Sashe 84
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
"Ko ba zaki zo bane, kika cake a wurin kina kallona?" Amina ta jingine Akwatin, ta zo tsakiyar falon, ta kwashe kwanukan ta kai Kitchen, ta zo kuma kwashe sauran, Mummy ta kuma kallonta ta ce "Idan kin gama, na fito da labulaye na barsu a kan gado, zaca cire na part É—ina gaba É—aya a sanya wannan, Carfet É—in bedroom É—ina ma, zaa a canza wani, wannan fita da shi za ai, Zakiru ya kai shi Car wash.
Amina kawai ta jinjina kai ta tashi, ta kai kwanukan ta dawo ta ja Akwatinta.
Hajara ce ta fito daga É—akinta, sanye da hijjabi alama salla tayi, ta washe baki tana faÉ—in "Amina ashe kin dawo ya hanya?"
"Lafiya lau Hajara, ya aikin?"
Hajara ta kwaɓe fuska ta ce "Aiki gashi nan, kin tafi kin barni, matar gidan nan da alama akwai abin da yake damunta, kullum cikin sauke mini kwandon bala'i take, da na motsa sai hantara, haka ita ma 'yar ta ta, kai wanan masifa ni Hajara wanan mutane kamar gadonta suka yi"
Amina ta ɗan taɓa baki ta ce "To Allah ya kyauta".
Hajiya Turai ce ta kalli Hajiya Zainab ta ce "Ita kuma wannan 'yar aikin taki daga ina na ganta da uwar akwati?"
"Wai nan ƙauye ta je"
Turai ta ce "Ni fa gani nayi tana wani ƙara kyau"
"Ke ni bar ni da zancen banza, Hajiya Salma, ya batun yarinyar nan da kika ce in haɗata da Khalil, da wuri zan duk abin da ya dace, kan ya lallaɓa ya koma wurin waccan shahshashar ban sani ba"
Hajiya Salma ta ce "Karki damu duk ranar da kika shirya, ki zo muje kiga yarinyar"
"Allah ya kaimu jibi, zan zo muje"
Amina ta shiga aikin canza labulaye, kamar yadda Hajiya Zainab ta umarce ta, Amina ba ta gama aikin nan ba sai bayan sallar isha'i, gaba É—aya ta gaji.
Kasancewar tafiyarsu ta ƙarato, ya sanya Amina ta duƙufa cigaba da bitar karatun da tayi, ana sallar isha'i, ta shige ɗakinta, hatta Abinci a ɗakinta ta ci.
Wajen sha ɗayan dare ta ga kiran Daddy, ta ɗaga ta saka wayar a handsfree taƙi magana.
A hankali ya ce "Meenalin Daddy"
"Na'am"
"Au na zaki kulani ba, ki ka É—aga wayata ki ka yi shiru?"
"Ai kaima watarn haka kake mini"
"To naji, zan samu tea?"
Amina ta É—an tura baki ta ce "Ni gaskiya a gajiye nake, daga dawowata aka sani canza labulaye da Carfet, da nayi niyyar ko girki na yi maka, amma ko akwatina ban ajiye ba aka sani aiki"
"Waye ya saki aikin?"
"Ai kai ma ka sani"
"To shikenan naji, da safe idan Allah ya kaimu, ki mini girki kin ji Meenalina, am missing your delicious food, kuma kinga kin fi kowa sanin Abincin da ya dace da ni"
Ta yi wani murmushi kamar tana gabansa ta ce "I Will in sha Allah"
"Ranar Wednesday zaku tafi, so ki cigaba da shiri, idan da wani abu da kike buƙata ki sanar da ni"
"Eh, abu É—aya nake so"
Cikin zaƙuwa ya ce "What it is?"
"Your presence their" tayi maganar a shagwaɓe.
"Rigimar ce ko, sai da safe" ya kashe wayar. Ajiye wayar tayi tana cigaba da mita, ta mayar da hankali ga karatunta.
Cikin rashin samun mafita, da rashin karsashi Khalil ya kira Mummy a waya, sai da ta kusa katsewa sannan ya samu ga É—aga.
"Yau ka ga dama ka neme ni kenan?" Yaji muryarta maimakon ko gaisawa ta bari suyi.
A saɓule ya ce "A'a ba haka bane, bani da lafiya ne"
"Eh, ko ba baka da lafiya ba? Kana fama da ciwon so ko, gubar Asirin da suka zuba suka baka a Abinci bata sake ka ba, to ka sani in kai sun shanye ka ni basu shanye ni ba".
"Mummy dan Allah duk a bar wannan maganar, ni kiranki nayi na gaisheki"
"Ka riƙe gaisuwarka bana so, jibi in Allah ya kaimu zanje naga iyayen yarinyar da na zaɓa maka, next za a kai kuɗin Aurenka da ita"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, dan Allah Mummy kar ki mini haka"
"Ai tuni ma an riga an yi, idan ka ga dama kayi mini biyayya, idan ba ka ga dama ba kabi 'yar matsiyata mai awara a hanya!!
AYSHERCOOL
08081012143