Sashe 60
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yauwa Abdul, ashe ka gane, wallahi yana daga cikin dalilan da ya sanya nake son taimakonta, Hafsa da gidan Aure ko makaranta ta dace, ba da zaman titi ba, Abdul na tsara irin rayuwar da zan yi da ita, yadda ta sha wahala a baya duk da farkon rayuwarta 'yar gata ce, amma ina son in ɗauke mata komai, yadda ba zata taɓa kukan wani abu ta rasa ba, sai abin da bani da damar sama mata, Abdul ba zaka gane ba, that girl deserve a shoulder to rest, akwai matsala idan Hafsa ta auri mutumin da bai San mecece ƙaddara ba, kuma bai san kimar mace ba, ya zan yi Mummy ta gane ne?"
Abdul ya jinjina kai, So kenan, mai sa mutum ya duƙa, ya susuce duk izzarsa da kuma taƙamarsa' A yadda Khalil yake ɗan gayu matashi mai ji da kuɗi, idan aka ce maka zai ɗauko mace kamar Hafsa ya ce yana so zaka ƙaryata, amma ya zauna sai sambatu yake yi.
Abdul ya ce "Khalil, naji duk bayananka, kuma na fuskance ka, zan tayaka da Addua, sannan zan cigaba da tunanin menene mafita ga al'amarin nan" da ƙyar Abdul ya ɗan rarrashi Khalil, ya rage damuwar da yake ciki.
Amina bayan barinta falo, da ta koma kitchen kuwa saida tayi kuka sosai, ita gaba ɗaya gorin nan da ake yi mata da kuma takura ya isheta, shikenan dan tana karatu wani ba zai kulata ba, kuma ita Bilal ba cewa yayi yana sonta ba, 'yan ajinsu suyi ta bada labarin samarinsu, amma ita sai samarinta na ƙauye, gashi Alhaji Ahmad yayi mata gori kuma ya hanata tsayawa da saurayi, ta zauna a kitchen tana ta kukanta.
Hajara ta shiga kitchen É—in ta tarar da ita, a zaune tana share hawaye.
"Amina kukan me kike kuma?"
"Ba komai" Amina ta faɗa a daƙile.
"Kawai jin daÉ—i ne ya sanya kika zauna kina kuka?"
"Nace miki bakomai, ki ƙyaleni" Amina ta faɗa a ƙufule, dan sa idon Hajara yayi yawa, komai ta gani so take sai taji ƙwaƙwaf, yadda aka fara da yadda za a ƙare.
Ta miƙe ta cigaba da aikin tana yi tana kuka, kamar ƙaramar yarinya.
Tun daga wannan ranar, Amina ba ta yadda ko hanya ta haɗata da Alhaji Ahmad, ganin idan ta gaishe shi ya daina amsawa, sai dai ya tsaya ta ƙureta da ido, dan haka gaisuwarma ta daina gaisheshi. Idan suka haɗu sai ta basar ta wuce abinta.
Da magariba Khalil ya takurawa Abdul, ya shirya suka tafi gidansu Hafsa, kasancewar ta san da zuwansu, ya kirata ya sanar mata, ya sanya ta shirya har da yi musu girki, ta saka ɗaya daga cikin kayan da ya kawo mata, a ɗinke, wani less mai matuƙar kyau da ya kawo mata shi a ɗinke.
Tun da ta fito hannunta riƙe da babbar darduma, Khalil yake kallonta, tayi masa kyau fiye da kullum, ga wani irin tausayinta da ya ƙara mamaye masa zuciya.
Tana Zuwa tayi murmushi ta ce "Yaya Abdul, kwana biyu ka ɓuya da yawa"
Abdul yayi murmushi ya ce "Ai tunda Allah yasa ku ka daidaita, bai kuma nemana in masa rakiya ba, shiyasa ba kya gani na"
"Yaushe zan nemeka, ka zo ka samana ido" Khalil ya faÉ—a yana sake mayar da hankalinsa a kan Hafsa.
Ta shimfiÉ—a musu sallaya, suka zauna ita kuma ta zauna daga gefe.
