Sashe 26
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sati ya shuÉ—e kusan kwanaki takwas, Yazeed bai dawo Makaranta ba, gaba É—aya hankalin Fadila a tashe yake, dan ba wanda ya san gidan su Yazeed balle a samo information akan halin da yake ciki, gashi wayarsa ba ta shiga sam.
Fadila Addu'a take, da fatan Allah ya sa ba mutuwa yayi ba, dan da ƙyar in ta tambayi malamai ba a ce tayi azumi sittin ba, saboda abin da ta aikatawa Yazeed, dan da gayya ta balbale shi da hayaƙi da kuma ƙura, duk dan ta muzguna masa.
Yau Saturday, kuma suna gaf da fara exams, dan haka akwai lecturer da ya ce, lallai su shiga Saturday, dan bai yi covering course É—insa ba.
Jiki a sanyaye take tafiya dama gashi ta makara, dan ƙarfe goma ya ce aje, yanzu kuma sha ɗaya saura mintuna goma sha biyar, haka ta tunkari ajinsu tana fatan Allah ya sa malamin ya bari ta zauna, tuni har malamin ya fara lectures, Allah ya taimaketa bai koreta ba. Tun da ta shiga ajin ya ƙura mata ido, ɗaga idon da za tai suka yi ido huɗu da Yazeed. Gabanta ne ya faɗi ganin yadda yayi wata muguwar rama, sauke facemask ɗin sa yayi, tare da yi mata murmushi, gaba ɗaya ya rame sosai, sai dogon hancinsa da ya sake fitowa.
Tsuke fuska tayi, ta basar kamar ba ta ganshi ba, ta nemi wani wurin ta zauna, tare da É—auke kanta da sashen da Yazeed yake.
Sai dai lokaci lokaci ta kan kalleshi, tare da sake tabattarwa da kanta yayi rashin lafiya sosai.
Haka aka gudanar da lectures É—in aka gama, aka yi Attendance.
Da yawa ɗaliban zasu zauna ne a school, suyi karatu, saboda gabatowar exams, wanda ita ma Fadilan ta yanke shawarar ta zauna ta yi karatu, dan idan taje gida bacci zata yi, sai dai kafin nan akwai buƙatar ta ɗan samo abun motsa baki, da zai ɗebe mata kewa yayin karatu.
Bayan tafiyar malamin daga aji, akai ta yiwa Yazeed ya jiki.
Fadila tana ta hanzari ta tunkari motarta, ta saka key tana ƙoƙarin buɗewa ta ji an kira sunanta "Fadila" waiwayawa tayi, taga Yazeed a bayanta.
Cikin murmushinsa da ya zame masa É—abi' ya ce "Kina lafiya?"
Ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Lafiya ƙalau".
"Dama na ce bari in zo in sake yin godiya ne, game da taimakon da ki ka yi mini, na gode sosai Allah ya bar zumunci" Wata uwar harara ta watsa masa, ta buɗe ƙofar motar.
"Au ashe fa ni mai laifi ne, na manta a ranar na ɓata miki rai, kiyi haƙuri dan Allah, naga baki ji daɗin abin da nayi ba".
"Ashe kana sane kai min abin da kayi mini ko?" Tayi maganar tana hararasa.
"Ai nace kiyi haƙuri ban kyauta ba"
"Kaji da shi" tayi maganar tana ƙoƙarin shiga mota.
Cikin harshen larabci Yazeed ya ce
"هل يمكنني Ø§Ù„ØØµÙˆÙ„ على jotter الخاص بي"
(*Can i have my jotter*)
Kallonsa ta yi saroro, ba tare da ta gane me yake faÉ—a ba.
Ya kuma maimaita mata abin da ya faÉ—a. Tsaki tayi ta ce "Malam speak what I can understand".
