Sashe 36
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kuma dan baki da hankali wannan sun miki kam da waɗancan ne? Ƙawayena ne wannan tun na ƙuruciya saboda baki da mutunci sai ki wulaƙanta su? Ke nifa na gaji da wannan iskancin naki, bari shi me gidan ya dawo, ki koma ƙauye ki cigaba da shan baƙar kuka. Kin zo birni kin sha miya zaki miƙe ƙafa kina mini iskanci" ta sunkuyar da kai tayi shiru ba ta ce uffan ba, suka haɗu su uku suka mata wankin babban bargo.
Tun abin na damun Amina, ta fara daina jin komai, ta fuskanci kamar ɗabi'a ce ta masu kuɗi, wulaƙanta wanda suke ƙarƙashin su, suka ƙare mata zagi da cin mutunci tsaf, sannan suka sallameta. Harabar gidan ta koma, tayi zamanta ya yin da Baba yake bakin gate yana aikinsa.
Abdul da Khalil ne zaune a É—akin Abdul, Khalil ya zuba uban tagumi.
Abdul ya ce "Wai kai Khalil meye haka ne? Sai ka sanya damuwa a ranka ka kasa sukuni?".
"Abdul ba zaka gane bane, ni kaina ban taɓa zaton abubuwa zasu cakuɗe mini haka ba. Baka san yadda nake jin yarinyar nan a raina ba, amma naga tana da taurin kai, babu alamar zan sameta na karaya Abdul".
"Haba Khalil, kar ka karaya, ka san meye matsalarka? Garaje da gaggawa idan kabi komai a sannu zai zo maka a sauƙaƙe, yanzu kana jin abin da nake ji game da ƙanwarka ko? Hmm haka al'amarin so yake, na san babban yaro kamarka da mata ke rushing a kansa, abin mamaki ne ace ya maƙalewa 'yar talakawa kamar wannan, amma haka sha'anin so yake. A yanayin Hafsa kamar akwai wani ɓoyayyen abu da yake damunta a zuciyarta, dan haka domin shawo kanta, sai ka rage shishige mata, da cigaba da nuna mata soyayya, ka danne son kawai ka nemi ku saba da ita. Ka dinga kyautata mata da kulawa ka fara gano meye matsalarta kan ka cigaba da nuna mata soyayya".
Khalil ya É—an yi shiru sannn ya ce "Kana ganin hakan mafita ne?.
"Ita ce babbar mafita, tunda soyayyar ce ba ta so, to ka bar shi a friendship ka gama fuskantar ta tukuna".
"Shikenan, zan jarraba hakan, insha Allah gobe in Allah ya kaimu zan koma wurin aiki, zan jarraba shawarar taka".
"Wai da gaske ba zaka gida ba?"
"Abdul idan naje Mummy tuhumata za tayi a kan dalilin dawowata, ba sai naje ba, sai nan da kamar 3weeks zan kuma dawowa insha Allah"
"To shikenan, Allah ya kaimu sannan ya daidaita ku".
Yau sai shida na yamma suka kammala jarrabawar yau, kanta har wani juyawa yake yi saboda ta gaji yau sosai da sosai, da ƙyar take iya ɗaga ƙafafuwanta, saboda zaman ajin. Jarrabawowin yau Alhamdilillah tayi abin Arziƙi da kanta, dan tayi karatu sosai da sosai.
"Hmmm Madam, glucose yayi ƙasa ne naga kina tafiya da ƙyar?" Cak ta tsaya tana ɗan sauke numfashi, ta waiwayo ta sauke masa gajiyayyun idanuwanta da suka ɗan yi ja saboda gajiya.
"Yau ko nemana ba ayi, tun shekaranjiya ko kallon in da nake ba balle a harareni. Amma ina fatan kin gama komai dai ko?".
"Ban gama ba, jira nake kazo ka ƙarasa mini"
Sauke facemask É—insa ya yi ya ce "Me kika ce?".
"Ban sani ba" ta faÉ—a ba tare da ta kalleshi ba.
"Kalleni ki faÉ—a mana idan ba tsoro ba" É—agowa tayi ta kalli Yazeed, sai dai tayi saurin janye idonta daga nasa.
"Dan Allah ka rabu dani".
"Muje in rakaki wurin motar".
"Ina da ƙafa ai" ta faɗa tana cigaba da tafiya sannu a hankali.
"Ai ƙafar taki ce kamar ta gaji, da ƙyar kike tafiya, ko in ɗauke ki in kai ki motar ne?" Ɗagowa tayi ta kalleshi ta mayar da hankali a kan tafiyarta.
Yusra ce ta tunkaro in da suke tana murmushi, ta kalli Yazeed ta ce "Patient É—inmu, kai ne ka warware haka?"
Yazeed ya yi murmushi ya ce "Alhamdilillah, jiki ya ware".
"Haka ake fata dama, madam zuwa nayi mu tafi gida tare, yau ba mota a hannuna".
Fadila ta ce "Gaskiya a gajiye nake gida zan tafi sai dai in ajiye ki a hanya".
"Aikuwa baki isa ba, nima a gajiyen nake, ka sa baki ta kaini gida mana" Yusra tayi maganar tana kallon Yazeed.
Yazeed ya ce "Wane ni, ku gaida gida".
"A'a ka tsaya, saita É—aukemu wallahi, muje ko rage maka hanya muyi".
"A'a ba zan hau ba, Allah ya kai ku lafiya".
Yusra ta ce "Dan Allah ka zo muje, ko a hanya mu ajiye ka".
