Sashe 82
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mummy ta zauna a kusa da Fadila ta ce "Ke, wata shwara Hajiya Salma ta bani a kan Khalil, kuma ina ga hakan zan yi, dan in nuna masa kuskurensa"
"Shawarar me kenan?"
"Ai da Abujan zanje in ga halin da yake ciki, ya É—au gaba dani ko gaisheni baya yi sai ya ga dama, shi ne Salma ta ce in rabu da shi, kawai in nema masa aure sai dai in ce ya dawo ga mata"
Fadila ta kalli Mummy ta ce "Kuma kina ganin hakan mai yiwuwa ne?"
"Me zai hana shi yiwuwa? Hakan ne kawai zai sanya in yi maganinsa, kuma in raba shi da waccan yarinyar da ya É—ora ransa a kanta".
"Gaskiya bai kyauta ba sam, nima ko magana nayi masa sai ya ga dama yake kulawa, amma kar ki aura masa wadda baya so ya wahalar da 'yar mutane a banza, kin san halinsa".
"Shi ya isa, zan nemo masa yarinyar wadda ta dace da shi, ba wannan shiriritar gayyar tsiyar da ya kwaso ba"
Fadila ta ce "Shikenan, Allah ya sa a dace".
Hajiya Zainab ta amsa da "Ameen"
Æangaren Hafsa kuwa, sayar da Æ™osai suka koma yi a cikin gida, da kayan su maggi da kayan kaÉ—in miya, Hafsa tayi iya Æ™orainta ta cire Khalil daga ranta, amma abun ya gagara, a zahiri ta cigaba da sabgoginta, tare da nuna komai ya wuce, sai dai walwalarta ta ragu sosai tana ta dannewa dan kar Mama ta gane tana cikin damuwa, sai dai ita kanta Maman ta damu sosai da rabuwar ta su.
Har zuwa wannan lokacin, Hafsa ba ta daina ɓuya tayi kuka ba, saboda ba ƙaramin so take yiwa Khalil ba. Dan har a yanzu wasu lokutan ji take yi tamkar ta mayar da layinta ta kirashi, amma sai ta fasa ta cigaba da danne abin a zuciyarta, tare da miƙa lamuranta ga Allah.
Washegari jama'a basu fasa cigaba da zuwa ganin Amina ba tare da yi mata sannu da zuwa ba, wajen ƙarfe goma na safe tayi wanka ta kintsa, ta cewa Inno zata je makarantar bokonsu, ta gayar da malamanta na makaranta.
Inno ta amince, Amina ta shirya ta tafi makarantar.
Malamanta sun ji daÉ—in ganinta, Malam Sunusi ya ce "Amina, sai wayar gari muka yi muka samu labarin wai kin gudu, kwatsam na haÉ—u da mahaifinki a kasuwa ya ce ai kina can wurinsa a birni"
Amina ta ce "Wallahi Sir a lokacin nan bani da wani zaɓi da ya wuce in gudu wurin mahaifina, Auren dole 'yan uwan babana za suyi mini a lalata mini karatuna, ni kaina ba a son raina na tafi ba, amma ina can wurin Babana"
"To Masha Allah, ya karatun naki, yace mini kin cigaba da karatunki"
"Eh sir na cigaba, ni shekara mai kamawa in Allah ya yarda zan gama Sakandire"
Nan malaman suka yi ta saka mata albarka tare da yi mata fatan sa'a da nasara.
'yan ajinsu duk babu, wasu sun yi Aure wanda Allah ya taimake su kuma sun cigaba da karatun.
Sai wajen azahar Amina ta baro makarantar, ta nufi gida, sannu a hankali take tafiyarta sam bat jin zafin ranar nan, duk da akwai nisa a tsakaninsu da makarantar, amma bata damu ta hau abin hawa ba, a ƙafa ta tafi tana tafe tana tunanin abubuwan da suka faru a baya.
Sautin ƙarar wani akwalan babur ne ya cika mata kunne, tana ƙoƙarin kaucewa babur ɗin amma burki ya ƙwacewa mai baburin ji kake gauuuu!!
AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA
       BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL
45
Gafe Amina tayi da sauri, shi kuma ya daki bishiya, ya kusa hantsilawa, Allah ya taimake shi bai faÉ—i ba, ya saki baki ya bi Amina galala da kallo "Amina" ya faÉ—a cikin mamaki.
HaÉ—e rai Amina tayi ta ce "Wannan wane irin abu ne, da ka bugeni fa shikenan ka cuce ni?"
"Haba Amina, ai kya bari mu gaisa, dama da gaske kin dawo garin nan, Allah mai iko"
"Kaga Jarmai, babu ruwanka dani dan Allah, ka fita daga harkata"
"Haba Amina, ki tsaya muyi magana mana"
Wata uwar harara Amina ta watsa masa ta ce "Muyi magana kace mini me? Da ka nemi jefa rayuwata cikin masifa"
"Amina ai shi masoyai ba zai taɓa zama maƙiyi ba"
"Can da yawarka, ai ni ban taɓa sonka ba, kuma ba zan ba ka fita daga harkata na gaya maka".
Ta juya ta cigaba da tafiya, hawa baburinsa yayi ya cigaba da binta, amma tayi masa banza kamar da dutse yake ba da ita ba, a haka har suka iso cikin gari, sai da ya bita har gida, amma ko É—aga kai bata kuma yi ba, balle ya sanya ran zata saurareshi.
A tsakar gida ta tarar da Inno tayi alwalar sallar azahar.
"Amina ina kika tsaya haka kin daÉ—e?"
"Ina makaranta, na tsaya wurin su Malam Sunusi na taho hanya wannan Jarman ya kusa bugeni da babur har ƙofar gidan nan ya biyoni yana mini magana, wai in saurareshi"
Inno ta jinjina kai ta ce "Lallai Jarmai ba shi da kunya, kinga yadda ya dinga yiwa su Baffa Bala zarya, yana neman ya kai su ƙara, suka ce ya bari idan aka ganki zasu ba shi ke, ya ce ko kyauta suka bashi ke ba zai karɓa ba, wai kin tafi yawon duniya"
Amina t girgiza kai ta ce "Allah ya rabani yawon duniya, yaje aniyarsa ta bishi"
"Kije kiyi salla, ki zo ki ɗibi Abinci, nayi waya da babanki a kan kayan nan da aka kawo, ya kira wayarki amma kin barta a gida, ya ce a ɗebarwa maƙota ma"
Amina ta ce "Na manta da wayar ne, a É—ebar musun, bari in yi salla"
"Aikuwa ana ta kiranki a wayar, ni dai ban iya É—agawa ba haka na barta"
Amina ta ce "Idan nayi sallar na duba waÉ—anda suka kirani, na san ba zai wuce Daddy ba".
Tun ranar da Kankiya ya kori Yazid daga aji, bai kuma zuwa ba, Fadila dai ta gaji ta sake kiran wayarsa, cikin sa'a taji ta shiga, sai da ta kusa katsewa sannan ya É—aga kiran.
"Assalamu alaikum"
Ta amsa da "Wa'alaikum salam warahmatullah, Yazid"
"Na'am" ya amsa yayi shiru.
"Kana jina?"
"Eh ina ji"
"Fadila ce"
"Na gane, ina jinki" taji haushin amsar da ya bata, amma ta basar ta ce "Ya jiki?"
Ya ce "Jiki Alhamdilillah, da sauƙi sosai"
"Naga baka kuma zuwa school ba tun ranar, shine na yi zaton ko jikin ne haryanzu".