Wani irin ƙasaitaccen murmushi Yazeed ya yi ya ce "Ni kuma gashi ban iya turanci ba, amma dai ina roƙon ki bani jotter ta ne, zan ɗan kwafi lectures da na yi missing, ance mini suna wurinki"
Tura baki tayi, tana wani basarwa, ta fara duba jakarta, ta zaro jottersa da bironsa ta miƙa masa.
Sansana jotter ya yi ya ce
Ø±Ø§Ø¦ØØªÙ‡ جميلة
(
*It smells nicely*)
Ƙaramin tsaki ta ja tana kuma ƙoƙarin shiga mota.
Riƙe ƙofar motar yayi ya ce "Malama kayana da saura" kamar ba shi yayi Maganar ba, ya wani basar, dan ba zaka taɓa cewa yana magana haka ba.
"Ban gane ba" ta faÉ—a tana kallonsa.
"Ina kuÉ—ina?" Ya faÉ—a ransa a haÉ—e.
"Hamsin ɗin?" Ta faɗa a wulaƙance.
Yazeed ya ce "Eh ai tawa ce ko?"
Tsaki tayi ta saka hannu a jakarta ta É—auko É—ari biyar ta ce "Ungo".
"Ni tawa nake so, amma dai shikenan na bar miki, ki zo muje muyi karatu tare, ki koya mini abin da aka yi bana nan, sannan baki mini ya jiki bama, kin kusa halaka É—an marayan Allah, ni yakamata ma ki gaya mini laifin da na yi miki kika tsane ni haka".
"Dan Allah ka bani wuri in tafi, ka tsayar da ni kana ta mini surutan banza".
"Subhanallah, yi haƙuri na takura miki, shikenan ki gaida gida" ya matsa ya bata wuri, ta shige motar ta, ta sauke glashin ta ce "Ka matsa kar in tada ƙura ka kama sumewa mutane".
"Idan na suma ma in dai kina nan ai ba damuwa" hararsa tayi, ta bawa motarta wuta ta wuce ta bar wurin.
Shi kansa Yazeed bai san yadda aka yi ya tsinci kansa, da ƙoƙarin tsawaita hira da Fadila ba, dan a rayuwarsa kusan shi mutum ne mai tsoron duk wani abu da zai haɗa shi da mata.
Sake shanshana jotter yayi, sai ƙamashin turaren Fadila take, ya fara bubbuɗewa, kawai ya ci karo da rubutun da ba nasa ba, kusan duk lectures ɗin da aka yi baya nan, ta rubuta masa a ciki.
Zubawa Jotter ido yayi, a hankali ya ce "Allah ya sa ki fara jin abin da nake ji a kanki" can kuma ya ce "Subhanallah, ba ajina bace" shikaÉ—ai yake wannan surutan, daga baya kuma ya ja jiki ya nufi masallaci.
Amina ta gama aikinta tsaf, ta zauna a falo tana karatu, Hajiya Zainab bata nan, Hajara kuma ta tafi yin sayayya.
Turo ƙofar falon aka yi, Amina ta waiwaya, taga baƙuwar fuskar da bata saba ganinta ba.
Yusra ta ce "Ina mutan gidan kuwa, naji kamar ba kowa?"
"Sun je Islamiyya a koya musu sallama, da yiwa wanda suka tarar sannu" Amina ta bata amsa.
"Ke, wacece ke kika gaya mini wannan maganar?"
"Ahh musulma mana Hajiya, ai a koyarwar addinin musulunci idan ka zo wuri da sallama kake farawa, kuma ka yiwa na zaune sallama, amma kawai kya shigo kanki tsaye ki hau Magana. Bisimillah shigo amma dai nan gaba ba a haka" saroro Yusra ta bi Amina da kallo, dan ba su taɓa haɗuwa ba sai yau.
Ƙoƙarin ƙarasowa cikin falon Yusra take, amma Amina ta miƙe ta ce "Hajiya ba fa banɗaki zaki shiga ba, ya zaki shigo mana da takalmi falo, ciresu a nan wurin ki ƙaraso" Yusra cire takalman tayi tana kallon Ikon Allah wurin Amina, dan ba ta san matsayinta a gidan ba.
