Sashe 28
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdul ya É—an murmusa ya ce "To ai kaine mutumina, kai ma izzar ce da kai da faÉ—an tsiya, mata kuma ba a musu haka, mussaman idan ana son farautar zuciyarsu. Idan har kana son Yarinyar nan ka ajiye taka Izzar, ka bita a yadda ta ke"
"Abdallah wai wace irin izza, bani da wata izza Wallahi".
"Haka dai kake gani, yanzun nan kana mini describing É—in ta, amma kana cewa gata dai ba kowa ba, meye wannan idan ba izza ba, koma dai menene ai sonta ka ke"
"Au dan na faÉ—i haka izza ne?"
Abdul ya ce "Khalil kenan, Amma tsakaninka da Allah, son Aure kake mata, ko dai wani abu daban?".
"Haba Abdullahi, ka taɓa ganina da harkar banza ne?"
"Ba haka nake nufi ba, akwai so wanda kake wa mace dan ka aureta, wata kuma burgeka take kana son ka mu'amalance ta kamar ƙanwarka, wata kuma tausayinta ka ke ji kawai"
"Nifa da gaske nake, Aurenta zan yi tayi mini".
Abdul ya ce "Ina muku fatan Alkhairi, Allah ya tabbatar da alkhairi" a ransa kuwa yana jinjina yadda iyayen Khalil zasu amince ya auri mai 'yar talakawa mai suyar awara a bakin hanya.
Fadila shirye shiryen fara exams ya yi nisa, tana ta fama da karatunta, sai dai girman kai ya hana ta koyi abin da ba ta iya ba, a ganinta hakan tamkar ƙasƙanci ne a gareta.
Tana zaune ita kaɗai a seat ɗin baya, ta ƙurawa littafi ido, Yazeed gabansa na faɗuwa ya tunkari in da take a zaune, sallama ya yi mata, ta amsa a ciki ba tare da ta kalleshi ba.
"هل يمكنني الجلوس"
(Can i seat)
Kallonsa ta yi, ta ɗauke kanta, Yazeed ya zauna a kusa da ita, ya kalli littafin hannunta ya ce "Sannu da ƙoƙari".
"Dan Allah malam kar ka zo ka isheni karatu zan yi".
Yazeed ya ce "Nima karatun zan yi ai" ya ciro jottersa ya ce "Ban miki godiya ba, naga kin rubuta mini duk abubuwan da aka yi bana nan, Na gode sosai ubangiji Allah ya ƙara basira. Amma dan Allah ina son ki ɗan yi mini bayani, akwai abin da ban gane ba".
"Baka iya karatu bane da sai na maka bayani ko yaya?".
"Karanta rubutu a rubuce ba shi ne ba, ka gane me ake nufi ko da ba ka iya karantawa ba shi ne mafi mahimmanci".
"Dan Allah ka tashi ka bani wuri".
"Ok, zan tashi amma bari in nuna miki wani abu"
Ya É—auki littafin gabanta ya kalla sannan ya ce "Ba wannan topic É—in yakamata ki duba ba, idan har ki ka gane bayanin wannan topic É—in shikenan, malamin ba zai tsawwala tambayoyi a nan ba". Ya buÉ—o wani topic É—in ya ce a "A wannan yakamata ki fi mayar da hankali"
Yamutsa fuska tayi, tare da tura baki kamar zata yi kuka.
Yazeed ya ce "Ya dai?".
"Ni fa na gaji da karatun nan, kaina kamar zai fashe bana gane komai ma"
"Kece kika wahalar da kan ki, ki ke karanta abin da ba shikenan ba, idan Malami yana bayani, ki dinga rubuta abin da kike fahimta a game da darasin, idan kika koma gida sai ki faÉ—aÉ—a bincike, sai ki haÉ—a ki tsinci abin da zaki tsinta ki haÉ—a, amma idan ki ka ce handout zaki haddace baki fuskanci darasin ba, zaki iya samun idea escape ma a wurin exams. Dan haka idan ana lectures a daina yiwa malamai tsiwa ana korar mutum daga aji, wani abin idan har aka yi baka nan ya riga ya wuceka kenan"
Murguɗa masa baki tayi, jin statement ɗin sa na ƙarshe, tare da cewa "Ina ruwanka da an koreni, bana son sa ido, ban littafina".