"Hmm in zo saurayinki ya kuma korata, jikin ne ban gama warkewa ba, wurin da aka mini aikin yana ciwo, likita ya ce in zauna a gida, ina ga sai lokacin exams zan shigo"
"To Allah ya baka lafiya, tun lokacin da ka daina zuwa na sanarwa HOD in sha Allah duk zaka yi exams É—inka ba wata matsala"
Yazid ya ce "Masha Allah, na gode sosai"
"Amma ka bani direction É—in gidanku, ko Asibitin da kake, zan zo in dubaka"
"No, unguwarmu ta talakawa ce sosai, idan kika ce zaki zo, motarki zata iya ɓaci, kuma ba zan so in wahalar da ke ba, na gode sosai"
Jiki a sanyaye ta ce "Ba damuwa ka gaya mini in zo"
Ya girgiza kai ya ce "Kar ki damu, hakan ma na gode sosai, sai anjima" ya katse kiran. Ta sauke wayar daga hannunta tana bin wayar da kallo.
Haryanzu Khalil yana fama da ciwon kai mai zafi, duk da yana ta ƙoƙarin danne damuwar da yake ciki, amma kallon hotunan Hafsa da duba previous chats ɗinsu ya zame masa kamar ibada, idan bai yi ba baya jin daɗi, gaba ɗaya ya rame sosai.
Gidansa da yake ta ɗoki yana ginawa, yana ƙaƙale gaba ɗaya ya dakatar da ginin, dan ji yake idan ba Hafsa ba babua wadda zai iya sanyawa a cikin wannan gidan.
Bayan sallar la'asar yaga missed video call É—in Fadila.
Kiranta yayi dan yaji dalilin kiran nasa da take yi. Ya ci sa'a tana Online, ta É—aga wayar.
ÆŠan zuba masa ido tayi, cikin damuwa ta ce "Yaya Khalil baka da lafiya ne?"
"Lafiyata ƙalau menene?"
Ta É—an rausayar da kai ta ce "Yaya Khalil me nayi maka ne?"
"Kamar yaya?"
"Naga idan nayi maka magana sai ka ga dama kake amsawa, ko a waya baka kirana"
Ya ɗan ɓata fuska ya ce "Ayyuka ne suka yi mini yawa sosai"
"Na sani, ba wani aiki da yayi maka yawa, ka rame fiye da yadda kake tunani, duk wanda ya ganka ya san kana cikin damuwa ne. Dama na kira in gaya maka ne, Mummy tana nan tana fushi da kai, wai kana gaba da ita, Hajiya Salma ta bata shawarar ta aura maka wata yarinyar, tun da haka ka zaɓa gara ka san abin yi"
Zaro ido yayi ya ce "Ban gane ba, kamar yaya a aura mini wata yarinyar, idan bana sonta fa?x"
"Nima ban sani ba, haka kawai Mummy ta gaya mini, gara ka dinga kiran Mummy kana gaisheta"
"Fadila ya ake so in yi da rayuwata? Yaya za ayi in gaba da Mummy, duk lokacin da na kirata sai ta mini faɗa ta ƙare mini zagi a kan Hafsa, ita kanta yarinyar mutuncina ya zube a idonta, ace uwata taje ta sameta ta ci mutuncinta wai ta rabu da ni, wanene ni ɗin? Kuma yanzu haka bama tare, yarinyar ce ta ƙarfafa mink gwiwa a kan mu rabu da juna, tun da Mummy bata so, amma gaskiya idan Mummy ta aura mini wata daban wadda bana so bata kyauta mini ba"
Fadila ta ce "To ni dai ban gaya maka dan ka tashi hankalinka ba, na gaya maka ne kawai dan ka san abin da kake ciki"
Ya jinjina kai tare da fesar iska daga bakinsa ya ce "Shikenan, na gode sosai" yayi disconnecting ɗin kiran, ya cillar da wayar gefe, ya dinga murza goshinsa, yana mamakin yadda Mummy ke biye shawarar ƙawayenta fiye da komai.
Sai da Amina ta idar da sallar azahar, sannan ta turawa Daddy saƙo "Can i call you?"
Kusan mintuna goma da tura masa saƙon, Daddy ya kirata.
Wani nishaÉ—i ne ya ratsa Amina, ganin kiran Daddy ta É—aga wayar tare da faÉ—in "Ina wuni?"
"Kin dawo kenan?"