"Babyna kina lafiya, ya kasuwa?"
"Alhamdilillah, ya gida ya su Mummy?"
"Suna lafiya ƙalau, kin yi mini kyau fiye da kullum, kamar in sace ki in gudu, Abdul ko zagawa zamuyi mu tataro mutane a ɗaura mana auren nan ne kawai mu huta?"
Abdul a ransa ya ce "Da ka ci ubanka la'ada waje a wurin babarku'
Amma a zahiri ya ce "Eh to idan ƙanwar tawa ta yadda, sai muje neman mutane a haɗu a ɗaura ai"
Hafsa sai sunkuyar da kai take tana jin kunya, Khalil ya leƙa fuskarta ya ce "Babyna, ki gaya masa kin amince, mun Matsu mu mallaki junanmu, ko yanzu a shirye muke a ɗaura"
Ƙunshe fuska Hafsa tayi, tana jin wata irin kunya tana ratsata, gaba ɗaya shi Khalil baya jin kunya.
"Ya kika yi shiru, in dai Abdul ne ki daina jin kunyarsa, a É—aura mana aure next year by now insha Allah idan baki haihu ba to muna nan muna rainon Babynmu a cikinki"
Miƙewa Abdul yayi ya ce "Khalil wannan fitsarar ta ka, ba ita ba ni kaina kunyar kake bani, bari in koma mota In jiraka" Dariya Khalil yayi, Abdul ya nufi ƙarshen layi in da suka bar motarsu.
Khalil ya matsa ya sake mayar da hankalinsa kan Hafsa ya ce "Amaryata, ɗago mana in ƙare miki kallo, baki ga yadda kika mini kyau ba"
A ɗan shagwaɓe ta ce "Wai sai ka ta bani kunya a gaban mutane"
"Suwaye mutanen, Abdul É—in? Ni banga wani abin Kunya ba"
"Ni na gani ai, amma kayi mini kyau sosai"
"Da gaske?"
Ta jinjina masa kai, yayi murmushi ya ce "Kyau sai ma ranar bikinmu yarinya"
Tayi shiru ba tace komai ba. "Babyna" ya faɗa murya ƙasa-ƙasa.
Ta É—an É—ago ta kalleshi.
"Kiyi magana mana"
"Yau ba 'yan maganar, na rasa me zance"
"You must say something, bari muyi Auren zobe, wata azurfa na saya mana tun last month, sai wannan watan Allah ya sa suka iso"
Ya ciro wata 'yar ƙaramar box blue black, ya buɗe sai ga wasu zobuna masu matuƙar kyau a ciki.
Ya É—auko na matan, ya kamo hannun Hafsa, ya kama yatsanta ya saka mata zoben. Da É—an sauri ta janye hannun nata, tana jujjuya zoben tana murmushi.
Ya miƙa mata masa hannun, ya ce "Nima sa mini"
Ya miƙo mata yatsansa, cikin rashin sabo, ta zira masa zoben. Hannunta ya kamo cikin nasa, ya ciro wayarsa, ya ɗauki hoton hannunsa da nata sanye da zobunan.
Daga nan ya zarce yana ɗaukarta hoto, hannunta da ke cikin nasa ba ƙaramin takurata, yayi ba amma ta kasa cire hannunta daga nasa, yayi ta musu hoto. Ba tare da ya cire hannunsa a nata ba ya ce "Hafsa zaki aureni?"
"Meyasa kake yawan maimaita tambayar nan? I will marry you in sha Allah My" tayi maganar tana masa murmushi.
"Murmushin nan naki yana killing É—ina, ki ce kina sona?"
"Ina sonka sosai, duk ka koya mini rashin kunya"
"Kina da kunya sosai, amma naji daÉ—i da kika rageta sosai a kaina, ina son matata ta zama mai kula dani sosai, ina sonki Babyna, ki cigaba da yi mana addua, Allah ya tabattar da Aurenmu, ya bamu ikon cin duk wata jarrabwa da ka iya taso mana"
"Ina yi mana"
"Yauwa Habibty, zuba mini Abincin in ci, kuma a bakina zaki bani"
Ta noƙe kafaɗarta ta ce "A'a zan dai zuba maka, sai bayan nikah zan dinga baka a baki"
Haka ta zuba masa Abincin nan, yana ci yana zuba santi yana koÉ—ata.