"Zan baki littafinki, amma kan in baki duba wannan, sai in ƙara yi miki bayani, zaki ga yafi sauƙi a kan wanda kike yi" kallon rubutun nasa tayi, har da wani larabci a ciki.
"Kaga nifa bana gane larabci" tai maganar tana wani basarwa.
Aikuwa Yazeed kamar an kunna fanfo, ya dinga zuba yana mata bayani tana saurarensa, babban abinda ya sanya shi farinciki, bai wuce saurarensa da take yi ba.
Sai da ya gama, tayi ajiyar zuciya, dan idan ta ce ba ta gane me yayi mata bayani ba tayi ƙarya, dan duk abin nan da ake, haddacewa kawai take ba ganewa ta yi ba.
"Na fahimta, Na gode sosai".
"Never mind ranki ya daÉ—e, bari inje masallaci"
Ta jinjina masa kai, bayan tafiyarsa, ta É—au jakarta ita ma tayi waje ta nufi gida.
Khalil an fara yi masa way da ga wurin aiki, a kan lallai ana buƙatar sa, ji yake kamar ya ce Ya fasa komawa, saboda yadda yake jin Hafsa a zuciyarsa, ji yake kamar ba zai iya tafiya ya daɗe bai ganta ba.
Ana gobe zai koma, ya je gidansu Abdul ya yi masa sallama, suka sake tattaunawa a kan yadda Khalil zai ɓullowa Hafsa, suka yi sallama Khalil ya tafi wurinta.
Wannan karon ba Mutane sosai a wurin nata, dan da alama ta kusa tashi ne ma.
Yana yin sallama a wurin, ta haÉ—e rai tare da amsawa ta É—auke kai.
"Ina wuni tun da ke baki iya gaisuwa ba".
"To ai nima bance ka gaishe ni ba".
Khalil ya numfasa ya ce "shikenan, ba faÉ—a na zo muyi ba, sallama na zo muyi zan koma wurin aiki insha Allah".
Hafsa ta ce "To ni ina ruwana da zaka tafi?".
"Amma dai at least ai kya yi mini A dawo lafiya ko?".
Hafsa ta ce "To Allah ya kiyaye hanya"
"Ameen Hafsat, ya jikin Mamana?"
"Wace maman taka?".
"Mamanmu mana, mamanki ai mamana ce ko abin ba kara ne?".
"Jikin Mama da sauƙi".
Khalil ya ce "Masha Allah, Alhamdilillah, amma sauƙi na bahaushe ko kuma ta warke?"
"Da sauƙi sosai" Hafsa ta bashi amsa a lokacin da hankalinta ya koma kan wata coustomer.
Khalil ya sa hannu ya É—au wayarta mai madannai, wadda ta sha jiki da yawa, lambarsa ya sa a wayar, ya kira lambarta ta fito a tasa, ya ajiye mata wayar.
Ya yi gyaran murya, wanda ya sanya ta waiwayo. Ya ce "Ko zamu je in duba Maman ne?"
Ta É—an waro idanunta ta ce "Saboda me? Ince ga wa ya zo dubata?".
"Coustomer É—inki, mai takura miki, kuma wanda yake fatan ya Aureki. Duk da ban gaya miki dalilin da ya sanya na nace ina ta bibiyarki ba, Hafsa ina sonki ne, kuma Wallahi da gaske nake, ni Aurenki zan yi, ina kishin ganinki a wurin nan kina wannan aikin"
Ai tuni ɗan annurin yau da ya gani a fuskarta, saboda zancen Mama da ya yi, ya gushe daga fuskarta, ta haɗe rai sosai da sosai tayi shiru taƙi magana.