"A'a ni ba zan hau ba, wa zai hau motarta, ko tuƙinma bata iya ba, ta watsar da mu a hanya, ku sauka lafiya" kallon Yazeed tayi, tama rasa me za ta ce masa.
Fadila na ƙoƙarin kunna mota ne, Yusra ta ce "Wallahi Fadila kun dace da gayen nan, anya ba sonki yake ba?"
"Amma baki da hankali ko? Ke na miki kalar sa, karki ɓata mini rai".
"Wallahi Fadila ni tausayi yake bani gaba É—ayansa, Wallahi kamar sonki yake"
Fadila ta haÉ—e rai ta ce "Yusra bana so, karki sake haÉ—ani da shi"
"Ai shikenan, bari mu zuba ido mu sha kallo".
Wani irin horn Fadila take yi a ƙofar gidan tamkar zata daki gini idan ba a buɗe ba, Baba kuma ya shiga banɗaki a lokacin, ba tare da ya kammala abin da yake ba, ya fito bagatatan ya buɗe mata gate ɗin, ai ko kashe motar ba tayi ba, ta fito ta hau Baba da bala'i ta in da ta shiga bata nan take fita ba, ya risuna ya dinga bata haƙuri.
Haka ta nufi cikin gida fuuu kamar guguwa, ba ta tsaya ta saurari Mummy tana da baƙi ba ta hau bala'i a falon "Gaskiya Mummy ku sallami wannan tsohon, haba ai ko aikin gwamnati ne ha kai yayi retire mutum sai bai san aikinsa ba, ya bar mutane a waje ina ta faman horn sai kace wani kurma, gaskiya na gaji a sallame shi. Ga securites nan na kamfani Daddy ya ɗauko amma ya dage a kan wannan baƙauyen, mara kuzari, saura kaɗan in zage shi yau". Jikin Amina ne ya ɗau rawa, ta kalli Fadila ta ce "Baban nawa zaki zaga?".
DOMIN GYARA SHARHI KO SHAWARA
08081012143
READ THE CHAPTER 16 OF GABA DA GABANTA AT AREWABOOKS
https://arewabooks.com/chapter?id=638b441e942c7e82ce7bfb71
GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143
P16
"Eh, shi zan zaga ko akwai abin da zaki iya yi a kai?" Fadila tayi maganar cikin isa da iko.
Maganganun Baba ne suka dawowa Amina a cikin kunnuwanta, tabbas idan ta ɗau mataki, ta san dole ta koma ƙauye, kuma babu abin da zai hana aurenta da Jarmai, jikinta na rawa hawaye na zuba daga idanunta, ta juya ta koma jikinta a sanyaye, Allah kar nuna mini ranar da za'a zagi Baba a gabana, ba zan iya jurewa ba.
Fadila ba ta kalli baƙin Mummy ba, ta wuce ɗakinta tana cigaba da huci kamar wata mesa.
Hajiya Turai ta ce "Wai dama 'yar mai gadinku ce?"
Mummy ta ce "Eh, 'yar sa ce".
"Lallai ne, ai gara da Fadila tayi mata hakan, yaran nan idan ana saurara musu miƙe ƙafa suke yi su yi ta iskanci kamar a gidan ubansu"
Hajiya Zainab ta ce "Wallahi kuwa, ai Fadilan ce dai-dai da su".
Fadila kuwa a gajiye ta ƙarasa ɗakinta, ta jefar da mayafinta, ta tuɓe doguwar rigar jikinta, ta shiga cikin banɗaki, ta haɗa ruwa mai ɗumi tayi wanka, ta yo alwala ta fito, sallar magariba ta gabatar ta idar, sannan ta shirya kanta cikin riga da skirt, na English wears ta fito.
Sai a wannan karon sannan ta gaida baƙin Mummy, ta wuce kitchen.
Amina ta gani a tsaye idanunta sun yi jawur, kamar ta kwana ta wuni tana kuka.
"What do you cook for dinner?" Fadila ta tambaya cikin ko in kula.
Zuciyar Amina na tafasa, tamkar ta ce mata ubanki na dafa, amma ta dann ta ce "Tuwon semovita".
"Ban ci Abincin rana ba, dan haka ba zan ci tuwo ba, ki dafa mini cous cous vagetable cou cous da irish, ki hanzarta kuma" tana gama maganar ta jiya ta fice.
Muciya Amina ta rarumo, ta É—aga sama kamar ta bi bayan Fadila, ta sauke mata wannan dogayen kafaÉ—un nata, masu kama da dirakun firamaren garinsu.
 Amina tana kuka tana yiwa Hajiya Zainab Allah ya isa, ta yiwa Fadila girkin nan ta kai mata, ta koma ɗakinta.
"Hafsa ni dai ina tsoron sake komawarki wurin sana'ar nan, bana son wannan yaron ya zo ya kuma É—aga mana hankali".
"Mama idan ba wannan sana'ar ba wacce za muyi? Idan a gida nace zan cigaba da saida awarar nan, ya zama mu uku muke awara a layin nan fa, kusan duk wata sana'a da zamu yi, a na yinta a cikin unguwar nan, zama haka ba zai yiwu ba Mama".
"Haka ne, amma dama can sana'ar nan ba sonta nake ba, bana ƙaunar zaman titin nan da kike yi, ni ban san ma yadda aka yi yaron nan ya san inda kike sana'a ba".
"Mama ba zai ƙara zuwa ba insha Allah, kuma kinga ai Khalil ya sa an mana tsakani da shi".
Mama ta ce "Ni kuwa naga kwana biyu ko kiranki ba ya yi a waya, ko wani abun ki ka yi masa ne?"