Ya kammala ci, ya ce "dama wancan ba ci zai yi ba, ya ce lemo kawai zai sha, na gode sosai matata in sha Allah, bari in tafi"
Hafsa ta marairaice ta ce. "Ni kar ka tafi yanzu, ban gaji da ganinka ba"
"Allah sarki sweetheart, ni kai na bana son tafiya, ban gaji da ganinki ba"
"Shikenan ma yi video call, kar kayi dare muje in raka ka mota"
Khalil ya ce "A'a, bana son ki wahala, ki ce ina gaida Mamana"
"Ni baka taɓa haɗani da Mummy na gaisheta ba"
ÆŠan dam yayi, sai kuma ya ce "Karki damu zan haÉ—aku"
Yana nan tsaye, sai da ta shiga gida, sannan ya nufi in da motarsu take. Jiki a sanyaye ya shiga motar ya zauna.
Abdul ya kalleshi ya ce "Baban soyayya, ka shanyani kana can kana soyewa, Allah yasa baka ƙone ba"
Khalil ya Shafi gemunsa ya ce "Kamar kar in taho, ina son yarinyar nan"
"Nima na ga alama, zan taya ku da Addua in sha Allah".
Da haka Khalil ya ja motar, ya tafi kai Abdul gida.
Washegari Monday, su Amina zasu koma makaranta, ta yi gugar uniform ɗinta, ta wanke jaka da takalminta, ta shirya litattafanta, tana ta kallon jakarta tana jin shauƙi da farincikin komawa makaranta, ta dinga tuna rayuwar da tayi a ƙauye, yadda ta dinga makaranta a wahale, wataran sai dai ta saci hanya ta je makaranta, idan ta dawo ta ci duka, amma nan duk da tarin ƙalubalen da take fuskanta, akwai Abinci, akwai wurin kwana mai kyau, gashi duk wani aiki da ake sakata, ba a sakata lokacin makarantarta.
"Kai Allah ya saka maka da alkhairi" ta faɗa a fili, sai kuma ta tuna da abin da Alhaji Ahmad yayi mata, sai ta tura baki tana ƙunƙuni kamar tana gabansa, ta tashi ta tafi wurin Baba.
Ganin fara'a a fuskar Amina ya sanya Baba yin murmushi ya ce "Uwata, murmushin me kike haka ne?"
"Baba ka san gobe in Allah ya kaimu zamu koma makaranta, shine nake ta jin daÉ—i, na wanke uniform É—ina na goge, shi ne nake jin daÉ—i"
Baba ya É—an yi ajiyar zuciya, ya ce ina zuwa.
Ya tashi ya shiga ɗakinsa ya fito da ƙatuwar leda, ya miƙawa Amina ya ce "Gashi in ji Alhaji Ahmad, jaka ce da takalmi ya ce a baki, kuma wai idan kinje makaranta ki je ki karɓa sabon kayan makaranta, Uwata ban taɓa zaton Alhaji Ahmad zai kyautata miki haka ba, bani da bakin yi masa godiya, sai fatan ya gama da duniya lafiya, Uwata ki same shi ki durƙusa har ƙasa ki yi masa godiya Amina"
Maimakon Amina tayi murna, sai ta É—an tura baki, dan ji tayi ma kamar ta ce bata so.
"Uwata ya naga kin haÉ—e rai"
"Ba komai Baba murna nake yi, Allah ya saka masa da alkhairi, na gode sosai, amma ai ni takalmi na da jakata da Uniform É—ina suna da kyau"
"Ba sai ki adana abinki ba, kuma ya mini ƙorafin idan ya baki abu ba kya karɓa, wannan kuma kin yi daidai, ki cigaba da kula da mutuncinki"
"To, In sha Allah Baba Na gode sosai"