"Hafsa maganata ce ta ɓata miki rai?"
"Dan Allah ka rabu dani, kar ka sake zuwa in da nake, ni ban fito sana'ata dan wani ya tausaya mini ba, ba ruwanka da sana'ata, kuma kar ka sake zuwa wurin nan, idan ba haka ba zan iya dena zuwa ni, in bar maka wurin".
A É—an rikice Khalil ya ce "Amma Hafsa...
"Malam bana son jin wata magana, ka ƙyaleni" tayi maganar a hasale.
Haka Khalil ya tashi ya baro wurinta, jiki a sanyaye, yana mamakin halayen Hafsa, wace irin Yarinya ce haka, dan ance ana sonki ki birkice ki kama masifa?.
A sanyaye haka ya koma gida, yana tunanin mafita, amma dole ya san abin yi, da zuciyarsa ba zata iya haƙuri da Yarinyar nan ba.
Da ya koma gida, a Falo ya tarar da Mummy, da Fadila suna kallo, suna hira, Amina nata gyara dining, in da suka ci Abinci suka bar wurin.
Fadila na ta bawa Mummy labarin Yazeed, yadda ya iya larabci amma bai iya turanci ba hadda cewa "Mummy kin gan shi kuwa, kayan da yake sakawa? Amma sai ƙwaƙwalwa kuma baya iya turanci a baki".
Mummy ta taɓe baki ta ce "Wasu lokutan dama haka ne, yaran nan marasa galihu da suke tashi a wahala, suna da ƙoƙari, sai dai na banza ne, dan ko sun gama karatun ba aiki suke samu ba, sai da su zama masinja a manyan ofisoshi".
Amina da ke aiki a ranta ta ce "Ji mata da mugun baki, wato É—an talaka ba zai huta ba, iyayenmu su yi muku bauta, muma muyi muku da 'ya'yanku, insha Allah ta Allah ba taku ba'
"Khalil lafiyarka kuwa, ka zo ka zaun kayi shiru haka?".
"Mummy bakomai".
"Ya fa bakomai? Ga yanayinka duk ya canza".
"Mummy wata Yarinya ce" sai kuma yayi shiru.
"Mai Yarinyar ta yi?" Mummy ta tambaya cike da zaƙuwar son jin ƙarshen zancen.
"Mummy Bakomai" ya faÉ—a cikin damuwa.
"A'a ka fara magana kace bakomai, ko dai ka fara Soyayya ne?".
"Eh to, Yarinyar ce dai haryanzu ban samu shawo kanta ba".
Mummy tayi murmushi ta ce "Ikon Allah, dama akwai lokacin da zaka samu macen da tayi maka, sarkin kushe kushe? A ina take kuma 'yar waye? Ina fatan ba gidan tsiya zaka je ka É—auko mana sirika ba?"
Gaban Khalil ne ya faɗi, be bawa Mummy amsa ba ya miƙe, ya ce "Idan komai ya daidaita za muyi maganar".
Fadila kuwa wani takaici ne ya mamayeta, da tausayin Yusra da take ji, gaba É—aya haushin Khalil ya kamata, ta tashi ta bar falon ita ma.
Haka Khalil ya kwana yana tunanin dalilin da ya sanya, Hafsa ta canza fuska dan kawai ya ce yana sonta, shi dai ya san ba muni ne da shi ba, dan ƙarewa ma mata ne suke rushing a kansa, bai taɓa tunanin Soyayya zata iya kai shi wurin mai awara ba, dan da shi a yadda yake tsara rayuwarsa, macen da ta kammala degree ma yake so, very matured lady, haka yayi bacci rabi da rabi.
Washegari tun sassafe, Fadila da Mummy zasu je unguwa, dan haka suka raka Khalil airport, su kuma suka wuce in da zasu.
Hajara ma shiri tayi, ta tafi kasuwa saboda akwai kayan da babu, mai zuwa kasuwar sayowar kuma Hajiya Zainab ta koreshi.