Yusra ta zauna, Amina kuma ta wuce kitchen, ta haÉ—owa Yusra ruwa da lemo, ta kawo gabanta ta ajiye mata ta ce "Ga ruwa ki sha, 'yan gidan basa nan, idan kuma zaki ci Abinci ne ki faÉ—i wanne zan dafa miki? Dan an cinye na rana, na É—an gidan nan ne kawai ya yi ragowa"
Sai yanzu Yusra ta gane matsayin Amina, a ranta ta ce 'Ina Mummy ta samo wannan tantiryar mara mutuncin 'yar aiki? Ka rashin kunya ga karrama mutane'.
"Ba Abinci na zo ci ba, ai ban miki kama da mai jin yunwa ba"
Dariya Amina ta yi ta ce "Haba Yayata,. Idan a jiki ake gane yunwa ko rashinta, ai cewa za ai baki taɓa cin abinci ba ma" ai gaba ɗaya Amina ta kashewa Yusra bakin Magana.
Ƙamshin turaren da ya karaɗe falon ne, ya sanar musu da zuwan Khalil, sai dai tun kan ya shigo, Yusra ta rasa nutsuwarta.
Kansa tsaye ya shigo, da sallama iya wuyansa wadda shika É—ai yaji kayarsa, jiki na rawa Yusra ta risuna tana gaishe shi. Amma ya amsa ba yabo ba fallasa, haka ya shigo falon da takalmansa, sai da yaje dining ya ajiye takalman a kan step É—in dining É—in.
Amina kuwa ta ƙulu, saboda yadda ya biyo har ta kan carfet da takalmansa, a fusace ta miƙe taje ta kwaso takalman Khalil ta je ta watsa su waje tana mita cike da tsiwa "Ai ni ba baiwarku ba ce da zan dinga aiki kuna takawa, sai na sake!"
SHARE PLEASE
GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143
P12
Sai da ta watsa takalman waje ta dawo falo, ta lura da yadda duk suka bita da kallo, mussaman Khalil da ya ke mata Wani irin mugun kallo, sai a lokacin ta sha jinin jikinta ta gano ta yi wauta.
Ɗan marairaicewa ta yi ta ce "Dan Allah kayi haƙuri ba dan halina ba, na gaji ne sosai yau na sha aiki, bayana har ciwo yake, na canza wancan carfet ɗin na bayar wanki, na saka sabo wankakke kuma ka taka mini da takalimi ai kaga ba zan ji daɗi ba, aikin da wahala, dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba".
Rai a haÉ—e ya ce "Ke na fuskanci ba ki da kunya ko? Tun ranar farko da na fara ganinki a gidan nan na fuskanci haka".
Amina kamar zata fashe da kuka ta ce
"To ai na ce kayi haƙuri, ba zan sake ba insha Allah, kuma rashin kunya ba halina ba ne, ba zan sake ba kayi haƙuri"
"Rufe mini baki malama, ki ɓace mini daga nan wurin 'yar ƙauye mara kunya kawai"
Amina ta juya baya ta murguÉ—a masa baki, tana yatsina baki a ranta ta ce "Ko ba komai, na faÉ—i abin da ke raina, ba zaku mayar da ni baiwarku ba"
Yusra ta jinjina hali irin na Amina, yarinyar akwai iya nuƙufurci, yanzu za ta maka laifi, kuma ta nemo abin da zata goge laifin nata.
Ta ɗan ƙurawa Khalil ido da yake zaune yana cin Abinci, cikin son lallai sai ya kulata ta ce "Yaya Khalil ita ma wannan maid ɗin Mummy ce?" Ba tare da ya kalli in da Yusra take ba ya ce "Me ya hana ki tambayeta tun tana nan?"
Yusra ta ji haushin amsar da ya bata, amma ta haÉ—iye ta tsuke bakinta, tana cigaba da satar kallonsa.