai maka jakar"

Khalil ya ce "A'a ka bar shi Baba, na gode, kayi zamanka"

Khalil ya nufi cikin gidan.

"Oh my God Mummy brother" Fadila ta faɗa da ƙarfi, tana maƙalƙale Khalil.

Tureta Khalil yayi ya ce "Ni cikani kar ki kada ni".

Mummy ce ta fito tana faÉ—in "Au, ashe da gaske kike, wane irin zuwa ne wannan ba sanarwa a safiyar nan, kamar korarre?"

Khalil yayi murmushi ya ce "Mummy kullum idan zan shigo kuma sai na faÉ—a?".

"Ahh ai sanarwar yana da kyau, amma dai ba wannan babur ɗin ɗan sahun ka hawo ka dawo gida ba ko? Kar kasa maƙota su mana dariya"

"Mummy kenan, Abdul ne ya É—akkoni daga filin jirgi".

Fadila ta tura baki ta ce "Sai murna na ke ka dawo, amma ko kallo ban isheka ba".

"To zan É—auke ki ne ina ihu nima?"

Mummy ta ce "Amma yadda ta damu da kai É—in nan, ai yakamata kaima ka nuna mata ka damu da ita".

Khalil ya ce "waye zai damu da wannan fitsararriyar? Bari in tafi É—akina in É—an watsa ruwa in huta".

Mummy ta ce "Bari a saka masu aikin nan su gyara maka, na san yayi ƙura, tun da saukar safe kayi, akwai sauran kayan karin kumallo, sai ka karya"

Ya ce "Ok shikenan".

Ya tashi ya tafi dining, ya zuba abinci yana ci, Fadila sai surutu ta ke masa".

Zuwa ƙarfe huɗu na yammaci, Khalil ya shirya cikin ƙananan kaya ya fice, da ƙudurin tafiya gidan su Abdul ya je ya ƙare masa rashin mutunci.

Yau kwana guda, da Baba ya roƙi Alhaji Ahamad kuɗin da zai biyawa 'yarsa kuɗin jarrabawa, kuma ya bashi damar ya karɓa a gurin matar gidan, amma sanin halinta ya sanya shi a fargabar yadda zai tunkare ta da wannan maganar.
Amma a rashin tayi akan bar arha, dan haka ya yanke shawarar zuwa ya nemi Alfarmar, ko Allah yasa ya dace.

Jiki ba ƙwari, ƙasan zuciyarsa yana Addu'a, ya tunkari babban falon gidan.
Da sallama ya shiga falon, sai dai duk da girman nan nasa da shekarunsa, baya hana shi shiga fargaba, idan har yayi tozali da Fadila, saboda gudun tozarci da wulaƙanci, kamar yadda ta kasance yanzu, ya tarar da ita hakimce a falon tana aikin na ta, na danna waya wanda a shi tafi ƙwarewa, danna waya kallon talabijin kai lomar Abinci sai kuma bacci da tarin rashin mutunci.

"Barka da yamma ranki ya daÉ—e" Baba yayi Maganar yana risunawa.
Ba ta É—ago ta kalleshi ba ta amsa sa da 'Yawwa'.

Ya É—an yi shiru sannan ya ce "Dan Allah hajiya fa".

"Tana sashinta".

'Dama Alhaji ne ya aiko ni gurinta".

"Sai ka zauna ka jirata, sai ta fito".

Bai ce komai ba, ya rakuɓe a falon, yana rarraba ido.

Fadila ta kara waya a kunneta tare da faÉ—in "Uwar bacci, tun É—azu na ke kiranki a waya, amma shiru ba kya É—agawa, dama ce miki zan Brother ya shigo gari fa, gara ki shirya ki bayyana".

"Girl are you serious?".

"Amma kin san bana miki wasa a irin wannan lamarin ko".

"Wow, Alhamdilillah aikuwa zaki ganni yanzun nan" suka yi shewa a tare, sannan suka yi sallama.

Baba Hassan tun yana zaman da marmari, sai da ƙafafunsa suka yi sanyi, ya gaji sosai, dan a ƙalla ya kai awa guda a zaune.

Ba tsammani sai ga Hajiya Zainab ta fito, ita ma É—auke da waya a kunnenta.

Ta zauna ta cigaba da wayarta, ba tare da ta saurari in da Baba Hassan yake zaune ba, hirar kasuwancinta kawai take yi, tare da ambaton Manyan kuÉ—aÉ—e a cikin wayar.

Sai da ta ƙare wayarta sannan ta kalleshi ta ce "Malam lafiya ka shigo mini falo ka ƙwafe haka kamar ana zaman fada?".
Chapter 4 · 0% Book details